Zaɓi na

Chapter 5

by @mrsalkali01

✨ ZABI NA ✨ 
 ✍️~Mrs Alkali ~



🆓 Page 5️⃣




Zara'u ne goye abayan machine din Mansoor daga anguwan su Jamila ya daukota dan nesa da gidansu yayi parking, sauka tayi tana tafaman waige waige don bataso baba su fito masallaci suganta Mansoor ne yace yanaga kina ta waige waige ne kamar mai duba wani abu , zara'u ne tace kaima kasan akoi matsala in su baba suka ganni da kai , daman nasan ba sona kikeyiba, ai cewar Mansoor,haba Mansoor yazakace haka kaima kasan ina bala'in sonka , zara'u kenan dakina sona ai bazaki bari araba mu ba , Mansoor wlh bawanda ya isa yarabani da kai, kuma kai ne mijina Insha Allahu wani irin dadi Mansoor yaji ganin yadda zara'u take mutuwar son shi ,toh yanzu sai yaushe zamusake haduwa kenan ,kinsan dai ban isa nazo kofar gidankuba tunda baba ya hana ,karka damu inkanason ganina sai ka fadawa Jamila in munje school saita fadamini kaga ba wanda zai gane muna haduwa da kai, Mansoor ne yace yauwa tawan kinkawo shawara me kyau yanzukam kiwuce gida sai da safe,
Zara'u ce ta juya zata tafi gida Mansoor ne yayi jaran murya juyawa tayi tace lafiya,uhm kinyi mantuwa ne, zare ido tayi tace mantuwan me kenan, dariya yayi yace gashi zo ki karba matsowa tayi kusa da machine din nasa , Mansoor ne yadan rankwafo kusa  da ita a hankali ya mannamata kiss tsigan jikinta ne yatashi da sauri ta matsa baya tace haba Nawan yanzu in su baba suka gammu fa dariya yayi yace kinga shikenan faduwa tazo dedai da zama sai baba ya hakura yasa adaura mana aure , dafe qirjinta tayi da hannunta tace rufamin asiri bakasan baba bane dariya yayi yace matsoraciya kawai, da sauri ta juya tana daga masa hannu tace yanzukam sai da safe , machine dinsa ya tayar yatafi. 
Idonta ne ya sauka akan baba da Yaya Aliyu dabatasanma yaushe yadawo garin ba suna tsaye abakin kofar gida da alama ita suke kallo wani irin Zillow kirjinta yayi da mugun qarfi addu'a takeyi acikin zuciyarta Allah dai yasa su baba basu gantaba kai da yau tashiga ukun ta tagama yawo, ahankali take tafiya kamar kazar da kwai yafashe mata aciki, karasowa tayi kamar me tsoron yin magana tace baba barka da warhaka baba ko kallon ta baiyiba yashige cikin gida , Yaya Aliyu ta kallah tace masa yaya barka da warhaka kadawo lafiya, baice mata uffan ba saima qara zuba mata mayun idanun sa dayayi, masu firgita mara gaskiya,
Jikin ta ne yadau rawa ganin yadda Yaya Aliyu ya zubamata ido  , juyawa yayi yabi bayan baba shima,
A tsakar gida yasamu baba yana tsaye , ya goya hannayensa a bayan sa sai zuwa da dawowa yakeyi maganar zuci yakeyi, shikam zara'u ce qaddarar sa amma insha Allahu yau zaiyiwa tufkar hanci, ace yarinya bata tsoron kowa ,Aliyu ne yazo zai gefta ta gefen baba ,ya wuce part dinsa baba ne yace Aliyu dawo inason magana da kai baice komaiba sai dawowa yayi yadan tsuguna agefen baba dayake tsaye,

Zara'u ce tashigo gidan sai wani rakubewa takeyi ajikin gini daganinta kasan ta shuka rashin gaskiya, baba ne yagaji da rakube rakubenta yace zaki karaso ne ko sai na takamiki wuya awajen, dasauri ta iso inda yake tsaye jekikiramin umman ku , wuce wa tayi dakin ummah dan isar da sakon baba.

