37
by @surayyahms
ABUNDA KE ƁOYE💫
arewabooks@surayyahms.
To All my group members i heart you❤️💋
⏯️3️⃣7️⃣
tanajinta daf dashi atake wani irin sihirtaccen ajiyan zuciya ya kufce mata inda atake qamshin jikinsu ya gaurayu dana juna yanamai fidda wani irin shauqaqqiyar qamshi me kara sautin bugun zuciya...
tsikar jikinta duk suka miƙe, jin nauyin mayun ruwan idanunshi daya kafa matasu akanta yana wani irin kallonta camly da kasala atattare dashi, tareda browsing halittar jikinta da sassanyar ruwan idanunshi masu masifar kashe gabobin jiki da jefa zuciya cikin wani duniyar garari..
bugawa kirjinta yake kamar zai ballo waje, gabaki daya taji ta kasa daga ido ta kalleshi dan kusancin dake tsakanin su yasa take jiyo yadda kirjinsa yake bugawa da karfin gaske..
karamin gyaran murya yay muryansa na fita kasa kasa yace malama sai yanxu kikaga aikan nawa?da kyar ta iya dago rikitattun idanunta ta kalleshi ta marairace murya tace"..i was thinking abt what u may like to eat shine yasa banyi sauri ba..dan karamin scoff yy da cute kamemmiyar smiles dinsa yace okay, toh Deceive me mana!! i knw ure not thinking abt me,ure just busy with ur friends!hmm su, kawar amarya manya! dada sunkuyar dakanta kasa tay cikin turo mai baki ahnkl tace "yaa toh me zan kawo maka kace kanajin yunwa..atakaice yace mata 'something fresh, pancakes or anything but freshly made ko kina wani abune na katseki..da sauri tace "a'a..i am, sai tay shiru, ahankli kuma akunyace tace...anything for you! tana fadin hakan ta miƙe tsaye ganin har yanxu mayun idon sa nakanta tace "i wll be back in 7minutes,..adan kasale ya gyada mata kai..
..wayanta ya hango kusa dashi kmr zai ce mata ta dauka but somthing deep in his hrt force him to keep quiet haka ta fita batay noticing cewa tabar masa wayarta a gefensa ba....
tana fita ya jawo wayar yanayin haske wani hadadden hotonta yagani akan screen din wanda yadau lokaci idonsa na kan hoton baiko kifta ido ba
daga kitchen kuwa ayaana tana shiga ta bude inda ammi take ajiye kayan su hadin pancakes din cos ammi has almost everything in stock wai indai na dafa abinci ne is like cooking is one of her favourite thing a duniyan nan, within minutes ayaanah ta gama kwaba cinnamon pancake with all the love in her heart
batay amfani da sugar ba tasaka masa pure honey da melted butter da asalin liquid milk da wani mayen vanilla flavour. sharply ta fitar da like 6 flaps of pan cakes a wuta, tana gamawa tasaka banana slices akai, tajera chocolate drizzle akn banana slices din carefully snn tabi kansu da pure honey in a stylish wavy drizzles, cikin nitsuwa ta jerasu akan wani white clean plate, atake cikin gaggawa ta dauki juicer ta zuba frozen straw berry ta hada fresh straw berry mint splash with just mint, lime da ice cubes cikin kankanin lokaci tasaka komi akan karamin tray tazo musu dakin nasa dashi...
karamin sallama tay lokacin hanklinsa yay nisa akan wayatta baima ji sallamn ta ba bare ya amsa ta, after 2-3 password trials he sumhow manage to use his name nd open her phone babu inda kuma baishiga ya leka ba sumtings make him go utterly speechless wasu kuma anan ne yagani yake shan mamakin su, like the amont of money da uncle moh yake tura mata, da flirt nd love text messages da mujaheed yake tura mata kowani safiya.
tunda ta leka ta bayansa taga wayarta ne a hannunshi gaban ta ya fadi kadan, how he opens it remain a mystery to her but dake tasan zucyarta awanke yake sai bata damu ba ta karaso, da karamin gyaran murya tace yaa ur food is ready ..qamshin pancake din yaji ya daga kansa suka hade ido ya mata wani irin kallon kishi daya dan tsorata jikinta a dan sanyaye ta taho gabansa ta aje plate din tanajin sautin saukar ajiyan zuciyarsa har yanxu baice mata komi ba da ido kawai ya mata alaman ta zauna kusa dashi tana zama yace" can u help me out with the food..ya nuna mata wayar dan ta gani dakyau.. yace i am busy here..karamin ajiyan zuciya tasauke ahnkli tace "sure...wanke hannunta taje tay ta dawo ta zauna kurkusa da shi, tana daukar pancake din tafara bashi a baki ahnkli yakeci har saida yacinye guda daya snn ya karbi abunshi ya fara ci dakansa yabi ya xuba mata ido yana kallonta da abubuwa aranshi yana tauna pancake din batare da ko kiftawa ba ayayinda ita kuma ta sauke kanta kasa tay shiru da fargaban me zai biyo ba in yagama karewa wayatta tanadi
Ya cigaba da tauna pancake ɗin a hankali every minutes zai juyar da ruwan idanunsa a kanta kamar wani mai karanta cikin zuciyarta
he was busy debating in his hrt, wani abu nace masa kodai ya kama kanshi ne ya basar, ko kawai ya fadi abunda ke cinsa acikin ransa, abazata kuma ya ajiye sauran bite din dake hannunsa a gefe yana jin bazai iya shiru ba, still yana kallonta da irin kallon nan da ya daɗe bai yi mata da wannan zurfin ba.
