ZAKIYYA Matashiya mai juyayyiyar Kaddara
5
by @sadiyanasir
Aliyu tun daga wannan rana bai sake zuwa gidan su Zakiyya ba. Amma kullum cikin tura mata saƙon gaisuwa cikin ladabi irin saƙon da yake bayyana kulawa da addu’a a gare ta ba tare da takura ko matsi ba. Irin sak'on nin da Aliyu ke tura mata yana sa taji nutsuwa a zuciyarta, lokuta da dama idan ta karanta takan tsinci kanta da murmushi tare da Tura mishi sakon
“Na gode da kulawa.”
Cikin ranta kuwa ta kan yaba kulawar da Aliyu yake bata, tana jin natsuwar da bata tab'a tsammani akan saba. Tsawon kwanaki goma sha takwas Aliyu ya d'auka kullum cikin Tura wa Zakiyya sako yake, A hankali ta fara sabawa da saƙon shi fiye da yadda bata zato. Ta kan so tace mishi yaushe zai zo, amma tunanin abinda za tace mishi sai ya hanata rubuta hakan, amma tabbas tana so ta sake tozali dashi ko da sau d'aya, don shigowar Aliyu rayuwarta ya rage mata radadin zuciya.
*****
Zakiyya ji tayi yau tana son tayi kwalliya, don rabonta da yin hakan tun lokacin Auren ta da Mahmod. Shaddar da tasa ranar wunin bikin ta shi ta d'auko ta saka ta d'anyi kwalliya kad'an. Tsakar gida ta koma ta zauna tacigaba da latsa wayarta tana bin duk message d'in da Aliyu yake Tura mata tana sake karantawa, kallo d'aya za kayi mata ka fahimci tana jin nishad'i a wannan lokaci. Sallamar da taji da muryar Gardawa yasa tayi saurin d'agowa. Halilu ɗan uwa ga Mama Rakiya ne ya shigo. "Sannu da zuwa Kawu Halilu?". Tayi maganar a ladabce tana mai durkusawa ta mika gaisuwa, idon sa akan Zakiyya sai wani lumshe ido yake yana kare mata kallo mai rikitarwa. "Maman tana ciki". Zakiyya tayi maganar tana wucewa d'akin ta. Miyau mai d'aci ya hadiye ya dan lashe baki ya wuce d'akin Mama Rakiya. Bai tsaya sunyi dogon gaisuwa ba yace. “Rakiya, wannan yarinyar Zakiyya Allah ya yi mata kyau sosai, da zaki bani ita mana?.”
Maganar Halilu ta shiga cikin zuciyar Mama Rakiya kamar wutar da aka hura da mai. "Halilu Zakiyya kuma?". "Eh mana Rakiya ko ban dace bane? In har ba maganar wani a k'asa ina ciki don Allah?". Ajiyar zuciya Mama Rakiya ta sauk'e. "Eh to gaskiya kwanaki Zahra tazo min da magana akan wani da suke tare, amma zanyi magana da ita, idan har basu tsayar da magana ba sai ka shigo". Washe baki yayi. "Gaskiya da zanyi miki babban tukuici Rakiya". "Uhumm kaji dashi". Su kayi dariya gaba d'aya.
Sai da Malam ya dawo bayan sallar Isha'i kafin Mama Rakiya ta d'ago da maganar. "D'azu Halilu yazo akan zancen Zakiyya, kuma bai zo da wasa ba, to kwanaki akwai wani da yazo, yanzu zan kira naji idan har babu wancan maganar zanba Halilu ita". Kallon ta Malam yayi wani miyau mai d'aci ya tsaya mishi a makoshi. "Halilu kuma Rakiya?". Tamke fuska Mama Rakiya tayi. "Eh ko shi d'in ba mutu bane? Wallahi matukar ba wancan maganar dole ta zamo Matarsa, akan me Miji yazo ace ba za'a bashi ba, jika ta za muyi musha ko meye? Idan kai zaman nata yana burgeka toni maganganu daga Makota sun isheni". Shuru Malam yayi baice komaiba sai zafi da zuciyarsa take.
Cikin gaggawa ta soma kwala kiran Zakiyya.
Da sauri ta shigo ta durkusa. "Gani Mama?".