Ba'afi minti biyuba saigata tadawo ita da ummah, malam lafiya kake kirana cewar ummah kenan, baba ne ya maida dubansa akan zara'u da ta sunkuyar da kai kai kace ta Allah ce,
Fadama umman ku me kikayi, cewar baba da idanunsa yake kan zara'u, shiru zara'u tayi , ummah ce tace mekikayi ne kam kinsa antasoni ina hutawa na, baba ne yayi gyaran murya yace tunda bazaki fada da bakinki ba bari ni na fada kuma ayau ayanzu zan yanke hukuncin da ya dace , inga wanda ya isa yajada zance na,
Babane ya shiga fadawa ummah abunda yafaru tundaga hawa machine din Mansoor har sumbatanta da Mansoor yayi mata, Aliyu ne yaqara sunkuyar da kan sa qasa , yana Wani irin runtse idanunsa, hannunsa na dama ya dunkule kamar mai shirin kai naushi, Allah ne kawai yasan halin da zuciyarsa take ciki, baisan ya akayi zara'u ta lalace haka ba , shidai ba haka yasantaba ,kuma yasan su baba suna qoqari akanta shima shaidane, a kan hakan, 
Baba ne yadaura da cewa tunda tanuna batajin magana kuma ban isa da ita ba toh daga yau bazata sake zuwa makaranta ba sannan nasaka ranar auren ta da dan uwan ta Aliyu nan da sati biyu masu zuwa, ba ummah da zara'u ba hatta Aliyu sanda yadago kai ya Kalli baba, dan zancen baba yazo masa abazata ne.
Ummah ce tace haba malam karkayanke hukunci cikin fishi mana, Zara'u yarinya ce yakamata kayimata uzuri zara'u ce ta fashe da kuka tace ni wlh bazan auri Yaya Aliyu ba ni Mansoor nake so shine ZABI NA baba ne ya kaiwa bakinta bugu , nan tashiga diddira kafar ta akasa ,tanacewa ni wlh sai dai akasheni Amma banason auren Yaya Aliyu, Aliyu ne ya zuba mata ido jin abunda take fada kai tsaye, shin yaushe zara'u tayi girman da zata dinga fadan irin wadannan maganganun,tsayawa tayi da borennata jin kaman ana kallon ta daga kanta tayi aikuwa da Aliyu ta hada ido ya zubamata mayun idanun sa maisa mutum yashiga hankalinsa, duk iskancin zara'u tana tsoron Yaya Aliyu duddah yana matuqar qaunarta tun tana yarinya har kawo yanzu komai shi yake mata amma hakan baisa yabari ta rainashiba, dan Aliyu irin mutanen nan ne dabasu cika shiga sabgar da bata shafesu ba, kullum fiskar nan tashi a daure tamau, dan bayason wargi,

Zara'u ne takoma bayan ummah ta buya ganin irin kallon da Aliyu yake mata tasan bazasu wanye lafiya ba dan ma baba yana wajen ne tasan da warhaka jikinta ya fadamata, ummah ce tace mata fito daga baya na kima daina buya Dan wlh indai ina raye ba wanda ya isa ya miki auren dole haka kawai ina gani acuceki, shi wanda yakeson hadaki dashi din wacce sana ah yake da shi in banda son zuciya irin na malam me aibun yaronnan Mansoor yana da aikin yi kikace har machine yake dashi ko, charaf zara'u ta chafke zance tace eyyi umman mu yanada machine roba roba kuma  aikin NEPA yakeyi (JET),
Baba ne ya girgiza kai yace wannan kuma ku tashafa koma dai mene ne nariga da nagama magana, aure ba fashi sati biyu insha Allahu,  ummah ce ta ce ai sai mugani intusa zata hura wuta jan zara'u tayi suka wuce daki sai mita taketayi.