KO BA SO..

Chapter 11

by @pinkylady

Layla

Da sauri ta gama shirya abincin sai da ta tabbatar komai yayi kafin ta dauka tray din ta nufi rom 050 zuciyarta cike da haushin yadda ta baro gift din da tayi niyyar maida masa shi yau, saboda saurin da ta dinga akan makarar da ta kusa yi. Ta na zuwa dakin da niyyar knocking sai taga kofar ta tafi ta bude, da mamaki ta shiga da sallama.

Sallamar ta datse,Hannun da ke dauke da tire din ta ji ya fara kyarma har, haka ma kafartata. Sakamakon hoton da idonta ya fara haska mata bayan shigowa dakin.

Yarinyar da ya ke rungume da ita, ya na bubbuga bayanta ahankali, ita kuma ta lafe jikinsa kamar kadangare...Da sauri ta janye idonta daga na shi da ya dago ya kalle ta ta dire stray din tsakar dakin ta juya da sauri ta ja kofar da karfi ta rufe.

Ajiyar zuciya ta yi bayan ta fita, haka ya ke daman? Sai kawai ta ji ya sure mata, daman da sauran haushin shi da take ji. Don haka ta sawa ranta ba ma zata koma ba, don zuwa yanzun ta tabbata ai abincin nata ya masa tun da bai taba complain ba. Ayyukan da suka rage mata ta cigaba da yi har lokacin tashin ta yayi, ta sauya kaya ta fito zata tafi.  Tana fita harabar wajan idonta ya sauka akan nashi lokacin da ya ke dagawa yarinyar data gani dazun hannu, duk da dai bata ga fuskarta ba amman ta tabbata ita ce. Dogouwar riga ce cikinta ta material, tayi rolling karamin veil, rabin fuskarta kusan a rufe da glasses din da ta saka.

Wato har sai yanzun? *'Dole ki dade fuska mana'* Ta fada a ranta, sai kuma tayi saurin kauda kanta tana istigfari tun da ba zata yanke mata hukunci kai tsaye ba. Da sauri ta wuce shi ta fita gate din har tana hardewa, kar wani tsotsan da zai sa ya sake wulakantata ya gifta kuma.

**

*Fahad*

Ayra da ke kuka ta dago jin karar rufe kofar ta kalle shi.

"It's okay abinci aka kawo min. Zaki iya ci?"

Ta girgiza kai. "Na koshi"

"Kar ki sawa kanki damuwa na fada miki, komai zai zo da sauki In shaa Allah. Zan yi magana da Mami in na je gidan"

Ta ida share kwallar da ta rage a kwarmin idonta tare da gyada kai. Ya sake kallonta da damuwa

"Kin tabbata abin da kike so kenan?"

Ta sunkuyar da kanta, sannan ta kuma daga kai.

"Shikenan, I'll try my best. Now mu ci abinci, sai ki koma gida. In dai kika tafi ba ci za kiyi ba na sani"

Ba tayi gardama ba tashi ta dauko abincin da aka aje ta matso da shi.

"Me yasa za a aje anan?"

Ya daga kafada.

"She might have a wrong idea"

"About?"

Ta tambaya da confusion.

"You being here, or maybe the hug"

Sai ta yi dariya. "Lalai, to bata ga muna kama ba?" Ya sake dage kafada, kafin ya sauko ya nade kafarshi.

"Wait.." Ta fada bayan ta bude abincin"

"Wannan ne break din?"

Yayi dariya.

"Ki ci kedai akwai dadi. Sai ki hada da tea"

"You and sakwara" Sannan ta mike ta wanko hannu ta dawo ta fara ci, a tare suka cinye ta na ta santi.

"Ni dai na san ba banza ka likewa wajan nan ba ashe da dadi abincin su. Kake min takeaway in zaka zo?"

Ya yi dariya.

"Please Yayaa. Zan fadawa Yaa Khalid tou shi ai na san ba zai manta ba"

Daga haka ta haye gadon shi, ta na latsa waya har bacci ya dauke ta. Bai tashe ta ba ya san Mami ta ke gudu don haka ya kyale ta tayi bacci mai isarta. Da ta tashi tayi sallar azahar ya sa aka kawo mata wani abinci ta ci. A lokacin wayarta ta dinga kara, da sunan Mami a sama.

Ta dago wayar ta na gwada masa. Yayi dariya

"Sai ki tashi ki koma gida haka nan" Ya kalli wayarsa da ke kara ya kauda kai ya san Khalid ne, kuma bai shigo bane don ya san suna magana da Ayra. Yau ne ranar taruwansu GHC kuma suna da sauran abubun da za su yi kafin lolacin. Haka kawai ya ke jin bai son zuwa yau din.