"Zahra tace min kina da wani Bazawari, shin kuna tare ko kin sallamesa? Domin Halilu ya ganki kuma yana bidar Auren ki, shiyasa nake so naji wancan maganar ina ta kwana?".
Zuciyar Zakiyya taji ya tsinke. miyau ta makale mata a makoshi. Ta san me zai biyo baya idan ta ce basu tare da Aliyu, Ta kuma san halin Halilu farin sani, mata uku garesa, ga tarin Yara ko wacce ita ke daukar nauyin kanta, babu mutunci a bakinsa, babu tausayi a halayensa. tsintar kanta tayi da cewa. "Mun gama magana da shi, yanzu haka Maganar sadaki muke.” Ta fada cikin rawar murya ba tare da ta shirya wannan karya ba.
“Shikenan,” Mama Rakiya ta ambata da murmushin da yafi kuka ciwo. “Idan kun gama dai-dai tawa ki turo shi gida a tsayar da lokaci. Bana son neman bata lokaci.” "To Mama". Zakiyya ta ambata ta mike jiki a sanyaye ta fita. Duk da ta samu mafita akan zancen Halilu amma zuciyarta take ta soma bugu tamkar ana bugun ganga a cikin kirjinta. mamakin kanta take, me yasa ta yi wannan karya? Me ya sa ta ce ta amince da Aliyu alhali babu wannan maganar? Tunawa da mugun halin Halilu da tabargazar da matansa ke yi kullum cikin kuka da cin zarafi yasa ta sauk'e numfashi tana jin a zuciyarta hakan da tayi shine dai-dai. Tunawa da irin karamcin Aliyu da yanda yake nuna mata kulawa Uwa uba natsuwar sa, maganarsa, yanda baya takura ta, yanda kullum yake tuna mata da Allah. Tsintar kanta tayi dayin murmushi ta kuma kudurta a ranta gobe zata kirasa yazo suyi magana don tsira daga tarkon Halilu. Da wannan tunani bacci ya ɗauke ta.
*****
Da asuba bayan ta idar da sallah, hannunta na rawa ta ɗauki wayarta ta rubuta sako kamar haka
“Aliyu… don Allah ka zo yau Ina son magana da kai.”
Bai dauki lokaci ba ya turo mata da amsa kamar haka.
"Ina maraba da duk lokacin da kike bukatar ganina, in sha Allah anjima kad'an ina tafe.”
Dogon numfashi taja ta ajiye wayar tacigaba da lazimi har gari ya soma Haske kafin ta fita ta soma had'a kunu. Tunda ta fito gun sana'arta take raba idon ganin Aliyu amma abin mamaki harta kammala ta shigar da komai bai zo ba. Jikin ta a sanyaye ta shiga wanka, fitowarta yayi dai-dai da Kiran wayarta da akeyi, da sauri ta isa d'aki ganin number Aliyu yasa ta d'auka murya a sanyaye. "Ki garceni Zakiyya uzuri ya hanani zuwa akan lokaci, yanzu gani a kofar gidan ku". "Toshikenan gani zuwa". Ta ambata gamida ajiye wayar ta shirya a gaggauce ta fita. A dakalin kofar gida ta sameshi zaune, tunda idonta ya sauk'a akan sa ta soma jin Mummunar fad'uwar gaba da bata San dalili ba, gefe kad'an ta zauna kanta a k'asa. "Barka da zuwa". "Yauwa barka Zakiyya da fatan na sameki lafiya?". "Alhmdullah lafiya kalau". "Masha Allah". Shuru ne ya biyo baya na d'an lokaci kafin Zakiyya ta soma magana cikin tsananin kunya da nauyin zuciya.
“Aliyu… na kira ka ne saboda wata magana mai muhimmanci. Bansan ta inda zan fara ba, amma ya zamo dole nayi ta” D'ago ido Aliyu yayi ya kalleta kad'an ya sauk'ar da kai, ba tare da ya matsa ta ko ya nuna damuwa ba. Muryarsa a tausashe kamar iska mai sanyaya zuciya. "Ki kwantar da hankalinki Zakiyya ki sanar dani komai, karki damu In sha Allah zan fahimce ki.”
