Kuncin zuci
by @bintuuu
Jingina Na'ima tayi da gadon still bata daina tunanin yanda rayuwanta ta dauko canji ba, ta rufe idonta wasu hawaye suka zubo daga mata, kuka tafarayi nan zaune abincin na gabanta, sai da tayi me isanta sannan ta share fuskanta, tananan zaune aka bude kofar dakin nata shafa ta sake shigowa wannan karon hannunta riqe da Ghana must go din Na'ima, tace "Yar nan bazaki hau gadon bane, ga kayanki nan" Na'ima ta gyada kai tareda miqewa ta karbi kayan shafa na bin ta da kallo sannan ta bude mata wardrobe tace "Sa kayan naki anan" bayan Na'ima ta ajiye gurin da shafan ta nuna mata sai ta sake komawa zata zauna a qasan shafa tayi saurin dauko blanket daga cikin wardrobe din ta ajiye nan gadon tana instructing dinta ta hau gadon, cikin sanyi Na'ima tace "Zan wanke hannu na" shafa ta gyada itadai bata daina kallon yarinyar ba, ganin ta qarama ga kyau, ga kuma wani sanyin nutsuwa atattare da ita, bayan ta wanko hannun a toilet ta hau gadon shafa tayi mata saida safe sannan ta kashe wutan dakin tareda rufewa bayan ta fita..
Daren ranan dakyar Na'ima tayi bacci, tana ta saqawa da warwara a zuciyarta, abu daya yake qara mata qarfin gwiwa akan zuwanta wannan gida, shine in ta tuna makarantar da kawun nata ya mata alqawarin yi....
Washegari bayan ta tashi tayi sallah batayi gigin fita daga dakinta ba, dan batasan me zata farayi bama a gidan, har gari ya gama wayewa kusan karfe takwas bata fito ba, sai da taji yunwa na neman nuqurqusar ta sannan ta bude qofan a hankali ta leqa babban falon, gidan shiru kamar Allah beyi halitta cikinsa ba, fitowa tayi ta tsaya bakin kofan tana bin ko ina da kallo sai ga shafa ta fito daga wani corridor dayake facing din Na'ima from other side of the falo, ganin Na'ima tsaye yasa shafa cewa "Yarinya kin tashi" ta qaraso ta sake cewa "Ya sunanki?" cikin sanyin murya ta amsa da "Na'ima" shafa tace "Sannu Na'ima" gyada kai tayi ta gaisheta, bayan ta amsa tace "Ki hau sama su Hajiya da Alhajin na can" Na'ima ta amsa da toh sannan ta nufi stairs dinda taga alhajin ya bi jiya, wani falo ta idda babba a saman, Hajiya zaune itada Alhajin a kujera daban, dagowa sukayi Jin takun mutum suka kalli Na'ima da tashigo wadda ganin kallonta suke yasa ta dan daburce, sai Alhaji Abdullahi yayi murmushi yace "Na'ima kin tashi, qaraso ciki" zama tayi nan qasan carpet ta gaishesu Alhaji ya amsa, Jin hajiya bata amsa ba yasata juyawa gurinta ta gaishe ta, ciki ciki ta amsa bata daina kallon Na'iman ba, Alhaji yace "Ya kwanan baqunta" tayi dan murmushi batace komai ba, ya sake cewa "Kin hadu da yayanki kuwa?" bai jira amsanta ba ya juya ya kalli Hajiya yace "Jiya ya kwana gidan nan ma kuwa?" Hajiya tace "Ya dawo cikin dare, bai tashi bane" Alhaji yace "Bai sake min maganan komawan nasa ba kuma" Hajiya ta sauqe numfashi tace "Yace bazai koma ba sai an canja masa, nazata ya fada maka ai" Alhaji yace "Wannan din ma bayaso kenan, makaranta ta uku fa kenan" Hajiya tace "Toh ya za'ayi, meye amfanin mu in baza mu masa abunda yake so din ba Alhaji, Allah ya hore ai sai masa " Alhaji ya gyada kai yace "I'll see what i can do then" tace "Da asuba na leqashi wai kansa na ciwo ne ma" ajiye shayin hannunsa Alhaji yayi ya miqe tare da cewa "Meya sameshi?" Tace "Ka tambayesa in kaje, nayi nayi ya fadamin yace in kyalesa bacci yakeji" nufan wani corridor Alhaji yayi dake nan falon zai dubo dan gudaliyan dan nasu da har sannan ko sallahn safiya ma be tashi yayi ba balle ya fito ya gaida iyayen nasa.....