A hankali ya miƙar da hannunsa ya riko nata hannunn tare da jawo ta kurkusa da shi har saida taji saukar hucin numfashinsa yanamai malala akan kyakyawan fuskarta.
Muryarsa a kimtse yace
..“Ayaana…tana daga ido kafin ta amsa shi cikin kafeta da kallo yace meyene ke faruwa atsakaninki da mujaheed?
tambayar taji ya fado mata a jiki kamar an watsa mata ruwa mai sanyi. ta daga kai a hankali kamr tana son ta yi magana saikuma taji kalmomin da zata furtan duk sun makale mata a maƙoshi.
matsowa ya karay idanunsa tattare da wani irin launin kishi mai hade da rikitaccen kallo
yace“ madam i’m asking you
“Ki fada min… why is he messaging you good morning my heartbeat every day?..
Ayaana ta rufe idanu tana jin jikinta nayin wani kalar rawa rawa taciki da wani irin shagwabben murya ta buɗe idonta a hankali tace yaaa i dont know..kasan he loves to jokes abt things, ni kuma harga Allah babu abunda ke tsakanina dashi....Ta ɗan yi shiru, tareda matsawa kusa ɗashi sosai nan ya lumshe idonsa ajiyar zuciya mai nauyi yanamai kufce masa ya kura mata ido kamar zai shige cikin ta...ahnkli yace “So ke kince min baruwanki da kowa ko? let me ask you, if he was the one dat ask u to make this for him will you come nd give me? da sauri Ayaana ta girgiza kai a hankali tana dan wasa da yatsun hannunta duk ta kasa kallon cikin idonsa sai ya miƙa hannunsa ahankli ya ɗago fuskarta yasa ta kalleshin na dolen-dole. snn yace “Ayaana.”
kirjinta na bugawa tun kan yay magana tace " i swear babu wani abu dake tsakanina dashi yaya wallh dagaske nake.
A hankali ya janye numfashinsa daga can cikin zuciyarsa ya ce“if u cant give him this pancakes bcos is mine, then stop giving him nd other men what belongs to me for exmple like ur time. yana fadin hakan ya saketa Snn ya ɗauke pancake ɗin yakai bakinsa yana taunawa ahnkl cikin wurga mata wani irin kallon mallaka mai nunnake da shauƙin soyayya me narka jiki da zuciya.
ji tay kamar zata nitse a wajen dan kunya takasa cewa komi wani irin ruwan shauqaqiyar soyayyarshi taji ya lullumeta daga sama har kasanta yana mata yawo duka ilahirin sansanin jininta da jjiyonta yana mata rawa har acikin kwawalwa.
batace masa komi ba face murmushi datake sakewa a kunyace yana gama tauna na bakinsa ta dauki mint splash din ta bashi ya karba yace "thank you" ta gyada kai..yana sha yay hamdala yace..madam take ur phone..tana karba kasar wuyarsa yace nd pls stop cheating nd deceiving me okay..
karamin dariya ya kufce mata cikin sanyin murya tace yaa i am not cheating or deceiving u.
yace hmmm..toh naji..ya kalle agogon sa yace tunda na koshi yakamata muje waje ko
gyada masa kai tay ya miƙa ya jawo rigarsa ya saka itakuma ta tafara tattara empty dishes din.. kafin ta gama ya bude closet dinsa ya dauko wata karamar box dan karamin abun wuya ne aciki dats made of pure gold amma irin mai round neck innan ne kuma rare design me masifar kyau
bakaramin dacewa da kayan jikinta yay ba idonsa nakanta yace "hey..turn around.. tana murmushi ta juya masa, ahnkli
ya matsar da jelar suman ta yabi ya samata abun wuyar wanda ya zauna mata damas akan wuyanta yamata mugun kyau bana kadan ba....
gaban madubi tay ta tsaya tanamai admiring har ya karaso daf da ita yace"did u like it?da sanyin murna a muryanta tace "its perfect
..tana fadin hakan ta ciro wayarta batare da ya shirya ba ta musu mirror selfie cikin basarwa tay kmr bada niyyar ta sakoshi a aciki tayba, irin hoton bazatan nan ne dayay mugun kyau, cos he is wearing his grizzly brown shadda ita kuma chocolate brown material nd they look absoltely perfect nd in love. daga nan har suka fito musu sukeyi akan hoto tace mai sam abun wuyanta kawai ta dauka bashi ba..yayi ta nuna masa taqi sam har ya gaji ya kyaleta.
