SADAUKARWAR SO.

15

by @jamilaumarjanafty

[12/23, 7:00 PM] Janafty: SADAUKARWAR SO..!!

(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)

Wattpad:@Jamilaumar315

Mallakar:Jamilaumar(Janafty)

Page1️⃣5️⃣

"Rumana taje tayi Jarabawan gwaji a asibitin Uduth na Intenship dinta kuma Alhamdulillah ta samu nasara,zasu fara dis coming Monday Taje Lagos ta karbo Result dinta daya riga yayi Ready Lokaci daya kuma nan da  sati uku Makarantar zatayi Bikin Yayesu wato Indection dinsu suna ta Shirye Shiryensu.

Cikin Nasara Rumana ta Fara Intenship dinta asibitin Uduth,ba kwana take yi ba Ranar Datake da aiki Tana zuwa ta Dawo ne Tunda an kawo Motarta Kirar 4matic,Bata da mtsalan komai Gefe Daya kuma ita da iyayanta suna ta Shirya Shiryan Indaction dinsu Umma ta saka an yimata Littafi da jaka mai Dauke da Hotonta na Rabo Sai Kofuna kanana na Shan Shayi Na Tangaran da Farantin Voul na Cin nama ko Saka Miya,Daddy kuma yayi mata Key holder mai Dauke da Hotonta,sannan kuma Umma ta Kira Mommy ta mata mganar su Cake da Donout da Sauran kayan Fulawan da za"a raba achan in sun isa Mommy tace ai Ta kwana Gidan Sauki Ta Dauki Nauyin komai Diza bangaranta kenan Komai zai Tafi Daidai da wannan mganar Mommy Tayi ma Diza mgana kan Tana son Tayi mata Kowannen Spicess 300 each,Tana son Spring rol sai Samosa Duka ayisa ana Gobe Tafiyarsu Saboda sai sun je Chan Sokoto Zasu Tafi Tare da Su Umma Diza Batayi kasa agwiwa ba Ta Kira Merry ta gayamata kuma ta bata a Rubuce Kuma taje da Kanta Taga yadda aikin ke tafiya,Dayake bangaran makeup dinta ta samu wata ma"ikaciya mai kwazo mai suna Madina itama Qualified ce kan Harkan kwalliyan da gyaran Jiki yanzu Har gyaran Kafa Diza sunayi a wajen sai aikin yazo mata Cikin Sauki Saboda Abun na Mommy ne da kanta Take Zagewa anayin Komai da kanta Saboda Tana so komai ya tafi daidai.

Mansur yasan da Labarin Zuwa Lagos yasan Rumana sai dai ba wani kyakyawan sani bane,Mastur kuma Abba da kanshi ya kirashi ya gayamai Kuma zai ji Dadi in zai samu zuwa Sai dai Mastur din bai da Ra"ayin zuwa ahalin Dayake ciki na Bama kansa kwarin Gwiwa kuma sunyi mgana da Daddy yace Dukkamsu Zasu Tafi Harda Diza Mommy kuma Tace Zata Roki Baba Habibu Ya bar Hajja da Aiya su Tafi Tare dasu,Jin haka yasa bai saka ma ransa ma zai je ba bayaso yaje Kowa ya Fahimci Halin Dayake Ciki..Domin ya Rame sosai sai Dan Wuya Duk yayi Zuru Zuru ga Rashin Barci ga Ciwon kai Bayason ya koma asibiti ace za"a kara kwantar Dashi yana so ya zama Very Strong ne baya son Saboda Mace ya kwanta Warwars Har wata Cuta ta kamashi kuma baya son koda wasa a Fahimci ya Taba son Diza acikin Ransa Shiyasa ya bama Abba Excuse da cewa aiki ya Rike shi bazai samu zuwa ba.

