ZAKIYYA Matashiya mai juyayyiyar Kaddara

7

by @sadiyanasir

Aliyu haka ya daure girman abinda ke damunsa a zuciya yacigaba da bawa Jidda farin ciki. Koda dare tayi bacci kasa ɗaukar Aliyu tayi, jin zuciyarsa yake kamar wuta, tunanin Zakiyya, tausayi, soyayya, da kuma nauyin amanar auren sa ga Jidda, duk sun yi masa cincirindo a zuciya. juye-juye ya rin kayi a kan gado, Jidda na gefensa amma ta yi kamar tana bacci duk motsin sa a kunnen ta. Da kyar ya miƙe ya fita ɗakin, zuciyarsa na nauyi kamar yana ɗauke da dutse. A parlor ya tsaya, ya ɗaura hannun sa a kirji cikin duhun dare iska mai sanyi na kadawa, zuciyarsa na rawar neman mafita. Ya jima yana zaga d'akin cikin rashin madafa, komawa d'aki yayi ya ɗauro alwala ya shimfiɗa sallaya, ya soma sallar dare da zuciyar da ta karye. Bayan ya idar d'aga hannayen sa sama yayi.

“Ya Allah, ka bani abin da zai zame min alheri da kwanciyar hankali a duniya da lahira. Kada ka jarabceni da abin da zai raba ni da iyalina. Ka bani ikon yanke hukunci na gaskiya. Ka bani ikon adalci idan har wannan Aure shine alkairi.” Idon sa jazur yake yin wannan addu’ar, zuciyarsa na ciwo saboda soyayyar da yake yiwa Zakiyya, da kuma kulawar da yake wa Jidda da ‘ya'yan sa.

A hankali ya koma gado ya zauna, Lokaci guda Jidda ta lumshe ido ta kalle shi a fakaice don bata so ya gane cewa idon ta biyu. zaune yake gefen gado, ya saka hannayensa a kai, yana numfashi mai nauyi.

Tausayin mijinta ya cika zuciyarta. Ta tuna yadda ya runtsa ido yana lallashinta. Ta tuna yadda ya tsaya ya ce ya fasa Auren ba don ya so ba, sai don ita ta huta. Ji tayi wani abu ya tokare mata makoshi, take taji

zuciyarta ta karye. “Wani irin soyayya ce haka Aliyu yake min? Da har zai iya cutar da kansa saboda ni? Shin meyasa ni ba zan iya jure wa zuciyata don farin cikinsa ba? Me zan ce wa Allah a gobe kiyama?” Ta lumshe ido tana addu’a a ranta.

Tana ji nauyin soyayyar da mijinta ke mata.

A hankali ta matsa gefen sa cikin nutsuwa ta kama hannunsa a sirrance ta matse. Da sauri Aliyu ya dago da mamaki, zuciyarsa ta buga da karfi.

Idonta cike da hawayen da ta ƙi zubarwa.

“Aliyu…” Ta kira shi da murya mai rauni.

Ya kasa cewa komai. sauke numfashi tayi zuciyarta na tsuma.

Cikin nutsuwa tace:

“Na yanke shawara.”

Zuciyarsa ce ta tsaya cak. "Batun auren nan… kayi na amince” Runtse ido yayi saboda nauyin wannan abu. Bai yi tsammanin jin haka daga gareta ba. Jidda ta cigaba cikin murya mai taushi amma mai nauyi:

“Ka yi aure idan zaka samu nutsuwa da alheri, ni kuma zan yi hakuri saboda kai. Don Allah ka sani ba don ban so kayi ba nayi kuka. Tsoron rabuwar mu nake yi. Amma naga yadda ka dage Allah ya sanya alheri.” Lokaci guda idon sa ya canza launi ya rike hannunta da sauri.

“Jidda…”

Ta girgiza kai.

