RUWA CIKIN COKALI

chapter 25

by @mamanafrah3028

***



*RUWA CIKIN COKALI* 
(Ya ishi mai hankali wanka)
 
                  
                NA


         MAMAN AFRAH

 
.        *Daga marubuciyar* 
  *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* 
      *****

           BOOK 1

         PAGE 2️⃣5️⃣



ALIYA

    Zaman dirshan ta yi a tsakiyar dalon tana kuka haiƙan, gabaɗaya duniyar ta mata matsi da ƙunci ji take tamkar ta kashe kanta ta huta wannan wace irin ƙaddara ce a cw Ibrahim wai ko ɗanɗanar tuwon bai yi ba don baƙinciki da takaici ma a ce wai wurgi ya yi da cokali me ɗauke da asirin a jiki kawai saboda an faɗa masa rashin lafiyar ubansa zai shikenan zai jiƙa mata aiki. Bayan ta sha wuya da kuma kasada wajen zuwa ta sauya cokalin da kuka mai ƙarfi ta rushe tana faɗin
    
    "Na shiga uku na lalace Allah ya isa tsakanina da uwar Ibrahim da ta kira shi ta faɗa masa rashin lafiyar ubansa har ya yi sanadin fasa cin tuwon da ya yi, daman ma uban nasa mutuwa ya yi mu ga tsiya" ,Ta faɗa tana haura ƙafafu duk ta cakuɗa gashin kanta, ɗifff ta yi kamar ruwa ya ci tw, tana saƙa da warwara ranta in ya yi dubu a ɓace yake gabaɗaya sai tsanar mijinta Kasim mata maza ya turnuƙe mata zuciya tana tuno irin yadda ta bashi haɗin kai a gadon su na sunna a daren jiya duk don tana cike da ɗoki da farincikin cikar burinta na auren Ibrahim ashe dai bata san tufkar da ta yi an warware mata ita gabaɗaya ba!.
    
  Sai da ta sha kukan takaicin ta tsagaita sannan ta janyo wayarta ta kamo sunan Umma ta doka mata kira Umma tana ganin kiran ta ɗauka cike da murmushi ta ce

"Tilon ƴata ki ce aiki ya kammala yanzu za mu fara baza capacity, wallahi naira sai ta ci ubanta a wajenmu, motoci da gidaje masu kyau sai sun san mun yo kuɗi mun kerewa wulaƙanci!" Ta faɗa tana jiran Aliya ta fara kora mata bayani Maimakon ta ji muryar Aliya cikin farincki tana mata bayani sai ta ji Aliya ta fashe da kuka Umma hankali tashe ta ce

"Kukan me kike Aliya? Buɗe bakin ki ki faɗa min wallahi gabana faɗuwa yake kar dai ki faɗaa min mummunan labari mai ya faru?"

 Aliya cike muryar kuka ta ce

"Umma bai ci tuwon ba" Umma tana zare ido tamkar kwarton da aka kama ta ce

"Bai ci tuwon ba to uban mai ya ci ko dai Jidda ce ta yi wani mugun tuggun da ya  sa bai ci ba, ko dai ta harbo jirginki Aliya ke kike haukarki?" Ta tambaya cike da zaƙuwar son jin dalilin.

Aliya ta ce

"Wannan tsohuwar tasa ce ta masa waya wai ubansa bashi da lafiya ya yanke jiki ya faɗi shi ne ya jefar da cokalin tsabar ruɗewa a sibiti ma ya kwana tuwon ya lalace an zubar" Ta faɗa tana kwashe komai ta faɗawa Umma da take jin ɓacin rai tamkar ta yi ƙaramar hauka, sosai ranta ya ɓaci ta ce

"Ki daina kuka Aliya in har ina numfashi a doron ƙasa saj kin cika burinki, ko ma in ce burinmu sannan a shirye nake na yi fatali tate da tarwatsa aniyar duk wani wanda zai kawo tsaiko a lamarin nan" Aliya sai ta ji ta ɗan samu ƙwarin gwiwa hakan ya sa ta sauke wata nannuyar ajiyar zuciya nan Umma ta yi ta bata baki a kan cewa ta kwantar da hankalinta in dai gidan Ibrahim ne ta gama shiga ta gama.

   Sun yi sallama bayan sun jajantawa juna Aliya saboda takaici ko da Jidda ta ƙarasa asibitin ta kira ta don ta ce ɗazu suna magana basu gama ba ta daina jin ta amma sai Aliya ta ƙi ɗaukan kiran don yanzu kawai haushin Jidda take ji.

  Washe gari Umma ta kira Aliyar tana faɗa mata tare za su je ajen bokanyar don ta faɗa musu abin da ya dace a yi domin ita yanzu ta gwammace ko salwantar da rayuwar Jidda ne a yi in har za a samu biyan buƙata duk da tana son a bar Jidda a rayw domin su ƙunsa mata baƙinciki irin baƙincikin da za ta gwammace gwara mutuwarta amma in hakan zai zama matsala gwara ta bar duniyar ma su su ci tasu duniyar da tsinken tsire mai tsini. Daga Abba har Kasim babu wanda aka faɗawa fitar hanya suka sata suka tafi yana kowane ya fita kasuwa. Ko da Amatullahi ma ta tambayi Aliya sai ta faɗa mata da Umma za su je wannan karon.

  Suna isa bokanya ta musu izini suka shiga. Bayan Aliya ta gabayar da Umma a matsayin mahaifiyarta sai kuma ta shiga rattabo mata bayanin yadda al,amura suka kasance wato yadda ba a dace da cin abinci da cokalin da aka yi asirin nan ba. Ta yi mamaki kuma ta jimanta abin domin tana tabbatar musu cewa da a ce ya ci abinci da cokalin nan da matsalar su ta kau har abada!. Sai dai matsalar idan aka yi aiki ba a maimaitawa sai dai a yi wani sabo. Nan Umma tw ce kawai a yi wani aikin.