Isa ya kira, don ya maida ita gida sannan ya raka ta har harabar hotel din. A lokacin suka kuma hada ido da yarinyar, ya kuma gane ta tabbas. Ya kauda kansa. Ya na tsaye har motar su Ayra ta fita kafin ya koma ciki.

A dakin ya iske Khalid ya na jiran shi, wanka yayi kawai ya tattara duk abin da zai bukata su ka fita don gidansa zai wuce idan sun tashi partyn nasu.

*******.       *********.      *********

**Golden Hour Club**

Karfe tara da rabi ya isa club din. Daga waje gate ne ba wani mai daukar hankali ba, haka hasken fitilan ma guda daya ne mutum daya ne zaune mai bude gate da rufewa. Idan an wuce gate din babban fili ne sai kuma wajan da aka tanada don aje motoci daga can gefe. Kofar shigar a dayan gefen ta ke daga hannun dama. A nan ne tarin securities suke da uniforms dinsu kowa, kallo daya ma in kayi masu za ka shaida ba wasa suka zo yi ba. A nan ne mutum zai nuna dan karamin katinsa mai ruwan gold, sai su saka na'ura su yi verifying kafin mutum ya wuce. Wannan kaidar dole ne ga kowa duk dadewar mutum ya ne zuwa haka kuma ga sabbin zuwa.

Duk da ya riga ya shigo amman har lokacin bai jin dadi zuwan, kamar ko yaushe da ya ke zuwa cike da doki. Shi kadai ya zo Khalid sun rabu tun daga wajan da akai masa gyaran gashi, na fuska da kuma saka kaya. Duk da wani lokaci suna zuwa da Khalid amman ba sosai ba. Isa kuma bai taba kawo shi ba a duk sadda zai zo shi ke zuwa, kamar yadda kowa a wajan ya ke zuwa da kanshi.

Ya mika card din sukai verifying sannan ya shiga. Ya na wuce kofar wadataccen haske ne da ya haske ko ina tamkar rana a wajan ma fili ne sai dai an kawata wajan da concrete chairs jefi jefi sai water pond a tsakiya, a kasan kuma grass carpet ne. Wata kofan ya kuma shiga a nan asalin hall din ya ke wanda ya ke a kawace da deco kala kala, a kowanne party da kalar deco'n da ake mashi. Wannan karon Red & white ne komai na wajan. Tables ne jefi jefi da kujeru zagaye da su a tsakar hall din kowanne an jera flowers masu kyau da empty plates, tissue da kuma expensive bottles of non alcoholic beverages. Sai kuma gefen hagu da na dama dogayen kujeru ne da zasu iya cin mutum shida a wadace da kananun pillows an jera.

A kallo daya ya fahimci kusan kowa da ya kamata ace ya na wahan ya zo, sun kuma yi kyau iya kyau. Shi din ma ya yadda da kyawun da yayi, brand din kayansa, boot, chains har zuwa hair style din sa kaf babu abin da yaji ya gaza. Ya na shiga kusan rabin mutanen da ke wajan suka dau sowa musamman daidaikun bakin da akan samu don su samu damar haduwa da celebrities, kamar shi dai.

***    ***

*Farha*

Tun da rana take zagaye-zagaye ta kasa zaune ta kasa tsaye. Ta dai san daman dole sai ta shirya yadda za tayi ta iya fita da dare, amman sam bata zaci abin zai zo haka ba in ranar ta yi. To me zata ce wa Abba? Ina zata ce zata je da har za tayi dare bata dawo ba? Da kyar ta babbuga abincin rana ta gama ta ci gaba da zagayen ta da neman mafita. A haka har Layla ta dawo. Tunani take ko ta fada mata gaskiya? Amman kuma ta san halin Layla sarai in dai ba wai ta kalla maganar da idon basira bane  ta fahimce ta, to fa ba zata taba bata goyon baya ba. Sai da akai sallar magriba Layla ta kalle ta.

"Me ke damunki ne?"

Ta kalle ta. "Ba komai"

Daga haka Layla ta juya ta ci gaba da linke shanyar da ta kwaso kafin a wuta ta goge su.

"Yaa Layla"

Ta kira sunanta a hankali cike da ladabin da a ba Laylar mamaki. Ta aje kayan ta juyo ta na kallon ta da kyau, don dai ita ta sn dole akwai abin da ke damun Farha ko kuma akwai abin da ta ke son ta yi wanda ta ke shakka.

