16
[12/23, 7:02 PM] Janafty: SADAUKARWAR SO..!!
(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)
Wattpad:@Jamilaumar315
Mallakar:Jamilaumar(Janafty)
Page1️⃣6️⃣
"Shuru Daddy yana ta jiran kiran Mastur kan mganar da sukayi zuwan da yayi mganar auransu Shi da Mansur ammh shiru bai jisa ba yayi mai uzuri saboda baida Lafiya kwanakin baya ammh ai yanzu ya samu sauki.
Mommy ne ta Shigo Falon Tana Dauke da kofin Coffea har ta isa gabansa bai sani ba,Sai da taja Center Table din gabansa ta Dora Kofin Tangaran din Tana Fadin"Alhaji lafiya kuwa..?
Ajiyar rai ya saki yana Fadin"Bani Coffea din.."Daukowa Tayi ta mikamai ya karba ya fara sha Gefensa ta Zauna Tana kallonsa Dago kansa yayi yana Fadin"Ina khadija..?
Mommy tace"Tana Dakinta.."Kai ya gyada yana Fadin"Mastur Shuru bai nemeni ba..Kuma bai zo ba.."Mommy tace"Topha..wani abu ne ya Faru..? Daddy ya ijiye kofin Gabansa saman Center Table din yana Fadin"Kan mganar auransu ne Asiya..Tun Zuwan da yayi mukayi mgana Dashi kan su Fito da Matan Aure Duk da Mansur yace akwai wacce yake so Tuntuni shifa..? Munyi mgana da Mallam Habibu shi kanshi ya kosa yaga kowannensu ya mallaki iyalinsa na kansa"Mommy tace"Hakane kam..Ai iyali Shine mutum..Toh Shi Mansur waya ce yana so..?
Daddy ya Dauke kai yana Fadin"Bai Fada ba..bansani ba..Yadai ce zai Fadama yayansa.."Mommy Na yar Dariya tace"Ai ni nagaya Tuntuni...Mansur Har gida Za"ayi da Diza.."Daddy ya Kada kai yana Fadin"Tunanin ku kenan..! In kuma ba ita ya Zaba bafa.."Mommy tace"Ai itama zai Zaba..In sun Boye Kaunar Dake Tsakaninsu mu ai basu isa su Boye mana ba.."
Daddy bai kara mgana ba illah Wayarsa Dake gefensa Daya Dauko yana Laluban Layin Mastur Sai da tagama Ringing bai Daga ba sai bai kara kira ba ya ijiye wayar ya Cigaba da Shan Coffea dinsa yana Sauraran Hiran da Mommy kemai kan Hujjansu na Soyayyace mai Tsanani Tsskanin Diza da Mansur bai ce mata komai ba Shima anashi Tunanin Hashashensa kenan Har Baba Habibu sai da ya Fadi haka Allah yasa dai Tunaninsu ya zama Daidai da Tunanin Mansur.
Kamar Minti Goma Tsskani da Kiran Mastur sai gashi ya Biyo Bayan kiran Daddy ya ijiye abunda ke Hannunsa ya Daga Kiran da Sallama Daga chan bangaran Mastur Daya Fito Daga Wanka Ruwa na Diga ajikinsa bai Tsane ba ya Zura Jallabiya mai Ruwan Toka,Sallar Isha"i yake son yayi Data kubcemai sai Shafa'i da wuturi yake da Niyyar yi sai yaga kamar wayarsa na Haske Dayake ya sakata a Silent ne,yana Dubawa sai gaya kiran Daddy,bai Daga ba sai ya Tada Sallar sai da yayi sallar Isha"i yana Zaune kan Darduma yabi bayan Kiran Daddy gabansa na Faduwa.
