SADAUKARWAR SO.

11

by @jamilaumarjanafty

SADAUKARWAR SO..!!

(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)

Wattpad:@Jamilaumar315

Mallakar:Jamilaumar(Janafty)

Page1️⃣1️⃣

"Sakon daya Turomata Shi ya Wanke mata zuciya har taji Kwarin gwiwan Cigaba da karatunta ta dauki lokaci mai Tsawo kafin Tattara komai gefe Daya ta kwanta Bayan ta Saka Hoton Mastur Gaba tana Kallo Tana auna Yadda take kaunar wannan Bawan Allah wanda Rabonta Dashi Tafi Shekara Hudu Tun Tana aji Biyu a makaranta lokacin tazo Hutu gida Shi kuma yazo gaida su Abba.

Haduwarsu Kamar almara ce Domin bazata iya Dora komai a game da Haduwar tasu ba bayan gaisuwa da Tambayan karatu Wata mgana bata Shiga Tsakaninsu ba bai wani Jima ba ya Tafi Lokacin yana Kano ne yana aiki,kafin kuma ya samu karin Girma Rumana Bazata iya Fadan Lokacin Dataji ta kamu da matsananciyar Soyayyar Mastur ba sai dai Hakan ya samo asali ne Daga Burgenta Da yake yi da kwazonsa da kuma kyawawan Dabi"unsa da kowa yake Mgana akansa.

Ya bar Gidansu Tun Bayan Daya gama Digree dinsa Azaria yaje yayi Service dinsa Har ya tafi Staff Collage Basu kara Haduwa ba,har ya Dawo Lokacin ita kuma ta Fara karatu anan Uduth kafin ta samu Course din Data ke Nema tatafi University of Lagos ta Fara karantar Medicine Kuma Mastur ya Taimaka Wajen zamowarta mai kwazo kuma ya bata kwarin gwiwa kan Abunda tasakama Gaba Saboda Farincikinsa yasa Ta Zage Damtse ganin Ta Zama Likita Ta lura Dashi akwai son Mace mai son Karatu da kwazo Shiyasa ta Dage.

Mastur baya Cika Hawa Sociol Media Kullim aiki kamar agogo Waya ma ba koda yaushe kake Samunsa ba ita da kanta ta Dauki Lambarsa a wayar Umma take Kiransa,kullun in ta Kirashi sai ya Tambayi mai mgana Wannan Dalilin yasa Bayan sun Hadu agidansu Lokacin Dayazo gaida su Umma ta karbi Wayarsa Tayi Saving din Sunanta.

Tana ji aranta Burinta zai Cika Da Zarar ta kamallah Karatu bata Damu da yanayinsa ba Tana Lakanta da Abun da Haka Nature Rayuwarsa Take abun Har mamaki yake bata bashi da Amini ko Aboki Sai Dan"uwansa Shi kadai ne Kaninsa kuma Amininsa wanda bai da Kamarsa sai Abokinsa guda Daya wato abokin aikinsa Acp Saleem kabir kumo tare suka samu Horo a Jos, Bazata iya Dora wani abu kan Mansur ba ko Diza Rabonsu da juna Tun Suna yara Sau Daya Umma taje da ita Zaria Lokacin Tana karama Daga wannan Zuwan bata Tunanin ta kara Zuwa ko Wamako Sun Dauki Shekaru basu gantaba Sun gaji dayi ma Abba mganarta sun Hakura sai dai yace Tana karatu,Diza zata Dora wani abu kan kamminta Saboda suna gaisawa ta Social media kuma Tana ganin Hotunanta ammh Ido da ido kam Bazata Dora komai a kanta ba,bata damu ba itama Haka take ayanzu Haka bata da wata Cikakkiyar kawa Tafi jin Dadin Rayuwarta Ita kadai Shiyasa Bata da wani Sakin Jiki Ballatana Saurin Sabo.

