KO BA SO..

Chapter: 10

by @pinkylady

Farha..

"I'm sorry sir..."

"I said get out my friend!"

Malamin ya buga mata tsawar da ba shiri ta saɓi jikkarta simi-simi ta fita daga ajin. Ita shaf mantawa ta yi bata saka wayar silent ba, ga wayar da danbanzan ƙara. Shi kuma ƙa'ida ne ma in ya shigo bai son jin karar wayar kowa, ko wani surutu da zai dauki hankali in yana koyawa. Don haka ne ya  watso ta waje ita da wayar da karar sakon ya ja mata. Ido biyu da sunan Beelah a notification din ya sa ranta yin sanyi, don ta zaci mtn ne ko wani spam message.

'Food Frenzy, 3:00pm.'

Wani tsalle ta daka. Da gaske ta dauki hanyar wayayyun mata wallahi. Ita kalar wadan nan wajajen ko a mafarki ina ta isa balle zahiri? Yanzun biyu har da arba'in, kenan sauran mintuna duka ashirin. Kenan tun dazun ma ta turo message din, da alamun network ya hana shi zuwa. Allah ya so ta yau wata doguwar rigar bou-bou ta saka ta kanti brown color, a cikin kayan da Beelah ta bata ne, ita kadai ce kayan sawa a cikin kayan ta gani bayan ta bude. Turaruka ne da kayan kwalliya na yan gayu, sai su earings da bracelet kala-kala. Ta yiwa su Umma karyar cewar Babansu Meenah ya kawo masu tsarabar Ummara dake su Meenah suna da hali sai ba su zaci karya ta ke ba, tun da wani lokacin Maman su Meenah har dinki tana yi masu da sallah ko wani biki na 'yanuwansu in za a yi anko sai a hada da ita. Dalilin saka rigar kuma hoto tayi niyyar yi a gidansu Meenah idan sun fito lectures, saboda yayanta da ke Karatu a Kano ya dawo hutu, kuma ya siya sabuwar iPhone 14 don haka suka ci burin caske hotuna. Yanzu kuwa sa rigar ya mata rana, da ko yaya za ta yi oho. Message kawai ta yiwa Meenah cewar ta wuce yin wani abin, idan ta fito nata lectures din ta wuce gida. Zata bata labari anjima.

Machine ta tara ganin babu Bus kuma ba alamun napep, su kayi cinikin in da za a kaita ta haye.  Dan nesa da Food frenzy din ta ce ya aje ta don kar a ga ta sauki daga machine, ta biya kudin ta ida takowa kasa. Ta na tura kofar ta shiga suka hada ido da Beelah da ke zaune daga hannun hagu. Kai tsaye ta karasa ta zauna tana fuskantar Beelah din. Agogo Beelah ta kalla hakan ya sa ta ce

"I'm sorry daga Makaranta na ke, ban ga message dinki da wuri ba"

Ta dauki cup din lemon da ke a jiye a gabanta ta sha kafin ta gyada kai.

"Ba damuwa"

Handbag dinta ta ke saman table din ta zuwa hannu ta dakko wani dan card karami, golden colour ta aje gaban Farha.

"Wannan ne katin ki, zaki shiga ko ina a wajan tare da shi babu mai ce miki don me."

Cikin murna ta yi saurin daukar katin yana juyawa, ji take kamar ta tashi ta rungume Beelah don farin ciki.

"Kayan da zaki saka suna mota"

Beelah ta sake fadi. A lokacin daya daga cikin ma'aikatan wajan ya iso ya aje plate biyu na roasted turkey breast

Lokaci daya ta ji cikinta ya yi kullewar yunwa saboda kamshin da ke tashi.

Kamar ta sa waya ta yi hoto haka ta dinga ji, ta daure kawai ta kauda kanta. Sai da taga Beelah ta dauki fork ta fara ci kafin ita ma ta fara ci. Bayan sun gama Beelah ta ce su je ta aje ta gida. A hanya shiru a motar kafin Beelah ta kalle ta

"Zaki iya min wata alfarma Please?"

"Eh mana , fadi ko mene"

Farha ta ce kai tsaye, ta na mamakin da zumudin menene zata yiwa Beelah uta ma ta birgeta. Ta gangara gefen tati kafin ta tsaya da motar ta kalle ta.

"A rayuwa ba abin da nake so irin na ga ci gaban Fahad Farha..."

An zo wajan..abu da jira ta ke. Tuni ta ida tattara duk wani hankalinta ta maida ga Beelah cikin zakuwa.

