AGOLA (Behind the palace walls)
Chapter 66
Chapter 66
Bayan wata takwas....
Leena da Malik sunga jarabawar rayuwa, har sannan Malik baya aiki, gashi kuma Daddy kamar ma ya manta da batun nema masa aiki, Rayyan kam avoiding duk wani abu da zai haɗa sa da Leena da Mijinta, avoiding ɗin sa yake yi, sai dai bayan ko wani karshen wata yakan ma Leena transfern 70k, duk da cewa yanzu mata biyu gare sa Leena duk san da ta samu kuɗi kuma food stuff take fara siya tunda ba aiki yake yi ba, hakan yasa Umma ɗan sauko wa, Ammi ma duk sanda ta samu kuɗi akan Leenan yake kare wa, duk wani abu da ya shafi Malik Daddy yama mance balle ya sama masa aiki, gaba ki ɗaya rayuwa ta juya musu baya. Leena tayi sallama a parlorn Mami, Sultan yace "Shigo mana Maman Nawaf" tana kan shiga ta ga Farida ta mike ta wuce ciki da ɗan saurin ta, hakan ya bata mamaki dan ta taɓa ganin ta a wani taro amma ta ɗauke kai hakan yasa tace kila bata gane ta bane, ta karasa cikin parlorn taga ashe ba Sultan kaɗai bane harda Sadeeq, hakan yasa kawai tayi gaisuwar in jam'i tace "Ina kwanan ku" Sultan yace "Lafiya klau, Leena" ta ɗan kalle Sadeeq taga danna wayan sa yake ba tare da ya ɗago ba ta taɓe baki tana kallon Sultan tace "Uncle Mami fah?" Yace "Tana ɗakin ta, ki shiga mana" hakan yasa ta karasa bakin kofar ɗakin Mami tayi sallama, Mami tace "shigo mana" Leena ta shiga, Nawaf ta kalla yana kwance jikin Mami, ta karasa ta zauna bayan sun gaisa tace "Ya jikin nasa kuma Mami?" Mami tace "da sauki Leena" Leena idon ta na kan Nawaf Mami tace "Nawaf je ka gaishe da Amma ko?" Sai ya mika mata hannu Leena ta ɗauke sa tana kallon sa duk surutun Nawaf da bakin sa yau tunda ta gansa haka ta san yana jin jiki, a hankali tace "Sannu Babyn Amma ko?" Ya gyaɗa mata kai, sai kuma ta mayar sa wajan Mami ta miƙe, tana kallon Mami tace "Bari zan tafi Mami dama nazo duba jikin na sa ne" Mami tace "Yanzu baki son zama idan kika zo, ko fah ruwa baki sha ba amma kike maganar tafiya" tayi yake tace "Wallahi Mami gidan kawata Zahra zan tafi, tun da akayi bikin ta ban taɓa zuwa ba" Mami tace "Ayyah, ki gaishe min da ita" Leena tace "In Shaa Allah" har ta fara gaba sai kuma Mami tace "Idan yayi hutu a school zai zo miki" Leena ta tsaya tana kallon Mami tace "Ni Mami nake ga da an bari ya cika shekara uku tukun nan amma yanzu me Nawaf zai iya?" Mami tace "A'a babu ruwan ki, ko asara ne zan biya wa jika na" Leena na dariya ta mata sallama ta fita ganin yadda Mami ke son Nawaf har mamaki take, Mami ta bita da kallo ganin kamar ciki ne da ita, a compound ta ga Sadeeq shi kaɗai har zata buɗe gate taji yace "Leena!" Ta ɗan saya sai kuma ta juya tana kallon sa ya karasa inda take sai dai ya ɗan bada distance between them yace "I'm sorry" tace "For?" Yace "Everything" ta dinga kallon sa da mamaki a hankali yace "Na san nayi making mistake, let bygones be bygones, kawai dai at least da nace sorry tun daga farko, tun da nasan ban kyauta ba" tayi murmushi tace "Ni nama manta dan ban rike komai a raina ba shi yasa nayi moving up" yace "Thank you" bata