Kamar yadda yayi alkawari Da Safe karfe 7am sai ga Kiransa Shi ya tasheta Daga barci Bayan gaisuwa da Tambayan karatu Basu Tsawaita mgana ba yadai Bata Shawaran ta yi karatu Sosai kada tayi wasa Daga karshe yayi mata Fatan alheri da Fatan Samun Nasara Tayi Godiya suka Rabu,Farinciki ya Cika Zuciyar Rumana da wannan Farincikin ta Wuni Har Umma sai da Tayi mgana bata ce mata komai ba Tadai yi Mirmishi kawai Ta kauda kanta ita kuma Umma Sai ta barsa a Kila Farincikin Dawowarta Gida ne yasa ta Fara"a haka.

Da Daddare da Abba ya Dawo yace mata Sabuwar Motar Da yayi mata Oder ta Iso Gobe Za"a kawota Gida Tana Company Rumana Tayi Murna Sosai ta Rumgume Abba Tana Godiya yace Gift ne in Tagama karatu Zata Fara Intenship Tayi amfani da ita Daman Rumana bata da Mota Saboda bata zama agida Tana Makaranta Shiyasa wannab karon ne in Tagama Zata Dawo Gida Tayi ta Murna Ranar da wannan Farincikin ta kwana Tare da Kaunar iyayan nata Har cikin Ranta.

*****

Zaria..

Zaune take acikin Karamin Office dinta Dake Shashen Makeup dinta Tagaji Sosai yau Tayi ma Mutane Dadama Kwalliya Sosai wuyanta ke Ciwo Tashi Tayi ta Shiga Tiolet din Dake office din ta wanko Hannunta Lokaci Daya ta Dauro Alwala Tazo ta Shimfida Sallaya Ta Tada Sallar azahar Bayan ta Idar ta Jawo Wayarta Tana Latsawa kafin ta Mike bata Cire Hijabin Jikin nata ba ta Zura Flat din Takalminta ta Fito Ta iske Hauwa na mooping din Wajen kallonta Tayi Tana Fadim"Hauwa Dubamin Littafin Nan gobe mutane nawa ne sukayi Buking din makeup..?

Da Sauri Hauwa Ta ijiye Sandan Mopping dim Ta Nufi Wani Durowa ta Jawo Cikin Zafin Nama ta Dauko wani katon Littafi ta Bude Tana Dubawa Kafin Ta Dago Tana Fadin"Madam Mutum 8..2 Daga Ciki House Service ne.."Kai ta gyada kafin tace"Hauwa na Fara gajiya da wannan aiki..Ki Sanar muma neman Mutum Daya mace Tazo ta Rika Taimaka Miki Am Tired.."

Hauwa Tace"Tom Madam..kuma naji ba kina Fadin zamu bude Wajen Saloon ba.."Diza Tana Kokarin Fita Daga wajen tace"Shima sai na samu mai kula da Wajen...Bafa zan iya wannan aikin ba Hauwa ni ba irinki bame Girman kauye kiyi ta aiki bakya jin kin gaji.."Tafada Lokaci Daya Tana Ficewa Daga wajen Hauwa Tayi Dariya kawai Domin kullum Haka Madam din Take Fada wai ita bata gajiya Ta Saba Aiki Ita Renin kauye ne Gaskiya ne ita yar kafachan ne Dake kaduna Anan Zaria Tana Hannun kanwar Babarta ne ita Ta Sakata Makaranta Koyin kwalliya Har ta kware Diza Ta Dauketa aiki Tana Biyanta albashi mai Tsoka Ammh Tabbas Bata Tashi Cikin Jin Dadi ba Ta Horu da aiki Sosai.

Diza Tana Fita Shashen Catering Dinta Dake Jikin Bulding din Wajen makeup dinta ta Nufa Tana Shiga ma"aikatan suka Fara Wlcming dinta suna Kiran ta da Madam Tana amsawa Marry ce Shugabar ma"aikatan ta na wajen ta Biyo Ta da Gudu Tana Mata Wasu Bayanai Bata Tsaya ba Tace"Merry muje Kitchen din..Hajiya Batula Ta GRA tamin Complain Cake na Rugujewa Ya akayi haka Merry..?