Abba ya Fahimceshi yace bakomai jin haka yasa Mastur ya kira Baba Habibu sukayi mgana kan ya bar Hajja da Aiya su Tafi Tare Baba Habibu yace ayi haka..? Shikenan Daman Mansur Shima yace Diza tace in bai je ba ita bazata jeba Zai Shirya su Tafi Tare Sai su Tafi Gabadaya shi dai bazai samu zuwa ba Saboda kasuwa Duk da akwai yara ammh ya kamata dai ya Tsaya Mastur na jin haka sai da Zuciyarsa ta Buga ya Riga ya Tabbatar ma kansa Shine yayi kutse Cikin Rayuwar masoyan Biyu suna Kaunar juna ya Zama Dole ya Binne abunda ke Ransa kada ya Fito Filo hakan ya Haifar da wata Mtsala wacce bayan Fatan Hakan.

Rumana da kanta ta Turamai gayyatan,yana ganin Kima da girman yarinyar yasa ya kirata ya bata Hakuri yace Hajja da Mansur Zasu Wakilceshi kamar yana wajen kana yana Tayata Murna Allah yasa taci Moriyan Abu Taji Dadi Sosai suka Rabu Cikin Girmama da juna da jin Nauyin juna,Bangaran Rumana kuwa ba Haka taso ba taso ne Lokacin da zata karbi Rantsuwarta Mastur din na wajen Domin da Taimakonsa da Jajircewansa Yasa ta kawo yanzu a matsayin likita Ta kuma Kalli idanuwansa ta gani Shin yana mata kallon Datake mai..? Yana tsananin Begenta kamar yadda take Begensa..? Ammh ba komai duk da haka batayi La"asar ba ba kuma ta Hakura ba Zata Cigaba da Bayyana alamu Har ya Fahimci inda ta Dosa..

Umma da Abba sun ji Dadin karan da Baba Habibu yayi musu sun Tsara Tafiyan Ranar asabar ne Taron Daga Zaria suka Tafi Sokoto Ranar jumma"a Baba Habibu kadai suka Bari agida gidansu Diza kuma megadi da Mama Fadime Wannan karon ma Diza na Motar Mansur ita da Aiya Dayake Shatar Motocin Haya sukayi guda Biyu Dayan Motar kuma Daddy kuma Hajja da Mommy ne sai Direba Dake jansu Da suka isa sun samu Tarba Sosai da karramawa,Umma da Abba suka Rasa ina zasu saka Bakinsu Goggo jummai da juma Suna ta kai da kawo Daga Kitchen zuwa Falo Suma Hardasu Za"a je Lagos Rumana tace don Allah azomata dasu Dayake ita Tun Jiya ta wuce Saboda Shirye Shirye.

Hajja da Aiya basu yi wani bakunta ba,Domin Daga Umma har Abba ba bakonsu aciki,Hajja ma sun Taba zuwa da Mommy Lokacin da Umma Tayi Rashin Lafiya sukazo suka kwana Daya suka gaisheta,suka koma Dayake sun je har gidan iyayan Mommy din Tafiyar ma Harda kannenta Guda Biyu maza da kanwarta Mace za"ayi ta Domin suma zasu yi ma Abba da Umma kara Hakan matukar yayi musu Dadi Mansur Da Diza kuma suna Gefe suna yan Hiransu Ba wanda ya damu dasu,Sanin Halinsu in Daya na Wajen Daman yana Tare da Daya Tun kafin ma Mansur din ya Furta Akwai wacce ya Dade yana so Kowayana kallon Soyayya ce mai karfi Tsskanin Diza da Mansur din Tun suna yara Shiyasa ba wanda ya Damu dasu Jiran Lokaci kawai akeyi ayi komai agama.