kara ce komai ba ta fita, ta shiga Motar ta da tayi packing a kofar gidan kallon inda ta taɓa zama a wajan years back, yadda Sultan ya tsaya yana mata magana, murmushi tayi ta tada motar ta bar wajan. Bayan tayi parking a kofar gidan Zahra ɗaukan wayan ta tayi ta duba address ɗin dan ta tabbatar da house no. Ganin gidan ne yasa ta sauka gatekeeper ya buɗe mata gate ta shiga a kofar parlorn ta danna bell ganin ba'a zo an buɗe ba yasa ta kira Zahra tana dauka tace "Ke gani a kofar parlorn ki" tana katse wayar aka buɗe kofar, mamakin ganin wanda ta buɗe mata kofar yasa ta tsaya kallon ta, Niswa tace "Ohh really? Da gaske Leena kece kika zo min?" Leena ta sake zama frozen jin furucin Niswa, ta kirkiri murmushi Niswa ta kama hannunta ta ja ta suka shiga parlorn sai ga Zahra ta fito daga dakin ta ita ma tsayawa tayi, ganin inda Leena ke kallo yasa Niswa kallon wajan, sai kuma ta ga Zahra, ta sake hannun Leena har sannan kuma murmushin fuskanta bai ɓace ba tace "Ashe ba waje na kika zo ba ko?" Leena taji wani iri tace "Kai Anty Niswa" Niswa ta kama hanyar ɗakin ta tace "Eh mana, Nima nayi mamakin ganin ki, ai baki taɓa attempting zuwa min ba" sai Leena ta ji wani iri, jiki a sanyaye tabi bayan Zahra, bayan ta zauna tana kallon Zahra tace "kar dai Niswa ce kishiyar ta ki da kika bani labarin ta?" Zahra tace "Eh Nima ban san hakan ba sai bayan da aka yi bikin sannan nake ganin cewa ita ce, amma kamar ita bata gane Ni ba" Leena tace "Ai da kin gaya min" Zahra ta harare ta tace "Na faɗa miki? Ai na san idan kika sani ba zaki zo ba" Leena tace "Dan Allah Zahra kuyi zaman lafiya, ki bata respect tunda dama ta girme mu, beside Kinga ko a wajan mijin ku itace uwar gidan" Zahra tayi dariya tace "Sannu Leena uwar son a zauna lafiya, toh ce miki nayi ina raina ta? Ai naga ta canza ba kaɗan ba dan Kinga yanzu wajan 5 months nake gidan nan daga ni har ita muna avoiding abun da zai shiga tsakanin mu na raini" Leena tace "Sure, yanzu ba kamar yadda take a da bane" Zahra tayi dariya tace "Ashe dai mun sake samun karuwa?" Leena ta harare ta tace "Ban sani ba" tana kara jan veil ɗin jikin ta, Zahra ta mike, taje ta dauko mata drinks da snacks, can Leena kuma ta wuce parlorn Niswa, bata daɗe ba tayi mata sallama. Leena na shiga parlorn Ammi ta zube akan kujerar Ammi tace "Oops wallahi nagaji" Ammi tace "Sai kace wadda tayi tafiyan kafa" Leena tace "Ammi ba kin san Zahra mai mata ta aura ba?" Ammi tace "Eh Meya faru?" Leena tace "Wallahi ashe mijin Niswa ne, shi kuma ɗan uwan su Zahra ne" Ammi tace "Ikon Allah". Leena bata wani dade sosai a gidan Ammi ba ta wuce gidan ta, tun kafin ta gama parking motar ta taga ana waso da kayan su waje, da sauri ta sauka tana "Malam lafiya?" Ganin Malik yana zaune a gefe yayi tagumi yasa ta yi wajan sa da sauri tace "Zauji, meke faruwa ne?" Ya ɗaga jajayen idon sa ya zuba mata a hankali kamar mai raɗa yace "Wai mai gidan ne ya bada umurnin su fitar mana da kayan mu sbd yana bukatar gidan sa" Leena ta dinga kallon sa da wani expression tace "Mai gidan kuma? Ina