  Bokanya ta yi jim ta ce

"Aikin da za a yi yana da hatsari kuma yana da ci, domin idan aka yi har sai ya fi na cokali zafi sai dai shi wannan aikin ana faɗar ladan da za a biya na aiki a nan take ta sanar da su za a biya kuɗin aiki dubu ɗari biyu. Daga Umma har Aliya kallon kallo ake domin kaf cikinsu babu mai dubu goma ma ta kansa a halin da ake ciki dai yanzu babu kuɗi sannan kuma suna buƙatar a yi aikin da gaggawa. 

  Bokanya ta basu kwana biyu a kan cewar idan an kawo kuɗi za a yi aiki. Tun da suka taho suka shiga zulumi da tunanin yadda dubu ɗari biyu za ta fito, idan suka yi hasashen kuɗin da  yawa sai kuma su tuna tasirin da aikin zai yi, tun da idan Ibrahim ya shiga hannunsu sai sun fanshe abubuwa da yawa.

  Sun rabu a kan cewa za su yi waya bayan sun tsara cewa Umma ce za ta kai wa Jidda kukan buƙatar kuɗin tun da suna ganin tana gidan daula ba za ta rasa kuɗi ba.

   Washe gari aka sallamo Daddy daga asibiti ya ware tass sai dai ɗan abin da ba a rasa ba. Jidda tana zaune a bakin gado Ibrahim ya zo ya zauna ya ce

"Habibty rufe idanunki" Wani kallon ƙasan ido ta masa sai kuma ta murmusa haɗe da runtse idanun, ya ce ta buɗe hannunta haka ta buɗe hannun sai da ya ajiye mata mukullin a kan hannun sannan ya ce

"Buɗe idanun" Tana buɗewa ta ga mukulli a hannunta mukullin mota, nan ta shiga tambayarsa ya sanar da ita cewa Abba ya siyawa mota, don dama yana da niyya. Wata iriyar runguma ta masa tana ta murna tare da jero masa wasu addu,o,i masu daɗi hakan ya sa ya ji matsayinta ya ƙara ƙaruwa a zuciyarsa. A ranar ne ta shirya domin zuwa ta isar da saƙonsa zuwa ga Abba bayan magriba tare suka je a motar direbansa yana biye da su don haka yana ajiye ta ya bata mukullin ya shiga motar da dirwban ya zo da ita ya ce an jima zai dawo ya ɗauke ta.

  Da sallama ta shiga gidan lokacin Abba bai dawo daga masallacin ishsha,i ba. Umma da take zaune a tsakar gida a kan tabarma ta buga uban tagumi ko da ta ji sallamar ma sama sama ta ji sai da ta ɗago ta amsa duk a diririce musamman da ta ga Jidda cikin shuga ta alfarma cikin shigar manyan hajiyoyi wani dakkaken leshi wanda ya amsa sunansa leshi da ƙaton mayafinta da ya rufe mata dukkan ilahirin jikinta, sai takalmi da jaka masu aji sarƙoƙin gwal ɗin da ta saka suna walwali su ne suka saka Umma jin zuciyarta har wani ɗaci-ɗaci take, ita kuma Jidda ba ita ce ta ɗakko kayan ba gabaɗaya Ibrahim ne ya ɗakko mata a cewarsa gwara ta je gida a ganta a ce ya iya kiwo sannan ya riƙe amana haka ya faɗa mata cikin wasa lokacin da ya ɗakko mata kayan.

 Umma dakyar ta yi yaƙi da zuciyarta ta ce


"Jidda sannu da zuwa farae amarya" Ta faɗa tana washe haƙora tare da nuna tsantsar murnar ganinta amma a zuciyarta baƙinciki ne fal domin jin wata tsanarta take ji, Jidda kuwa sai ta ji wani daɗi take ganin tamkar mahaifiyarta ce a gidan, sosai take jin Umma har ranta. Umma sai nan nan take yi da ita amma shigarta ta tsaye mata a rai kuma ta tsone mata ido!.

 Sun gaisa ta ɗakko mata ruwa, tana jin a ranta tamkar ta zuba maganin mutuwa Jidda ta sha ta mutu kowa ya huta a kan yadda take ganin ya sha gabansu, take ganin tana zaune cikin haɗaɗɗe kuma tsararren gida amma tata ƴar tana can gidan mata maza, mata mazan ma Allah baku mu samu.


 Ruwan ta sha tana ta yi wa Umma godiya don har mamaki take idan ta ga Umma tana nuna mata so da kulawa tamkar ba waccan Ummar da ta bata wahala ba, tamkar ba Ummar da ta ɗora mata karan tsana ba.


  Umma cike da wasa a zahiri ta ce

"Ai na ɗauka ma ko bakya iya shan ruwan gidan namu ba" Ta faɗa a zuciyarta kuma tana cewa

'Kin kusa zama tarihi a wajen Ibrahim ɗin da kike taƙama da shi'

  Jidda tana ƴar dariya ta ce

"Haba Umma ta yaya haka zai faru ni da gidanmu ni da na taso na girma ina shan ruwan"

 Umma ta.ce


"Ai da na ga yanzu kin saba da ruwan faro wato ruwan roba" Sosai Jidda take dariya Umma kuma a fili fuskarta ɗauke da murmushi amma a zuciyarta tana fatan Allah ya kawo ranar da wannan murmushi da farincikin zai bar kan fuskar Jidda ta dawwama cikin ƙunci.


  Suna ta taɓa hira tana cewa ta zuba mata tuwo ta ce a ƙoshe take, a nan har tana bata labarin yadda take jin daɗi idan Aliya ta kai mata ziyara a fili Umma ta ce

"Ke da ƴar uwarki haba Jidda  in Aliya bata je wajenki ba waye zai je"

 A zuciyarta kuma ta ce

"Ita ma tata ce take kaita, za ki gane baki da wayo ne lokaci yana zuwa sannan za ki yi hankali ki gane ba kowa ake ba yarda ba a rayuwa, domin kamar yadda bahaushe ya ce


'Makashinka yana tare da kai!'

