AGOLA (Behind the palace walls)

Chapter 57

by @hauwajaywrites

Ta fito tana sanye da blue Abaya, kallon Nawaf dake kwance jikin Ammi tayi tace "Nawaf, I'm going to see uncle, do you want to come with me?" da sauri ya tashi a jikin Ammi yana kallon Leena yace "Yes Amma!" ya karasa wajan ta da gudu, tana dariya ta rike hannunsa, tana kallon Ammi tace "Ammi sai na shigo" tace "Okay" daga haka suka fita tana rike da hannun Nawaf tun basu karasa compound ɗin ba Nawaf ya cire hannun sa a nata ganin Abban sa da yayi da gudu ya tafi wajan sa, shima da tun fitowar su idon sa na kan su, fuskar sa ɗauke da murmushi ya karasa ya daga Nawaf sama yana dariya shima Nawaf ɗin dariya yake yi, bayan Leena ta karasa ta taɓe baki tace "toh ko na koma ne tunda naga kamar wajan Nawaf ka zo?" ya ɗan tsakaita dariyar sa yace "Sorry, Madam" ta wuce ta zauna kan dadduman da aka shimfiɗa masa ta fara danna wayan ta, Malik ya juya ya bi bayan ta yace "wallahi Abaya ba karamin kyau yake miki ba, idan nayi kuɗi dole kayan sakawan kanwa ta ya koma Abaya" ta ɗanyi murmushi ta ajiye wayan ta tana gaishe sa, Malik ya rasa menene but He really knows one thing for sure, sai yana tare da Leena ne kaɗai yake samun wata nutsuwa da kwanciyar hankali, duk wata damuwar sa sai ya nema ya rasa and He always feels connected to Ammi so much because he experiences a peace that comes when he is in her presence, shiyasa baya yarda har ya zo gidan ba tare da ya gaishe ta ba, tamkar wata ɓarin shi yake jin ta, a hankali yace "Leena" ta zuba masa ido tana kallon sa, bayan sun ɗanyi hira yace "Toh kai ni wajan Ammi na na gaishe ta" tace "Okay" yana rike da Nawaf ya mike, tun da Mummy ta shigo da motar ta tayi parking idon ta na kansu, Malik ya kalle ta ganin kallon kurullan da take musu yasa a hankali ya juya yana kallon Leena da tun sau ɗaya ta kalle ta ta ɗauke kai yace "Who is she?" tace "Dan Allah kar ka sake kallon direction ɗin ta, Step Mum ɗin Ayaan ne" Malik ya dinga kallon ta da mamaki sai kuma yace "Toh ai dole zamu gaishe ta" tace "Ka gaishe ta amma banda ni" Malik ya sake juyawa yaga har sannan fuskar ta da mamaki karara yace "Good evening, Ma'am" da accent ɗin sa mai daɗi, ga mamakin sa yaga ta ɗauke kai ta wuce ciki kamar zata tashi sama, Leena na kallon sa tace "Na you sabi, ai sai da nace karka gaishe ta, toh kadan ma ka gani" daga haka suka wuce ciki dan gashe da Ammi da yace. Wannan ranan Mummy ta kasa bacci, fuskan Malik haka ya ta mata gizo, ga kuma wani bugawan da zuciyar ta yake yi idan ta tuna, wani zufa ne yake karyo mata idan har ta tuna cewa Leena zata sake aure kuma bata ga alama dai wannan jikin sa yasan wahala ba, sai ta mike zaune a razane. Layla ta raka mijin ta har bakin motar sa sai shagwaɓa take zuba masa, bayan ya shiga motar ta mika masa jakkan sa cike da shagwaba tace "kace ma Babyn kar yayi motsi ni kam" ya jawo ta sannan yayi kissing dogon cikin ta yace "Hey! Our very own unborn, yau kar ka buge Momman ka ko? tana jin zafi, idan zaka yi motsi kar kayi da karfi, Okay ɗan Albarka?" Layla ta turo baki tana kallon sa "wato ma yayi motsi zaka ce masa?" Yayi dariya yace "toh ai ya zama dole yayi motsi Baby, alamar yana lafiya