Mansur da Daddy Daki Daya aka Saukesu,Mommy da Hajja Kuma Dakin Umma Aiya kuma Dakin Goggo Jummai Diza kuma Dakin Rumana aka Sauketa Tasha mamakin ganin Tarin Littafan karatu Dakin Rumana Tajinjina mata gaskiya ita bazata iya wannan Wahalar ba Sam,Tun adaran Juma ta gama Hada Duka abubuwan da zasu Tafi Dashi Jirgin karfe 7am na Safe Zasu bi zuwa Lagos Domin Taron karfe 9am za"a Farashi Rumana sai kira Take Tana magiyan su Taho da Wuri Mastur kuwa Mansur ya Kirashi ya gayamai gasu a Sokkoto Gobe Zasu wuce Lagos yayi musu Fatan Isa Lafiya da Dawowa Lafiya basu Tsawaita Hiran ba Domin Tun bayan Bayyanar al"amarin Mastur ya Daina yadda yana wata Doguwar Hira Da Mansur din bayason ya Tado mai da Mikin Dake Zuciyarsa alhalin yana son ya zama Very Srong akan lamarin

Washegari Tun kafin 7 suka isa Filin Jirgi Tare zasu yi Tafiyan Har da yan gidan su Mommy,Lokaci na cika bayan an Tantacesu suka Lula sai Lagos wajen 10 suka isa Wani Abokin Kasuwancinsu Abba Alhaji yusuf Dake nan lagos din ya zo da Dan"sa Mas"ud da Matarsa da suka zo da Motoci suka Daukesu Dirrct sai Cikin makaranta Sun iske ma an Fara Taron Hall din ya Cika makil ba Tsaka Tsinke Dakyar suka samu Wajen shiga Daliban suna Chan gaban Wajen Prof dinsu Dukkansu Sanye da Gown din makarantan na gamawa Dama Tun Dazu Rumana ke waige waigen Neman Danginta sai ga Kiran Abba yace ta Juyo gasu nan abaya Lokacin ta Data mike Ta Dago musu Hannu Umma ta mike ta Daga mata sai da taji Tahowar kwallah Tayi matukar murna da ganinsu Duka Don ita suka zo Daman tasan da zuwan su Diza Uncles dinta ne bata san da Zuwansu ba sai da ta gansu kawai Diza kuwa Daga nesa ne Shiyasa basu yi wata mgana ba.

Bayan Bayanai Daga malamai,Masu Ruwa da Tsaki magabata da Masu Makarantar sai aka Fara kiran Daliban Daya Bayan Daya Rukuni Rukuni Domin karban licence da Rantsuwa Wanda prof da kanshi Zai basu,Rumana Tana Daga Farko Farko Lokacin da aka Damkamata Licence dinta Sai ga Hawayen Farinciki Haka ta Dagashi Sama su Umma suna gani Diza da Mansur kuma sai Video suke,Umma Hawayen Farinciki take suka Rumgume da Mommy Suna Murna,bayan angama basu Rantsuwa sai aka koma Kiran Dalibai da suka Fita da Firstcallas,sai ga sunan Rumana Muhammad Wamako a mtsayin wacce ta Fita da Firstcallupper,Murna Farinciki kamar ta suma Bata Taba Zata ba ammh Sauran abikom karatunta sun san ta Chanchanta Domin akwai ta Da kokari Hazaka guruwa ce ta karshe Rumana Har kan Step ta Taka aka karramata kuma aka Bata Waje Tayi jawabin Godiya ga Iyayanta kana aka Gayyaci Alhaji Muhammed Mahaifin Rumana shima ya isa kan step dim yayi jawabin Godiya Cikin Alhafari.

Farinciki ya cika Zuciyar Umma da Abba yau din Rana ta Musamman ce Rumana Tana kuka Tana Rike da kambon karramarta da licent dinta,Murnan Burinta na Farko ya Cika Saura na Biyu cikin Shaukin Farinciki ta Fito da Wayarta Ta Tura ma Mastur Text.

Salam Alhaamdulillah..Yau na Cika Burina na Farko..Na zama Likita..Saura Dayan Burin nawa Wanda ba wanda ya sanshi Sai Allah..I LOVE U Ya Mastur..And i Mean it..Daga haka ta Turamai Tana jinkamar ta sauke wani Nauyi Daya Dade acikin Zuciyarta.