Bayan fitan Alhaji, Hajiya ta maida kallonta kan Na'ima wadda da alamu ma sun manta tana zaune nan falon, dan gyara zama Naima tayi alamun she's uncomfortable na kadaicin nasu, Hajiya tace "Shiga dakin can ki wanke min toilet din ciki, ai kin iya ko?" Na'ima ta gyada kai tareda miqewa ta nufi dakin da Hajiyan ta nuna mata, abunka da yarinta haka Na'ima ta cire hijabinta ta tsugunnan nan qasan bandakin ta rinqa dirzar sa da soso tana kora ruwa, ga yunwa sai cinta yake a sannu, bayan ta gama Hajiya tace ta dauko tsintsiya da mopper ta karkade nan falon saman, nan ma ta hau shara tana kade ko Ina Hajiyan na zaune tana danna wayarta jefi jefi take nuna mata yanda zatayi mopping din, bayan ta gama ta sauqa qasa hannunta da bokatin shafa ta fito daga kitchen tace "Inata jiran sauqowarki 'yar nan, zo kici abinci" da sauri Na'ima ta gyada kai tabi bayanta hannunta riqe da bokatin, anan kitchen din shafa ta bata shayi da biredi ta zauna tafara sha, ko kurba uku batayi ba taji Hajiya ta yanko mata kira da qarfi, jikinta na rawa ta ajiye kofin shayin ta fice zuwa falon, a matakalan stairs ta ganta tsaye fuskar nan babu annuri tace "Canjo ruwan da nasaki kenan" Na'ima tace "Gashican Ina canjawa ne Umma" Hajiya tace "Ba sunana Umma ba" Na'ima tayi saurin gyada kai tace "Toh" sai kuma ta sake cewa "Inje in dauko bokitin?" Hajiya tace "Tambayata kikeyi ma" nan ma Na'ima tayi saurin jijjaga kai tace "A'a kiyi hakuri" ta juya cikin sauri zata je dauko ruwan mopping din da ta baro a kitchen, shafa na bin ta da kallo har ta dauka ta fita batace komai ba....
Ranan Hajiya bata dubi qananun shekarun Na'ima ba haka ta rinqa yanko mata aiki kamar wata babba, haka ta rinqa aiki daga wannan sai wannan bata zauna ba, da rana suna aikin abinci itada shafan Hajiya ta shigo kitchen din, ganin Na'ima na faman gyara hijab tana aikin wanke kayan miya yasa ta cewa "Ki cire hijab dinnan karki saka mana datti a abinci" itadai Na'ima komai akace sai cewa "Toh" takai hannu ta cire hijab din, Hajiya da shafan sukabi gashinta da kallo wanda ke dunkule an daureshi da igiyan zani da aka yaga, tun parking dinda Anty Amarya tayi mata da zata zo ne akanta jikinta kuma sanye da wata kodaddiyar atamfa, ganin Hajiya na kallonta yasata kai hijabin kanta da nufin daurashi sai Hajiyan tace taje ta dauro dankwali ta dawo,
Haka suka rinqa aiki itada shafa kuma dayake ta dan saba da wahalan sai bai wani dameta ba, komai akasata yi take cikin azama gashi tayi hakuri da yunwan cikin nata bata tambayi shafan ta bata guntun biredin nata na dazu ba, bayan sun gama shafa ta fita kai abincin dining tadawo ta cigaba da hada juice din kankana, Na'ima na nan zaune an saka mata abincin a plate tanaci a hankali, data gama sai ta miqawa Na'iman tray me dauke da jug tareda kofuna tace ta kaiwa su hajiya suna can dining area, wanke hannunta tayi ta karba ta nufi fita daga kitchen din, da Hajiya ta fara tozali sannan wani farin saurayi da bazai wuce shekaru 24-25 ba yana nan zaune gefenta yanacin abincin shima, sai Na'ima taji shakkar qarasawa gurin nasu gudun Hajiya tayi mata fadan batayi daidai ba, dago kai saurayin yayi yadan tsaya kallonta hannunta riqe da tray, juyawa yayi ya kalli uwar tashi yace "Who is she?" Hajiya bata dago kanta ba tanacin abincin tace "Mahaifinka ne ya debo ta daga qauye jiya" yasake juyowa ya kalli Na'ima sai kuma ya daga wani cup nan gefensa ya miqo mata alamun ta zuba masa abun hannun nata, da saurinta ta qarasa ta zuba masa yana bin zara zaran yatsunta da kallo, bayan ta zuba masa yana kallonta yace "Shekarar ki nawa?" Hajiya ta dago kai ta kallesa tace "Bilal....." ya juyo yana kallonta ta jijjaga masa kai alamun bataso sannan ta kalli Na'ima tace "Je ki gama aikin dana saki" Na'ima ta juyi ta koma kitchen din Bilal na bin bayanta da kallo...
