Kamar da wasa pg 9
by @mrsomar
KAMAR DA WASA 💘
Page 9
Fatima Isa
(Mrs Umar)
Gwaggo Hakima tsaya a tsakiyar farfajiyar katafaren gidan Shattima kamar sarauniyar da aka ɓatawa mutunci. Idanunta kamar wuta, zuciyarta tamkar gobara, bakinta kuwa, tamkar bututun hayaki
“Hamma Yusuf! Amina! Ku fito wannan karon ba lokacin shiru bane! Wallahi yau sai dai wani ya faɗi, ko wata ta faɗi!”
Yapendo ta tsaya a gefenta, hannayenta a cikin gyalenta, idonta cike da wutar izza. Yusura na gefenta, Karima a bayan su. Tsayuwarsu kaɗai ya isa ya janyo ’yan aiki da sauran matan gida su fara leƙowa daga shashe-shashe.
A take a wajen kowa ya fara fitowa cikin hanzari.
Aunty Amarya da Hajiya Binta. Uncle Musa Anisa na take mata baya Karima ta juyo da mamaki, ganin shigowar Imran.
Hanifa ta fito, tana kallon abin kamar fim.
Ubbah na fitowa cikin sauri, Dada na biye da shi, dukkan su a cikin ɓacin rai.
Dada ta kalli Gwaggo Hakima, murya na ɗaukar sanyi da ikon mallaka
“Me ke faruwa haka? Kike neman tarwatsa mana gida da safe haka Hakima?”
Gwaggo Hakima ta gyara tsayuwarta, tana kallon Ubbah da Dada kai tsaye.
“Ni wallahi da gangan na taso da hayaniya. Saboda tun jiya kuke kulle kulle, ku da Aisha, saboda ku yi gaggawar daura wa Shamsu aure da wata kuma saboda munafunci shine aka ɗaura auran ba tare da sanin kowa ba. Wannan shashanci ya ishe ni! Ita dai Yusura ya dace ta aura Shamsu. Ba wata banza can ba idan kuma ba haka ba Hmm"
Dada ta ɗan tabe baki, tana kallonta irin na mace mai cike da haƙuri da kai zuciya nesa.
“To idan Moddibo bai zaɓe ta ba fa?"
" Wannan ai shi ne babban kuskure.”
Yapendo ta ƙarasa gaba, ta ce da karfi
“Zaɓi? Amina wannan ba batu ne na zaɓi ba! Kema Amina kin san yadda Yusura ta kasance tana son Shamsu kuma dukan ku kun sani. Ya ƙwace mata zuciya. Sai ki ce bai san da soyayya ba!”
Karima ta ƙara a hankali cikin Fulfulde
“Walla,de min jooɗi fuw seto o waari,o Holla mo yide ”
Yusura hawayenta suka gangaro saman fuskarta sannan ta ce da muryar da ke daɗa sosan rai
“Dada, Ubbah! Ni dai ba na neman komai face adalci. Idan har na cancanci a manta dani, to yanzu zan bar muku gidan gaba ɗaya.”
Gaban Dada ya faɗi. Tuni fuskar Ubbah ya kara ɗaure ta. Aunty Amarya da Mamma (Hajiya Binta) suka kalli juna.
“Yusura kiyi shiru abi komi a hankali mu zauna a tattauna muga abinda ya dace ayi"
Gwaggo Hakima ta daga hannu sama tana fadin.
"A’a Hamma Yusuf. Wannan ba zaman tattaunawa bane. Sai kun zauna ku yanke hukunci sannan zaka dawo kana wata magana. amma wallahi da rai da lafiya sai dai an sa kafa a hana. Sai dai wani abu ya faru, amma Shamsu da Yusura babu wanda ya isa hana su aure”
Kafin wani ya ƙara magana, Ammie da Naana suka fito daga ƙofar shashen Dada, su biyun kallo suke kamar ba su fahimci komai ba.
Ammie ta yi ƙarfin halin cewa.
“Me ke faruwa haka da safe nan?”
Wata banzar dariya gwaggo Hakima ta saki mai cike da raini.
“Au. kun fito kenan? Toh ku zauna ku saurara, domin yau maganar mu ba za ta tsaya nan ba. In har waccen Naana ce da kuke shirin maƙalawa gudan jininmu ba tare da sanin mu ba. Ku sa rai sai mun tashi hankalinku daga ku har zuri'arku"
Yapendo ta amshi batun rai ɓace
"Kai yanzu Isuhu har ka yi girman da zaka watsar dani ka nunawa duniya ban isa da kai ba har zaka yanke hukunci ba tare da sanina ba to ai ka yi dai-dai haka ake so. Yusura kuma babu ubanda ya isa ya hana ta auri Shamsu a wannan gaɓar"
Shiru ya ɗauki gidan. Kowa ya kasa motsi. A lokacin S.Y Shatiima ke fitowa jikinshi sanye da Kayan motsa jiki hannun shi na hagu rike da ƙaramin towel yana goge fuskarshi. Cike da izza da takama ya iso wajen fuskarshi a tamke babu sauki a cikinta
S Y Shatiima ya tsaya a tsakiyar farfajiyar gida kamar dutse. Ido cikin ido Gwaggo Hakima ke kallonshi. Ya share zufa a gefen fuskarshi.
