Chapter 3
by @mrsalkali01
✨ZABI NA ✨
✍️~Mrs Alkali ~
🆓 page 3️⃣
Hadiza Bataso riqon Aliyu yadawo hannun su ba sai dai bayadda ta iya hakan yasa bata damu da shiga sabgarshi ba , bata masa mugunta, Amma kuma babu shakuwa irin na da da uwa a tsakanin su shiya yanzu da ta haifi Ibrahim yadawo kullum Aliyu yana makale dashi kusan ma shi yayi renon Ibrahim, wanda hakan bakaramin dadi yakeyiwa malam Amadu ba inyaga yadda Aliyu yake kula da dan uwan sa Ibrahim yanajin dadi sosai hakan yana tunamasa yarantar sa shida marigayi mahaifin aliyu.
Tunda Hadiza ta haifi Ibrahim batasake ko batan wataba , harsun fidda tsammani, kwatsam sai ga Allah ya azurta hadiza da wani cikin a lokacin Ibrahim yana da shkara 7 yayin da Aliyu yake da shekaru 12 alokacin yagama primary zai shiga jss1,
Hadiza da malam Amadu sunyi matuqar murna sosai don abunda su kacire tsammanine don malam Amadu akoi shi da son yaya kona makotane , haka Hadiza tayi ta jan ciki har Allah ya sauke ta lafiya awannan karon tasamu yarta mace ,zo kuga murna awajen wannan ahlin, Masha Allah ran suna yarinya taci sunan mahaifiyar Hadiza wato Fatima inda suke kiranta da zara'u,
Duk wani renon zara'u da kulawarta Aliyu ne keyi tun malam Amadu yanamasa fadar cewa Reno na mata ne har ya hakura ya barshi dan yaga bashi da niyar dainawa, wani irin so Aliyu yakeyiwa zara'u wanda hakan ya haifar da shakuwa sosai atsakanin su, zara'u yarinya ce mai shiga rai , gata yar lukuta , Masha Allahu da ita,
Tunda malam Amadu yaga yadda Aliyu yake son zara'u yayi wani alkawari azuciyarsa wanda dagashi sai Allah ne kawai suka sani, yabar abun azuciyarshi.
Haka rayuwa tana ta tafiya shekaru sun shude inda ayanzu Aliyu yagama secondary school dinsa, har yasamu admission a GSU wato gombe state university inda zai fara karanta LLB common and Islamic law, Ibrahim kuma ayanzu ne yake SS 1,
Zara'u tana primary 6 a wannan lokacin, Aliyu yafara karatunsa cikin nasara da konciyar hankali dama mutum ne mai kokari akan abunda yake so, haka rayuwa tacigaba da tafiya yau fari gobe baki,
Akwana atashi asaran me rai Aliyu ya kammala karatunsa na LLB common and Islamic law sunyi graduation lafiya ya tattaro yadawo gida inda yanzu sauramasa tafiya law school ayayinda Ibrahim yake kokarin shiga level 1 a bangaren computer science ,
Zara'u tana SS 1 amma inkaganta zaka zaci taje SS 3 sabida yanayi na girman jikinta zara'u tana da kiba yar lukutace tana da matsakaicin tsayi wankan tarwa dace tanada ma dai dai cin hanci baicika tsawo sosai ba, Zara'u ta hadu da wata Qawar ta mai suna jamila a makaranta , nan fa suka kullah kawance ,jamila irinyarannanne da basajin magana hakan ne yasa da suka hadu da zara'u kawancen nasu ya dinke sosai dan itama zara'u ba bayaba wajen Rashin jin magana, gashi ummah bata ganin laifin ta komai tayi sai tace ai Yarinya ce watarana zata bari
Haduwar zara'u da Jamila yasa idon zara'u yakara buduwa sosai dan yanzu haka zara'u tana da saurayinta dayake zuwa gurinta hira me suna Mansoor, suna haduwa abakin layi dan su baba basu sani ba.
Mansoor matashi ne me kimanin shekara 33yrs dan bazai girmi Aliyu ba yahadu da zara'u ne ta sanadin qawar ta Jamila,
Watarana zara'u taje gidan su Jamila tana rakota anan Mansoor yaganta yacewa Jamila yanason ta Jamila datayiwa zara'u maganan Mansoor daga farko bata amince ba sai daga bayane da Jamila tayi ta Zugata kan ta amince , soyayyah sukafara da Mansoor a boye dan agida ba wanda yasani a hankali Mansoor yake kara budewa Zara'u ido don shima irin samarin nanne masu latsa yan mata ,dudda yana son zara'u hakan bai hanashi taba sassan jikinta ba in sun hadu da farko zara'u bata so Amma daga baya da tafadawa jamila sai tace mata ai wannan bakomai bane yanzu haka akeyi ai wayewa ce da haka zara'u tafara sakin jiki dashi har yasabarmata da taba ko ina ajikinta hakan ne yasa zara'u jin tana qara son Mansoor, jitakeyi bazata iya rabuwa dashiba dan ba qaramin so take masa ba,
Hakan ne yasa tace ya karaso gida su baba su san da zamansa ,a lokacin daya fara zuwa wajen baba neman izinin hira , baba ne yace masa yayi hakuri dan ,yayiwa zara'u miji, awannan lokacin ne ummah tace batasan zanceba wayene ,mijin da baba yace yayiwa zara'u n , baba ne yasanar da ummah Aliyu ne mijin da ya zaba mata amma daga ummah har zara'u sunki amincewa , da zancen Aliyu.
Baba yasha alwashin dazaran Aliyu yadawo gida wannan karon kafin yatafi law school din sa sai ya daura musu aure inyaso inyadawo daga law school din sai ayi taron biki ,jin wannan bayanin yasa hankalin zara'u yatashi dan ita nan duniya bata da miji sai Mansoor acewar ta kenan ,yadda takejin son Mansoor azuciyara wlh ko kasheta baba zaiyi bazata auri Yaya Aliyu ba,
Ummah ma ta tsaya kai da fata baba bazai hada auren zara'u da Aliyu, ba me Aliyu yake dashi yaron da haryanzu baba na dawainiya dashi ko makarantar bai gamaba ina amfanin ka sai da akuya ta dawo tana cimaka danga , toh wlh bazatayiwuba, wannan kenan.