"Ina jin ki"

"Uhm..Yaa Farha. Daman dai na ce barin fada miki.."

Sai kuma ta yi shiru. Layla ta ci gaba da kallon ta. Hakan ya sa ta fahimci ita dai take jira.

"Uhm..Ina son na je wani waje ne..da dare ake yi"

Ta ida maganar tana kallon fuskarta don ta karancin fuskarta.

"Ina ne? Me ake yi wajan?"

"Dan taro ne, kuma uhmm..Fj zai je ne har ma an bani card din gayyata"

"Kuma shi taron har sai da dare ake yi? Ke ma kin san Abba ba zai taba bari ki sa kafa ki bar gidan nan da dare ba ko?"

"Eh na sani, shi yasa ai nake fada miki"

"Me ne nawa a ciki to Farha? Ko kina ganin in na tambayar maki Abba zai bari ki fita?"

"A'a..ba ki gane ba Yaa Layla"

"Fahimtar da ni"

Ta fada ta na ci gaba da kallon ta.

"In za ki min cover in je shaf shaf in dawo?"

Kallon da Layla ta yi mata ya sa ta ji zufa ta karyo mata. *Shikenan ba za tayi ba* ta fadi a ranta

"Farha, koma ina ne zaki je kiyi hakuri ki fidda shi a rai, in kina da rabon ganin Fj za ki ganshi"

Ta mike tsaye.

"Ai ke tsiyata da ke kenan, ba za a taba abin arziki da ke ba a rayuwa. Kuma ni sai na je koma mene zai faru in na dawo sai ya faru"

Sakin baki Layla ta yi tana kallin Farha. Da man da tsohon haushin Fahad din da take ji, da kuma ganin yadda ya wani rungume mace ba ko kunya ya sa ya ida fice mata a rai, tun da daman ba wai ya na birge ta bane.

"Babu in da zaki Farha, ki rubuta ki aje. In kuma kika cigaba da min rashin kunyar da kika faro zan je na fadawa Umma abin da kike shirin yi, sai in ga idan ita ma hakan zaki fada mata"

Kwalla suka kawo idon ta.

"Ke ni ban taba ganin in da yan'uwa suke haka ba, ni dai na san bani da wacce zata iya rufa min asiri a duk duniyar nan in ba ke ba Yaa Layla shi yasa ma kika ga na tunkare ki da maganar, amman sai kika watsa min kasa a ido, kika nuna min ban isa ba, ban isa na roki alfarma a wajan ki ba"

Jikin Layl yayi sanyi, tabbas ta na son Farha kuma zata iya mata koma mene, amman wannan wani abu ne da ta san ko me ya faru da sa hannunta a ciki. Laifin zai zagayo ya sargafe ta ne a matsayinta na babba. Kuma yadda ta san Farha da kwallafa rai ga abu, balle yanzun da take ganin ta samu damar da zata ga Fj..za ta iya cewa a tsawon rayuwar Farha ta ta'allaka burinta ne kaf a Fj don duk wanda ya san Farha ko da zaman mintina talatin ne to tabbas zai shaida soyayyar da ta ke wa Fj. To ita yanzun ya za tayi da ita. Ta daga kai ta kalle ta, ta ga ita take kallo idanuwanta cike da roko.

"Ina kika samu card din shigar?"

"Yaa Layla labari ne mai tsawo, amman na miki alkairib zan fada miki. Yar uwar shi ce ta samo min wallahi ba karya nake ba.."

Karar wayarta ta katse maganar sunan Beelah ya fito. Ta dago mata wayar alamun ta gani, sannan ta dauka tare da sa speaker.

"Kin tafi wajan makeup din?"

"Yanzun zan tafi."

Ta fadi tana kallon Layla da ke kallon ta.

"Okay, ki hanzarta saboda zai dauki lokaci, zan kira ki anjima"

Ta katse kiran.

"Ita ta samo min" ta fadi tana aje wayar.

"Ki bani address din, wajan kwalliyar da na wajan taron. Sannan kar ki sakr dare yayi sosai baki dawo ba, har Umma ta fahimci baki nan, kin amince?"

Da sauri ta daga kai da tsananin farincin da Layla ta yi mamaki. Dukkan location din da Beela ta tura mata tayi mata sharing san

nan da sauri ta dauku duk abin da zata bukata, ta rungume Layla ta ce

"Thank you My love"

Ta leka taga ba kowa tsakar gidan ta fita da sauri.

**Present**

🦋🦋🦋