S Y Shattima yana da tsaye yana da faffaɗan ƙirji irin na masu motsa jiki a kuda yaushe, bazamu kirasa fari ba haka kuma zamu kirasa baki ba fatar jikinshi a murje take irin mai ɗaukar ido nan ce, yana da dogon hanci bakin shi ya ɗan sirka da Pink gashi daidai fuskarshi ko baka kaunar Allah kallo ɗaya zaka yiwa Shattima kasan ya hadu ajin farko.
Bai ce uffan ba. Sai bayan ya ɗan juyar da kai ya kalli Dada da Ubbah dake tsaye sannan ya ce
"Me ke faruwa ne da safennan haka? Waye ya tada hankali a gidan nan sai kace ana cin kasuwa?"
Muryasa mai sanyi amma cike da gargaɗi irin na soja da ke iya sa ƙaramin yaro ya tsaya chak.
Gwaggo Hakima na ƙoƙarin ɗaga murya, amma Shattima ya ɗaga mata hannu alamar enough
"Gwaggo wai ke kam wacce irin maca ce sam bakya son zaman lafiya? Tunda auren ki ya mutu kika dawo gidan nan shi kenan gidan nan bai sake samun zaman lafiya ba me kike so ki zama ne haba dan Allah"
Cikin fushi Yapendo ta amshi batun.
"Dole kace haka mana dan uwarka ta sakaka a ɗaki ta kitsa maka abinda take so har ka amince da auren Naana to ku sani kunyi a banza dan yau ba sai gobe ba za'a sake ɗaura maka aure da Yusura"
Wata malallaciyar dariya ya sake tare da kallon inda Yapendo take a rashin sa'a idonsa ya shiga cikin na Anisa amma sai ya basar. Ya wane sake tamke fuska yana nuna Yusura.
"Wannan abin ita zan aura to ai ko mata sun kare a duniya aka ce Yusura ta rage kadai zan aura wallahi sai dai na mutu ba da aure ba dan da na aur..."
"Moddibo! Ya isa haka"
Ammie ta katse S.Y Shattima cikin sauri saboda gudun abinda zai sake faɗa.
Uncle Musa ne ya yi gyaran murya cike da kamala ya ce
"To yanzu mu tsaya mu saurara! Wannan gidan ba kasuwa ba ne, kuma ba ofishin siyasa ba ne. Gidanmu ne. Duk wannan hayaniya da faɗa, sai ya nuna cewa babu wanda ke jin wani. Amma ai mu iyalin juna ne ko?"
Ya ɗan juya yana kallon Ubbah, sannan ya kalli Shattima.
"Shamsu! kai ne babba a cikinsu. Idan kai ka zazzage harshe kamar haka, to me kake tunanin yaran za su koya? Ai da kai suke kallo. Kuma ya kamata mu gane cewa aure ko da kuwa yana da wahala ba dole bane sai an tilasta maka shi"
Dada ta ɗan jinjina kai, tana dafa kirji.
"Moddibo ka rage zafi. Na san ba ka ji daɗin yadda aka zo da lamarin ba. Amma maganar da ka yi yanzu ta yi muni sosai. Yusura ’yar uwarka ce. Kuma Mama da Hakima ko da suna da laifi, bai kamata a ci mutuncinsu haka ba. Saboda su ɗin ba sa'an yinka bane"
S.Y Shatiima ya juya, ya ɗan ja numfashi, sannan ya kalli Yapendo da idon da ke cike da gajiya da damuwa.
"Ni ban taɓa raina ki ba. Yusura kuma na san kin fi kowa sanina a nan. Ban taɓa kallon daya cikin ku a matsayin soyayya ba, dukan ku 'yan uwa na dauke ku wanda muka fito ciki ɗaya. Kuma wallahi idan da ke ce na zaɓa da ba a sha faɗa ba. Sai dai kash babu wannan a zuciyata"
Yusura ta sunkuyar da kai, hawayenta na zuba a hankali, Yapendo na janta da gefe, tana rarrashi.
Anisa ta kalli Shattima cikin ɓoyayyen tausayawa, zuciyarta na ruri da wani nau'in kunya da ba za ta iya fassara ba.
Naana ta matso gaba, muryarta a natse.
"Ni ba ni ce na matsa wa kowa ba. Kuma wallahi idan aure na ne ke haddasa wannan faɗa, to zan barshi bana so a samu matsala a sanadina"
Shiru ya sake sauka.
Ubbah ya kalli Dada, sannan ya ce:
"To a yanzu, lokaci ya yi da za mu zauna mu yanke hukunci. Ba wai faɗa za mu rika ba. Kowa ya zauna da zuciya ɗaya, a ci gaba da zaman lafiya idan har muna son mu zauna da juna lafiya."
Kuka Naana ta fashe dashi mai cin rai tare da isa wajan Shattima ta zaɓe ƙasa tana faɗi.
"Please Hamma Sham na rokeka ka datse igiyoyin auren mu tun kafin na zama sanadin rabuwar kan ahali ɗaya, idan har yara kake tunani ni zan zauna dasu ko ba tare da igiyar auren ka ba"
Ido ya lumshe saboda ya tabbatar idan bai yi wani abu a wannan lokaci ba Naana zata iya sakawa a saka shi abinda bazai iya yi ba wannan karon. A hankali ya duka a karo na farko ya kai hannun shi jikinta ya ɗaga ta tare da kama hannunta ya fara tafiya da ita ba tare da ya kalli kowa dake wajen ba.
Salati gwaggo da yapendo suka saka har suna haɗa baki...
#Son zuciya
#Soyayya
#Yaudara
#Makirci