Alhajin da Na'iman bata sake ganinsa ba kenan a gidan sai da tayi kwana biyar dan da sassafe yake fita sai kuma dare can yake dawowa kasancewar dan kasuwa ne babba sai ya zamto har tafiye tafiye yana yawan yi akai akai, a 'yan kwanakin nan Na'ima ta gane shayi ruwa ne a fagen aiiki gurin Hajiya, zuwa sannan ma bata ganin Bilal a gidan dan inta san ya fito cin abinci ma zamanta takeyi a kitchen ko dakinta har sai taji ya tafi, abincin dare daman can falon saman yawanci shafa take kai masa shida Hajiyan..
A rana ta biyar din ne tayi sa'ar samun Alhaji a falon lokacin da taje gaishesu, Bilal na kishingide kan kujera yana danna waya ya dago ya kalleta, ganin Na'ima yasa Alhajin cewa "Ayya daughter kinyi ta cigiyata ko" tayi murmushi ta zauna nan qasa kan carpet ta gaishesu Bilal na kallonta, amsawa sukayi har da Hajiyan, sai Alhaji yace "Yau dai zanyi waya inji batun makarantar nan, nadan shafa'a wallahi" ya kalli Hajiya yace "Kuma baki tunamin ba" Hajiya ta dan juya kai tace "Nazata kana sane toh" yace "Wallahi na manta, I'll talk with sufi anjima se yazo ya kaita su mata interview" Hajiya ta gyada kai, ya sake cewa "Ba'a siyo mata kaya bane, what is she wearing haka" ko ci kanka Hajiya batace ba ta juya kai tana kallon Tv, ganin bazata kulasa ba yasa shi dauko waya yayi transfer din kudi nan zuwa account dinta yace "Ki aika ko shafa ta siyo mata kayan anjima" sai sannan ta gyada kai ta juya gurin Bilal tace "Babana akawo maka shayin nan?" ya girgiza kai tareda cewa "Bazan sha ba dai Hajiya" cikin lallashi tace "Ayya bakaci komai ba dai har yanzu, ko ayi maka kunun madaran?" sai sannan ya gyada kansa ya maida hankalinsa kan wayarsa, kallon Na'ima Hajiya tayi tace "Je ki kiramin shafa" Na'ima ta amsa da "Toh" sannan ta tashi ta fice tabarsu nan zaune falon.....
Daren ranan Na'ima ta fito daga kitchen zata je dakinta Bilal ya shigo falon ta kallesa, sai lokacin ta qara lura ma harda qaramar chain ashe a wuyansa, kansa cike da gashi me uban yawa ya tara da wani farin dan kunne qarami maqale a kunnensa guda daya, sauqe idonta qasa tayi ganin yana kallonta, cikin sanyin murya tace "Ina wuni" bai amsa ba yace "What's your name?" tace "Na'ima" yace "Shekarunki nawa?" nan ma a hankali tace "Sha hudu" kallonta ya rinqa yi tun daga sama har qasa kafin ya wuce zuwa stairs, sai sannan ta sake numfashin da take ta riqewa tun dazu tayi saurin shigewa dakinta, cikin tsakiyar dare tana cikin bacci taji qarar mota alamun an shigo gidan, farkawa tayi adan firgice ta miqe jin qarar motan da dan qarfi ta nufi window tana leqawa, Bilal ta gani ya fito daga cikin wata sport car anan parking space, hannunsa riqe da karar taba yana zuqa, saurin sauqe labulen Na'ima tayi gudun kar ya kamata tana leqensa, jefar da taban yayi sannan ya shiga gidan, samun Hajiya yayi tsaye nan gurin stairs cikin kayan bacci tana jiran shigowarsa, tana ganinsa ta marairaice murya tace"Babana bazaka dinga haquri da fitan daren nan ba Fisabilillah, hankalina baya nutsuwa kasani har se ka dawo, haba dan Allah" be kulata ba yazo ze wuce ta kusa da ita ta dan riqo hannunsa ganin alamun yau ma ya shawo abar, tace "Muje ka cire kayan nan duk wari suke" ya gyada kai idonsa yayi jaaa baice komai