  Sunanta taɓa hira har Abba ya dawo, ya yi farincikin ganin Jidda musamman da ya ganta cikin farinciki da kwanciyar hankali, tabbas yana son Jidda yana jinta a zuciyarsa tamkar ƴar da ya haifa wani lokacin har tana jin son Jidda yana barazana ga son da yake wa Aliya wato son Jidda yana neman linka shi.

  Ta gaishe da Abba cike da girmamwa tana jin ya maye mata gurbin mahaifinta har abada, bata da wani uban da ya wuce shi tana bashi matsayi irin matsayin da baki ba zai iya fasaltawa ba. Umma tana jin haushin yadda yake nunawa Jidda kulawa amma haka ta danne. Tana tsokanarsu wai ƴa da uba an daɗe ba a haɗu ba. Bayan an ɗan jima ta buɗe jakarta ta ɗakki mukullin motar ta miƙa masa tana faɗa masa Ibrahim ne ya saya masa mota buɗar bakin Abba ya ce

"Mota kuma Jidda?" Umma ranta a matuƙar ɓace amma haka ta daure ta nuna murna. Jidda tana dariya ta ce

"Mota Abba ita ce dai za ka ganta a waje sabuwa dadal" Ta faɗa tana dariya.

 Idanun Abba suka kawo ruwa yana jin cewa shi ya sa aka ce ba a yi wa ɗa da dukiya mugunta domin baka san mai amfanarka ba.

  Ya yi farinciki har ya rasa da wane baki zai ambata murnarsa sai albarka yake sakawa Jidda da Ibrahim yana ta musu fatan alkairi a rayuwar aurensu, tare da nemar musu tsari daga dukkanin sharri. Jidda sai amin take cewa inda Umma duk ta ji kamar ta fasa ihu saboda takaici da baƙinciki musamman yadda yake ta zabgo addu,ar nema musu tsari da kuma ta dawwamar da farinciki sai take ganin kamar addu,ar da yake yana adawa ne da cikar nasu burin.

  Farincikinsa ya kasa ɓoyuwa har sai da Ibrahim yan dawo ɗaukan Jidda ya kira ta a waya inda ta sanar da su zai shigo haka ya shigo Abba ya yi ta masa godiya da kuma addu,a Umma ma haka ta daure tana masa godiyar amma ko da wasa bata yi addu,a ba.


  Sun musu sallama inda suka tafi.

   Washe gari da yamma Jidda ta fito wanka tana zaune gana mudubi tana shiryawa shi kuma dama ta bar shi a sama yana ƙarasa wani aiki, ƙaran wayarta ne ya dakatar da ita daga shafa powder da take ta ajiye sosan shafa powder ta ɗakko wayarta ganin sunan Umma ta ɗauki wayar da murmushi bayan sun gaisa Umma ta shiga tambayar lafiyarta da ta mai gidan har tana faɗa mata da safe sun je gidan su Ibrahim ɗin ita da Abba sun duba Daddyn nashi.

  Bayan Jidda ta musu godiya sai kuma Umma ta yi shiru har sai da Jiddan take tambayat shirun da ta yi, Umma ta ce

"Wallahi dama wata damuwa ce nake da ita Jidda ina fata za ki share mini hawaye"

 Jidda ta ce

"Subhanallahi damuwa kuma Umma?" Umma jin duk Jidda ta rikice tana nuna damuwa sai Umma ta cr

"Wallhi kuwa wani ɗan uwana ne a ƙauye jeji suka shige shi ƙafa tana nan suntum sai wari take to an kai shi wajen me magani sai aka yanka kuɗaɗe masu yawa, har dubu ɗari biyu da hamsin to yanxu sun haɗa dubu hamsin dubu ɗari biyu suke nema na ce bari na gwada sa,a ta a wajen ɗiyata mai tausayi ko za a dace!" Ta faɗa tana aikawa Jidda harara ta cikin wayar. Ajiyar zuciya Jidda ta sauke ta shiga faɗa mata cewa bata da kuɗi don jiya ta yi sayayyar wasu kaya a online za kawo mata sai dai za a iya samun dubu saba,in.

  Umma ta ringa faɗa tana cewa

"Yanzu Jidda har sai an koya miki dabarar zaman aure a gidan mijin, tun da har kika samu kika auri mai aljihu da maiƙo ai kamata ya yi kike farauto mana karki yarda ki zauna kanki da murfi don yanzu kowa ya waye" Jidda cike da rashin fahimta ta ce

"Wallahi Umma ba na iya tambayar Ibrahim kuɗi ina nufin ba na iya roƙonsa, sai dai a ɗan jinkirta idan har da kansa ya bani kuɗi sai na cika miki" Umma ta hau faɗin

"Kidahuma kike so ki zama?" Wannan ya yi daidai da zuwan Ibrahim bakin ƙofar ɗakin Jidda jin tana cewa

"Umma in saci kuɗin Ibrahim kuma? Gaskiya ni ba zan iya yin sata ba ko kuɗin waye in dai ba nawa ba ne bare na Ibrahim" A daidai nan ya tura ƙofar gabaɗaya ta rikice ta saki wayar ma daga hannunta ta faɗi ƙasa sa,ar ta ɗaya wayar bata yi komai ba.

  Sai ya nuna mata bai ji abin da take faɗa ba, dama kuma ya san ba za a taɓa haɗa baki da Jidda a cuce shi ba ya yarda da ita 100%
  Wayar ta ɗauka ta kashe da sauri jin yana cewa har yanzu bata gama shiryawa ba, duk ta rikice yanayin da ya ga ta nuna har ya so bashi dariya amma ya danne.


   Umma wani ƙuduri ta ƙudurta a ranta cewa za ta yi maganin Jidda don sai ta mata abin da wani maƙiyinta ma idan ya ganta sai ya tausaya mata.