Merry Tace"Mah ba laifin mu bane.."Diza bata kara mgana ba Har suka Dangana da Katon Kitchen din Dayaji kayan Eletronic na wuta,gasu nan kala kala,Saboda ayyikansu ga Ma"aikata ne sai aiki suke Layi Layi Tabi Tana Dubawa Tana kallon Merry tace"Merry ki Rika Dubawa Fa..Bana son mtsala..Bana son Complain in bazaki iya wannan aikin ba Juz Tell me.."

Da Sauri Merry Tace"Sorry Mah.."Diza tayi karamin Tsaki Tana Fadin"Ma"aikatan da kika Dauka basu kware bane Merry..?Kinsan bana son aikin son rai ko..? Kizo kina Korarmin Costumer saboda Shirmenki Bazan Dauka ba.."Ita dai Merry Hakuri kawai take bata suma Ma"aikatan Catering Din Bangaran Kitchen din sai Hakuri suke bata akwai Musulmai Sosai Yaran Ciki kadan ne Gyara Tsayuwa Tayi Tana Fadin"Wacece Tayi Cake din Jiya..?

Merry Ta Nuna Wata Farar Budurwa Tace"Gata nan Fatima ce..Kin santa ai Mah..Tana da kwarewa She know her work Sosai.."A Karkace Diza ta kalli yarinyar kafin Tace"Fati..ya akayi haka kuma..?

Bayani ta Fara mata inda ta Samu mtsalan Karamin Tsaki Taja Ta Cire Hijabin Jikinta da wayarta ta mikama Merry ta Rawan Jiki ta Karba Cikin Takunta na isa ta isa gaban Fatima Tana Fadin"Yau ni zan gasa cake dina Da kaina..Ku koma gefe ku bani Waje.."Tafada Muryanta na Bayyana Bacin Ranta da Gudu Merry ta Dauko Wata FararRiga kamar ta ma"aikatan Kitchen din ta Dorama Diza Duk suka koma Gefe suna kallonta nan da nan ta Fara aiki Lokaci Bayan Lokaci in Tana Bukatar wani abu Zata ce su miko mata.

Agabasu Tayi komai ta gama aikin Diza na Musamman ne Bayan Ta gama gasa Cake din tace kowa yayi Testing haka suka Dauka suna ci suna Mirmishi suna yaba mata,Mirmishi Tayi ta isa gaban Merry Ta Cire mata Rigar Jikinta ta isa ga fomfon dake kitchen din ta wanke Hannunta,Tazo ta karbi Hijabinta da wayarta Ta Juya Tana Fadin"Bana so in sake jin wata Mtsala ok..?

Dukkansu suka amsa da Yes Mah.."Merry Tabi bayanta da Gudu Tana Bude wani Littafi Tana mata mgana Har Haraban Catering din,Kanta ta Dafe Tana Fadin"Merry kiyi yadda kika saba..Everthiny yana Hannunki..Ki turomin komai ta Wayar kamar yadda kika Saba zan Duba in na isa gida yanzu am Tired bana gane komai.."

Merry Ta Rufe Littafin Tana Fadin"Ok mah.."Diza bata kara mgama ba ta wuce Bangaran makeup dinta ta samu Hauwa Tagama gyara Wajen Ciki taa Shiga Ta Cire Hijabin Jikimta ta Ninkesa gefe,ta Dauki Vail dinta Ta saka asaman kanta,ta Dauki karamar Jakarta da key din Motarta Ta Fito Tana kallon Hauwa Tace"Ki kulle ko"ina go Home and Rest.."

Hauwa Ta Bude baki Zatayi mgama Diza ta Fice Tana Fadin"Ke ki tafi Gida nace ko..? Duk wanda yazo ba ma nan Saboda Buking din mu na yau is Over.."Daga haka ta karisa Ficewa Daga kofar glass din,Haraban Adana Motocin na Haraban Wajen ta Nufa Ta Shiga Motarta Ta Bata Wuta Megadin Dake Tsaron Kofar Wajen ya Bude mata get ta Fice Daga wajen da Gudu ta Dauki Hanyar gida Ta gaji so take tayi wanka Taci abinci ta kwanta ta Huta Mansur Baya nan Tun Jiya yana kaduna Taron su na Siyasa kuma sun yi waya Dazu yace Ba lalle ya Dawo yau ba sai gobe Duk kewa ya Isheta Gidan ma ba Dadi Shiyasa tazo Office nan ma aiki Duk ya gajiyar da ita.