ba suka wuce dakinsa dake nan falon saman shima, jibgewa nan kan gadon yayi bai cire kayan jikin nasa ba sai Hajiya ce ta miqa hannu ta cire masa takalman kafan sa tana kallonsa, Alhaji ne ya shigo dakin ransa a dan bace yace "Bilal sit up and take off those cloth" Hajiya ta dan riqo Alhajin tace "Easy mana, kansa ke masa ciwo dai" yace "Bakiji kayan na wari bane" ta dan marairaice tace "Yanzu ze cire ai" Bilal ya mirgina dayan side din gadon cikin magagi yace "Oh God" Hajiya ta riqo Alhajin tace "Mutafi, da asuba ze cire kayan" sai Bilal ya sake riqo kansa bai ce komai ba, atare Hajiyan da alhajin suka duqa cikin damuwa suka fara tambayansa meya faru, ya bude idonsa da yayi jaa a hankai yace "Ku barni nayi baccin" Hajiya ta gyada kai tareda lulluba masa blanket tace "Toh shikenan sai da safe mayi magana" ta riqo hannun Alhaji suka fice, nan bakin qofar dakin suka tsaya bayan ta rufo kofan a hankali, Alhaji na kallonta yace "It's getting worse, we have to do something" Hajiya ta kwantar da murya tace "Mubari zuwa safiya tukunna, sai mu sake masa fadan cikin lallami, har yanzu dai bai cika ashirin da biyar ba, da sauran sa a fagen hankali Alhaji" sai Alhaji ya gyada kai tareda cewa "Banason yabi jikinsa muzo muna danasani ne" ta gyada kai itama tace "Mubi komai a sannu tukunna, yaron nan kasani shi kadai ne farin cikinmu, tun yanzu in mukace zamu taqurasa sai ya shiga wata hanya daban kuma" a haka Hajiya ta lallaba mijin nata suka koma makwancinsu zuciyarsu cike da tararradin hanyar da dan gudaliyan nasu dauko....
Washegari Na'ima taje falo gaishe da Hajiya ta sameta zaune ita da shafa dake tsaye, gaishe da Hajiyan tayi bata amsa ba ta cigaba da maganan da takeyi da shafa, bayan shafa ta gama sauraron saqon da Hajiyan ke bata ta juya ta fice, jawo ledan gefenta Hajiyan tayi ta wullo wa Na'ima a jiki tace "Ga kayan nan, sai ki dena saka tsummokar nan kuma, ya isa haka" Na'ima ta riqo ledan tace "Nagode Hajiya Allah ya saka da alkhairy" gyada kai kawai tayi bata ce komai ba, ganin shirun yayi yawa yasa Na'ima miqewa ta fice daga falon riqe da ledarta, duk da kayan ba wasu na azo a gani bane hakan bai hana Na'ima yin murna sosai ba, ta fito da kayan da daddaya tana kallo, dinkin kaya kala shida, hijabai guda uku da takalma guda uku, murmushi ta rinqa yi tana gwadawa a jikin ta nan gaban mirror, sai data gama gwadawa sannan ta maidasu cikin wardrobe nacikin jakanta kuma ta adanasu suma bata zubar ba, da rana saiga sufi yazo kaita makaranta, sai lokacin ta gane ashe shine driver'n daya kawosu daga Adamawa lokacin da zasu zo garin kano, Sufi PA din Alhaji ne dan yawanci ba aikin waje ba har na cikin gida yana sashi yayi masa su, dazasu tafi Hajiya na dakinta tana bacci bata fito bama...
Wata makarantar kudi Alhajin yasa aka kai Na'ima, sai baza Ido take tana kallon yaran manyan mutane a nan cikin compound din makarantan, basu wani bata lokaci ba bayan interview din a inda sukaga kan Na'iman na ja sosai, daukanta Jss 1 sukayi akan zuwa gaba dole a mata jumping dan tayi girma a jss 1 a wannan lokacin..murna gurin Na'ima ba'a cewa komai, ranar uniform dinda suka bata ma kasa sakawa tayi a wardrobe, nan ta ajiye su kan gado bini bini tana kallo...