gidan Daddy ne?" Yace "Sun ce an sayar da gidan ai" Leena ta mike tsaye tana unlocking wayan ta, Malik yace "Me zaki yi?" Tace "Zan kira Daddy mana" yace "No, don't" ta kalle sa sai kuma tace "Sai muyi ta zuba musu ido?" Masu fitar da kayan na aikin su basu fasa fitarwa ba duk da yadda Malik yace su basu notice ɗin kwana biyu amma sunce A'a suma umurni aka basu. Daddy with shock ya tsaya kallon Ammi yace "An sayar da gidan kuma? Yanzu ina ita Leena?" Ammi tayi shiru tana kallon wani wajen, Daddy ya fara kiran Rayyan, yana ɗaga wa Daddy yace "Rayyan ko zaka je gidan Leena, wai an sayar da gidan so masu gidan suna fitar da kayan su, kaje gidan kaga meke faruwa kafin na tura lawyer na dan ni ban sayar da gida ba" Rayyan was shocked da jin furucin Daddy. Daddy ya tsaya kallon evidence ɗin wanda aka sayar masa da gida, gashi kuma takardun gidan ne ba wai na bogi bane, Daddy kansa ya ɗaure dan da gaske komai na gidan ne amma waya sayar shine amsar da yake nema, Rayyan ma yayi shiru yana tunani, Daddy ya sa aka kwashe kayan na su yace su koma gidan sa da zama kafin nan, Malik yaki ganin har ran Daddy ya ɓaci sannan ya yarda, shi kuma gani yake kamar ba zai iya zama a cikin gidan su bane, yasan da kunya, yanzu addu'an sa bai wuce Allah ya sa ya samu aiki bane, ya bawa Leena rayuwar farin cikin dan yasan tayi kokari da shi. Bayan sun koma gidan Daddy da zama, an basu BQ, Daddy kuma yasa a masa binciken waya sayar da gidan shine kawai abin da yake bukatar sani. Bayan sati da komawar su gida, Leena ta fito daga part ɗin Hajiya ta wuce BQ inda yanzu suke da zama ita da mijin ta, tana shiga taji wayan ta na ringing da sauri ta karasa ta ɗauki wayan ganin Muhammad ke kiran ta yasa tayi receiving call ɗin, bayan sun gaisa Muhammad yace "Leena toh sai ku shirya yau, gobe ku taso zuwa nan Abuja dan jibi suke son ganin ku" Leena tace "Ya Muhammad ka manta ban yi makaranta ba, sai dai miji nane" yace "Kar ki damu, yanzu za'a iya ɗaukan ki a hakan saboda Daddy yayi magana kin san senator ne shiyasa, so da ke da mijin na ki duk zaku samu aiki amma ina so kina farawa dan Allah Leena ki koma school" Leena taji hawaye ya cika idon ta, addu'an ta kenan kwana biyun nan Allah ya bawa mijin ta aiki kawai ta tuna da Muhammad tana masa magana gashi ko sati bai ɗauka ba yace suje ana neman su, Muhammad ya katse mata tunani yace "Sai kun zo ɗin, ki gaida min mijin na ki" A hankali tace "Mungode" yayi sauri ya katse kiran dan baya bukatar godiyar ta, Leena ta fashe da kuka ta rasa me take ji, a haka Malik ya shigo ya ganta da sauri yayi kanta yace "SubhanAllah Meya same ki dear?" Tana share hawayen ta tace "Yanzu Muhammad ya kira Ni, wai gobe mu tashi zuwa Abuja, mu tafi da takardun mu jibi zamu yi submitting Application sannan su mana interview" Malik ya mata wani kallo yace "Who is Muhammad?" Da sauri ta gyara tace "Wani cousin ɗin Ammi ne fah" sai sannan ya sake fuskan sa yace "Toh Allah yasa mu samu, Allah ya kaimu" ta amsa da Amin ta fita zuwa bangaren Ammi dan ta sanar da ita abin da ake ciki..