Bayan sun gaisa da Tambayan Mutanen gida,Daddy ya Tambayeshi jikinsa da kuma aiki yace komai lafiya Daddy ya gyara Zama yana Fadin"Mastur ya najika Shuru ne..? Mastur yaji Faduwar gaba Cikin Sanyin Rai yace"Shurun mene Daddy..? Daddy yace"Kan mganar da mukayi kwanaki mana mganar Auran ku kaida Mansur..Kun kai mun zali kuma zaman hakan bai dace ba.."
Mastur yaji wani irin yam acikin jikinsa cikin wani irin Yanayi da kuma Dauriya Da Sadaukarwa yace"Daddy ai Mansur ya gayamin Diza yake so.."Daddy ya kalli Mommy yana Mirmishi yace"Alhamdulillah..Dama Hashashenmu kenan Allah yasa albarka..Kai kuma fa..? Kana da wacce kake so ne..?
Mastur Dayaji wani irin Shock acikin Jikinsa kenan kowa yasan suna son juna Shine bai sani ba..! Allah ya gode maka da Yasani Tun kafin ya Furta yana sonta Da bai iya yafe ma kansa ba in har ya Fara Takara da Abunda kaninsa ke so,Cikin Karfin Hali ya Bude baki yace"Babu Daddy..Ni bansaka aure nan kusa ba..Amin hakuri zuwa gaba.."ya karishe Fada yana Jingina kansa da Bango Jinsa kamar zai Fadi yana Daga Zaune,zuciyarsa Tana wani Zafi kamar Zata kama da wuta.
Daddy yace"ba mganar ayi maka hakuri Mastur..Mansur fa kaninkane..Kai ya kamata ka farayi kafin shi..Tunda abun ya zama haka ya zama Dole kaima ka Fito da matar aure a Hadaku Dukkanku mu aurar daku Rana Daya.."Mastur yama kasa mgana sai maida Numfashi kawai yake Har sai da Daddy yace"Mastur Lafiyanka kuwa..?
Cikin Dafe kansa yace"Bakomai..Daddy adai kara min Hakuri ban da Wacce nake so..Ban kuma san a ina zan samu ba.."Daddy yayi Dariya yana Fadin"Baka dai Nema ba...In da ka nema zaka samu mana..Yanzu dai ka Kokarta ka Shigo wannan Satin sai muyi mgana Gabadaya.."Mastur Daman yana Cikin wani Hali Da Sauri yace"A"a Daddy basai nazo ba.."Daddy ya katseshi da Fadin"Sai fa kazo...mganar kuma wacce kake so kafin kazo ka Duba ina son inji Labari mai Dadi in kuma babu Ni ina da wacce Zan Baka ka aura wacce nan gaba Zaka Dawo ka Godemin.."
Mastur yaji kamar ya kurma Ihu saboda mganar Daddy ammh kuma bazai iya mai gaddama ba,Kansa kawai ya Sunkuyar kamar yana gabansa yana jin yadda yake saramai Shi dai Toh kawai yace bai ma san Sadda Daddy ya Datse kiran ba Kamar ya kwanta anan kasa yayi ta kuka da Birgima haka yake ji Saboda ya samu Saukin Nauyin Dake Cikin Zuciyarsa ammh kuma yakasa kukan Zucci da Yawan Tunanin Dayake yi suna karamai Rashin Lafiya da Rashin Natsuwar Zuciya wanda baya Fatan haka ya Shafi Lafiyansa da karfin Gwiwansa.
Daddy na gama Waya da Mastur ya kalli Mommy yana Fadin"Hashashemu ya zama gaskiya..Mansur dai yar gida Za"ayi da yarki Khadija.."Da sauri Mommy ta Washe baki Tana Sakin guda Daddy yana Dariya yace"Shi Mastur yace bai da wacce yake so kuma baisan ina zai samu ba.."Mommy tace"Kaji wani Zence..? Kamar sa ne zai ce ina zai samu mai Sonsa..!?