“Amma ina da roƙo guda ɗaya kacal?.” Zuciyarta ta yi wani irin bugawa. "Don girman Allah,” ta ɗago idonta tana masa kallon roƙo, “kar ka hada mu gida daya. Kar ka sa ni da ita cikin inuwa daya. Zan jure duk sauran wannan kawai ka kyale ni.” Dakin ya yi shiru na wasu sakanni.

Shiru mai nauyin da ya sa hancinsa ya yi sanyi.

A hankali ya jijjiga kai ba don ya so ba, amma saboda ya san wannan roƙon ai ya dace.

“Na amince miki Jidda.”

Ya faɗa da murya mai rauni. Bazan hada ku gida ɗaya ba, zan kiyaye ki, zan kiyaye gida, zan kiyaye adalci.” Sai ta sake fashewa da kuka mai sanyi ba irin na zafi ba, wannan kukan daga zuciya ne. Aliyu ya rungumeta kamar ba zai sake taba. A zuciyarsa yana jin wani abu mai zafi. Lumshe idonsa yayi zuciyarsa na bugawa da soyayya biyu, da wacce yake nan yana ji tana taso masa, da wacce yake wa Jidda. Cikin wani irin yanayi bacci ya d'auke su ko wanne da abinda yake sakawa a zuciya.

Washe gari kasancewar weekend ne Aliyu yana gida, saboda ya faranta ran Jidda a flight mood yasa wayarsa ya zauna tare da ita yana bata farin ciki. Don yasa mata nutsuwa a zuciya ko masallaci zai tafi a gida yake barin wayar. Sai dai lokuta da dama idan ya zauna Zakiyya ce keyi mishi gizo, yana so yaji muryarta amma haka yake d'aurewa.

Zakiyya kuwa abin duniya ya isheta tsawon

kwanaki biyu bata ji daga gare shi ba ko sau ɗaya. Messages d'in da yake turo mata shi take bi tana karantawa sai tayi murmushi mai rauni.

Wani lokaci sai ta soma tunanin " Ko dai ba lafiya ne?” Ganin bata da bai bata wannan amsa yasa sai ta kawar da tunanin, amma tabbas tana jin son Aliyu yana ƙara bayyana mata fiye da ganewa.

Ranar data kasance Monday da yamma yana dawowa daga aiki a gajiye, wayarsa ta yi vibrating.

Idanunsa suka haska, ganin sunan ya soma tunani Zakiyya. "Kai Aliyu ka ɗauka ko ka bari?” Ya yana lumshe ido bugun zuciyarsa na Karuwa ya danna answer a hankali.

“Assalamu alaikum Ranka shidade kana lafiya kuwa?” jin muryarta yayi tazo masa da taushi da nutsuwa ta saka shi saurin jin kewarta. “Wa alaikumus salam Zakiyya ta, lafiya lau, kiyi hakuri wallahi na shiga damuwa ne da wasu abubuwa na gida, amma kina zuciyata.”

Ta yi shiru, tana sauraron sa sosai. "Karki damu ba matsala bace zanyi magana dake in sha Allah idan na fita a gida.” Wani abu ya tsinke a zuciyarta ba ciwo ba. “Shikenan ka kwantar da hankalinka Aliyu Allah ya daidaita maka al’amuranka. In sha Allah idan ka samu lokaci sai mu yi magana. Na barka lafiya.” Ta kashe kiran a hankali. D'aki ta koma ta kwanta ta runtse ido “To me ke damunsa? Me ke masa nauyi haka? Ko dai Matarsa bata son Aure ne?” A lokaci guda

ta fara tunanin barkatai.