Shikuwa Mastur yana Cikin Office dinsa yana aiki yaji Shigowar Sakon Rumana Zuciyarsa sai da ta Buga Daya ga Sakobta Daman yasan Za"a Rina Ya dade yana Tunanin hakan sai dai bai taba Zaton shi nan kusa ba,kansa ya Dafe kawai yana jin wani irin Faduwar gaba,Tun bayan Daya Fahimci Mansur na Son Diza ya gama Tsara Rayuwarsa na cewa bashi ba wani jin Dadi ballatana wani abu na Farinciki ba aikinsa kadai zai sakama gaba bai kawo ma zai iya auran wata mace ba Domin zai Cutar da ita ne ya zauna da ita baya sonta Hakan kamar karuwa ce Zai zauna haka koda bazai Dorar da wani Farinciki ko Jin Dadi game da Rayuwarsa ba Ammh Zai ji sukuni da jin Dadi in har Mansur ya auri Diza ya kasance Cikin Farinciki.

Yana ganin Sakon yayi sauri ya goge bai maida mata da amsa ba Sai ma Tsausayi da ta bashi ta Fada son wanda bai Dace da ita ba Bai taba mata kallon so ba Kallon kanwa yake mata Tunda yake mace Daya ya mallakama Zuciyarsa kuma Ita Din ya Riga yayi alkawarin Sadaukar da ita ga kaninsa Bashi da wani Gurbi da zai iya sakata,Shiyasa ya nuna kamar bai ga Sakonta ba ya koma ya Jingina da kujera yana Fama da Sukan Zuciya ayadda yake kwana baya Barci ga Nauyin kai da Saranwan kai ya Tabbata da yana zuwa asibiti aka auna sa Za"a ga Ya kamu da Hawan Jini Gashi mgungunansa sun kare kuma bai koma baya son yaje a Bayyanamai Wata gazawar Tashi ne Shiyasa kokarinsa Da sai ya Nuna bakomai bai sani ba Hatta Ma"aikatan Dake karkashinsa Sun Fahimci Yallabai baya Cikin kwanciyar Hankali Jarumin Namiji mai cikar Zati da Haiba Duk ya Susuce ya koma wani iri Dashi Rashin son Hayaniya da rashin son mganarsa sai ya karu Yawan kadaicin Dayake samar ma kansa yana kara Hadasamai Abubuwa Dadama bai sani ba.

Achan Lagos kuwa Taro ya Tashi Lafiya su Rumana bayan sun gama Hotuna da Mate dinsu da malamansu ta Nufo inda iyayanta suke ita da Wata kawarta yar Kaduna Basma Lawal ita iyayanta na London Mamarta ta raka Babanta adubashi yana Fama da Mtsalan koda Sai yayanta ne da kanwar Mamanta suka zo mata ita kadai ce kawarta Basma Duk Fadin Jami"an saboda bata da Sakin Jiki da mutane.

Ta gabatar da Basma gasu Umma Suka gaisa cikin Fara"a suna Tayasu Murna nan ta kira yayan nata da Anty ta suka gaisa da su Umma Duk da Abaki suka san Labarin Rumanan sai yau suka ganta,Rumana bakinta Har kunni suka Sarke Hannu da Diza Suna gaisawa yau da sun Hadu bayan sun kwashe Shekaru Rabonsu da ganin juna Sai dai ta Waya ganin Hotunan juna,Diza ta sakar mata kayattacen Mirmishi Tana Fadin"Congratulation Sister..Allah yasa albarka.."

Rumana Cikin Muryanta mai Cike da Natsuwa Ta amsa mata Tana Fadin"Ameen ya Allah..Nagode.."Diza ta kada kai Tana Fadin"Sunana Khadija Sunusi Tureta(Diza).."Rumana tayi Karamar Dariya Tana Fadin"Haba Diza ke din ce bangane ba..?umma kinji Diza Tana Zaton ban ganeta ba..?Umma tace"Ai ku kuka sani. in baku gane juna ba..Kunyi Sakaci da Zumunci Alhalin kuna yara Baku da aiki sai akaini Wajen Diza akaini Wajen Ruma.."Gabadaya aka saka Dariya koda ganin yadda Umma Tayi mganar Rumana Har kasa ta Duka ta gaida Daddy da Alhaji Yusuf suna ta saka mata albarka cikin Sha"awa Daddy yana ji aransa yau Dama Diza Tayi karatu ita da ta sakashi alfahari,Haka ta duka ta gaida Mommy da Hajja da Aiya Sai Matar Alhaji Yusuf Hajiya Laure,Suka Rumgume da Goggo Jummai Juma kuma an samu nayi sai Faman saki baki akeyi ana kallo,Suma Uncles dinta haka ta bisu Daya bayan Daya ta gaishesu suka amsa cikin Alfahari da ita Umma ita ta kalli Rumana Tana nuna Hajja Tace"Kin ko gane Hajja Mahaifiyar Mastur.?