Leena ta fito daga part ɗin Ammi, sannin Malik ya dawo dan baya yarda ya wuni a gidan sai ya lura goma ya wuce sannan sai ya dawo ko kuma da yamma ya dawo, tana cikin tafiya zuwa BQ ta tsinkayi muryan Rayyan "Hey Leena" ta juya sai kuma da murmushi shinfiɗe a fuskar ta ta karasa inda ya ke tace "Yaya ina wuni" Yace "Lafiya kalau" tace "Ya su Anty Layla da Leena na?" Yana murmushi dan yaga kamar ma Leenan tafi Layla kishin kara mata aure da yayi yace "Ba zaki tambaye ɗayar Antyn na ku ba?" Ta taɓe baki tace "Ni na santa ne? Ai gashi na tambaye wanda na sani" yayi murmushi yace "Yanzu Husnan ne baki sani ba? Tun da kina yarinya take zuwa gidan nan" ta taɓe baki sai kuma tace "Yauwa Yaya kasan me? Gobe fah zamu tafi Abuja jibi wai zamu je interview" jikin Rayyan yayi sanyi dan shi bai so hakan ba yaso ace shine yayi fighting mu su yace "wa zai kai ku?" Tace "I think motar tasha zamu bi, ko kuma mu tafi da nawa motar" ya Harare ta yace "Dama kin taɓa bin motar tasha ne? Lokacin da kike lafiya baki bi ba sai yanzu da kike da karamin ciki? See you" Leena ta ji kunya ya lulluɓe ta "Zan duba if there's available flight mu gani" tace "Toh Shikenan, Mun gode" daga haka ta karasa. Da safe bayan sun ma Ammi da Hajiya sallama sai da suka biya gidan Umma wanda tayi ta musu addu'ar nasara da kuma Allah ya tsare su. Bayan flight ɗin su yayi landing, drivern da Muhammad ya tura shine ya je ya ɗauke su, a kofar wani apartment yayi parking, Malik ya sauka sannan ya riko ta ta sauka, ya kwashe musu trolley ɗin sannan suka jera tare zuwa cikin apartment ɗin. Leena na zaune akan gado kafafun ta na kasa, Malik na duke a kasan yana masa mata su dan ƙafan sun ɗan kumbura, tace "Twin, yanzu Ni dan Allah me za'a bani bayan ba karatu nayi ba?" Ya Kalle ta sai kuma yace "Kin san yanzu yana yin kasan it depends on Who you know ne, kuma ai kince Mutumin senator ne so yasan yadda zai yi ai" ta gƴaɗa masa kai yace "Sai dai gaskiya dole ki koma school, saboda Karki ji daɗin kuɗin ki manta makaranta" tayi dariya. Washe gari da safe drivern da ya ɗauko su a airport shine ya sake zuwa, bayan yayi dropping ɗin su a wani babban organization suka sauka, ta Ciro wayan ta a jakka ta mika masa tace "Gashi, call him sai ya faɗa maka inda zamu nufa" Malik ya karɓi wayan da take mika masa, baya ya gama magana da Muhammad ya mika mata wayan, hannun ta ya rike suka nufa ciki, dake ko wani office da suna a jikin, a haka har suka haura second floor, wata mata ta karasa wajan su tace "Hello! Are you the ones Sir Muhammad said would be coming?" Leena tace "Yes, Ma" tace "Alright then, welcome! Come with me, please" suka bi bayan ta, a wani babban office ta kai su tace "Oga is in his office having breakfast, Once he's done, he will let you know so you can go in" Malik yace "Alright, thank you" daga haka matar ta fita a office ɗin, su kuma suna zaune a ciki sannan akwai wani office a cikin inda suke, wanda suke kyautata zaton shine office ɗin da take magana akai, after like 30 minutes ya buga kararrawa wanda hakan yasa wata PA ɗin sa fitowa a wani office ta karasa ciki da sauri ba'a dau lokaci ba ta fito tana kallon Malik tace "Sir, Ma, zaku iya shiga" suka miƙe suka shiga office ɗin nasa, Mutumin yana kallon system ɗin gaban sa, Matashi ne amma daga gani kuɗi ya zauna masa, Leena ta kalli mutumin sai kuma ta kalli Malik haka nan taji zuciyar ta ya tsinke ganin kaman da suke yi, Malik kuma shi tunanin sa ai ɗan uwan Leena ne, dole kila suyi kama, da hannu Mutumin ya nuna musu kujera su zauna wanda har sannan bai ɗago ba, gaishe shi da Malik yayi yasa ya janye idon sa akan system ɗin zuwa gare su, da sauri ya mike tsaye yana kallon Malik cike da mamaki bakin sa na rawa ya furta "Yarima!!!" Malik da Leena suka kalli juna, ya mayar da kallon sa kan Leena yace "Lil sis?"
Idan ban samu more reaction da yawa ba mu da update sai Monday, thank you.