   Wani filinta ta je ta ɗaga ta sayar Abba ma bai sani ba suka haɗa kuɗin suka nufi wajen bokanya. Bayan sun damƙa mata kuɗin ta tashi tsaye tana riƙe da wani ƙaramin kasko take kewaya ɗaki a take hayaƙi ya fara fitoa daga kpwace sukurwa ta ɗakin. Lokaci gida hayaƙi ya baibaye ɗakin su duka a tsorace suke sai da ta gama ta koma mazauninta ta zauna ta dube su ta ce

"Yanzu mai kuke so a yi" 

 Umma ta yi karaf ta ce

"So muke a saka masa son Aliya yadda ba zai taɓa rabuwa da ita ba yadda zai tsani duk wanda ya kushe ta ko ya nuna sai ya rabu da ita, sannan a saka soyayyarta a zuciyar surukan nata wato iyayan Ibrahim ɗin, shi kuma mahaifinta wato mijina a saka masa son auren nata kuma kar ya taɓa tambayar dalili ita kuma Jidda a sanya ta zama akwai ya babu kakar wajen uba"
 
  Aliya ta ce

"Kawai gwara ya danƙara mata saki lokaci guda idan dai ya yanke igiyar auren dolenta ta tafi ai"

 Bokanya ta gyaɗa kai tana wani haɗe halen magani sai kuma ta shiga kiran sunayen wasu aljannu kafin ta buɗe hannu su Umma sai ganin wani magani suka yi kulle a farar leda an ɗorowa Bokanyar a tsakiyar hannun.

  Nan ta miƙawa Umma magnin ta ce

"Wannan garin maganin za a saka shi a hancin sabuwar gawa ta namiji, bayan an masa wanka an saka likkafani kafin a rufe kan za a cire audugar hancin sai a zuba maganin a duka ƙofofin hancin sai kuma a mayar da audugar a rufe, yadda gawar nan bata da wani sauran amfani haka Jidda ba za ta sake amfani a wajen mijinta ba kuma a take zai sake ta, sanann son Aliya zai shiga zuciyarda daram, sai kuma mahaifinta da ko ma waye ba za su taɓa kawo tsaiko a kan auren ba, babu ma mai tambayar don mai aka yi " Umma tana dafe da ƙirji da hannu biyu sai karkarwa take jin furucin bokanya, tana tuna naira dubu ɗari biyu da suka bayar yanzu kuma ga wani ɗanyen aikin da take ji har gwara na cokalin da Aliya ta yi.

  Aliya tana zare ido ta ce

"Bokanya ko za ki sauya aiki?" Umma ta shiga gyaɗa kai alamar gamsuwa da maganr Aliya ita kuma Bokanya ta ce

"Ai in mun faɗa sai an yi kuma ba za a canja ba, mene ne abin wahala a wannan aikin ku da kuke neman biyan buƙuta ai ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba, da kuka ci sa,a ma ban ce ku yi ridda ba"

 Suna haɗa ido suka juya suna kallonta suka haɗa baki wajen faɗin

"Ridda?" Bokanya ta ce

"Ridda mana mutane nawa ne suka yi ridda saboda su samu biyan buƙata, mutane nawa za su zo mu basu hutun yin sallah na kwana arba,in ko satittika ko watanni kuma su yi"

 Umma ce cikin sanyin murya ta ce

"To ai bokanya ta yaya za a yi mutum ya iya zuwa wajen gawa har ya yi abin da kika faɗa ba tare da tonuwar asirinsa ba?" Da wata mahaukaciyar dariya ta bushe ta jima tana yi sannan ta haɗiye dariyar ta hanyar haɗe rai sai kuma ta ce

"Komai a tsare yake, don haka akwai maganin da zan bayar da kowa sai ya suma a take a wajen " Umma suna gyaɗa kai ita da Aliya kamar ƙadangaru Bokanya ta miƙa

"Wnanan maganin ne na sakawa a hanci, wannan kuma daga kin shiga gidan makokin sai ki ambaci sunan mamacin tare da fakar idanun mutane ki juye garin maganin a hannunki sai ki hura da baki ta yadda maganin zai bi iska kuma ko wani ya gani ba zai tambaya ba, kina yin haka kowa zai faɗi sumamme har ki je ki gama abin da za ki yi idan kin gama sai ki ƙara ambaton sunan mamacin kowa zai tashi kuma kowa ba zai taɓa sanin ya suma ba"

  Sun karɓo sun taho Umma tana ta adana maganin, don Bokanya ta ce a tsakanin su kowa zai iya yin aikin tun da an yi maganin da sunan waɗanda ake so aikin ya ci, don haka sai Umma ta ce za ta yi ita kuma Aliya dama ta ce tsoro take ji. Aliya gida ta wuce, Umma ma ta wuce gidan don Abba bai dawo daga kasuwa ba.

  Umma ta je ta ɓoye maganin a wata sabuwar samirar ta, tana zaune da magriba bayan ta idar da sallah, tana jingine da bango Abba yana masallaci lokacin sai kawai daga masallaci ta ji ana sanarwa ana cewa


"Innalillahi wa inna ilaihi raji,un Allah ya yi wa malam kalla rasuwa, za a yi sutura da ƙarfe bakwai na safe, Allah jiƙansa ya gafarta masa" Zuruf Umma ta miƙe tsaye gabanta yana faɗuwa, don ta san lokacin aiwatar da aikinta ya yi duk da tana da mugun tsoron gawa, amma haka za ta durfafi wannn al,amari saboda malam kalla maƙocinsu ne daga can gefe!.


    


SADIYA

  Da tsananin mamaki ta ɗago tana kallon Meenal wacce take tsaye hankali kwance take zaro baƙar magana, ta rasa mai ta tsare mata a gidan bayan ita ta zo ta samu a gidan amma tana son fitar da ita daga gidan mijinta ta ƙarfi da yaji!.

