KO BA SO..

Chapter: 3

by @pinkylady

                

Ya fi minti goma a tsaye bakin gate din gidan nasu ya na tunanin shiga ko ya wuce. Khaleed dai ya zubawa sarautar Allah ido, don lokuta kalar wannan ya kan bashi iska yayi tunanin da ya ke so.

Tun da suka iso Isa( direban Fj) ya bude masa motar ya na tsaye yana jiran ya fito. Shi din ma saurayi ne kamar su. Dukkansu shiru su ka yi, don abu ne da suka riga suka saba duk idan zai shiga gidan nasu.

Hannunsa ya cusa cikin sumar kansa ya sosa kafin ya fito daga motar. Bakar riga ce a jikinsa mai dauke da farin rubutun 'Save me' dara dara a gabanta, sai blue jeans. Hular da ke rike a hannunsa ya kafa ta kare fiye da rabin fuskarsa kafin kai tsaye ya tunkari gidan ya shige.

Babu kowa a tangamenen falon sai katuwar tv da ke manne a bango ke surutu. Da desert boot dinsa ya taka ya samu daya daga cikin kujerun ya zauna tare da daukar remote da aka ajiye a wajan ya sauya tasha zuwa ST Naija. Ku san minti goma Mami ta fito da waya kare a kunnenta, ganinsa ya saka ta yi sallama da wanda ta ke wayar. Baƙa ce sosai tana da manyan idanu da dogon hanci sai dai dan karamin jiki ne da ita ba kiba ba tsawo. Ta na sanye da doguwar rigar atamfa kamfanin vilisco tun daga sama har kasa beadwork da stones work ne ta ko ina. Kallo daya za ka shaida kudi da gayu sun samu wajan zama.

"Ah Fahad ka shigo? Ai da ka shigo ina ciki"

Ya yi murmushi tare da gaishe ta. Ta amsa tana wucewa kitchen, sai ga ta da tire shake da kuloli ta dire gabansa, ta koma ta dakko wani tiren mai dauke da kayan tea da ta ajiye.

"Na san dai ba ka karya ba, kuma da gani ma gaba kaci daga nan ko?"

"Kamar kuwa kin sani, daga nan sai Kano. Amman ban jin ina da lokacin tsayawa cin abincin nan gaskiya, don za mu makara."

Ya karashe maganar ya na kallon agogon hannunsa.

"A'a ina za ka dauki hanya ciki ba komai?"

Ta miƙe. Dariya ya kuma yi

"Allah Mami kar ki damu zamu samu wani abu a hanya, ban so in wuce ban ganki ba ne shiyasa na biyo. I missed you so much"

"To yaya zan yi da kai Fahad? Babu yadda ban yi ka dawo gida ba ka maƙale, abinci kam ba za ka tafi haka ba gaskiya. Ina zuwa"

Ta koma kitchen sai gashi ta fito da food flakes mai silver uku daga ciki, ta fiddo a kowacce ta jera ma shi, dankalin turawa, farfesun 'yan ciki sai soyayyan kwai.

"Gashi to ka daina wasa da cikinnan naka. To ina ma za ka samu karfin wakar cikin ba komai?"

Ta faɗi ta na dariya. Shi ma dariyar yayi ya miƙe tare da daukar abincin.

"To zan wuce, sai na dawo In shaa Allah"

Ya fadi ya na kallon corridor da zai sada shi da sashen Abba. Ta lura da hakan sarai, sai ta share kawai ta yi murmushi.

"Shi kenan, idan ka dawo ai ka sauka a nan ko?"

Ya shafa gashinsa.

"Sai na dawo din" har ya juya ya juyo ya dube ta

"Ayraa fa?"

"Ta na can tana baccinta na sabo, yau ba makaranta"

"Okay, a gaishe ta idan ta farka."

Ya fada ya na ficewa. Ta bi shi da addu'a. A harabar gidan suka hade da Jaheed, suka kalli juna kowa ya ɗauke kai ya wuce. Idan ba fada maka akai ba ba zaka ce 'yan uwa da suka fito tsatso daya ba ne balle da basa kama ko ta ina don Jaheed kalar su daya da Mami sak! Shi kuma da an gan shi an ga Abba ko baka sani ba ka gansu za ka shaida hakan.