Haka rayuwan Na'ima ta kasance gidan kawunta, da shafa kadai take samun yin dogon magana dan Hajiya dai qarara ta fito fili ta nuna mata bata yinta kuma, Alhaji kuma yau yana gida gobe baya qasar haka dai rayuwan take tafiya, ta fannin Bilal kuma sai tayi sati basu hadu ba dan in akace yau yashawu ma sai ya wuni a gidan yana bacci Hajiya na leqashi, baya yawan zaman falon qasa sosai saidai na sama gurin Hajiya wanda nan din daman ba gurin zuwan Na'iman bane, duk dare kuma yanacan club sai daren ya tsala zai dawo yayi ta buga horn yana tada duk masu bacci a gidan, ana cikin haka Alhaji ya sake nema masa wata makarantar a qasar Europe, wata university dake nan cikin Luxembourg, dakyar suka lallabashi ya tafi hoping that a wannan karon Bilal zai maida hankalinsa yayi abunda ya kaisa batareda ya sake katse karatun nasa ba...
Watarana Na'ima ta dawo daga makaranta ta samu Kawu Ayuba nan tsaye a compound din yana jiran Hajiya tayi masa iso, yakai minti talatin a wajen tsaye bata aiko ya shiga falon ba, Na'ima na ganin kawun nata tayi saurin qarasa gurinsa tana murmushi ta gaishe sa, yana kallon ta cikin fara'a yace "Na'ima haka kika koma?" tayi dariya tace "Kawu yasu Umma da Anty Amarya?" Yace "Duk sunanan lafiya sunce a gaisheki suma suna nan tafe, zasuzo ku gaisa" Na'ima ta gyada kai still tana murmushi, duk da ba wani dadin kawun nata tajiba a rayuwa ba at least taji sanyi da ta gansa, saboda har yau zuciyarta ta kasa amincewa nan din da take zaune shima kamar gidan babanta ne..
Suna nan tsaye kawu Ayuba yace ta shiga ciki, wucewa tayi ta shiga falon, a hakimce ta samu hajiya tana zaune anan falon gabanta kuma wasu laces ne nan kan table tana waresu da daddaya, ganin Na'ima yasa ta cewa "Je kice baban naki ya shigo" Na'ima ta juya ta samu kawu Ayuba nan tsaye ta isar masa saqon, cikin azama ya amsa da "Toh" ya biyo bayan Na'ima suka shiga falon tare, bayan sun gaisa da Hajiyan inda dakyar take amsawan , kawu Ayuba yace "Dama inata kiran layin Yaya ne baya tafiya shiyasa na zo da kafata in sanar masa Allah ya yiwa Goggo rasuwa satikai biyu da suka wuce" Hajiya tace "Baya qasar yanzu tukunna" Kawu Ayuba yace "Allahu Akhbar, ashe shiyasa layin baya tafiya" tace "Allah yaji qanta, in ya dawo za'a fada masa" kawu Ayuba ya amsa da godiya, nan Hajiya tayi shiru bata sake cewa komai ba, ganin yanayin atmosphere din yasa shi cewa "Toh Hajiya ni zan wuce, Allah ya qara girma" ita ta fara miqewa tace "A gaida gida" sannan ta wuce stairs Ayuba ya dan bita da kallo sai shima ya miqe, fita yayi daga falon Na'ima dake jiran taji fitarsa ta fito daga dakinta cikin sauri ta bi bayansa, anan compound din tace "Baba" da dan qarfi, juyowa yayi ya tsaya har ta qaraso ta miqa masa ledan hannunta me dauke da sabbin kayanta kala biyu da kuma tsofin datazo dasu gidan harda takalmi kala daya da hijabi guda biyu tace "Baba gashi a kaiwa salame" karba yayi yana murmushi yace "Allah ya miki albarka Na'ima" ta gyada kai yasake cewa "Ki bi mutanen nan sau da qafa kinji" ta amsa da "Toh" hawaye na kawowa idonta tace "Baba yaushe zanje in ga goggo" shiru yayi be ce komai ba da farko sai kuma yace "Ki bari sai iyayen naki sun baki iznin zuwa tukunna kinji" ta gyada kai tareda cewa "Toh" da haka sukayi sallama kawu Ayuba yabar gidan ko ruwa Hajiya bata bashi yasha ba balle azo batun kudin mota kuma....