suna fitowa sarari kuma kamar basu ba, his face remain stiff nd emotionless ita kuma normal take tahowa agefensa dede kofar sashen falon hjya mairo ya tsaya ya leka ciki yace guys ya kamata mu wuce ko..
one by one su jamal sukay sallama da ammi karama, lkcin zainab arifah tashiga daki kara shafa powder sabida ji datay suna maganan wucewa tasan dolene ibaad zai fito she really want him to introduce her to his gangs of frends dataji sun bala'in burgeta sabida wankan ajinsu da swags dinsu na wealthy background
kafin su gama sallama da ammi karama su fito already ya sako ayaana agaba har sunje waje ta gaban motarsa suka tsaya...friends dinsa suna isowa wajen su taji ya kama hannunta calmy ya dada pulling inta by his side yadda zai basu clue she is his special sumone batare da ya furta ba, da sigar tsokana jamal ya kare musu kallo ganin dacewarsu a fili yasa yay murmushi me shegen sanyi yace "ohhh wow finally", da sanyin fara'a ayaana ta fara gaishe su, each one of them with calm respect kowa yagaya mata sunansa da kansa..kai tsaye yace mata these are my best frends..nd guys this is ayaanah...dariya me sanyi farhan yay yace "you mean 'the our ayaanah..ibaad yadan hararesshi prince hassan yace she is perfect!!
hajiya ayaana we are hoping to come for ur own celebration soon..mune kirjin biki aiko..
...murmushi me sanyi tay tadada boye fuskarta ata gefensa abazata tareda kankame hannun ibaad din nata cikin nata hannun sosai..
the air almost stand still nd heavy ayayinda uncle moh da taragon abokansa suka fito waje shima yafito rakasu atake atake yanayinsa ya canza dan baima iya basarwa ya bi ya tsaya cak yadan kuresu da ido, wutar kishi kamar zai fasa kwayar idonsa daya ga yadda ayaanah ta wani irin rike ma ibaad hannu shyly and lovingly kuma tana tsaya daf daf dashi kamr ma zata shige jikinshin daga tsaye...wanda ko kai makaho ne kasan dole ne da wani abu dat is going on awajen musm da abokansa suka famar nuna gamsuwar su da ynyin ayaana sosai..har jamal yanacewa wata rana zai kawo mata matarsa har gida suna gaisawa.
sabida wannan dan uban embrassment din yasa uncle moh yay saurin kauda kansa bai sake abokansa sun dago da wuri ba face Alhaj ameer da already yasan fuskar ayaanah a hoto atake atake jikinsa ya bashi cewa abokinsa baijin dadi kishi har ya sauya ma ruwan idonsa kala cikin rufa masa yay maza suka bar ta wajen suka fita can can waje
...yayi ta basu haquri wai amaryan tashi tayi nisa amma soon zai kawota har gidajensu agaggaisa.
suna rabuwa da aboknsa ya shigo gidan da bacin rai baiko kallesu ba ya wuce ciki ya kira mujaheed yace maza maza yaje ya kira masa ayaanah ynxun nan...mujaheed har yaji tsoro da irin tune din daya masa maganan..ya fito kenan sai ga zainab arifah ta fito a rude suna hade ido tace "hey dan Allah ina gayun nan sukayi? yace ohh ai ibaad yazo sun fita waje halama sun tafi
...da wani irin sauri ta kama hanyar wajen har tana haki tana kuwa hangosu da ayaana ta tsaya cak jin numfashin ta ya dena fita wani abu kamar mashi taji ya cakke ta dagata yadda ibaad ya wani makale ayaana agefensa hannunsa sakale da juna...at that moment da kallon banza na kisa da tuni ta kashe ayaana dashi daga inda take,saida ta gama kare ma yanayinsu kallo da kyar cikin fizgo kanta daga fushin ta karaso wajen su da wani irin murmushin makirci tace "hi..sauran suka mata kallo daya farhan ne kawai ya amsa ta.., tace har zaku tafi awwn..nd i tot we shud get to knw each oda more..tana maganan amma so take tazo kusa da ibaad sai taga ayaana ta daga ido tana kallonsa da wani irin shagwabben ido kusan babu hali takwace hnklinsa daga wajen ayaanah
...zatay magana cikin katseta jamal yace "whats dat ur name ma..anyways. sum oda time in munxo.. da wani irin kinibibi ta takune fuska tace but he dint even introduce us..da karfi tace ibaad...a dan shashance yace ohhh guys this is a cousin sister..prince hassan da already is very irked da kalar rawan kantan a mugun miskilance ya daga hanci sama yace "huhhnn i felt that. ta iya surutu kam, sannunki toh! farhan yadan yi dariya baice komi ba ya kalle ayaana with soft smiles a fuskanshi yace baby gal it was nice meeting u, ayaana tay mrmshi tace pleasures! wani irin rudani zainab arifah taji ya rufeta ta kasa gane komi sai tay shiru
...jamal yace guys ya kamata muje ko..shima ya kalle ayana yace madam we will meet at the dinner, yeah? ahnkli tace yeah..ta kallesu duka da sanyin murya tace thank you i raally apreciate..prince yace pleasues is all ours babygal..