A gefe guda Aliyu ji yayi wani sanyi na ratsa ilahirin jikin. “Zakiyya mai sauƙin zuciya kina da hakuri sosai, ina jin dad'in wannan halin naki” Ya k'arasa ciki inda Jidda take zuciyarsa a rikice. A toilet ya samu Jidda tana wanke jikin Hafiz suna dariya ita da Farra saboda kukan wanka da keyi. "Mahma ya kike mishi dariya Kuma?". Yayi maganar yana ajiye Laptop Briefcase d'in sa. "Oyoyo Abba?" Farra ta fad'a tana fad'awa jikinsa, riketa yayi a jikinsa yana mata wasa har Jidda ta kammala shirya Hafiz ta soma bashi nasa kulawar.

Washegari daga office gun Hajiya ya nufa. Da sallama ya shiga gidan kansa a sunkuye yake tafiya, zuciyarsa na bugawa cikin natsuwa na samun maslaha saboda amincewar Jidda da ya samu. A falo ya same ta tana duba tasoshin TV, ta ɗago da murmushin da kullum ke nuna gata da girman d'an nata.

“Aliyu, lafiya? Ka shigo kamar mai tunani.”

Ya durƙusa ya gaishe ta. Ta dade tana kallonsa kafin ta ajiye remote.

“Ina jinka?” Numfashi ya sauke mai nauyi.

“Hajiya… komai ya daidaita tsakanina da Jidda.” Ta ɗan runtsa ido tana jiran ƙarin bayani.

“Jidda… ta amince da aure na biyu.” Hajiya ta ɗago kai da mamaki kafin murmushi ta bayyana a fuskarta.

“Lallai? Jidda ce da kanta?” Ya gyara zamansa. "Eh Hajiya da kanta ta yanke shawara, ni kaina nayi mamaki, kuma ta nuna min kulawa fiye da yadda bana zato.” Hajiya ta yi shiru na ƴan dakiku tana nazari, ajiyar zuciya ta sauk'e alamar gamsuwa.

“Alhamdulillah, haka rayuwa take tare da hakuri ake gina gida.”

Aliyu ya ɗan matsa gaba kad'an "Ina so na gaya miki… yanzu zan sanar da Zakiyya zan kuma sami Baba karami a kai kud’in aurenta kamar yadda ya dace. Ina so komai ya kasance cikin tsari da mutunci, ba tare da wata hayaniya da d'aukar dogon lokaci ba.”

Hajiya ta kalle shi sosai ta yi murmushi irin na uwa mai alfahari da ɗanta. "Allah ya tsareka, Aliyu, tabba idan ka rike adalci za ka ci nasara. Ka tabbatar ka kyautata wa Jidda, kada ka bari zuciyar ta ta ji komai. Ita tayi abin da mata kaɗan ke iya yi.” Ya durƙusa ya sumbaci hannun ta.

“Amin Hajiya zan kiyaye.”

Ta daga hannunta sama cikin natsuwa:

“Allah ya baki ikon kula da gidaje biyu. Allah ya sanya alheri a zuciyar dukkan matan ka, Allah ya hana fitina.”

Aliyu ya amsa “Amin” zuciyarsa na sanyi. Bai jima a gidan ba ya fita ya d'auki hanyar gida, yau zaije gun Zakiyya da magana mai dad'i na zancen Auren su. Gidan sa ya wuce kai tsaye, bayan sallah Magrib bai b'oye wa Jidda ba, ya sanar da ita zaije yaga Zakiyya. A zuciyarta taji babu dad'i amma bata nuna mishi a fuska ba tayi mishi fatan alkairi. Da murmushi ya fita akan fuskarsa, yana hawa machine murmushin da bai yiba tsawon kwanaki ya bayyana. "Allah ka sanya alher ya ambata ya tashi machine d'in. Cikin nishad'i yake driving Machine d'in sa,

yana isa unguwar ya dan tsaya kafin ya k'arasa gidan ya lumshe ido ya daura addu’a a zuciya sannan ya kira wayarta. Zakiyya na ganin kiran tayi murmushi ta d'auka. "Amincin Allah ya sameka a duk inda kake?". "Tare dake Matar Aliyu". Wani irin fad'uwar gaba taji ambaton kalmar Matarsa da yayi, take tsohon ciwon dake zuciyarta ta motsa. "Gani a kofar gidan ku". "Ina fitowa". Ta ambata tana sharar kwallah daya zubo mata, murya a hankali ta furta. "Ba zan gajiya dayi maka Addu'a ba Miji na har sai ranar da k'asa ta rufe ni, ina son ka, ba zan iya had'a soyayyarka da kowa ba". Ta mike jiki babu kuzari ta kimtsa.