Daddy ya mike yana Fadin"Ki barni dashi..In yazo ban ji wata mgana ni Zan Samo mai wacce ta Dace dashi.."Mommy Ta Bisa da kallo Tana Fadin"Wacece ta Dace dashi Alhaji..? Yana Shiga Cikin Bedroom dinsa yace"Nima bansani ba Tukunnah.."Daga haka ya Shige ya barta Tana Tunanin wacece bata bama mganar Muhimmanci ba Ta koma Murnan Abunda Daddy ya gayamata Bata Bakinciki Domin Mansur ya auri yarta Daman Ta Dade Tana Hangen Dacewarsu da juna ba Tun yau ba,Kamar tatashi taje Ta gayama Diza sai kuma ta kwabu kanta tace yaran Zamani yanzu haka kar suke kallonmu Farinciki yaki barin Ranta Taso ta Kira Hajiya Farida Ta gayamata abub Arziki sai kuma Taga Dare yayi ta bari sai gobe Tashi Tayi ta Tattara kololin abincin da Daddy ya gama ci ta Kai Kitchen dim kasa da Mama Fadime suka Hado suka ma Juna Sai da Safe Dakin Diza ta Leka Ta iske tayi barci Wayarta Ta Fadi gefe Dariya Tayi ta Shiga Dakin ta gyara mata kwanciya ta Dauke mata waya ta Dora saman Side Drower din gadon ta KasheMata Wutan Dakin ta Fito Bayan taja mata Kofa Sama ta Haura zuwa Falonta sai da ta Rage Hasken Falon kana ta Tura Kofar Bedroom ta Shiga ta maida kofa ta Rufo.
****
Bangaran Rumana kuwa Ta shiga Tashin hankali na Damuwa na Rashin ganin Amsan Sakon Mastur Zuwa gareta,bayan ta Riga ta gayamai Sirrin Zuciyarta Wanda kuma Batayi nadama ba,abun yaki barin Ranta Ta shiga Damuwa Rashin Sanin makomar Soyayyarta.
Gashi Bayan Dawowarsu Daga Lagos Mas"ud nata kiranta Bata san ina ya samu Lambarta ba,ya riga ya gayamata Sirrin Zuciyarta kuma Ya gayamata He is Ready,aure yake so in har ta bashi Dama zai gayama Mahaifunsa Ita ta Dakatar Dashi Ta gayamai akwai wanda Take so ammh bai Hakura ba kiran Safe Dabam na Dare dabam yana Beging dinta Ta soshi Text kuwa baya gajiya na kalaman kauna Gareta,Ammh bata Taba maida kai ba Bashi bane agabanta Wanda Take son wannan Kulan Daga gareshi bata son makomarta ba,abun ya Dameta yau haka Tatashi Sukusuku aikin Dare tayi Wato Call,Sai wajen 7am na Safe ta baro Cikin asibitin a Motar ta Zuwa Gida Ta gaji Ga barci acikin Idanuwanta ga Damuwa sai taji kamar ta Kirashi sai kuma ta kasa batasan me Zata ce mai ba ko Sirrin Zuciyarta Dakyar ta iya Fadamai shima Sakon Text masages.
Haka ta shiga gida Tana layi saboda gajiya da Barci,Da juma ta Fara cin karo Ta gaisheta da kwana bata iya amsa mata ba ta mika mata Karamar jakar hannunta da Lapcaot dinta Ta Haura Sama Juma ta Biyo bayanta Zuwa Dakinta Tana Shiga gado kawai ta Fada tana jin kamar kanta na Sara mata nan Saman gadon juma ta ijiye mata kayan ta Fita zuwa Kasa Kitchen ta shiga Domin Hadama karamar Hajiya Abun karyawa.
Rumana ta Dade kwance kafin Tatashi Tana Rangaji ta Fada Tiolet Tayi wanka Tazo ta Shafa Lotion dinta ta Sauya kaya zuwa Saukakkiyar Doguwar riga,Koda taFito Har Juma ta Hayo mata da Breakafst dinta Tea kadai tasha Ta Fito Daga Dakin Zuwa Falon Ummanta ta same su ita da Abba suna karyawa nan ta zauna kusa da Abbanta Tana gaishesu da kwana suka amsa mata Cikin Fara"a da soyayyah.