Koda ta isa Gida Mommy nada Bakuwa direct Dakinta ta Shige Tayi wanka kafin ta Fito Mama Fadime ta kawo mata abinci Ta Zauna taci ta koshi Tasha Ruwa Ta Ture komai gefe tabi Lafiyan gado sai barci bata Farka ba sai da Taji kiran Sallah Daga masallacin gida kana ta mike ta Fada Tiolet ta Dauro alwala Tazo Tayi Sallah kana ta gyara Fuska ta Fito Zuwa Falo Har Lokaci  Bakuwar Mommy bata Tafi ba Abokiyar kasuwancinta ne Samata Haura Suka gaisa Tace mata ta Dawo Tun Dazu yanzu Zata leka gidan su Hajja suyi Hira da Aiya tace mata adwwo Lafiya..

Gidan su Mansur ta Shiga Suka Hadu da Aiya sukayi ta Shan Hira Sai Da ta Tsaya taci Tuwo Miyar Dan kubewan da Hajja Tayi ta koshi kana lokacin Har Baba Habibu ya Dawo Tare da Usaman suka Fita itama Tazo Gidan duk irinsu Aiya nw masu Barkwanci Gida ta Koma Lokacin Daddy ya Dawo Ta Haura Dakinsa suka Sha Hiransu Har Mommy Tazo ta Samesu Lokacin Tuni Bakuwar ta Tatafi Abinci Daddy yaci ta zo suci tace ta Koshi Taci Tuwon Hajja,Nan Mommy ta Daga waya ta Kira Hajja tace itama Zataci Tuwon ga Fadime nan Zata zo ta karban mata Jin Haka yasa Shima Daddy yace Tuwon ZAICI Diza nata Dariya Mommy ta Sauka kasa Tayi ma Fadime mgana ita taje ta karbo musu sukaci Har da Saura na Dumamen gobe Mommy na Fadin Kwalelen Diza ita kuma Tace Ai Tana da Hajja Bata da wata Damuwa,sun Dade suna Hira sai Wajen goma ta Baro saman Zuwa Dakinta Daman Tayi Duka Sallolinta agidan Su Mansur Tana komawa Tayi wanka Ta Saka kayan Barci,sai ga kiran Mansur nan suka Sha Hira yana Ta bata Labarin abubuwan da suka Faru a wajen Taronsu na partysu har sai da ta Fara Jin Barci kana ya kyaleta suka Rabu kan sai gobe Zai Dawo Daganan barci ya kwasheta mai Cike da mafarkin Abun Sonta.

*****

Zaune yake acikin Office dinsa yayi Nisa cikin aikinsa yaji wayarsa Dake gefensa ta Dau kukan neman agaji Lokacin Daya ga sunan mai Kiran Wato BABA SULE sai da Ransa ya kara Baci da al"amarin Mansur a karo na ba adadi.

Bai Dauki kiran ba saboda yana Tsakar aiki ne sai da lokacin Sallar azahar yayi ya fita yabi Jam"i sukayi sallar Sai bayan sun Idar ya koma gefe ya Kira Baba Sule din Sun Dade suna mgana Ran Mastur in yayi Dubu ya baci da al"amarin Mansur Hakuri ya bama Baba Sulen Tare da mai alkawarin wannan Weekend din Insha Allahu Zai je Zaria kuma Zasu zo Har Maruka din da Mansur din Tunda ya Rainasa Bayajin mganarsa Da haka suka Rabu da Baba Sulen Cikin Bacin rai ya Kira Mansur din ammh bai Daga kiransa ba Ransa ya kara baci Shiyasa Sam bai so Mansur ya shiga Siyasa ba Sanin Halinsa na Shiririta da Shirme,Da Rashin maida Hankali kan abu mai Muhimmanci ammh anfi karfinsa bashi da yarda Zai yi ne.