  Meenal ta ƙara haɗe rai haɗe da yatsina fuska ta ce
"Ina fatan kin fahimta, ko kina kokwanto a kan hakan ne in nuna miki zahiran" Ta faɗa tana kama ƙugu da hannu ɗaya, Sadiya danne takaicin da yake ranta ta yi ta ce

"A kan mai zan yi mamaki ai shi mutum ba a gane shi a fuska sai dai ɗan adam bai isa ya zartar da abu a kan mutum ba sai abin da Allah ya rubuta a kansa, idan har ruwana ya ƙare a gidan nan dole zan bar gidan idan ruwan shana bai ƙare ba kuwa babu wanda ya isa ya dakatar da hakan" Ido ɗaya ta kanne tana bin Sadiya da kallo kawai sai ta juya tare da yin ƙwafa ta shige ɗaki. 

   Zuwa jimawa aka fara sallama, bayan an amsa masa ya sanar da cewa mai yin kicin ne da mai gidan ya kira, Sadiya dai ta masa iso ta ja ɗanta suka shige ɗaki. Nasir kuma yana fita da ya je ya gidan Hajiya ya same tw zaune ta duka uban tagumi duk ta yu baƙi ya rasa ma mene ne ummul aba,isin hakan ya zauna bayan ya gaishe ta ta amsa tana sakin doguwar hamma ta ce

"Nasir yanzu sai da na maka waya shi ne za ka zo? Yanzu sai ka kwana ka tashi baka ma zo inda muke ba Nasir?" Ɗan sosa ƙeya ya yi ya ce

"Wllahi Hajiya abubuwan ne suka sha kaina amma baki da lafiya ko" Ta ɗan kai hannu ta taɓa wuyanta da ya yi ƙashi ta ce


"Amma da duk abubuwan da suka maka yawa duk safiyar Allah sai ka zo gidan nan, kuma da kake maganar ko ina lafiya ai yunwa ita ce babbar rashin lafiya" ,Da mamaki ya ce
"Rashin lafiya kuma? Yunwar ce rashin lafiyar hajiya bakwa cin abinci ne" ,Ya faɗa lokacin da ya ga Hibba da Husna ma sun fito sun zaune su ɗin ma duk sun yi rama.

  Hajiya ta ce

"Yanzu Nasir har sai wani ya faɗa maka ba ma girki ai ba girki ne ba ma yi ba ƙoshi ne kawai ba ma yi, yanzu a ce yaran nan su je su yi bautar girkwa yarinyar nan Meenal abincin kari amma take tsakura mana wani ɗan mitsitsi kamar wanda muka roƙa yanzu saboda isa ma wai hatta madara da milon ta daina tsakura mana sai dai mu sha lipton kawai kp yau da suka kawo sai haƙura na yi na sha koko haba a kan mai yarinya ƙarama z ta zama ita take juya ragamar gidanka Naasir" Iska ya hurar yana kallon yadda su Hibba suke zumɓura baki ya ce

"Haba Hajiya ita fa Meenal gidanta ne su kuma yaran nan su ma idan suka je gidajensu sai su dafa abin da suke so, sannan maganar madara cewa ta yi ta kusa ƙarewa a bari ita take sha idan tana tskurawa ba zai isa ba to kin ga ba sai an saka mata rani ba, sannan maganar rashin zuwana Hajiya da fa abincin safe nake zuwa ci yanzu kuwa kin ga  acan gidan ake dafawa... Tun kafin ya kai ƙarsheb maganar Hajiya ta fashe da wani kuka mai kamar jiniyar motar ƴan sanda, ta ce

",Yanzu Nasir ni kake faɗawa wannan maganar? Wato har gorin aure kake wa ƴan uwan naka saboda wanncan matar mai ƙira kamar ta barewa, to ahir ɗinka idan ma ƙarfinka aka fi zan yi maganin abin" ,Tsaye ya miƙe cikin halin ko in kula ya ce

"Ni zan wuce, dama zuwa zan yi in kira me aikin kafinta zai je can gidan ya yi aa Sadiya kicin ɗin langa langa saboda Meenal ta ce bata son wannan haɗen kicin ɗin" ,Ya faɗa yana tashi tare da gyara zaman hularsa da yake ji kamar bata zauna ba. Da kallo sula bi shi su duka, don yanzu babu wanna soyaya da kulawar da yake basu kawai tamkar ma hankalinsa ba a kansu yake ba, sannan ita Hajiyar ko ta tsawatar a kan rashin adalcin da ta ji za a yi wa Sadiya na yi mata kicin ɗin langa-langa duk da dama abu ne da suka saba na tashin yi mata a adalci da alama Allah en ya fara kawo wacce za ta mata maganinsu.

  Yana fita sai da suka ji tashin motarsa sannan Hibba ta ce

"Hajiya Yaya Nasir da tamkar ba ya cikin hayyacinsa wallahi ina jin an fi ƙarfinsa ne wato an masa asiri" Husna ta karɓe maganar da faɗin

"Ai dama daga ganin abin ma a hankalce an sana cewa Yaya ba zai aikata haka ba"

 Hajiya ta goge wani hawaye mai zafi ta ce

"Ni wallahi abin nan neman fin ƙarfiba yake domin na kasa gane kai da ƙafar abin nn na yi da na sanin auren nan da ya ƙara sannan ina zargin Meenal da mahaifiyarta a kan komai duk da mahaifiyar tata tana nuna min bata ma san abin da Meenal take yi ba sai ta ce wai ita ba za ta tsawatar mata ba ai ni da ita babu bambamci zan iya tsawatar mata bayan yanzu yarinyar nan ji take kanta ɗaya da ni ta ɗauke ni tamkar sa,arta, wai har ni Hajiya Mariya ce sirija take juyawa sannan har ta bada umarni muka bi ni da ƴaƴana wai ƴaƴana ne suke zuwa suna mata girki kullum da safe sannan ta tsakura mana abincin son ranta, wallahi ko a mafarki ban taɓa tunani ba"

 Hibba ta ce

"Hajiya ai wallahi yadda kika san wani tsoronta aka saka mana a rai" Haka suka ci gaba da jajantawa suna tunanin yadda za su samo mafita a shawarar da suka yanke dai zuwa wajen malami ne sai dai babu kuɗinnzuwan don yanzu kuɗin da Nasir yake basu duk ya ɗaure bakin aljihunsa sai na annabawa.