Numfashi ta sauke a hankali hannunta na rawa tana dan murza yatsunta. "Dama jiya d'an uwan Mama yazo” Tsayawa tayi da maganar jikinta ya dauki rawa. D'ago ido Aliyu yayi kadan alamun sauraro. "Kawu Halilu ya samu Mama Rakiya da zancen yana son Aure na. Na san halin shi sosai nayi mishi farin sani tabbas ba Mutumin Arziki bane, ba zan iya shiga gidan Kawu Halilu matsayin mata ba.” Ta runtse ido, hawaye na taruwa a gefen gashin idonta. “Don tsira daga fad'a wa hanun Kawu Halilu na faɗa musu cewa kai da ni mun gama magana tura ka gida nake shirin yi .”
Aliyu bai nuna yaji mamakin maganar ba. Bai kuma zaro ido na jin ba zata da tayi mishi ba, sannan bai yi wata tambaya da zata kara gigita ta ba. Sai dogon numfashi daya sauk'e mai nauyi kamar wanda ya daɗe yana tunanin irin wannan rana zata zo. "Amma kayi hakuri da irin gangancin da nayi?". Murmushi Aliyu yayi daya baiyana hakorar sa waje. "Kina jin cewar kamar ba kiyi min adalci ba?” Zakiyya ta share hawayen gefen idonta da zanin jikinta. “Bazan boye maka ba… ban san me yasa na fadi hakan ba, nayi haka ne don nema wa kaina mafita Amma bana son ka ji kamar ina tilasta ka ko ina saka ka cikin wani yanayi” Shiru ne ya sake rufe tsakanin su amma irin shiru mai dadi, wanda muryoyi ke daɗa bayyana a fili.
Aliyu matsawa yayi kad'an kusa da ita cikin nuna kulawa.
“Zakiyya… tun ranan farko da na ganki ina cikin damuwa, na yi addu’ar Allah ya bani kwanciyar hankali akan ki. Duk abin da ya kawo ki gare ni yau ba tilas ba ne Addu'ar da mukeyi ne, ki sani babu wani abu da kika fada da zai daga min hankali.” murmushi ya sakeyi mai nutsuwa.
“Amma zan Tambaye ki abu guda ɗaya amma kada ki yi min karya gazkiyar ki nake da bukata. Shin kina jin zaki Aure ni don mafita ne ko kuwa kin samu nutsuwa da nine?.”
Numfashi ta taji ya tsaya . Har yanzu kanta a kasa, amma zuciyarta tana bugawa kamar ana kirga mintina tsakanin rai da mutuwa. Bud'e baki tayi da siririyar muryar ta.
“Nayi maka karya a gida ne don tsira daga ukuba.” ta tsaya, zuciyarta na rawa, “ban san me yasa zuciyata take jin natsuwa idan ina karanta sakonninka ba. Ban saba jin haka ba tun rasuwar Mahmod.”
Aliyu ya dan sunkuyar da kai. Wannan karon shima kalamanta sun taba shi.
“Shikenan,” ya ce cikin sanyin murya. “Idan abin da ya faru ya sa na zama kariya a wajanki even na ɗan lokaci wallahi babu abin da ya kaishi dadi.” Zakiyya tayi shiru tana jin yadda maganarsa ta ratsa ta. Tana jin wani irin sauki a kirjinta da bata taba jin irinsa ba tun rasuwar mijinta.
Aliyu ya mike a hankali. “Bari na koma kafin mutane su fara fitowa su ganki a nan. Ki kwantar da hankalinki. Maganar Halilu ni zan tsaya a tsakanin ki da wannan lamarin.” Ya dan yi murmushi, “Idan kuma kina so mu yi magana sosai ki bani lokaci na musamman ba irin wannan ba, zan zo duk lokacin da kika shirya.”
Zakiyya bata motsa ba, sai kai data ɗago a hankali. Idonta cike da rawar jin tsoro, kunya, da wani natsuwa mai sanyi. cikin siririn murya tace
"Na gode… Aliyu.”
Ya daga kai yana yi mata nuni da girmamawa, sannan ya juya ya tafi cikin nutsuwa kamar wanda ba ya son daukar hankalin kowa. Idon ta akan sa harya b'ace ma ganinta ta dafa kirjinta. Zuciyarta na bugawa sosai ba bugun tsoro ba, bugun sabon abu da ya fara girma a hankali, wanda bata san sunansa ba tukuna.