kenan" ta sakar masa murmushi tace "A dawo lafiya" daga haka ta juya zuwa cikin gidan shi kuma ya wuce office. Mama dake zaune ita da yaran ta Ayrah da Baby, tana kallon su tace "Toh ai sai kuje mata weekend ɗin nan, idan kuma ta shiga watan haihuwar ta ke Baby sai ki koma gidan da zama tunda Ayrah aure zata yi, dan ma mijin na ta likita ne" Ayrah tayi dariya tace "Kai wallahi ban taɓa ganin wanda soyayya ya canza sa ba kamar Anty Layla, da a gidan nan ko kwano bata ɗauka da sunan aiki balle shara, hatta ɗakin ta fa sai dai nayi zuciya na gyara mata amma wai yanzu ita ce mai gudun housegirl wai zata na kallon mata miji" duk suka kwashe da dariya Mama tace "Amma ina bata kazan ta ko?" Baby tace "Chap, ai Mama idan kika je gidan Anty Layla banda kamshi da sheki babu abun da yake yi, kuma da kanta take yi" Mama tace "Dama iskanci ai guri ya samu" kamar daga sama suka jiyo muryan Mummy na doka sallama, Ayrah ta kalli Mama tace "Mama dan Allah kar ki kula ta, yanzu wani matsalar ta ne ya kawo ta" Baby ta taɓe baki tace "yau tasan da gidan nan kenan, ina ko sannu bata cewa Anty ba" Mummy ta sake doka sallama Mama ta taɓa Ayrah data amsa, Ayrah ta amsa, sai gashi ta shigo a birkice kamar wacca ta fito daga prison, su Ayrah suka gaishe ta daga haka suka mike zuwa ciki, Mama ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya tana girgiza wa, ta turo ɗan-kwalin kanta zuwa goshin ta tana kallon Mummy irin kallon rashin mutunci, Mummy tayi yake tace "Haba Aminiya ta" Mama tace "ki faɗa me ya kawo ki ki bar min gida Malama" Mummy tace "yanzu dan Allah akwai abinda har zai shiga tsakanin mu? Haba mana, so kike duk zumuncin mu ya watse?" Mama tace "kin gama?" Mummy ta zauna dirshen kasa tace "Dan Allah ba wannan ba, wallahi wata matsala nake ciki, ba matsala ba ma, matsalsalu ne suka min yawo, and I'm ready to spend ko nawa ne" Mama nan da nan ta sake fuska tace "Haba, ai ba wanda zai ji kanmu, kar ki damu komai ya wuce ai" Mummy tace "Nagode, wallahi kin san Shegiyar Leenan nan ta kawo wani gaye? Ina faɗa miki mutumin nan yayi mugun haduwa iya karshe, taya ina raye zan bar Leena da wannan mutumin" Mama tace "Sai me kuma?" Mummy ta gyara zama ta fara koro mata bayanai. Bayan tafiyar Mummy, Mama ta jawo wayar ta ta shiga kiran Layla, Layla dake kitchen tana dafa Lunch ta fito a kitchen ɗin tayi wajan wayan na ta da ɗan sauri, ganin Mama yasa ta ɗauka ta samu waje ta zauna, ko amsa gaisuwar ta Mama ba tayi ba tace "Layla kina jin surkuwar ki yanzu ta bar gida na" Layla ta sake baki tace "Toh uban me ya kawo ta? yanzu kila Leena tayi sabon saurayi ko kuma dan motar da aka tsayawa Ammi" Mama tayi 'yar dariya tace "Kin gama sanin halin matan nan" Layla tace "Allah yasa baki kula ta ba?, Ki cemin korar kare kika mata, please" Mama tace "kee, ai na kula ta, Malami na take son na kai ta" Layla tace "Mamaaa meyasa zaki kula ta dan Allah?" Mama tayi wani murmushi tace "Haba Layla, sai kace baki san wayee mahaifiyar ki ba? dama auren Ayrah ya tsaya min a rai, yanzu kinga zan samu na zare kuɗin gado da kujeru a jikin ta baki na alaikum" Layla tayi dariya tace "Kai wallahi Mummyn nan bata da wayo kwatakwata, haka fa Mama a jikin ta