Akalan kiran ya maida kan Baba Habibu Shi kan sun Dade Suna mgana Baba Habibu ya gayamai Mansur baya gida yana Kaduna Shima ba mganar da bai mai ba ammh bai Sauraresa ba Sai yace zai je bai samu Lokaci bane,Mastur Yayi shuru kawai bai ce komai ba baisan meke Damun kanin nashi ba ammh Wannan karon zai ji Dalili sun Rabu da Baba Habibu kan zai zo wannan Weekend din Sai ya saba ma Mansur Ransa sai ya baci da wannan Shirmen nashi ace kai baka san Mahaifinka da yan"uwanka ba..? Kamar wani Sakarai ya zama Dole ya Fuskanci bacin Ran abunda ya aikata.

Aranar da Daddare Mansur ya Dawo,sai daya Dawo ne ya samu Lokacin Kiran Mastur yana ganin Kiran yaki Dagawa Saboda Ransa ya baci Har Washegari ma yayi ta Kiransa yayi masa Banza Sai Mansur din ya Tashi Hankalinsa yasan Tabbas akwai wani abu,Har Baba Habibu da Hajja ya sama cikin Damuwa yana Magiyan su Kira Ya Mastur sun Tambayesa yayi mai wani Laifi ne..? Hajja ce ta Biye mai ta Kira Mastur din Bai Daga ba sai Daga baya ya Kirata Yana jin Korafin yace bakomai ya kashe wayarsa Duk sai Mansur ya Tsargu Baba Habibu kuwa daya san Komai sai bai Tanka ba baice komai ba,Ya bari ne Shi Mastur din su gamu da Mansur din Tunda bayajin mgana.

Mansur ya Damu matuka Dalilim haka yasa ya kira Diza Tace mai Tana Office Tana da aiki bai jira cewarta ba ya Datse kiran Mota ya Dauka sai Ma"aikatanta,Kuma fa jiransa ake yi a Karamar hukumar Sabongari suna da Taron Matasan yan Siyasa ammh suna ta Kiransa yaki Dagawa Dubasu Diza na Tsaka da yi ma wata Budurwa Makeup Mansur ya Shigo Wajen Hankali tashe bai ma Jira mganarta ba ya Finciki Hannunta ya Turata Cikin Karamin Office dinta itama Hankalinta atashe take kallonsa kafin tace"Mansur Lafiya..?

Tafada Cikin yanayin Damuwa da kuma Halin Data gansa Neme neme ya Fara Kafin yace"Ina wayarki..?

Mamaki ya kara kamata tace"Menene wai..? Wayata Tana Falon chan.."Bai ma Tsaya Sauraranta ba ya Fice Hauwa Data Karbi aikin Diza Tana karisawa ya tambaya ina Wayar Diza ta nuna mai Inda take ijiye nan Saman Madubi,Dauka yayi a gauggauce ya koma Ciki Diza Da Tayi Tsaye Tana kallonsa Hannayenta Saman kirjinta Bata Tankamai ba Har ya Lalubo Lambar Mastur Datayi ma Saving da Ya Mastur ya kira ammh Wajen kira uku bai Daga ba kawai sai ya Dafe kansa yarasa Abunda kemai Dadi.

Diza tazo kusa Dasshi Ta warce Wayarta Tana Duba wanda ya Kira Da Sauri Ta Dago kanta Cikin Dimuwa kada ace wani abu ne ya samu Ya Mastur din Tace"Me ya Faru..? Wani abun ne ya Faru da Ya Mastur din..?

Mansur bai sami Zarafin mgana ba sai da ya samu Waje ya zauna yana Sauke Numfashi yace"Dani dai ya sama My Firstlady,..Tun jiya nake kiran Ya Mastur yaki Daga Kirana bansan Laifin me nayi mai ba..kuma fa yana Amsa Kiran Kowa Sai nawa ne inata kira bai amsani ba.."Diza Datake kallonsa ta Sauke Numfashi acikin Ranta kuma Hamdala Take yi,da ba wani abu bane mara kyau ya samu ya Mastur din ba.