Umma ce ta kalleta Tana Fadin"Lafiyanki kuwa Ruma..? Naganki kamar baki da lafiya..? Rumana ta Sauke Idanuwanta Cikin gajiya Tace"Bakomai Umma..Gajiya ce Kawai sai Dan Ciwon kai dana Dawo Dashi.."Da Sauri Abba ya Dafa Kanta yana Fadin"Ayyah Sannu..Tashi kije Ummanki Ta baki Mgani kisha zuwa anjuma in bai sauka ba kije kiga Likita.."Umma ta mike Tana Fadin"Bari na Dauko mata panadol,tasha..Gajiyan Aiki ne Da Zirga Zirga.."Tafada Tana Shiga Cikin Bedroom dinta Sai gata Ta fito bata Dade ba,Ta mika ma Rumana panadol din Ta karba Lokaci Daya Umma ke Fadin"Kin karya..? Rumana ta gyada kai Tana mikewa Tace"Bakomai fa Umma..Call din ne ke Wahalardani baka samun yi barcin kirki.."Abba yace"Watarana sai Labari Rumana..Allah ya bada Lada.."Umma na Zama Lokaci Daya Tana Dariya Tace"Ameen dai..Ammh fa Gwannati na Biyansu Alhaji.."Shima Dariyan yayi yana Fadin"Duk da haka Aikin su na Taimakon al"umma ne.."Rumana na jinsu bata ce komai ba ta Fice suka Rakata da Ido Cike da Tsausayinta da Kaunar Diyar nasu Tilo Dasu ka Mallaka.
Rumana na zuwa Daki Ta Sha panadol ta kwanta Sai barci Bata Tashi ba sai wajen 10am na Safe wanka ta sake yi Taji tana jin yunwa ta fita zuwa Kitchen Ta Hada Complex ta Dawo Daki Bataji Motsin Goggo Jummai baTafi Tunanin Tana Dakinta ta kwanta Sama ta Haura Tana Tunanin sai Zuwa anjuma Zata Shiga ta Dubata.
Kan gadonta Ta Haye da Mug din Da Cokali Tana shan Complex din a Hankali,Lokaci Daya ta Jawo wayarta Tana Latsawa Kiran Basma Tagani Lokacin kila Tana barci ne,Kiranta Tayi suka gaisa Ita Basma a Zaria Abu Take Intenship dinta Labari sukayi kadan kafin suyi sallama Kurama wayar ido Tayi Tana wani Tunani bata son ta Kirashi Bata da abun Fada sai kawai ta yanke Shawaran Turamai Sako da Sauri Ta ijiye mug din hannunta saman Side Drower din Gadonta ta Fara Rubutamai Sako.
Salam ya Mastur How are u Doing..? Kaga sako na baka ce komai ba..? Ko baka sona ne..? Kuma ban yi maka a mtsayin irin Macen Dakake Muradin ta Zama Abokiyar Sirrinka ba nan gaba..Plz ka Fadamin mtsayina awajenka..Nidai kaji Sirrin Zuciya Am in love wit U..Bazan iya Rayuwa mai cike da Sukuni Da Jin Dadi ba in baka..Plz Help ur Sister Rumana Muhammad Wamako...
Tana gama Rubutamai ta Turamai Cikin karfin gwiwa ta koma ta Kwanta kawai jin komai ya Daina mata Dadi wayar na Hannunta Tana Bukatar amsar ko Cewarsa So take ta Dakatar da Mus'ab kafin ya Sanar da Mahaifinshi mgana ta Dawo kunnin Abbanta Tana da Tabbanci bazai mata auran Dole ba ammh kuma bazata iya mai gaddama akan komai ya Umarceta ba.."