kika min kayan kitchen, dake ita tasa ran Malamai bata gane komai ba" a haka suka dinga hira Layla tunawa da tayi da girkin ta yasa ta yanke kiran ta wuce kitchen. Gaba daya Mummy ta rasa meke mata daɗi damuna ya sake cunkushe mata amma tun da ta samu Mama take jin ta at ease, dan ta lura Kawarta Amina bata kai Aminiyarta capacity ba, tana zaune a office ɗin ta tana cika wasu files sai ga kiran Mama ya shigo wayan ta da sauri ta ɗauka gudun kar ya yanke bayan sun gaisa Mama tace "Toh Mutumin nan yace ki turo da 100k kafin a fara aiki" Mummy tace "Toh turomin da account numbern da zan sa kuɗin a ciki" daga haka ta katse immediately sai ka text ɗin Mama da account numbern Ayrah, Mummy tayi forwarding wa Rayyan, ganin haka Rayyan dake zaune a office ɗin sa dan ya gama aikin sa na wannan ranan ya kira Mummy dan neman karin bayani game da Account details ɗin, da sauri tayi receiving bayan ya gaishe ta ta amsa tace "Kaga account details ɗin da na tura maka?" yace "Eh, Mummy" tace "yanzu nake son ka tura 100k ma account ɗin sai ka turomin da evidence of payment" yace "Toh Mummy, bari zuwa ko anjima zan tura" ta masa tsawa tace "Yanzu nake bukata Malam" yayi ɗan shiru sai kuma yace "kiyi hakuri, bari na tura yanzu ɗin to" daga haka ta katse kira ta mike ta fara tattara kayan ta zata wuce gida. Leena na kwance jikin Ammi tana karanta message ɗin Muhammad daya tura mata tun jiya sai yanzu ta buɗe, ta mikawa Ammi tace "Ammi ki kalli message ɗin Muhammad" Ammi ta karɓa ta gama karanta komai sai ta kalli Leena tace "Allah sarki, yana jin ba daɗi ne amma tunda har ya nemi yafiya kuma yace shi bada sanin sa bane kuma har kinyi aure ki yafe masa kawai" Leena ta mike daga jikin Ammi tace "Ammi Ni fah ban rike sa a rai ba" Ammi tace "Sure! Kawai kice masa komai ya wuce ai tuntuni" Leena ta gyaɗa mata kai ta shiga typing. Washe gari da yamma, Leena na zaune tare da Malik da yake bata labarin tana ta dariya dan ita har mamaki how nice He is take yi, Rayyan ya shigo ya same su a haka ya karasa suka gaisa da Malik, Leena ta kalle sa tace "Ina wuni Yaya, Anty Layla da jiki?" yace "Alhamdulillah" yana kallon Malik yace "Idan zaka tafi let me know, please" Malik na murmushi yace "In Shaa Allah" daga haka Rayyan ya wuce cikin gidan, bayan wasu mintuna Malik yace zai tafi hakan yasa Leena kiran Rayyan a waya yana ɗauka tace "Yaya yace zai tafi wai" yace "Okay, ce masa ina zuwa" daga haka ya katse kiran Leena na kallon sa tace "Barin shiga, Chat you later" yace "Okay, sister" daga haka ta shiga bayan ta hango Rayyan na taho wa. Sake gaisawa suka yi, Rayyan yace "Dama magana nake so muyi Malik idan har ba damuwa" Malik da accent ɗin sa yace "Okay, Babu damuwa ina ji" Rayyan yace "Naga kana yawan zuwa wajan Leena, and duk lokacin da kazo nakan ganta tana walwala sosai har da dariya ma, shine nake son dan Allah ka faɗamin me a tsakanin ku?" Malik yace "Nothing, sir. Kawai dai na ɗauke ta tamkar kanwa ta ce dan ina jinta sosai a jiki na, kuma ina tsananin tausayin ta dan tausayin nata ne ma yasa har muka shaku yanzu" Rayyan yace "So fah?" Malik yayi shiru Rayyan yace "Talk to me please, say out your mind?" A hankali Malik yace "Idan nace maka