Aliyu A dakalin kofar gidan su Zakiyya ya zauna, Zakiyya ta fito cikin nutsuwa ta isa garesa, zama tayi nesa dashi kad'an tana jin bugun zuciya, tunda ya kirata da kalmar Matarsa ta nemi duk wani kuzari nata ta rasa. Bayan sun gaisa shuru ne ya biyo baya kafin daga karshe Aliyu yaja dogon numfashi. "Zakiyya… kina lafiya kuwa?” Murmushin karfin hali tayi. "Alhamdulillah! Lafiya kalau .” Ta amsa a hankali ba tare data daga kai ba. Numfashi ya sauke mai nauyi, kamar wanda zai fito da abin da ya jima yana boyewa cikin zuciyarsa.

“Na zo ne akan maganar Aure na dake Zakiyya? Sannan na baki hakuri na rashin jina da kikayi kwana biyu". Ta ɗago kai a hankali ta kallesa alamar sauraro.

“Na fuskanci matsala a gida tsakanin ni da Jidda akan maganar Auren ki. Amma a yanzu komai ya daidaita kafin in zo wajenki. Na yi magana da Jidda, na bayyana mata komai, na nuna mata ina sonki, ina so in yi aure da ke saboda ina ganin alheri a rayuwarki, ina ganin halinki, ina ganin irin natsuwar ki…” Ya tsaya, zuciyarsa na rawa. Zakiyya ta sunkuyar da kai sosai, har hawayen da ta daɗe tana riƙewa ya soma cika idanuwanta. Aliyu ya ci gaba da magana cikin murya mai karyewa. "Zakiyya.” Ya kira sunanta cikin sanyi da matsananciyar nutsuwa. Ta ɗago kai a hankali, idonta ya cika da hawaye masu nauyin farin ciki da tsoro.

“Na zo gareki saboda ina son ki kuma ina son ki da aure. Ina so in zamo mijinki na halal. Ina son in sanar da iyayenki, in kawo kud’in aure kamar yadda ya dace. Ina so ki zama halal a gare ni.”

Gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, hawaye suka fara zubowa a idonta ba tare da ƙarfi ba, hawaye masu sanyi, masu kunya, masu farin cikin da ta dade bata samu ba. Ya matsa kaɗan amma ba sosai ba don kare mutunci. "Meye ya sakaki kuka?". Murmushi Zakiyya tayi. "Bakomai Aliyu". “ Zakiyya Ina so ki yarda dani kinji?.” Ta share hawayen ta sannan ta yi murmushi mai rauni, idonta na rawa. “Na yarda Aliyu.” Ta fada a hankali kamar magana zata tsage mata zuciya. Numfashi ya sauk'e. "Ina so kiyi min iso zuwa cikin gida gobe da laasar zan gaida Malam da Mama, ke kuma sai ki sanar dasu za'a kawo kud'in Aure su bada lokaci". "In sha Allah". Zakiyya tayi maganar a hankali. Aliyu bai d'auki lokaci ba ya mata sallama akan sai gobe. Da shigarta gida d'akin Mama Rakiya ta nufa ta sanar da ita sak'on Aliyu. Shekeke Mama Rakiya ta kalleta. "Meye wani zuwa gaisuwa sai kace wata Budurwa? Abinda nake bukata ya kawo sadaki bana son wani fi'ili". "To Zakiyya tace ta mike zuwa d'aki jiki a sanyaye....