"..ibaad ne ya fara hango mujaheed, yana isowa ya babbasu jamal hannu akay sai anjima snn ya kalle ayanah yace "softy in kin gama kixo ure needed inside urgently
..ibaad yay kamr zai dago abun sai kuma ya basar ya mata ido akan taje, sallama ta ma su jamal snn tabi mujaheed din abaya cikin sanyin takunta mai daukar hankli basuyi nisa ba mujaheed yace mata babansa ke kiranta a sama snn ya dawo
kamr lost zombie zainab arifah ta tsaya cos they dint really give her an ounce of attention musmn prince da gabaki daya ajin yarinyar bai masa ba..
she is too over confident nd wild for his liking, irin babu nitsuwa da jan aji na mata ajikinta sai sam baison suyi hiransu da ita..ayaana na shiga baifi da minti biyu ba ibaad ya shiga motarsa sauran abokan ma kowa ya shiga nasa motar suka bar gida suka nufi hotel inda ango yake domin a shirya xuwa dinner da dare.. tsaye xainab tay da mujaheed awaje tun bayan tafyarsu take kawo masa sukar ayaana, sai ce masa take ayaana bata da tarbiya, bata da aji tabiyo abokan ibaad ne dan wani acikinsu ya ganta yace yana sonta, ah ah ayaanah is too cheap, ayaana is too fake , bata san meyasa ibaad yake sake mata ba, bla bla bla..suna tsaye awajen ta kirga kagagun lefukan ayaanah sunkai dubu but still bataji zucyarta yaimata sanyi ba..
hakanan ta nace mujaheed ya rakata wajen kawayenta su nala acan xata shirya sai suje dinner tare dan tanaso ne no matter what dai abokan ibaad su san da ita she just cant be feeling left out while ayaanah is enjoying all the petings frm ibaad alone.
daga bangaren ayaana kuwa tana isowa ciki already mujaheed daya rakota ya koma waje ya gaya mata babanshi ne yake nemanta a sama
sosai gabanta ya fadi amma sai ta basar cos her heart is too happy abt ibaads gesture for her to feel fear, da dan gwarin gwiwarta ta karasa har sashensa..
tay sallama bai amsa ba harta karaso ciki da ladabi ta tsuguna tace uncle ance kana nema na..
mikewa zaune yay yana mata wani irin kallon bacin rai yace "sai yanxu ne aika na ya isa wajenki..zatay magana ya haura mata "Dont speak when i am speaking..kawai dan kin maidani bansan menakeyi ba kika kama kikaje wajen wanda suka fini muhimmci awajen ki dake baki da kunya ko, is it akan those chewing gum boys zaki share kirana? ayaana kin ban mamaki wallh
fushin da hatsala da yake mata maganan dashi yasa tay shiru batace komi ba for a while sai can tace uncle nifa yanxu ne akace min kana kirana
.. da bacin rai ya mike tsaye "Hey Dont you ever lie to me.. kar ma ki soma maidani bansan menakeyi ba, anan agaban abokaina safiya tace min kince acemin ba aganki ba..i have to pretend, it hurts me.. but i make a joke out of it nace musu safiya batason taje aikin ne kawai tace haka...nd i was calling ur line kinata wani danna min user busy ashe keee kinsan me kikeyi..ure with those chewing gum boys ai dole ne bazaki dauke wayata ba..nd u saw me outside kikay banza dani wai yaushe na fara wasa dake ne ehhh..
hawaye masu zafi ya cika akwayar idanunta sabida fushin da yake mata maganan dashi muryanta na rawa rawa tace i am sorry uncle, i tot she was joking shiyasa nace mata haka kuma ni ban san ma ranka zai baci ba har haka ba dan Allah kay hakuri...
memakon data fadi hakan ya rage fushin mana sai ma ya cigaba da mata ihu sai hargagi yake yana cewa haba da Allah ayaana kin bani kunya yau wallah..kin kunyatar dani agaban mutane, he was angrily stressing dat he has plans
yace..baki kyautamin ba
snn..bazaku tashi bada hakuri ba sai kinga kun cuce mutum nd please mind urself, kome kikeyi inhar ni ne nace mikizo to maza kizo.. shi ibaad ne waye shi?ai in da kina darajani koda wasa bazaki dauki kirana abun wasa ba.
tunda yafara masifar shiru tay masa batace uffan ba hawayenta na zuba ahnkli,
he talk , talk, talk..har ya gama batace masa komi ta tashi tana kuka ta fita..
tana ficewan kuma sai yaji hanklinsa ya bala'in tashi, wanda kusan hali ne ajikinsa, he love to over react musmn in abu ya shafi kishi ko wani abu da baixo dede da raayinsa ba..