bana son ta nayi karya, da farko a matsayin sister na ɗauke ta amma daga baya komai ya juya har ina ji ba zan iya rayuwa ba tare da ita ba" Rayyan ya rintse ido, yace "Why not ka faɗa mata?" Malik yayi murmushi yace "A'a, saboda kullum maganar ta ba zata sake aure a rayuwar ta ba, hakan yasa saboda kar na rasa ta na gwammaci nayi shiru" Rayyan yace "Zan mata magana" Malik ya kalle sa yace "A'a kar kayi, nasan yaudarar kai na nake yi, ba zan iya rike Leena ba, salary na bai taka kara ya karya ba sannan kuma Ni ke ɗauke da nawin iyaye na, ina jin abincin da Leena zata ci a wata har ya wuce salary ba, balle ma yanzu bani da kuɗin auren" Rayyan yace "Zan maka akwati da kuma Sadaki, and I promise you in shaa Allah bayan auren zan nema maka aiki" Malik speechless ya tsaya kallon Rayyan, Rayyan ya gyaɗa masa kai. Leena taji karan shigowan message wayan ta, zata karbi wayan a hannun Nawaf ya fara tsala mata ihu da kyar ta lallaɓa sa ta karɓe, ganin alert ɗin 300k tayi ta kalli Ammi tace "Ammi kin san nawa Sadeeq ya turo?" Ammi tace "sai kin faɗa" tace "300k fah, amma yana da hankali kuwa? Ko ce masa akayi Nawaf yana iya cinye 200k da yake turowa a baya ne" Ammi tayi murmushi tace "kila yanzu zai ce ai Nawaf ɗin na girma ne Shiyasa ya kara, amma Nawaf ɗin nawa yake ma ai ko 50k ne ba zai cinye ba" Leena ta taɓe baki Ammi tace "Inaga har da ke yake yi" Leena tace "A'a fah, dan ɗan sa yake yi" daga haka ta shiga typing ta tura masa message ta mika wa Nawaf wayan. Bayan isha'i kamar daga sama suka jiyo muryan Mami na sallama Ammi ta amsa mata, bayan ta shiga Nawaf yaje wajan ta da gudu yana murna, ɗaga sa sama tayi tana masa dariya kamar yadda shima yake mata, wanda ya kawo ta ne ya fara shiga da wasu kaya yana ajiye wa nan bakin kofar, kayan wasan yara ne birjik Mami ta tsayawa jikan ta, su keken yara, motar wasa and other stuff, Ammi ta tsaya kallon wanda ke shigo da kayan har sannan, can sai ga Leena ta fito sanye da hijabi ta karasa tana gaishe da Mami, Mami da fara'ar ta ta amsa tana tambayar ta ya hidima, kallon kayan da aka shigo da su tayi tace"Allah amfana Mami" Mami bata ce mata komai ba, Nawaf duk da bayi da wayo amma yasan cewa kayan na shine sai murna yake yana nuna wa Amma, daga haka Leena ta mike ta koma ciki, Ammi ta lura kamar har sannan Mami na jin kunyar ta dan haka yasa Ammi janta da hira, da zata tafi Ammi ta kwalawa Leena kira bayan ta fito tace "Mami zata tafi ne" Mami ta juyo tace "kinga na manta Jiddah fa ta haihu" Ammi tace "Ma Shaa Allah, me ta samu?" Leena tace "Allah sarki, ina jin yanzu bata da layi na ko nice banda nata dan yanzu bana ganin ko status ɗin ta ma" Mami na murmushi tace "Ta samu 'yarta, eh toh ina ji itace bata da naki dan kwanaki ta canza waya" Leena tace "Mami ki gaishe ta kafin naje" tace "In Shaa Allah" daga haka Leena ta koma ciki, Ammi kuma ta raka ta har gate. Tunda Malik ya koma gida maganganun Rayyan ne ya tsaya matsa a rai, at this point zai iya cewa be san me takamaima yake ji a ran sa ba, fargaba ne ko tsoron ratsa ta, ya jingina kansa a jikin wall ɗin ɗakin sa yana tunani dan haka ne ma yau da daddare ya gagara kiran ta dan bai san ko Rayyan ya tsanar mata ba.

***