"Amman taurin kai ne da shi. An mashi aikin makoshi ba da jimawa ba, ba kowa ya sani ba saboda abin zai iya shafar wakarshi."

Ta bude ido sosai cikin mamaki. Beelah ta gyada kai tana sake saita fuskarta yadda zancen zai ratsa  Farha dakyau. "Na yi-na yi yake shan magani wallahi yaki, tun da ya ji sauki. Kuma in hat bai sha ba likita ya ce ba a san me zai faru gaba ba, tun da bai gama warkewa gaba daya ba"

Ta dan dakata, ta na nazarin fuskar Farha da tausayi ya gama shafewa.

"Na yi duk kokari na, karshe kin ga ko na kira baya dauka guduna ya ke akan hakan, to ni damuwata akan competition da suke yi a GHC kar ya je ciwon makoshinbya taso a can... shi yasa nake son ki min alfarmar nan"

Ta miko mata wata takarda a nannade.

"Ki zuba masa a drinks dinsa a wajan."

"Ta yaya?"

"Na fada maki komai mai yiwuwa ne in dai kin shiga ciki.  Idan kin je zan kula da sauran abubuwan daga nan waje na"

Ta gyada kai cikin gamsuwa, ta yarda da duk abin da Beelah ta fada.

"Idan ya sha zai warke?"

"Ko bai warke duka ba zai samu damar yin wakar shi lafiya lau kuma ya ci"

Cikin jin dadi ta karba, a ranta tana tunanin yadda suke da FJ din, amman bata tambaya ba. Sai da ta kai ta har lungun da zai kaita gida ta aje ta, sannan ta ce ta dauki kayan da ke seat din baya wanda su zata saka a daren gobe. Ta jaddada mata ta fito karfe tara, zata tura mata address din dazata je a mata kwalliya da na   venue din sannan ta bata wata takarda ta ce ta hardace abin da ke ciki da shi za tayi amfani tayi introducing kanta a wajan.

*** ****

Cikin kwalliyarta fes kamar yadda ta saba sai zuba kamshi ta ke ta tura dakin Daddy ta shiga. Ya na tsaye ya ba kofar baya tare da waya a kunnensa. A yadda ta ji muryarsa a dan kausashe ta san fada ya ke kuma dai tatsuniyar gozotba ta wuce ta koki... Sai dai ba ta hada kan zancen ba ta ga ya katse wayar tare da juyowa. Murmushi ta masa tare da fadin.

"Sannu da dawowa, ai ban ji shigowar taka bane sam. Ina can ni da rigimammen dan naka"

Ta sa dariya tare da girgiza kai ba tare da ta idasa maganar ba. Murmushi ya yi shi ma kafin ya ce

"Amin afuwa Madam, ma shigo ne ina ta waya shiyasa. Barin watsa ruwa dai tukun"

Ya ida maganar ya na aje wayar gefen gado tare da fara balle maballen rigarsa.

Murmushi kawai ta yi ba tare da tace komai ba ta wuce washroom don hada masa ruwan wanka. Kafin ya fito ta fita parlour kai tsaye dining area ta nufa don sake tabbatar da komai ya yi lafiya lau. Duk kuwa da ita da kanta tare da Ayra suka shirya abincin daren. Ayra din ta kira da waya cewar ta yi sallah ta sauko Daddy ya dawo.

Cikin kasa da minti talatin duk suna dining table din da babu Fahad, ba Jaheed.

"Kun yi magana da yaron can akan program din nan kuwa?"

Maganar Daddy ta yanke shirun wajan. Ahaf! Mami ta fada a ranta, ta riga ai ta sani. Yar dariya ta yi tace

"A'a gaskiya, ban ma yi tunanin yi masa magana ba"

Yadda ya ke kallon ta, ta san karin bayani yake jira. Don haka ta ci gaba

"Dan Allah ake sararawa yaron nan yayi harkokinsa..."

"Harkokinsa na me? Har wani abun kirki kika dauki sana'ar tashi? Kodayake ai ke kike kara goya masa baya yake abin da ya so. To ki ma fada masa idan har ban ga keyarsa wajan program din nan ba ya nemi wani uban ba ni ba!"

Ya aje cup din ruwan da a da yake kokarin kaiwa baki ya mike.

"Daddy"

Ayra ta kira sunansa cikin karyewar murya mai nuni da a koyaushe kuka ne zai biyo baya. Juyowa yayo ya kalle ta, sai kuma yayi kokarin boye fushin da ke fuskarsa da murmushi ya dawo ya zauna.