sashen ammi karama ta nufa takoma dakinta da zafin masifar da yy matan aranta tana gama share hawayenta ta shiga wanka tabi ta doro da alwala tay magrib da isha snn ta sako doguwar hijab ta wuce dakinsu kulthum inda za'a musu shiri na fita dinner tareda amarya, jim kadan aka fara tsantsara musu make up, amarya zata saka champainge gold sukuma wani irin saki ne burnt orange me masifar kyau sukay ankonsa. aka tsantsara musu kwalliya still ayaana ta maida abun wuya da ibaad ya bata a wuyarta dake gwal ne me tsadan gaske kowa sai yaba design in yake bcos of how unique nd simple akayishi babu hayaniya, tuni ta debi kashin uncle moh ta watsar cos she was abslutly feeling herself da abun wuyan nan da yayanta ya bata kowa yake yabawa...
around 10pm aka gama komi kusan kowa xaije wajen dinner biki ammi karama ce kawai bappa zaidu yaqi sam ya amince mata taje wani taron dare dan haka ita da wasu bakinsu tsofi aka bari agidan suka dai. kowa yaga amarya kulthum da abokanta sai an ce tubarkallah masha Allah, so young so beutiful and elegant
kayansu is extremely sophiscated da slay queen styles na dinkunan zamanin nan..
tsabar rawan kai haka zainab arifah ta dinka wata expensive lush material kalar kayan kawaye zak zak dan kawai ta jero da ibaad a bridal train a musu hotona, unfornatly sai shikadai ne bai iso hall din da wuri ba, ya zamana abdlgaffar ne yau zai tsaya a spot din babban abokin ango, addini ya shiga jikin ibaad and it feel odd for him yaja jama'a sallah bada jimawa snn yaxoshi tsakiyar jama'a yana dantse rawa byan bai ma iya rawar ba.
in oda not to spoil maher day sai ya bar abdl gaffar a spot dinsa he was no where to be found har aka gama shirya train din amarya da ango zasu shige cikin hall kenan zainab arifah ta jirashi har ta gaji sai daga baya ta hakura taje ta mannu da mujaheed suka shiga atare..bayan shigarsun bada jimawa ibaad ya taho ankon fararen kayan sukayi ango kuma yasa brown kusan irinna matarsa bakaramin kyau sukayi ba. table of six six aka bawa duka abokai da kawayen amarya prince hassan yaxo da yar budurwansa yasmine
kaita babanta is a minister she was soo cute too, farhan da jamal agefe, tun kafin ibaad yazo jamal ya kirawo musu aayaanah tana zaune dasu, ibaad yana zuwa table dinsu ya cika..
wani irin haushi da karsashi kamar zai kashe zainab arifah da already ta hakura ta zauna tare da mujaheed da su anty safeera da mum dinta hajy hamida da hidimar dinnern kawai ta iya zuwa dan tasan akwai masu kudi anan xa'a bajintar nuna arxiki...
yau kusan ranan ammi babba ne da kawayenta duk dama sunji mugun haushi da sukaga ammi karama batazo ba dan dagangan suka yi plan na games na truth or dare, quiz, wakokin habaici da wasu shagalinsu na mata da zasu walakanta ammi karama dashi abainar jama'a ita da gang din kawayenta su kusan sunkai sha biyar anci ado kure adaka kamr matayen sarakuna da gwamnoni
haka aka sha shagali
hanklin zainab arifah da uncle moh gabaki daya nakan table din ibaad da ayanaz kowa yana jira daya acikinsu ya tashi, zainab tana Allah Allah ayaana ta mike sai ita ta koma seat inta, she cudnt go dazu sabida abokan ibaad din basu wani bata fuska ba kuma da sukazo ayaana kawai suka jawo jiki, shikuma uncle moh ya rasa yadda xai yi su kebe da ayaanah ya lallabeta ya bata hakurin akan irin abunda ya mata daxu har ya sata kuka..
the waiting seems endless all this while ibaad yaki ya tashi koda xai tashin ma tare da ayaanah suke zuwa sama daga manni sai daukar hoto kuma haka zai sakota agaba tana gefensa har su dawo wajen xamansu atare, here nd der cikin jama'a zakaji ana bala'in ririta gulman dacewarsu..
it was the worst night for xainab arifah tun tana daurewa bata son daukar abun serious har ciwon ta yaso yafara tashi mata, worst not with the way with the way her friend ruqqy is qouting" wann yarinyar kam ta kwace miki saurayi".all the pain has gotten to her neck, duk da uwar notice me da barin kudin manni data dingayi
haka har aka gama dinner arnd 12pm na dare tanaso waikoda ibaad yaganta su gaisa da kawayenta da nashi abokan amma inaa, ashema 11:30 ya sabule ya kai ayaanah gida yace ma abokansa ai tana da ciwon mura wai sanyi zai kamata....
har gidan kuwa yakaita kafin ya dawo hotel few minutes kafin sauran angwaye suka fito washe gari sassafe ya raka jamal har airpot da suvenrs na biki sabida aikin dake gabansa da gaggawa. da shi da su farhan dukka aka gama hidiman budan kai da su da sassafe, sann aka ma kulthum nasiha aka kawota gidan ammi babba, anan za'ayi wuni snn amarya da ango su kwana daya kafin nan washe gari su wuce malaysia atare. .