  Naair yana fita ya bugawa me aikin waya ya sanar da shi su haɗu a gidan nasa, sai ya riga Nasir ɗin zuwa yana dawowa gidan ya nuna masa inda za a yi kicin ɗin haka suka tafi suka siyo komai na aikin mai baro ya kawo langa langa da katakon aka shiga aiki tuƙuru!.
  An gama kicin tass mai aikin ya tafi don sai da ya sallame shi ya tafi kasuwa. Bayan ya tafi Meenal ta fito daga ɗakinta Sadiya tana jin lokacin da ta je take cewa


"Kai amma kicin ɗin ya yi kyau ji langa langan gar sheƙi yake, amma shi ma me aikin nan da ɗaurin tsantsa yake wato gar wani wajen ɗora kwanuka ya mata to Allah kyauta, din dai dama da irin wannan kicin ɗin ta dace" Sadiya bata ce komai ba ta yi kamar ma bata san mai take cewa ba don ta san tana faɗa ne don ta ji. Ko da aka kawo nepa haka ta ƙure kiɗa a gidan don ta turaw Sadiya haushi kan rashin nepar ita kuma sai ta tishe kunnuwanta kamar ma bata san tana yi ba, domin ko da almajirinta ya zo ɗaukan talla ta ce masa firjin ya samu matsala don haka ta kwashe gabaɗaya kayan cikin ta bashi ta ce ya je ya sadakar kar su lalace!.

   Meenal duk wannan abin sa ta yi wa Sadiya bata haƙura ba tun da burinta ta baƙanta mata rai ita kuma Sadiya tun da ta lura Meenal tana cikin mata masu kishin kissa da kisisina sai ta tattara kamarinta ta ajiye a gefe kuma ta saka a ranta duk runtsi za ta saka haƙuri da juriya ta san da cewa watarana sai labari kuma duk abin da ka yi haƙuri to watarana Allah zai maka sakkaya a kansa, domin wanda aka zalunta babu shamakin addu,arsa uabnagiji zai karɓe ta ko da bai yi adsu,a ba za a masa sakkaya wannan kaɗai take sakawa a ranta ta ji salama.

  Meenal ganin Sadiya ta danganta da maganar yanke wuta don da kuɗinta ma Naair ya ƙi ya saka a amayar mata jawai donnya nuna bata da kima da muhimmanci, sannan bata da wani galihu a wajensa, bai san darajarta ba, ganin ta mayar da hankali a kan sauran kasuwancinta na cikin gidan tana damƙar cikinikinta, kuma sai ta ga kullum tamkar ƙara buɗe mata hanyoyin samu ake don jama,a haka suke turruruwa wajen saye mata jayan tamkar kyauta take rabawa, don sai ma ta fara zargin ko dai wajen malamai ta je ta nemi kasuwa wato ko da maganin kasuwa take amfani shi ya sa take samun ciniki..

   Abin da bata sani va shi ne Sadiya babu abin da ta riƙe sai addu,a idan ta yi sallah tana ɗaga hannu ta faɗawa ubangiji damuwarta sannan ta roƙe shi ya kawo mata kasuwa me albarka ya ƙara kawo mata masu sayen kayanta ta ko ina, hatta bashi da sauran masu kasuwanci suke kuka da shi idan an karɓi kayansu bashi ba a biyansu ko a basu rabi a hana rabi wata ma ta cinye kenan, to Sadiya babu mai riƙe mata kuɗi kuma addu,a ce makamin saboda tana faɗawa ubangiji ya raba ta da ƴan bashi duk wani wanda zai cinye mata kuɗinta Allah ya nesanta ta da shi.


 Yau ya kama Laraba Sadiya ta tambayi Naair zuwa gidan Kaka dubiya saboda Kaka tana zazzaɓi danyake jiya ta faɗa masa da ta ganshi a tsakar gida kuma ya amince, don har yau Nasir bai shiga ɗakinta da sunan tana da baki ko matsayinta na matarsa ba ita bata ma taɓa jin ƙarin aure irin wannan ba a duk da tana ji a labari ana cewa wata idan aka mata kishiya mijin yana neman ta bashi kwananta ya ƙarawa amarya wani ya siya wani kuma ya ƙwata ta ƙarfi, kwanaki ta ji labarin matar da ta ce tun da mijinta ya yi aure shekara uku bai kusance ta ba, kai ɗakinta ma sai ya ga dama zai shiga kuma ba ya yin sama da minti goma zai fita, ashe dai ita ma al,amarin yana zuwa kanta rayuwa kenan.

  Yana tafiya kasuwa ta shirya ta shirya Kalifa ta tattara kayan sana,arta ta saka a kicin ta janyo kicin ɗin ta kulle haka ma falonta. Meenal da bata san Sadiya ta tambayi Nasir fita ba sai ganinsu ta yi da shirin fita Sasiyar tana sanye da atamda glitter da ta saya a wajen maman afrah an mata ɗinkin ya yi kyau sai hinabi mai ƙasan net wanda yake pink ya yi daidai da wata ƙananun fulawowi pink da suke jikin atamfar sai takalmin ta marar tudu. Ta yi kyau sosai ga Kalifan ma sanye da riga da wando ƴan kanti sun yi kyau da ɗan takalminsa sosai suka fito abinsu sai kawai ta ji ƙyashi cewa wannan fa da kuɗin sana,a Sadiyar ta saya tun da ta san cewa Nasir ba zai saya musu ba. A zuciyarta ta ce

'Wannan matar matuƙar tana sana,a za ta fara haɗa kafaɗa da ni tabbas amma zan yi maganin abin' Ko kallo bata ishi Sadiya ba ta kama hannun Kalifa suka fice daga gidan sai ƙaran rufowar ƙofar gidan ta ji.