"Ci gaba da cin abincin ki." Kawai ya fada, don shi ma ya san soyayyar da ke tsakanin Ayra da Fahad mai girma ce. Ya na kallon yadda ta ke share hawaye akai akai ta na cin abincin da tuni ya daina mata dandano a baki.

Mami ce ta katse shirun fa fadin,

"Baka tambaye ni me Jaheed din yayi ba"

Yar dariya yayi yana kallon ta.

"Riguna da huluna ya sa aka buga masa masu yawa, akan program din nan. Ya na can yana rabawa matasa lungu da sako ban san dai me yake son aiwatarwa ba, amman ya ce surprise.

Dariya Daddy yayi cike da jin dadi. Ya na son support daga Family dinsa akan komai da ya ke, Fahad ne kawai ya ki tankwaruwa da ya rasa yadda zai yi da shi. Fahad din da ya gama sawa buri da nufin ya dinga maida kafa a duk in da ya janye tashi, shine yanzu ya ke watsa masa kasa a idanu da hannuwa biyu dumu-dumu.

Ayra ta mike ta kalla Daddy ta ce

"Daddy sai da safe" Hakan ta yi ga Mami sannan ta wuce ba tare da ta jira amsar su ba.

Daddy ya kalla mami, ita kuma ta daga kafadu biyu alamun bata sani ba. Duk da ta san ita ma halin yar tata tsab...

Program ne da yake son budewa tare da ministry of health duk da ba wannan bane farko, ya yi ire-iren su barkatai, wanda a karshe Fahad din ne silar datsewar program din da ya jawo masa asarar da har gobe bai son tunawa. A yanzun kuma da yake da girma dumu-dumu a cikin gwamnatin yake son dawo da program din don shi ne matakin da ya ke ganin zai kai shi har in da ya ke son ya isa...Taro ne na murnar kaddamar da wanzuwar program din, nasarorin da ya ke son cimmawa, da wadan da ya cimmawa a baya, dangantakarsa da Familyn sa da sauran tambayoyi. Wanda za a yi  tare da manyan kusoshin gwamnati wanda abin ya shafa da kuma baki tare da nasu Family din. Wannnan dalilin ne ma ya saka dole Fahad ya bayyana a wajan, ban da haka baya fatan inuwarsa a wani abu kalar wannan kuma.

Jaheed ya shigo a daidai lokacin da suke shirin hawa sama.

"Sai yanzun?"

Mami da ta fara ganinsa ta fada da sigar tambaya. Ya karaso in da suke ya russuna kamar yadda ya sabayi ya gaishe da Daddy.

"An ce kana ta hidima ko"

Cewar Daddy bayan amsa gaisuwar. Yar dariya ya tare da jinjina kai.

"Haka ne, amman sirri fa ne"

Ya fadi ya na dariya tare da kallon Mami saboda ya san ita ce zata fada. Su duka dariyar su kayi kafin Daddy ya gyara murya hade da fadin.

"Zan tura maka wasu yan canji, sai ka kara. Allah ya yi maka albarba"

Daga haka ya wuce. Mami ta bi bayan sa da murmushin jin dadin da take jin kamar ta taka rawa.

*****

Fahad

Ya na tsaye ya yaye cottons din window'n  dakin yana kallon view din waje da ko ina haske ne tamkar rana, hasken taurarin da suka cika sararin samaniya ya kara kawata wajen da ya ke jin nishadin kallo. Karar da wayarsa ta yi ya saka raba hannuwansa da cotton din sannan ya dakkota ya amsa.

"Ayi min hakuri..."

Abin da ya fara fada kenan bayan daga kiran.

"Yayaa!"

Sai da ya zare wayar daga kunnensa, kafin ya sakr maidawa cijin dariya ya fadi

"Za ki toshe min kunnuwa ne Ayra?"

Ya na jin dariyarta a wayar kafin ta ce,

"Za ka zo kafin ranar?"

Ya fahimci ranar da ta ke nufi don haka kai tsaye ya ce

"Ban tunanin zan zo, ki na bukatar wani abu ne?"

"Zan zo gidanka"

"Ina skye royale kuma.."

Bata jira ya ida ba ta ce zan iske ka a can da safe tun da yanzun dare yayi, Mami ba zata bari na fita ba.

Duk da yana da muhimman abubuwan da ya kama

ta yayi a safiyar goben bai hana ta zuwa ganin nashi ba, tun da ya san ba zai samu zuwa gidan ba don yanzun. Kuma Ayra ce zai iya kashe abubuwa da dama dominta.

🦋🦋🦋