Ammi babba bakinta har wuya tsabar murnan irin goma na arxikin tsaraba da ta samo abikin nan...not untill dataje tana ma maheer ɓaɓatu ta tsince shi yana waya da ammi karama duk ya daga hankli ita kuma tanata bashi hakurin cewa ai babansa ne ya hanata zuwa dinnern sa amma in sha Allah itace zata fara xuwa gidansa bayan sun wuce malaysia da amaryansa gobe
...daga jin haka kishi ya bi ya rufe ma ammi babba ido..
duk inda bappa zaidu yay sai ta bishi da habaici damuwarta wai baya kishinta fatima dake itace gwall dinsa ai bai sake tay kwalliya taje ta shiga cikin maza tay rawa da dansa ba..
Shareta yay har ta gaji da habaice habaicen tay shiru bai kulata ba..
bayan biki family house yadan yi shiru dedekun bakin nesa ne kawai basu watse ba washe gari da sassafe uncle moh ya dinga tura ma ayaanah text akn taxo ta samesa yana son magana da ita,wanda ko daya bai shiga ba dan tun wajen dinner data lura da take taken sa tabi tay blocking layinsa ta hada da dansa dayake aikowan ma tay blocking..
tun jiyan kuwa mujahed yaso ya nunnata ma abokansa as wife to be dinsa, like he alwys told them shima auren gidan nan dai zaa masa da ayaanah irin yadda akayi na kulhum da maherr, yayita kiranta wajen dinnern nan amma lambarta bai shiga ba kuma althrou yaganta tana tareda ibaad ne wanda kowa yasan ba a ma ibaad irin wann rainin bare yazoshi ya kirata agabansa sai kawai ya basar da komi
dake tay blocking dinsu both uba da dansa tay baccinta bata ga wani abu da suka turo ba kuma kirar kodayansu bai shiga wayarta ba, kwanan kulthum daya tare da angonta agidan su bappa zaidu yay musu nasiha duk family aka rakasu airpot da yamma suka wuce malaysia atare da zimman few weeks frm now zasu dawo gida sabida krban trnscrpt da sauransu wanda zaa ma kulthum transfer ta koma da karatun can malaysia inda mijinta yake da zama yanxu..
bayan wucewar amarya da ango satin gabaki daya an daukeshi ne wajen kewa da kuma sallaman baqi musmn ma na nesa da sukaxo musu, for good 6 days ayaanah taki sam ta hada hanyarta da su uncle moh, tun bai gane tana dodging insa ba har yaaxo ya gane mujaheed ne kawai hanklnsa yay nisa sabida shine yake yawancin jigilar kai jama'a aiport ko tasha sai bai wani lura da cewa blocking insa ayaana tay ba, he just tot irin mood swing na missing din kulthum ne kawai yake kan damun su ita da sultana bcos they really cried lkcin da kulthum zata bar gida.
daga gefe kuwa uncle moh sosai ya shiga hayyacinsa ya sissiya abubuwan duniya da yawa harda sarkan wata gwal wanda zai lallashe ayaanah dashi dan ta dena fushi su dawo daidai. sam baiyi tsammani dan ya mata fada zata dauke masa wuta haka ba. he was really worried nd remorseful gashi so yake within 8 months frm now tana gama scndry school dinta sai ya shigo ma hajya mairo da batun aurensa da ita..
bayan sati guda da biki anty safeera ta farka da wani irin laulayi dake ta jima tana family planing harga Allah bata masan ciki ya shigeta ba kawai gani tay kominta na canzawa she just left it a matsayin stress ne na bikin yarta datayi
ranar asabar da sassafe ta gaya ma uncle moh cewa batajin dadin jikinta xataje asibiti yace mata bari yay wanka kawai yazo yakaita dakansa a duba masa ita.
dakinta ta nufa dan ta shirya tagama amai kenan sai ga mujaheed ya shigo dubata...
shiya taimaka mata ta kimtsa kanta, lckin duk ta damu sosai harma tafara suspecting cewa koma cikin ne da ita, tafara hawaye tana cewa mujaheed gaskiya batason ta sake haihuwa sabida dakyar take sha kuma gashi ta balain jimawa bata haihu ba zata sha wuya..mujaheed yanata dariya yana lallashinta yana ce mata zata iya, ahaka ahaka har ya shigo mata da batun ayaana
saidai wann karon he was damn serious abt it, yace mata in 1 nd half years zai gama 4yr course nashi daykey a univrsity dan haka yanaso shima yay aure kafin yaje masters a dinsa kasar waje kuma harga Allah ayaana yake so kawai ya aura
anty safeera taji dadin haka, kodan ma kanana kanan zargin dake ginuwa aranta game da alaqar ayaana da uncle moh ya kare akawo ma weird gifts dinsun nan full stop...