  Ranta yana ta ƙuna ta koma ɗakinta. Can zuwan an jima ta ji ana ta buga gidan ta taso rai a ɓace ta zo ta ce

"Wai waye? Bashi ko tara za a damu mutane da buga ƙofa?" Muryar wani namiji ta ji yana tambayar mai gidan yana nan ta ce masa ba ya nan ta juya tana jan wani tsaki ta dawo gidan kamar an ce ta duba ƙasa a gabanta sai kawai ta ga mukullai, kallon mukullin take sosai tana son sanin mukullin mene ne don ta san ba na Nasir ba ne. A zuciyarta ta ce

"Sadiya" Kai ta shiga gyaɗawa alamar tabbayarwa ta tsugunna ta ɗauka tana duba mukullan a take wani tunani ya faɗo mata, da sauri ta koma ta sakawa ƙofar gidan sakata ta dawo da sauri mukulli ɗaya ta saka anjikin ƙofar ɗakin Sadiya sai ya shiga sai dai bai buɗe ba sai da ta sake gwada wani ya buɗe ƙofar wani tsalle ta yo da ihu a fili ta furta

"Tsuntsu daga sama gasasshe" Falon ta shigo wani ƙamashin freshner mai sanyin ƙamshi ya dakar mata hanci ko ina tsaf a gyare wajen freezer ta nufa ta buɗe tana taɓe baki sai ta ga babu komai a ciki an ma goge ta tass. Wani tsaki ta ja a fili ta ce

",Ba ke ce a gabana ba, bakya cikin target ɗina, tun da ke na gama da nake ɓangaren tun da an cire wutar nepar baki da sauran wani amfani sai zama a wajen" Ta faɗa tana jan murfin ta rufe freezer ta nufi cikin bedroom. Yadda gadon yake a ɗame shi ne abin ya bata mamaki sannan zanen gadon fari ne tass mai manyan flowers blue baki ta taɓe tana kallon kayan kan madubin.

 A fili ta ce

"Yanzu zan yi abin da ya kawoni" Ta faɗa tana ajiye mukullin hannunta da yake da ta buɗe ƙofar da shi ta shiga, tana ajiyewa a zuciyarta ta ce

'Da zafi-zadi ake dukan ƙarfe, kuma da sanyin safiya ake kama fara, ba zan tsaya kallon ruwa kwaɗo ya mini ƙafa ba, in dai zaman kishi ne ni babu macen da za ta iya gagarawa da ni domin sai na mata kishi da kissa ƴar ƙasa yadda sai ta ji tsanar gidan mijin da kanta don sai na takurawa kishiya" Ta faɗa tare da buɗe drower Sadiya ta shiga bincike kayan kawai take watsowa ƙasa amma bata ga abin da take nema ba. Haka ta gama bincikenta ta mayar da su yadda suke tamksr bata taɓa su ba domin ta iya takunta.

  Haka ta gama dubawa amma bata ga abin da take nema ba, ranta sai wuya yake saboda ta san tabbas yau wata dama ce da ta samu wacce ba lallai ta same ta ba. Ƙarƙashin gado ta shiga dubawa amma bata gani ba, tsaye ta tashi ta tsaya rana riƙe da tsantsa ta damƙe fatar bakinta da haƙorinta na sama. Duk cikin wani abu da take gani za a ɓiye abin da take nema ta duba amma bata gani ba, gadon ta taka ta duba saman drower nan ma babu sai da ta sakko ta lura da ƙaramar lokkar jikin bed side drower da sauri ta jufi can ta buɗe sama da ƙasa amma babu. Kasancewar biyu ne sai ta koma ɗaya gefen ta buɗe ta saman sai ta ga panties ɗin Kakifa ne a ciki wanda suke a laye, tsaki ta yi ta tuƙunɗuna su ta tura ta rufe lokar, tana janyo ta saman sai ta ga wata ƙaramar jaka pose taɓa jakar ta yi ai kuwa ta ji ɗan tudu da sauri
ta fito da jakar tana fatan a dace tana buɗewa kuwa ta ga abin da take nema wani murmushi mai bayyana haƙora ta yi ganin kuɗaɗen a ciki a laye suke kasancewar pose ɗin tana da ɗan girma, ƴan dubu dubu ne a laye sai ƴan ɗari biyar biyar sai ɗari bibiyu da ƴan ɗari ɗari. Ganin kuɗin cunkus sai abun ya bata mamaki a ƙiyasce tana tunanin kuɗin nan zai iya kusan kaiwa dubu ɗari. Fito dansu ta yi duka ta zige zip ɗin ta buɗe ɗaya gefen sai ta ga ƴan hamsin hamsin ne da sauran canjuna a ciki su kuma dai ba su fi dubu biyar ba fito dansu ta yi duka a fili ta furta


"Wai dama sana,ar cikin gida tana kawo kuɗi har haka? Lallai wannan ake cewa bar ganin ka tara ka kiyayi mai nema ashe har tana samun rufin asiri a sana,arta haka lallai na yi sake!" Ƙaran bugun ƙofar gida ne ya ankarar da ita vata san lokacin da ta tashi tsaye daga zaunen da take ba, ga kuɗin duk ta baza haka ta shiga haɗa su tana karkarwar jiki don ta san asirin ta zai iya tonuwa tunanin ta ma Sadiya ce ta dawo duba mukullin da ta jefar. Lokar ta mayar ta rufe ta naɗo ƙasan rigarta da ta zuba duka kuɗin sai da ta zo faon a guje sannan ta tuna da mukullin da suri ta juya ta ɗakko har lokacin tana ji an bugawa fitowa ta yi amma bata rufa ɗakin ba ta ce

"A nan ne? Waye?" Ta faɗa tana jiran jin muryar Sadiya kawai sai ta ji muryar wata yarinya ta ce


" Mango da zoɓo za a bani" Wani uban tsaki ta ja ta ce

"A kan wani mango za ki zo ki damu jama,a to an dajna siyar da mango da zoɓo a nan" Yarinyar ta ce

"To akwai pure water?" 