*

"Kun gaisa da Abba?"

Khalid ya tambaye shi, bayan ya zauna Isa ya rufe motar  Sai da ya jingina da motar ya sauke ajiyar zuciya kafin ya dubi Khalid din, ya kaɗa masa kai. Bai kuma cewa komai ba suka ɗauki hanyar Kano.

*********

Da sauri ta sauko daga napep din ta sallame shi kafin ta shige cikin hotel din. Yau kwanan ta na huɗu kenan da fara aikin. Aikin safe aka bata 07:00am-12:00pm kuma an gargadeta da babu makara sannan babu kalula, don idan kayi kwana uku baka zo ba a wata to ka sallami kanka, ko da ba a jere ka yi su ba. Idan ma rashin lafiya ne to za ka kawo medical report, idan kuma ka ci ka rashin lafiya ma to za a sallameka ba zaka iya ba kenan. Shi yasa a wajan ta lura kowa tsan-tsan ya ke aikinsa, ko irin firar nan ba'a cika yi ba da an zo aka gaggaisa kowa zai kama aikinsa ne. Kitchen din da aka kaita na musamman ne don VVIP kawai ake wa girki a ciki, sannan babu wani abu wai kuskure a lissafin su shi yasa ma aka ware shi daban daga kitchen din da ake duk wani abinci. Ko mai za ka girka to kawai ya zama perfect dari bisa dari. Ko a afron dinki ba a yarda aga wani datti ba ko maikon girki, balle ki sa ran za ki yi wani rashin tsabta. Sannan duk wanda yayi girki to shi ke da alhakin kai wa bako abincin, zai tsaya har sai ya ci, idan bashi da wani complain to sai ka koma bakin aikinka. Idan kuwa matsala aka samu na rashin iyawa ko wata kazanta ga abinci to kora ce kai tsaye don baka dace da wurin ba. Idan kuma VVIP ya yabi aikinka har kyauta ma sai ka samu, don hannunsu a sake ya ke wajan kyautatawa ma'aikatansu, kawai kuskure da asara ke basa dauka, yan kasuwa ne na hakika.

Sai da ta yi sign sunanta da lokacin da ta zo kafin ta saki ajiyar zuciya. Common room dinsu ta shiga,locker  da aka bata ta bude ta ciro uniform dinta riga da wando blue and white ta saka sannan ta dauki afron ta wuce kitchen din. Dubawa ta .yi ta ga me zata girka a yau. Don kullum akwai abinda kowa zai yi, mutum biyu ba sa girka abu daya, don ma kar laifin wani ya shafi wani. Chips za ta yi, ta ci sa'a ana ta fere dankalin, duk abin da ya shafi fere-fere doya dankali to akwai masu yi daban. Sai idan aikin flower ne kai za ka tsaya ka dinga bada awon komai da yadda za a buga fulawarma, don idan abu bai tashi ba duk daga kai ne. Haka su ka dinga kai-kawo, masu Tea na yi, masu farfesu da sauransu.

Wajan sha ɗaya da rabi tana cikin tsame dankali wanda shi ne na karshe da ta gama shikenan sai ta jira shabiyu ta yi, ta tafi gida.

"Ina 016?"

Ta dago ta na kallon mai kiran, suka hada ido. Kallon number da ke jikin kayanta ta yi taga 016 din a rubuce ya bata tabbacin ita ce.

"Ba za ki iya cewa gaki ba?"

Ta fada da alamu ranta a bace ya ke.

"Yi hakuri" kawai ta fadi ta na ajiye matsamin.

"Gobe 12-6 za ki yi"

Ta gyaɗa kai. Bata kuma ce mata komai ba ta juya ta tafi.

Lokacin da lokacin tashin ta yayi ta sauyo kaya ta yi sign out ta fito. Har ta kusa isa gate din ta ji ana kwala mata kira a baya. Ta juya. Daya daga cikin wacce su ke aiki tare ne. Da murmushinta ta karaso in da ta ke, ta mika mata hannu.

"Sunana Zee"

"Layla" ta fadi ta na bata hannu suka gaisa.