tana murmushi tace masa inkuwa ayaana zai aura zata goyamai baya dari bisa dari..
he was soo happy da yanayin yadda anty safeera ta amshi maganan, sharply yace mata zaiyi tunanin yadda sai fito fiki ya gaya ma ayaanahh qudirinsa acikin satin nan ko kafin watan nan ya kare kar kuma wani ya rigasa furtawa.
daga kofa uncle moh yay shiru yana jin duk wani hira da sukeyi gabansa yarinka faduwa yana jin wani irin jiri jiri na shirin kwasarsa daga tsaye
sanin cewa yana da zafin zuciya bazai ma iya jurewa ya kallesu da wanna maganan har a tunkaresa da shi ba yay maza ya fasa shiga dakin ya koma room dinsa ya dauki car key yabar gidan, basu kara ganinsa ba, duk kirar data masa saican ya tura mata text yace mata "urgency ne ya fitar dashi, kawai taje asibitin ita daya inya dawo zaizo yaji.
awajen abokinsa ya wuni wajen neman mafita., ita kuwa tun da laulayi ya lafa ta debi kashin asibiti ta watsar bataje ba, kowa ya hallara akayi wkends babu uncle moh ranar agidan gabaki daya sai can dare ya dawo nan ma bai kula kowa ba ya kulle kansa a daki cikin tunanin shawarar da alhaj ameer ya bashi na tura mujaheed karatu wani kasa tareda saka masa sharudan cewa bai amince yay aure ba sai ya kammala har matakin masters dinsa da niyar kafin nan ya dawo ai riga y aure ayaanah sai kuma yaga ta tsiyan.
zainab arifah ta musu sallama, itama tabar nigeria ranar sunday da matsancnin damuwr ayaana a ranta..
bayan kamar sati biyu masu kyau da kammala bikin kulthum lokacin komi na gidan ya fara dawowa daidai ranar alhamis da yamma ayaana ta dawo daga lesson wanka kawai tay ta saka doguwar rigan atampa holland dark green colour ya mata kyau sosai ta daura dankwali, kunun madara me dumi da ammi karama tay ta dauka tazauna tana sha gidan yay shiru she was just wondering yaushe ammi karamn zata dawo daga aiki dan tunda kulthum ta bar gida she have been lonely dake safiya bata ma kulata ita dayanta yanxu take zama inba dai chating sukeyi da sultana awaya ba....
toh yanxu ita kanta sultanan bata da wani time sosai sabida soyayyarta da ahmd ya kara yin karfi ya dage da batun zai shigo gida da maganan aure.
ayaanah tagama shan kunun ta kenan har zata danna ma ammi karama kira tamata shagwaba caraf sai ga safiya ta shigo suna hade ido tace ke ayaanah hajiya tana kiranki acan shashenta ta ni kiy sauri kifita kallon series zanyi tun kafin ammi ta dawo ki hada mun makrcin dakika saba..
ayaana batace mata uffan ba ta bar wayarta anan daga ita sai dankwalinta data kifa akan doguwar sumanta ta wuce sashen hajya mairo,...
tana isa ta bakin kofar ta tsaya cak musmmn da taji muryan uncle moh ne ata ciki suna magana da hajiya mairo yi tay kamr zata juya ta koma sai kuma she cant run away from him forever gara dai tay facing issure din, ita haka kawai de takejin batawani son ta cigaba da tarayya dashi,koma meyene intention dinsa kawai gara ta hakura, kwana biyun nan data guje shi ya zamana da babu shi arayuwarta bakaramin kwanciyar hankli ta samu aranta ba.
dakyr ta tattaro makanta nitsuwa tay sallama a nitse ta shigo babban falon wanda tun shigowarta wnn dan uban qamshin turaren wutar dake mamayrta ya sa ya zuba mata idanunsa har ta karaso ta zauna kasa cikin nitsuwa
fuskarnta a basake ba murya kasa kasa tace "ina wuni uncle...yay wata yake yace lafiya dear yaya kike..kafin ya dora tace" hajy ke kika aika nazo??" cikin kyabe baki..haj mairo tace o.. o..o ..o dama muhammadu ne yazo min da wata magana, yace ranar daga miki fada kawai kika hau dokin zuciya kika dena gaishesa waike kina fushi dashi, yoh inbanda kinsamu kansu suna shagwaba ki har ke kin isa babban mutum dayakai ya haifi biyun ki ya miki fada kihau fushi dashi kudai rinka ma kanku fada ayaanah
muryanta kasa kasa tace "hajy nifa banyi fushi da kowa ba
"to toh muhammadu kaji ai agabanka ta karyata ka,ikon Allah ayaanah ashe haka kike baki da kunya?