Suna Tsaka da Meeting yaji Shigowar Sakon Rumana bai Duba sai da suka Tashi Daga Taron ya kuma Office dinsa ya Zauna kana ya Duba Sakon nata kalamanta sun kara kashemai Jiki kamar wani mara Lafiya,Gabadaya yau yazo dai Office ne ammh bayajin zai iya yin wani aiki kasala Duk ya Rufeshi da Nauyin Zuciya Shi yama manta da Sakon ta Domin Halin Dayake Ciki yafi Tunanin Rumana sai da yaga Sakonta ya Tuna da ita da Abunda ke Tafe da ita.
Kansa ya Dafe yana Tunanin Rumana Zata Kara Sakashi Cikin Wani Halin Daya ke Fatan fitansa nan kusa sai dai kalamanta sun kashemai jiki Sosai Yasan Zafin so da Dafinsa Tunda yana cikinsa Har yanzu bai kai ga Fita ba in yace Yana Sonta Domin ya Farantamata ya Cutarda ita..Zuciyarsa bata da wani Wajen da Zata sakata Har Abada Bazai ce Rumana ba ta Cika macen da kowani Namiji zai iya mallakanta ba No Rumana mace ce Kin kowa kim wanda ya Rasata sai dai ba ita Zuciyarsa taso ba Bai taba kallonta da wani Siga ta Soyayyah ba Kada ya barta Jira ya kasa maida mata da amsa sai da yaga wunin Ranar Kiranshi ta Dingayi Sai da ya koma Gida Bayan yayi wanka yayi sallah kana ya Dauko Wayarsa ya Rubuta mata sako.
Wslm..Rumana ya aiki..?Ko Daya Taya zan ce bana sonki.? Alhalin kin mallakin Duk Abunda wani Lafiyayyan Namiji yake nema wajen mace..! Kawai dai bana so ki shiga Damuwa ne Saboda ni ko ki zauna kina Bata Lokacin ki akaina..Ni ba yanzu Zanyi aure ba Rumana..Kiyi Facing din Reality dinki Ina Miki Fatan alheri Arayuwarki..Mastur Habib Doguwa..
Yana gama Tura mata ya Kashe wayarsa ya koma ya kwanta yana Jin kamar bai kyauta mata ammh kuma Hakan shine Daidai.Inhar ya amsa mata yayi mata karya kuma yaci Amanarta yagayamata yana sonta ahalin bai taba sonta ba auranta ayanzu Tamkar wani Nauyi ne Za"a Doramai akansa Wanda kuma Faruwar hakan kamar wani babban al'amari ne na ganin irin Halin Dayake Ciki na Kokarin Binne Diza Daga Cikin Ransa.
Rumana kuwa Lokacin Data ga Sakon Mastur Kamar ta Suma Saboda bakinciki Ta Takaichi Tayi kuka awannan Daram har ta bama uku Lada Kenan ya Mastur baya sonta..? duk irin Tarin kaunar Da take mai..? Sai wata Zuciyar tace mata a"a ba haka yace ba yace ne kada ya barki kina Jira Ba yanzu zai yi aure ba Tuna haka yasa taji Sanyi aranta Tayi alkawarin Zata iya Jiransa ko nan da Shekara Goma ne in dai zai aureta Bazata Damu ba Koda gari ya waye Ta Shiga Dakin Umma gaishe su ita Abba sai da sukayi mganar Kumburin idonta sai tayi karyan Da Safan ne Wani abu ya Fada mata Abba yace in ta isa Wajen aiki ta bada a Dubata Inda wata matsalan tace to,allah ya taimaketa aikin Safe gareta 2pm zata Dawo Gida sai abun yazo mata da sauki ammh ko achan asibitin Sai da abokan aikin nata suka Fahimci ba Lafiya ba saninta mai kazar kazar da Zafin nama ammh yau ta zama wata so Silent da ita.