Rumana ta Sunne kai Tana Fadin"Umma naga kamar su ai.."Mommy Tayi Dariya Tace"Kai Dota har kin ga kamarsu..Ai Mastur ma yafi kama Sosai da Baba Habibu.."Rumana tace"Shi nasanshi ai suna Zuwa Da Daddy.."Umma tarike Baki Tace"Kaji ja"ira sau daya ne fa..Lokacin da sukazo Daurin Auran kanina Salisu Asiya Lokacin ita kuma Ta Dawo Hutu.."Mommy tace"Anyi haka Tare kuwa suka zo..Yar nawa akwai kwalkwalwa gashi mun ga Ranarsa yau..'Hajja dai na Gefe Batace komai ba sai Mirmishi Take Aiya ce ta gyara Tsayuwa Tana Fadin"Wai ni baza"a nemi wajen Zama bane..Mufa ba iyalan Megidana bane Yan Sanda da suke kwana atsaye basu gaji ba..Wlh nagaji.."Tafada Tana yamutsa Fuska Umma Tayi Dariya Tana Fadin"Yi hakuri Aiya..Mu karisa Wajem Inuwar Chan a Shinfida Manyan Darduma sai mu Zauna mu Huta muci abinci..Ruma Taho muje kayan ki na Mota.."Rumana tace Toh Har zata Bisu sai ta waiga Tana kallon Diza wacce ke jan gefe Tare da Mansur da Mas"ud suna Hira Basma kuma Daman Tatafi ita da Anty da yayanta inda sukayi parking dim Motarsu itama Jama"a sai Binta suke Juniors dinsu Domin ita ta Kirasu Zata basu kayan Rabon duk su Raba kamar zata Bi bayan su Umma sai ta Fasa Domin ta gane Fuskar Mansur Ta Taba ganinsa yazo Gidansu Wajen Mastur Lokacin Ta Fara Uduth kafin ta samu Addmission ta koma Lagos da karatunta.

Sallama Tayi musu Lokaci Daya Tana gyara Zaman gown din Rigarta Gabadayansu suka waigo Suna kallonta Diza ce tace"Yauwa Taho muyi Hoto.."Jin haka yasa ta karisa kusa da ita Diza ta kalli Mansur Tana Fadin"Dauke mu da wayarka.."Tun kafin ma ta gama mgana ya Fara Daukansu Mas"ud na Gefe Shima yana ta Daukansu Rumana kawai yake kallo yana mata Mirmishi Domin kallon Farko Da yayi mata ta Shiga Ransa a kasar Waje yayi karatunsa yanzu Haka Shine Manaja a kamfanin Sarrafa Biscuit Warrper,Yana ganin Rumana kawai yaji ya samu Matar Aure ta gama Tafiya da Duka Tsarinshi na Macen Dayake son Aura.

Sai da suka gama Hotunan kana Diza Ta kalli Mansur Tana Fadin"My Honourable ga Fa Rumana..My Childhood Friend kuma Diyar abokin Daddy Abba da Umma.."Mansur ya saki Mirmishi yana Fadin"Naganta Jinta yafi ganin Hotonta Firstladyta..Ina kallon yanayinta ta Sauyamin kenan ta zama wata so Classic koda yake Likita ce fa da kanta sai mun zo allura Allah ya Sa albarka.."

