Chapter 2
by @mrsalkali01
✨ ZABI NA ✨
✍️~Mrs Alkali
🆓 Page 2️⃣
*ASALIN SU*
Malam Amadu Kalam asalin sa mutumin garin Kalam ne ,
"GARIN KALAM"wani yankine da ke cikin kauyukan garin dukku, a yanzu haka yana zaune ne a cikin garin dukku, a anguwar Nasarawo inda yake zaune da matar sa daya mai suna Hadiza ,suna da yaya uku Aliyu shine babba amma ba malam Amadu bane ya haifeshi ba dan yayansa malam Ibrahim ne da Allah yayiwa rasuwa shida iyalinsa yaya jummai sakamakon hadarin mota da sukayi a hanyarsu tazuwa gaisuwa zuwa garin Kalam, duka motar ba wanda yarayu sai dansu kwaya daya mai suna Aliyu, sakamakon malam amadu su biyu kawai iyayen su suka haifa shida dan uwan sa malam Ibrahim, sai riqon Aliyu yadawo hannun sa a lokacin matar sa Hadiza tana dauke da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe Aliyu yana da shekara biyar iyayensa suka rasu ,
Randa iyayen aliyu sukayi kwana arba'in da rasuwa aranar ne Hadiza matar malam Amadu ta haihu, tasamu danta namiji ,
Ran suna yaro yaci sunan mahaifin aliyu wato Ibrahim, bakaramin qauna malam Amadu yakeyiwa Dan uwan sa marigayi malam Ibrahim ba shiyasa da Allah ya azurtashi da samun yaro namiji ya mayar masa da sunansa,
Bahaka ummah Hadiza taso ba don taso ayiwa mahaifinta ne tokwara amma malam Amadu yace sai gaba in Allah yasake basu wata haihuwar, bakaramin kona mata rai abun yayiba amma haka tayi shiru ta hakura sabi da tasan malam amadu ba kanwan lasabane,
Malam Amadu irin tsayayyun mazan nanne a gidajensu ,don yana da rufin asirinsa dedai gwargwado kuma manomine sannan yana harkar seye da seyarwa na buhuhuna a babbar kasuwa bawanda bai sanshiba a wannan yankin, indai kace malam Amadu mai hatsi to fa harcikin rumfar sa za a kaika.
Malam Amadu Ya tsaya sosai akan iyalinsa hakan ne ma yasa ummah Hadiza take shakkan yimasa wani abun , Hadiza irin matannanne masu shegen son kansu ,gason abun duniya wannan halinnata yasa malam Amadu yatsaya akanta yake taka mata birki game da wasu abubuwan, da take aikatawa .