******
Duk yadda Mastur yaso Zillema Zuwa Zaria hakan bai samu ba Domin Bayan Kiran Daddy Baba Habibu ma ya kirashi yakaramai mgana bashi da Wata Mafita na Shiryawa ya Tafi Zaria Ranar Friday yabi Jirgi Zuwa kaduna Daga chan ya Kira wani Sargent Dake aiki nan Headquater yan sanda ta Jahar kaduna ya Daukeshi amotar Aikinsu Zuwa Zaria,wajen 9pm na Dare ya iso bai gayama kowa ba sai da suka gansa kwatsam Adaran Sargent din ya koma Kaduna.
Mansur da Hajja Haka suka Tasa Mastur gaba suna Tambayansa Wani irin Ciwo yayi ya Rame haka..? Yayu baki kamae wanda yaShekara yana wata Cuta Aiya ma ta kasa mgana Baba Habibu ma bai ce komai ba ammh Shi kanshi yasan Dan nashi ya Rame duk ya Lalace sai kashin Wuya da kwarmin Idanuwa ammh Dai bai yi mgama ba Mastur kuma Sai yace yanayin aiki ne ammh Lafiyarsa kalau ko da Gigi bai Fada musu ya kamu da Hawan Jini Saboda baya son a Mtsamai sai an ji Dalilin kamuwarsa da Ciwon yana Matashinsa mai kananan Shekaru.
Sai da asuba suka Hadu da Daddy a masallaci Shi kansa sai da yayi mganar Ramar Mastur yace Gaskiya zai bincika in za"a iya mai Trasfer ya bar kudu ya Dawo arewa ammh Mastur yace A"a domin abaya ne yake son Zama kusa da gida banda yanzu da komai ya Riga ya Lalace Daddy yayi mgana da Baba Habibu kan zuwa anjuma zasu Hadu dukkansu nan Falon gidansa su Tattaauna da Haka suka Rabu Shi kanshi Mansur bai ji Dadin Ganin yayan nashi haka ba Duk da ya san sa Miskili ne ammh wannan karon Miskilancin nashi ya karu Sosai Sai ya Shige Daki baya Fitowa Ko Falon Hajja Daya kan Zauna wannan karon ko Sau Daya bai Zauna ba suna gaisawa yake Mikewa ya koma Shashensu Mansur kuma Baya samun Zama Saboda Zabe ya kusa suna ta Shirye Shirye in ya Dawo kuma da Daddare Domin su zanta Daya Fara mgana sai Mastur din ya Fara Hamman karya kamar yana jin barcin in yaga haka sai ya kyaleshi yana mai Uzuri saninsa agogo ne Sarkin aiki Shi kuwa Mastur gujema mganar Diza yake bayason Ya bar wata alama da Za"a Fahimci wani abu.
Aranar Diza bata nan Tana kaduna sun je wani Training ne na Koyon Wasu Snack din kayan Fulawa Wajen Kwana uku anayi kullum sai taje kaduna ta Dawo Ranar ne na Karshe sai Gabda mangariba ta iso Gida ita bata ma san Mastur yazo ba Mansur ne ke gayamata kuma suna Dan Jumawa basu Hadu ba Zabe ya kusa kansa yayi Zafi baya zama agida,Watarana ma Baya kwana agida yakan kwana agidansa Dake GRA wanda ya mallakeshi Lokacin Daya Zama kansila Sai da sukayi mgana ta waya sama sama Shima din Ba Lokaci basu yi mgana ba kwana Biyunan sai Bayan tayi wanka Tayi Sallar mangariba ta Fito Falo ta Haura Saman Wajen Mommy Tayi mata Sannu da gida anan ne Mommy ke Fadamata akwai Zama Yau da Daddare inji Daddynta.."