Mirmishi Tayi Tana Fadin"Laifi kayi mai.Yanzu haka wani abu yace kayi kaki yi Saboda Halinka na Shiririta.."Hararanta yayi yana Fadin"Ni ke Shiririnta ko... ? Lalle ma kin ga gadon Barcina.."Dariya Diza Tayi Tana Zama kujeran Dayake kai Tace"Eh mana ai ba karya nayi ba..Kai da kayi Tunani kila ka gane Laifinka..Nima Laifinka ya Shafeni yaki Daga Kirana..saboda yasan Dole muna Tare.."Mansur yayi Shuru yana wani Tunani Shi dai bai gano Laifinsa ba ga wayarsa sai Kira akeyi a kira wanchan akira Wannan yaki Dagawa Diza ta Mike Tana Fadin"Wai baka ji ana Kiranka bane..?

Karamin Tsaki yaja yana Fadin"Kan Taron Matasanan ne Dana gayamiki Zamuyi a karamar Hukumar Sabongari.."Tabe baki Tayi kafin Tace"Ka Tashi to ka tafi mana..Bafa Dadi haka kada ka manta Kujeran Charman kake nema kuma Matasa suke da Zabe in kayi haka kuma Yaushe Zamu Samu nasara..?

Tafada Tana Tsareshi da ido Kai ya gyada yana kallonta kafin ya Sauke ajiyar rai yana Fadin"Kuma fa hakane..Shiyasa nake Sonki Firstlady na akwai Hangen nesa.."Yafada yana Dariya itama Dariyan tayi Domin inda Sabo tasha Jin wannan kalmar Daga bakinsa Bata Taba Dsukanta awata kalma mai Muhimmanci ba ganin Shakuwar Dake Tsskaninsu da Mansur din Itama Takance mai Haka Tunda ai kaunace da Shakuwa mai karfi a Tsskaninsu.

Kai ta kada mai Tana Fadin"Toh ka tashi kaje gida ka Shirya ka Tafi..Mganar Ya Mastur kuma Laifi fa kayi mai kasan Irin Hukuncinsa ai bana mgana bane..Kaje ka Dawo Zamu Tattaina mu gano Laifinmu.."Tafada Tana yar Dariya Mikewa yayi yana Fadin"Shikeman bari..Naje kinsan Dole na Damu Kinfi kowa Sanin Halin Yaya Mastur Bana son na Bata mai rai..Balle har yayi Fushi Dani yayi min Fada.."Diza tace"Kaje zamu yi mgana in ka Dawo Nima ba Dadewa zanyi yanzu zamu yi Cloosing duka Buking din mu na yau ya kare..Hauwa kuma House Service Zata tafi yanzu.."Bai yi mgana ba ya Fice kawai ta Tako mai baya Har Kofar Wajen ta Rakashi Tana kara Bashi baki ganin ya Damu Har ya saki ransa suka Rabu kan sai sun Hadu agida ahaka ya Fito ya Shiga Motarsa ya Fice Dagawajen Gida ya koma yayi Wanka yan Party dinsa da magoya Bayansa na waje suna Jiransa suka Rankaya suka Tafi ammh Zuciyaraa sam ba Dadi kuma yakasa gano Laifinsa.

Shi kuwa Mastur yaga Kiran Diza yana gani yasan Mansur ne,Domin Diza Bata kiransa yana mamakin Girman kanta Bazai iya Tuna Ranar Data Kirasa ba Shiyasa yaki Daga Kiran kuma bai bi Baya ba ya Sharesu kawai so yake Yaje gida su kebe adaki Shi da mansur yaci Mutumcinsa Sosai yadda Zai Shiga Tataitayinsa.

Shiryen Shiryen Tafiya Weekend ya Fara Yaso ya Tafi a Jirgi sai kuma yasa yace bari yayi Tafiyar Mota yaso yatafi da Sargent Inuwa Daman shine Sargent dinsa sai kuma ya Sauya Shawara gwara yayi Driving da kansa wannan karon yaje Gida Duk da akwai Nisa bai Damu ba ya saba Tafiye Tafiye masu Nisa Duk da wani Lokacin ajirgi yake yinsu....!