Yafada Cikin barkwanci Mirmishi kadai Tayi kafin tace"Ameen Nagode.."Kai ya kada yana Fadin"Sunana Mansur Sulaiman Doguwa...Shakikin kani ga Dcp Mastur Habib Doguwa nasan kin Ganeshi shi.."Wani kayattacen Mirmishi ta saki kafin tace"Haba dai kaima ai na ganeka Ko ba kai bane Honourable..?Baki ya Rike yana Dariya yana kallon Diza ita kuma sai ta Dauke kai tana Dariya Mus"ab ya kallah Shi kuma ya Daga hannu yana Fadin"A"a bani na gayamata ba..Ni yau ma nasan da Honourable nake Son abota.."Sai Dariya ta kamasu Dukkansu banda Rumana Data Murmusa Mansur ya kalli Diza yana Fadin"Kalli Rumana..Don Mirmishinta da yanayinta bai miki da Kama dana Yaya Mastur ba..? har ajinsu iri Dayane Basa son mgana da yawan Dariya sai basarwa.."Rumana ta kafeshi da ido Lokaci Daya kamar yadda Diza ta kafeshi da Ido nan da nan Annurin Fuskarta ya Dauke Shi kuwa ko ajikinsa Ya juya yana Gayama Mas"ud yana bashi Labarin yanayin yayan Nashi Rumana kuwa Juyawa kawai tayi tace suzo su Tafi chan wajen iyayan nasu Diza kuma wani Wutan kishi ne ke cin Ranta Don me Mansur zai Hada Abun kaunarta da wata Duk Sai taji Dan Sakin Jiki Datake da Rumana ma ya Dauke,ahaka dai suka karisa wajen su Umma inda suka Saka manyam Dardumai suna Zaune zaune Rumana kuma su Mansur suka Firtotomata da Manyan Ledojin da Kayan Rabonta ke Ciki ta Dauka ta bama wasu Mata Sauran kuma ta tafi Wajen Basma suna Rabaawa itama Yayanta sun zo mata da nata.

Sai La"asar suka bar Cikin makarantan zuwa Gidan Alhaji Yusuf Domin suyi Salloli suci abinci su Huta acikin makaranta sukabar Rumana Zata Tsaya tayi Parking din Duka kayanta Sai gobe Zata Taho da ita zasu Wuce,Haka kuwa akayi Washegari da Safe Tayi bankwana da Jami"ar lagos Basma ma da Safen suka Tafi Mus"ab Abba ya wakilta yaje ya Taho da ita Shi da Mansur Duk da Mus"ab din sai saka baki yake bata bashi wani Fuska ba suna Mota sanda suka Daukota Tafi maida Hankali Wajen Hiran Mansur wanda Haka kurum yake sakata Nishadi ko Domin yana Dan'uwan abun kaunarta ne Bata sani ba Diza kuwa da Mansur yace Tazo suje tace Tana wani abu Alhalin kuwa Tun mganar jiya ce Take jin Haushin kowa Mussmman ma Rumana bata kaunar ganinta.

Jirgin karfe 4pm suka Shiga Zuwa Sokoto suka yada Zango a Gidan Abba Dake Sokoto,Sun so su wuce aranar Abba ya Hana sai da suka kara kwana Anan Sokoton,mommy dai Gidansu Taje ta kwana Diza kuma ta bita Hajja da Aiya ne da Mansur da Daddy suka kwana anan Gidansu Rumana,Washegari kuma Sai da suka Fara Biyawa ta Gidansu Mommy aka gaiggaisa kana Suka wuce Filin Jirgi Daganan suka Shiga Jirgin Kaduna,Rumana Da ita akaje Rakiya sai dai ta Fahimci Diza ta Dauke mata ba kamar Haduwarsu a Lagos ba sai bata kawo komai ba ta Danganta Hakan da kila gajiyace,Sun Rabu Cikin aminci Umma da Abba nata Godiya Mansur ya karbi Lambar Rumana yace Dayaji Ciwin kai zai kirata ya Dauketa Personal Doc dinsa sai Dariya ake a kaduna suka sauka Motor Haya kamar yadda sukayi a zuwansu suka Hau Zuwa Zaria Wajen mangariba suna Gida Hankalin Abba da Umma ya kwanta da suka yi waya sukace sun sauka Lafiya kowa Gidansa ya Nufa Domin sauke gajiya sai dai Baba Habibu ya Dawo ya iske sun Dawo Daman bai da Mtsalan komai Megadi gidan Daddy Mama Fadime ke bama abun karinsa na safe da Abinci Dare in ya Dawo Daman Mommy Ta bar mata Sallahu