Meenal ta ce

"Babu pure water sai ubanki" ,Ta faɗa a zuciye yarinyar ta ce

"Na gane ki ba anty Sadiya ba ce kishiyarta ce ƴar baƙin ciki wataƙila antyn bata nan" Tana faɗar hakan ta ɗauki dutsi ta buga a ƙofar da ƙarfi ta zuga da gudu, Meenal tana so ta zo ta buɗe ƙofar ta kikkifawa yarinyar mari amma kuma abin da take yi ya fi wancan. Ɗakin ta koma ta ɗakko jakar ta rufe lokar ta tsaya ta tabbatar da komai yana yadda yake ta fito ta zo ta kulle ɗakin. Ɗakinta ta nufa da sauri ta je ta juye kuɗin a jakarta ta fito da pose ɗin a hannunta kicin ta je ta ɗakko ashana ta xo ta kyarta ta sakana jikin pose ɗin ganin jakar ta kama ta sheƙe da dariyar mugunta, sai da ta ƙone ƙurmus ta tattara ta kwshe ta je ta yi fuloshin ɗinsa a toilet.

     Mukullan ta ɗakko ta zo wajen zaure ta jefar da su a ƙasa ta koma ta kwanta a bedroom ɗinta tana lissafa kuɗaɗen da ba da guminta ba ta samu tana jin daɗinsu.

  A fili ta ce

"Sadiya mu zuba ni da ke yanzu dai baki da tsumi baki da dabara idan musgunawa ta ta ishe ki ke da kanki za ki san na yi" Tana cikin wannan maganar sai sheɗan ya ƙara kissima mata wani mugun abun da sauri ta tattara kuɗin ta mayar tana mayar da jakar drower ɗinta ta fito daga ɗakin, mukullan ta sake ɗauka sai kawai ta nufi kici ɗin Sadiya ta buɗe ta dawo ta buɗe ƙofa ta aiki wani yaro ya siyo mata kananzir ta rufe ƙofar ta je ta yi abin da za ta yi ta mayar ta rufe ta ta kai ƙaramar jarkar lemon coca cola da aka sayo a ciki ta ba wani almajiri shara ya zubar mata dama jarkar tana ciki.


 Sadiya sai bayan magriba ta dawo bata ma san ta jefar da mukullin ba sai da ta dawo ta buɗe aljihun jakarta ta ga ba ya nan ɗan ja baya ta yi tana haska fitilar wayarta kawai sai ta ga Kalifa ya miƙo mata mukullan ta tambaye shi sai ya nuna mata ƙasa kusa da inda take tsaye hakan ya sa ta gane a gabanta ya ɗakko sai ta yi tunanin yanzu da ta buɗe jakar ya faɗo bata sani ba.

   Hankali kwance ta buɗe musu ƙofar suka shiga don zuciyarta wasai take ji babu damuwa domin Kaka ta mata nasiha da kuma ƙara bata haƙuri a kan lamarin zaman auren ta tana nuna mata komai ya yi farko yana da ƙarshe don kowace gona tana da kunyar ƙarshe ta faɗa mata idan dai mace ta haɗu da fitinanniyar kishiya ko fitinanniyar uwar miji ko dangin miji sai ta yi haƙuri duk mai haƙuri watarana zai dafa dutse har ya sha romonsa. Ta ƙara koya mata dabaru da kissa da za take nunawa kishiyar duk abin da take mata ba ya damun ta.

  Sai batun ƙauracewa ɗakinta da Nasir yake da ma ƙaurace mata baki ɗaya shi ma ta ce ta yi haƙuri lokaci ne, sannan shi lokaci alƙali ne watarana da kansa zai neme ta don Kaka ta faɗa mata cewa namiji tamkar sauyin abinci haka ya ɗauki mace ta bata misali da cewa shin za ta juri cin abinci ɗaya kullum? Wato koyaushe a ce ta ci shinkafa da miya sai Sadiyar ta nuna za ta so sauyi watarana mana yau ta ci shinkafa gobe taliya jallof jibi wake da shinkafa ta haka Kaka ta nuna mata cewa to akwai ranar da Meenal za ta gunduri Nasir ɗin ya ji yana son kasancewa da Sadiya don kowacce mace halitta da baiwar ta da ban wata ta fi wata kawai dai idan kana da kyau sai ka ƙara da wanka!.

 Sai da ta buɗe drower za ta ɗakko rigar bacci bayan ta yi wanka sai kawai ta ga kamar dai kayan ba haka suke ba, saboda Sadiya tana da lura da al,amura kawai sai ta fara zargin kayanta ba haka ta bar su ba duk kuwa da Meenal sai da ta gyara komai, a ƙarshe Sadiyar ta saka a ranta cewa ita da ta kulle ƙofar ɗakinta kuma ma ai babu yadda za a yi a shigo mata ɗaki me ma za a yi a ɗakinta.


   Bayan sun kwanta Kalifa ya yi bacci, don tana jin lokacin da Nasir ya dawo amma ko ɗakinsu bai zo ba dama kuma ta san da hakan. Kuɗin da maƙociyar Kaka ta bata na kayan kori da spices da ta ce a turawa maman afrah za a kawo musu curry kwano ɗaya spices na shayi rabin kwank sai spices na girki kwano ɗaya, jan yaji rabi yajin daddawa kwano ɗaya, sai kuma kuka da kuɓewa da niƙƙaƙƴiyar daddawa.  Don ita ma natan babu, kuɗin ta ɗakko ta lissafa tana tunanin da safe za ta yi wa maman afrah magana ta tura kuɗin sai a sako musu a mota. Lokar da take ajiye kuɗaɗenta ta buɗe za ta saka kuɗin a ciki domin tana da kuɗi a monie point sai ta yi wa maman afrar transper, tana buɗewa ta ga wayam babu jakar gabanta ya buga da mugun ƙarfi, ta sake dubawa amma babu jaka babu alamar ta, lokar ta ciro daga ciki dukanta ta shiga leƙwa amma jakar ta ce ɗaukeni inda kika ajiye!.

  MAMAN AFRAH
   ***