AMRAH

AMRAH PART 09

by @hussainyusuf


AMRAH 

<<PART 09>>

Maigari yana zaune tare da fadawansa, Malam Buba yana durƙushe a gabansu, ya sunkuyar da kansa ƙasa, hawaye na zuba daga idanunsa. Mutanen gari ne suka zagaye su, kowa sai faɗi yake a yi wa Malam Buba hukunci.

Sai da Maigari ya ɗaga hannu sannan kowa ya yi shiru. Ya dubi mutanen ƙauyen ya ce, "Yau ɗin nan za mu yankewa Malam Buba hukunci saboda taurin kan da ya nuna a lokacin da za a tafi da hatsabibiyar ƴarsa. Don haka jama'a, muna neman shawararku. Wanne hukunci ne ya fi dacewa da Malam Buba?"

Nan fa wajen ya kaure da hayaniya. Wasu na cewa a yi masa bulala, wasu na cewa a kashe shi. Kowa dai da abin da yake faɗa a wajen. Da Maigari ya ga hayaniyar ta yi yawa, sai ya ɗaga hannu kowa ya yi shiru. Sannan ya yi gyaran murya ya ce, "Za mu yi wa Malam Buba bulala ɗari da hamsin yanzun nan. Hakan ya yi muku?" Cikin haɗin baki mutane suka amsa da, "Eh, hakan ya yi!".

Nan take Maigari ya umarci wani ƙaton mutum mai suna Gargaji ya zo ya yi wa Malam Buba bulala. Malam Buba ya kwanta, Gargaji ya rinƙa tsula masa bulala, ba tare da sassautawa ba, har sai da ya yi masa bulala ɗari da hamsin cif.

Kasa tashi Malam Buba ya yi. Sai Maigari ne ya umarci wasu matasa suka ɗauke shi suka kai shi gida, rai a hannun Allah. Inna Ladidi ta rinƙa kuka, tana gasa masa jikinsa da ruwan ɗumi.

Bayan an kai Malam Buba gida, Maigari ya ce da yamma za a haɗa gagarumin shagali a garin, a ci a sha, saboda murnar rabuwa da hatsabibiya Amrah.

Maigari yana rufe bakinsa, sai aka hango Shamaki yana cin gudu kamar zai tashi sama, jikinsa duk ya ɓaci da jini. Nan fa hankalin kowa ya koma kansa, ana jira ya ƙaraso a ji mene ne ya biyo shi haka yake cin gudu.

Shamaki yana isowa, ko gaishe da Maigari bai yi ba. Ya ce, "Ranka ya daɗe, kowa ya yi ta kansa yanzun nan! Amrah tana hanyar zuwa garin nan, kuma ta hallaka Boka Durwas da sauran bokayen da ka aika ni kirawo wa." Yana gama faɗin haka, bai tsaya jin amsar Maigari ba, ya ci gaba da gudu ya nufi gidansa.

Kafin Maigari ya samu bakin magana, tuni jama’a kowa ya fara neman mafaka. Kafin kowa ya bar wajen, sai aka hango Amrah tana tafiya. Ita ba a ƙasa take ba, ita ba a sama take ba, ƙafafunta dai ba sa taka ƙasa. Ta saka kaya irin na ƴan matan Fulani. Ta caɓa wata kwalliya a fuskarta, wacce idan ka yi mata kallo ɗaya, ba za ka sake na biyu ba, saboda munin da fuskarta ta yi.

Nan fa kowa ya fara yunƙurin guduwa gida, amma sai suka ji kamar an saka sarƙa mai ƙarfi an ɗaure musu ƙafafu. Da suka ga sun kasa guduwa, sai ihu da kururuwa ya kauraye wajen. Babu mai jin na ɗan'uwansa, kowa ta kansa yake.

Maigari yana zaune a kan kujerarsa, ko ta ina zufa ke tsatstsafo masa. Ya cire rawanin ya jefar, ya cire alkyabbar tasa ma ya jefar. Ya kwanta a ƙasa yana kururuwa kamar sabon mahaukaci. Sai faman ba wa Amrah haƙuri yake, saboda gani yake idan Amrah ta ƙaraso wajen, shi za ta fara hallakawa, saboda ya fi kowa laifi a wajen.

Tana ƙarasowa wajen, ta ji kururuwar da mutane suke yi ta yi yawa, sai ta daka musu tsawa. Nan take, kowa ya yi shiru, kamar mutuwa ce ta gifta.

A hankali ta fara tafiya, amma ƙafafunta ba sa taka ƙasa. Ta ƙaraso inda Maigari yake zaune. Saboda tsananin tsoratar da ya yi, duk ya jiƙa tufafin jikinsa da fitsari.

Wani kallo ta watsa masa, ta ce, "A cikinku waye ya daki Baffana?" Gaba ɗaya suka yi shiru, sai dai wannan ya kalli wannan. Amrah ta daka musu tsawa da ƙarfi, ta ce, "Ba tambayar ku nake yi ba?"

Hussain Yusuf✍️