Sai da Safe Baba Habibu ya Shiga yayi ma su Daddy barka da Dawowa Daman Ya kira Abba awaya ya Tayashi Murna Tun Ranar.

Kafin Barowar Daddy Sokoto sunyi mgana Sosai da Abba kan Rumana ya gayamai yana son Tayi aure,Damuwarsa Daya bata da wani Tsayayye,Daddy ya nusar dashi da kuma Shawaran kada ya matsa mata sai Ta Fito da Miji ya Cigaba mata da addu"'a Allah zai Fito mata da miji nagari kada ya Damu anan ne yake Tambanyanshi Diza fa Daddy yake gayamai ita ai suna Hashashen sun Daidaita da Mansur nan ya gayamai duk yadda ake ciki Abba yace Tabbas ko bai Furta ba akwai Soyayyar a Tsakaninsu,Daddy yace Dukkanmu Haka muke Tunanin Iyayansu Mata ma sun Dade suna Zargin haka sai dai kasan yaran Zamani gwara abari su Furta sai ayi komai Cikin Farinciki,Sun Rabu kan cewa Duk yadda ake ciki zai Kirashi ya gayamai Domin shima ya gayamai Baya son Diza ta Fita wannan Shekaran bai aurar da ita ba.

Sati daya da Dawowarsu Daga Lagos Bikin kanwar Mansur yazo Tafiya ta kama Dole Mommy Bata je ba ammh Da Diza aka Tafi da Hajja da  Balaraba da Aiya wacce Tace sai taje Ranar Daurin Aure kuma Mansur da Daddy da Baba Habibu da Kawu Usman suka taho aka Daura aure Dasu Aranar suka Juyo Daman Mansur yana da Taro Washegari bai kwana ba Dayake ya zo garin kafin Bikin har ya bada Duka Kudin Kayan Dakin Sakinan A Maruka suka kwana Daya Suka koma Ririwai suka kwana Daya,Duk da Diza tasha zuwa Saboda Tana Rako Mansur in zai Taho Diza Taga Busharan da aka so a likama Abun sonta Duk da Taga yanayinta Sai da taji Kishinta itafa bata kaunar Wata Mace ta Rabi abunda take kauna Sam,Sai washegari Daddy ya Turo da Direba ya Taho ya Daukesu suka koma Zaria Mastur kuwa Daman yace bazai samu ba,bai gaya musu bane bashi Da Lafiya Ciwon ya kara kwantar Dashi wannan karon dai bata kaishi asibiti ba sai agida Likita yazo ya Dubashi gwajin Farko ya Tabbatar mai ya kamu da Haawanjini shi bai ma yi mamaki ba Domin yasan ko Ciwon Zuciya akace yana Dashi bazai musa ba akwanakin yana ji kamar bazai iya Wannan Sadaukarwan ba yana ji kamar zai gaza sai dai kuma karfin Halinsa da Juriyansa sun gaza Ya nuna Rauninsa.

Dalilin haka yasa ya Fara Rubuta Labarinsa da Soyayyarsa da Diza Tun Ranar Daya Fara sonta acikin wani karamin Diary dinsa Dayake Rubuta Muhimman abubuwansa,In yana Rubutawa yana jin Sauki acikin Ransa,Shiyasa yake Rubutawa ammh yana mai Boye mai kyau Domin baya Fatan wannan mganar ta Fito har wani Daga Cikin Ahali yasan da ita.