Chapter 4
by @mrsalkali01
CIGABAN LABARI*
✨ZABI NA ✨
✍️~Mrs Alkali ~
🆓 Page 4️⃣
Baba ne yake zaune a tsakar gida yanajin yar radion sa labarun BBC yake saurara , Ibrahim ne ya shigo gidan bakinsa dauke da sallama hannun sa rike da katoton jaka irin na yan makarantarnan, kallo daya zakayiwa fiskarsa kasan yana cikin farin ciki, dan hausawa sunce labarin zuciya atambai fiska, baba ne ya amsa sallamar tare da maida hankalinsa akan Ibrahim din ,ganin yashigo da jaka a hannunsa, wani matashi ne yashi go mai kimanin shekaru 33yrs fari ne sosai dan haskensa har daukan ido yakeyi yana da tsayi don inmutum zai kalli fiskar sa sai ya daga kai ,fiskarsa na da dan kiba kadan amma ba sosai ba , ga bakin sajensa konce luf luf akan fiskarsa kasancewar gashisa yana da laushi har wani sheki yakeyi wanda hakan yakara wa fuskar sa kyau da kwarjini na musamman yanada hanci mai tsaye irin na larabawa ,gawasu irin idanu yan madai daita masu bala'in kyau da daukar idanun mekallion sa fararene tas saikace nono ga digon bakin ya kara haska cikin idanun nasa sosai cikin su har wani kyalli sukeyi , giranshi acike yake da bakin gashi wanda ya kwanta suna da dan fadi kadan har kamar zasu hade da juna ,sabida yanda gashin yacika wajen bakinsa madai daicine mai dauke da lips pink colour sunada dan kauri kadan , gawani rami da yadan lotsa a gefen kumatun sa , wato dimples,wani irin bakin gashi ne mai laushi yake konce akansa wanda hakan bakaramin karamasa kyau yayi ba, Masha Allah kai kace shiya hallicci kansa , bazakaso dauke idonka akansaba in kana kallonsa sabida irin baiwa na kyau da Allah yamasa kai kace ba dan Nigeria bane dan yanayinsa yafi kama da larabawan Qatar .
Inda baba yake zaune ya nufa kafin yakaraso baba ya tashi daga kan kujerar dayake zaune yana cewa kaga mutanen boko ,yau dai Allah ya nufa angama wanna bokon dan murmushi yayi kadan dan da wuya kaga murmushi akan fiskarsa tsugunawa yayi agaban baba yace munsameku lafiya, baba ne yayi saurin dagoshi yace lafiya qlu gadanga kusar yaki, yanzu nake ta tunaninka araina ai ashe kana tafe, Masha Allahu maza kashga daki ka huta zuwa anjima makara gaisawa, da kyau toh baba ina zara'u da ummah, cewar Aliyu,
Babane yaji wani irin dadi azuciyarshi ganin yanda Aliyu daga dawo wan sa har ya tambayi zara'u ko hutawa baiyi ba murmushin manya baba yayi yace naji umman ku tace taje gidan su kawarta Jamila, kansa ya kada alamar ya fahimta inda dakunan su suke ya nufa ,wato bangaren samarin gidan.
Dakunane guda biyu a jere daya na Ibrahim ne dayan kuma nasa bude kofan dakin yayi , shiga yayi komai na nan yadda yake , katuwar katifa ce shumfude a kasa irin wacce ake ajiyewa a kasannan, sai dan madai daicin drower mai dauke da bangare biyu ajikinsa ,bawani tarkace a dakin , sai carpet da ke malale a tsakiyan dakin sai dai akoi dan kura aciki sabida andan kwana biyu ba ayi amfani da dakinba ,don tun komawarsa ba ashare dakinba , Ibrahim ne yashigo dauke da jakansa , ajiye jakan yayi agefe yace yaya bari in sharemaka dakin, juyawa Ibrahim yayi dakin umma ya nufa , tsintsiya ya dauka ummah ce ta kalleshi tace mezakamin da tsintsiya, ummah dakin yaya Aliyu zan share masa ,tsaki ummah tayi tace wato yadawo shi ne baizo yagaisheniba koda yake ai ba uwar sa bace shiya sa dan dani na haifeshi bazai wuce daki baigaisheniba, baba ne dayake jin abunda ummah take fada ya girgiza kai dan inda sabo ya saba da irin wannan hali na ummah nanma yana takamata birki ,ne shiyasa take dan shakkah,haba Hadiza yaron da yadawo agajiye ai kyabari ya huta tukunnah kafin kifara karanto korafinki , cewar baba, dake kallon ummah,hmmm malam kenan dan gaban goshinka yadawo ko zakafara ko ai dayake kai kadai yadauka a uba kai ya tsaya ya gaisheka amma ni dake ba uwar sa bace ai bai nemi inda nake ba dadin abun ma dai nima na haifa ba za amin gorin haihuwa ba.
Baba ne ya kallah Ibrahim dake tseye rike da tsintsiyar har yanzu donyasan in dai yatafi ummah batace yajeba toh ya bonu da masifanta kenan wuce kaje ka sharewa yayan ku dakinsa cewar baba,
Wucewa Ibrahim yayi atsaye yasamu Aliyu dan dakin ko ina yayi kura ba wajen zama ,baranda ya fita yanajiran Ibrahim yagama sharar ,