Diza ta kada kai Cikin mamaki Tana Fadin"Mommy wani irin Zama kuma..?kuma dawa dawa..? Mommy tace"Kanmganar ku ne keda Mansur..Sai Mastur..Zama Kuma da Duka Iyayanki mana.."Diza Taji mamakin abunda Mommy Tace Cikin Dubanta Saka saka tace"Mganata ni da Mansur kuma Mommy..? Wata mgana..?
Mommy Data ga Kamar Diza na Raina mata wayau ta Harareta Lokaci Daya ta Mike Tana Fadin"Bansani ba..Kinga In kin Sauka kasa ki Fada Fadime ta Shirya komai da wuri Alhaji ya kusa Karisowa.."Tafada Lokaci Daya tana Shiga Cikin Bedroom Dinta.
Galala Diza ta Bita da kallon Bata gane inda ta Dosa ganin ba wanda zai gayamata yasa ta Zakuda Kafada ta Fice Zuwa Falon kasa,Tana Latsa wayarta,Kitchen ta Shiga suka Gaisa da Mama Fadime ta gayamata sakon Mommy kana ta Fice Zuwa Dakinta Duk yadda Taso ta manta da mganar ta kasa Lokaci Bayam Lokaci abun na Fado mata sai da Merry ta Kiratanr suka Fara lissafinsu Kana Ta saki mganar suna gama wayar kuma ana Kiran Sallar Sai ta tashi Daman Tana da alwalanta ta tada Sallar Tana Idarwa Ta zauna nan kan Darduma Tana Addu"a Lokaci Daya kuma Tana Tunanin wani irin Zamane Mommy Take nufin Za"ayi a kansu..?Rashin samun amsa yasa ta Jawo wayarta Ta Kira Mansur ammh bai Daga ba sai ta kyaleshi gefen gadon ta Zauna ta Rafka Tagumi haka kurum Take ji Jikinta Duk ba Dadi da Faduwar gaba.
Tana nan Zaune Tayi Nisa a Tunaninta Taji mganar Daddynta ya Dawo chan kuma Taji Muryan Hajja suna gaisawa da Mommy Taji kuma mganar Aiya Data Mansur bata dai Taji ta Mastur din ba Bata Dauka ma ya Dawo ba,Zuruf ta Mike Jikinta na Rawa Daidai Lokacin da Wayarta Ta shiga kara Tana Dubawa Taga Mansur ne Gabanta sai ya Fadi ta kasa Daga Kiran Har ta katse Haka kurum Tunda Taji mganar Mommy Gabanta ke Fadi Ta na nan Tsaye Taji Shigowar Mommy Dakin Tana Fadin"Diza ki Fito Falo..Ana mgana.."
Zuru Diza Tayi mata da idi Ita kuma Mommy bata gane ba ta Dauka irin kunyar nan ne na Mata Mirmishi kawai Tayi Ta Fice Tana Fadin"Ja"irai Daga ke Har Mansur din.."Diza bata jita ba ita daj jikinta ne yayi sanyi Da Hijabin Sallar Dake Jikinta TaTaka ahankali ta Fita Zuwa Falon Tana jan kafa sai dai Tasha mamakin ganin Mastur Zaune Gefen Mansur,Sai Baba Habibu kan kujera kusa da Daddy sai Mommy agefe Chan Nesa Ita da Hajja Wacce ta saka Hijabi Sabanin Mommy Data saka Mayafi Aiya kuwa na Kujeran mai kallon su Daddy.
Kafafunta Taji sun fara rawa Tunda ta Fito Falon Mansur ya kafeta da ido yana Mirmishi Mastur kuwa da gabansa ke Faduwa bai iya Dago kansa ba Hailala kawai acikin Ransa Allah ya Rufamai asiri kada yayi acting din da za"a gane He is Love with Diza Shiyasa bai ji ma Sha"awar kallomta.