"Ya aikin?"

"Alhmdulillah, ke fa?"

"Ni ma. Kin san me yasa ka maida maki aikin rana?"

Ta dan kalle ta da mamaki sannan ta gyada kai alamun a'a.

"A ka'ida, sai an yi sati biyu ake canza duty, kawai an canza ki ne don an yarda da aikinki. Mai kula da sashenmu abokin yayana ne shi ya sa na ji sun yaba girkinki."

Ta dan yi dariya. Layla kuma ta yi murmushi ta na jin dadi a ranta.

"Gobe muna da babban bako ne, wanda kowa ke burin zuwansa Skye Royale. Kin san wanene?"

Layla ta yi dariya da alama Zee akwai sururu kamar Farha. Ta girgiza kai. Ta dan matso kamar za ta yi mata rada ta ce

"Fj!"

'Fj' ta nanata aranta ta na son tuna a ina ta ke jin sunan. Dan zaro ido Zee ta yi

"Fahad Jamil fa, mawakin nan ɗan Hon. Jamil Usama?"

'Farha's crush' ta fada a ranta.

"Ohh! Na gane shi"

Ta faɗa.

"Ya na yawan zuwa hotel din nan duk idan ya na gari, sai yayi sati daya ko biyu ma. To saboda abincinsa ne ya sa aka maida mu rana"

Layla ta kalle ta, sai ta saka dariya.

"Eh ni ma da rana aka maida ni, shi yasa da Sarah ta zo dazu ta ke fushi don sun so ta  yi ma a bata special duty, karshe sai aka maido ta na safe. Ta na bala'in son Fj duk in yana nan bata ko son tafiya gida"

Ta sake sa dariya. Ta lura ta na da yawan dariya.

"Amman sai kin kula wallahi, sosai ma kuwa kar ki sake ki yi abin da zai yi complain don akwai shi da zaben abinci ba komai ke masa dadi ba sannan.."

Sauran maganarta ta datse hango motar yayanta.

"Laa Yaya?"

Ta fadi cike da mamaki, ta kalli Layla.

"Sai mun haɗe gobe, ki zo da wuri wallahi"

Ta gyada kai kawai, ta fara kokarin tsaida abin hawa.

***

Farha

"To ai kaf tallar L&L Luxurious ban taɓa ganin Model din da riga ta fito haka da kyau ba ta haskaka ba"

Ta fada  idonta akan hoton FJ. Sai ka rantse da man ta san kamfanin ne.

"Ji jar nan ma dai"

Meenah ta tabo dayan hoton.

Suka saka wani ihu, Farha har da tsalle. Duk ta bi hotuna da videos din ta dakko, ta je page dinta ta daura da caption din

'Everything is ugly untill FJ were it'

Ta saka heart emojis. Sannan ta yi tagging dinsa da sauran fan pages dinsa. Cikin mintuna kalilan kuwa aka dinga like ana comments..

"Yaya Layla"

Ta kalli ƙofa jin Meenah ta kira sunan Laylah. Da sauri ta isa gabanta ta na mika mata wayar

"Duba duba ki gani, kyau iya kyau"

Ta fadi ta na zoomin hoton Fj. Ta kalla sau ɗaya ta kauda kai. Har ta wuce ta dawo ta sake karbar wayar ta kalli hoton da kyau. Ya na tsaye gaban hanger da ke jere da riguna T-shirts kala-kala, sanye da ɗaya daga cikinsu mai ruwan ƙasa an rubuta L&L da manyan baƙi mai turuwa(Bold) sai Luxurious din da kananan rubutu a karkace (Italic), daga ƙasa. Fuskarsa ta kalli gefe cikin salo da kwarewa a iya talla.

Miƙa mata wayar ta yi bata ce komai ba. Farha ta bata rai, ita ta fi son ake yabonsa kamar yadda ta ke yi, hakan fasa mata kai ya ke.

Ta na kula da ita t

a yi murmushi kawai ta na gaisawa da Zee kafin ta cire hijab ta fara cire kaya burinta kawai ta ji ruwa na ratsa ta, saboda zafin da ake yi.

🦋🦋🦋