cikin katsesu yana wani irin sum sum yace aah hajiya karki mata fada dan Allah. ai leifina ne da ban tsaya na lura da uzurinta ba...ayaana dear, i am sorry kinji ko i shundt have shouted at you ranar kiyi hakuri kinji dear
hajy ta nuna masa yatsa kai muhammadu ya isheka haka, akan me? ita awaye da zaka zo kana wani langwasa mata murya..ba kirarta kay ranar tay banza dakai ba shone kuma kaine zakazo kana bata hakuri..daka mata fadan sai me? waye ke moruwa dakai inba ita ba, har wani fushi kika tsira da manyan ki..lallai tab di jamm...irin tarbiyan da kuke basu kenan, basu darajaku yanxu ke ayaana ko duka muhammadu ya miki shi ba' kusan asar ubanki bane.? tunda ya kai haifeki ai sa'an ubanki ne marar kunya kawai taɓabbiya. maza maza ki bashi hakuri bana son iskanci da bude idon banza da wofi.
muryan ayaana na rawa rawa tace "kayi hakuri uncle nifa ban rainaka ba..ranar naga kanata masifa ne shiyasa sai bance komi ba amma ni ban raina ka ba
yadda ayaana tay maganan da bacin rai hajiya ta harxuka tace 'ke da Allah karya kikeyi inba raeni ba meye ne..kice kawai kina dai tare da ubanki rayyanu bazaki iya saba masa ba dake ya hure miki kunne kina raina manyan gidan nan kamar yadda shima yake raina uban kowa.. toh muhammadu ya gaya min komi, ince dai akan shi rayyanun ne kikaki zuwa kirar da ya miki ranar? toh wllh wallah ahir dinki da raina min ɗana akan rayyanu, dan kinga yana sake miki.. yana tausayin rayuwarki toh wallah bazaki hada kai da rayyyanu kuna walakanta shi ba..tunda kikazo garin nan meye muhamadu ya ke miki inba alheri da rufin asiri ba...snn kece ynxu zaki tsiro masa da iskanci da rashin kunya har wani kina fushi dashi kajimun shashasha marar hankli toh wllh karna sake jin haka
kaikuma muhammadu wallah banason irin wannan shegen gurbataccen tarbiyan da kuke bawa yaran nan, yanxu ka kinkimo wayann kyautuka harda sarkan gwal zaka bata ita da laifi kuma zaka kara lallata da kyauta wato kenan tacigaba da yin abunda take maka na rashin kunya kenan ko?
yace ahhh hajiya Allah ya huci zuciyarki nifa bance ki kirata ki haura mata da fada ba, ai leifi na ne dana mata fadan ko..ni sulhu kawai nake so.
ya juya ya kalle ayaana a marairaice yace ayaana dear kiyi hakuri...i bot this gifts for u ina fatan zai saka komi ya wuce...
ayaanah tafara hawaye
batace komi ba dan ranta bakaramin soyuwa yake mata ba...
hajya tace ohh bazaki amsa shi ba, ni wallh da bari kay naci ubanta toh meye haka ana bata haquri tana mana kuka ke kenan baza a gaya miki gaskiya ba ko rainashi dakikeyi abu mekyau ne...
ta share hawayenta ahnkli tace hajiya naji nace yayi hakuri...ke fa bakisan asalin abunda ya faru ba kinata min masifa
..tace nayi din, saiki tashi ki dakeni nasan cewa a nonon rayyanu kika tsotsi rashin kunya Toh wallh baki isa k raina muhammadu agidan na zuba miki ido ba
mikewa ayaana tay tace "ni zanje daki kaina namin ciwo..
hajy zatay magana uncle moh ma ya mike tsaye da wani irin sigar lallami hajya dan Allah ya isa haka..kinga kinsa kanta na ciwo..dear kije abunki kihuta nasan kin gaji...ince dai komi ya wuce..ahnkli ya matsao kusa da ita yace i wll call u with my new numbber dan Allah ki dauka zamuy magana a atacan i am sorry for all this kinji ko...ayaana taki tace masa uffan hawaye na zuba a idonta...ya kuma cewa zan bar miki gifts dinki anan inkin huce saikizo ki dauka kigayamin in sun miki kyau...
da wani irin masifa hjya tace "ana miki magana kinayin shiru ma mutane..chab din jammm ahhtoh lallai ayaana wuyarki yakai na yanka..toh wallh wallah har shi rayyanun dake hure miki kunne bai isaaa muhammadu yana masa magana yana kin amsashi ba maza kifita kibamu waje marar kunya kawai. inbanda samun waje waye zai dauki wnn rainin agidan nan inba muhammdu ba..
da wani irin sauri ayaanah ta fice a sashen tana shiga sashen ammi karama suka ci karo da ita a kofa tana kkrin shiga, suna hade ido wani irin kuka ta fashe da shi cikin sauri ta rungumi ammin tana kuka mai zafi jikinnta atake atake ya dau wani irin zafi sosai...
#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata
*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*
*WATTAPAD @SURAYYAHMS*
*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED*
#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025