Aiya ce ta kirata tace tazo ta Zauna kusa da ita shi ya bata kwarin gwiwan karisawa ta Zauna Wajen kafafunta Lokaci Daya Tana gaida Baba Habibu da Hajja Mansur Dake kallonta ta Kallah sai taga yau yana mata wani irin kallo Mastur kuma bazata ce komai akansa Ba Domin kansa yana kasa ne ko Motsi ya kasa.
Daddy ne ya Bude Taron da addu"a kafin ya Kora da Jawabin Abunda ya Tarasu ya Karishe da Fadin"Kai Mastur kai ne Babba Ta kan ka Zan Fara Yaya muke ciki..? Ka samo Yarinyar da zaka aura..?
Dam gabansa ya Fadi Lokaci Daya Dana Diza Data Dago Tana kallonsa Lokaci Daya Tana Zare ido,Mastur kuwa kansa na kasa yakasa Dagowa Dakyar ya iya Muskutawa ganin Kowa Shi yake jira yace"A"a Daddy..Ban samu ba.."Daddy yace"Kaji Aikin ko Habibu..? Baba Habibu yace"Mastur ai Halinsa kenan komai Sai yace bai Duba ba..Bansan yaushe zai saki Jiki da Mutane haka ba.."
Yafada yana kallonsa Mastur kuwa kai ya kara Saddawa gabansa na Faduwa,Kai Daddy ya Jinjina yana Fadin"Bakomai Tunda kai baka Duba ba..Ni zana Duba maka na samo maka wacce ta Dace Dakai.."Mastur dai bai ce komai ba Aiya ce Tace"Da hakan ma akayi..Domin Dagani ai megidana baya kula kowa.."Diza kuwa ji Tayi kamar Ta Suma Saboda Zafin kishi Dana Zuciya Mastur din nata ne ake mganar an zabamai mata bata Dawo Cikin Hayyacinta ba Taji Daddy na cewa"Duk da Mansur ya Turo Yayansa Mastur ya gayamin Zabinsa.Ban yi Musu ba sai dai gashi gamu ya Sake maimaita abunda yace ma Dan"uwan nashi.."Sai kallo ya koma kan Mansur ita Diza ma Lokacin Ta Daina Fahimtar komai So take ta Mike tayi mgana ammuh kuma Jijiyon jikinta sun saki.
Mansur ya Zunguri Mastur Dake zaune kamar mutum Mutum Tunda ya sadda kai Kala bai ce ba Kansa na kasa yana Fama da Zuciyarsa wajen Raunin Datake so ta bayyana.
Cikin Rada Mansur ya Sunkuyo yana Fadin"Ya Mastur ka Fada musu.."Mastur ya kalleshi da Lumsassun Idanuwansa masu cike da Damuwa yace"Ka gaya musu da kanka..!.
Daddy ne yayi gyaran murya yana Fadin"Mansur kayi mgana mana..?duk da Sunsan mganar suna Bukatar kara jinta Daga bakinsa.
Kansa ya maida kasa Bayyan ya kalli Diza ita kuwa So take taji wayake so Wacce bata Taba saninta ba Alhalin basa Boye ma juna komai kamar a mafarki taji yace"Baba Daddy..Ni ba wacce na Dade ina son acikin Raina sai DIZA ita nake son Aura ta zama Matata.!
.
Diza Dataji mganar kamar saukan aradu akanta Ta Zabura Ta mike Dafe da kirji bayan Tayi Cilli da wayarta Mommy kuwa da Hajja da Su Daddy Sai Washe baki suke Mastur dake duke bai Dago ba yana kokarin Sarrafa kansa yaji muryan Diza da karfi Tana Fadin.
"A"a..Kada muyi haka Dakai Mansur..Wata Dizan ni..? A"a ni ba Soyayyah muke ba..A Dan"uwa Amini na Daukeka Mansur kar ka Hanani mallakan mafarkina..Tun Bayan Dana Mallaki Hankalin kaina Na Fahimci ba wanda nake so Sai YAYA MASTUR...!