Chapter 6
by @mrsalkali01
✨ZABI NA ✨
✍️~Mrs Alkali ~
🆓 Page 6️⃣
Baba ne ya maida kallon sa kan Aliyu dayake tsugune har yanzu bai motsaba, baba ne yace Aliyu kayi hakuri na yanke hukunci batare da na tuntubeka ba, Aliyu Dan Allah ina son ka auri kanwar ka zara'u, sunkuyar dakansa kasa yasake yi , baba ne yaci gaba da cewa bazan boye makaba Aliyu najima da yin wannan kudurin acikin zuciyata lokaci kawai nake jira saigashi zara'u ta dauko hanyar lalacewa agaban ido na da naso saita kammala karatunta na secondary kaima naso sai kaje law school kadawo sannan ayi maganar auren ku toh Amma naga hakan bazaiyiwu ba Zara'u batajin magana, Aliyu ina nema kamin wannan alfarmar ka auri zara'u nan da sati biyu masu zuwa inyaso bayan andaura muku aure zaka iya barinta anan katafi law school dinka tunda kace shekara daya zakuyi kaga itama sai taci gaba da karatunta, nima hankalina zaifi konciya in da igiyar auren ka akanta , nasan ko bayan raina zaka rikemin zara'u da amana ,
Ahankali Aliyu ya furta insha Allahu baba, baba ne yace nagode Aliyu Allah ya maka albarka ya jikan yaya Ibrahim, ameen ya furta akasan harshen sa, baba ne yace zaka iya tafiya, tashi yayi yanufi part dinsa, wani irin tafiya yakeyi cike da takama da izza kai kace wani jinin sarauta ne, kofan dakin ya tura shiga yayi , zama yayi abakin katifan sa ,harga Allah yana mugun son zara'u, Amma kuma agaban sa tace bata son shi , gashi bazai iya musawa baba maganar sa ba, tashi yayi ya dauro alwala, nafila yashiga yi don neman zabin Allah.
Zara'u ne zaune agaban ummah sai rusa uban kuka takeyi,tana jan hanci, ummah ce tace zakimin shiru ne ko sai natashi na lillisaki awajen , maimakon tayi shirun kamar yadda ummah tafada saima kara volume din kukanta tayi, tace ummah kinajin abunda baban mu yace ni zaiyiwa aure nan da sati biyu wlh sai dai akashe ni Amma nibazan auri Yaya Aliyu ba Mansoor ne ZABI NA, cikin sigan rarrashi ummah ta ce toh ya isa haka , ki kontar da hankalinki indai ina raye baki da miji sai Mansoor kinji ko , gyedawa ummah kanta tayi alamar taji, ummah ce tace tashi kiwanke fiskanki ,maza kizo kici abinci ,tashi tayi buta ta dauka tanufi bandaki.
Mansoor ne yaje gidan su Jamila yaro ya aika aka kirawo ta, fitowa tayi Mansoor tagani zaune akan machine din sa roba roba gaisawa sukayi, ya labarin kawarki ne , cewar Mansoor dayake tambayar Jamila,gaskiya yau kusan kwana biyu kenan ko makaranta bata je ba dama anjima zanje gidan su in duba ta ko lafiya, gaskiya kam yakamata ki dubomin ita, dariya Jamila tayi tace kaga masoyan asali, hannu yasa a aljihun wondon sa wata yar waya keypad yaciro kirar techno mikawa Jamila wayar yayi karba tayi tace wannan pha, kikaimata wayan kice injini taboye wayan zamudinga gaisawa,
Amma Mansoor gaskiya ina tsoro kasan babanta yahanata riqe waya, dariya yayi irin na wayaiyun yanduniya yace haba jamcy karki bani kunya mana ,wayar ce bazaki iya bata ba , to ai kar agannine na ke tsoro haba kema ya za ayi kibata agaban wani ai boyewa zakiyi ,toh shikenan, tunda kana tare da machine sai kamin left kawai, baki da matsala, hawa machine din Mansoor Jamila tayi ,
Dake banisa sosai anguwan na sun tafiyan minti 5 ya kawosu anguwan su zara'u daga nesa da gidan Mansoor ya tsaya Jamila ce tace yazaka tsaidani anan wannan ai wulaqanci ne, Mansoor ne yace akoi matsala ne in baban ta yaganni, kedai sauka anan kawai kya karasa da kafa ,sauka Jamila tayi,tanufi kofar gidan su zara'u ,
Zara'u ne take taya ummah girki tankaden garin tuwo take mata, Jamila ce tayi sallama da sauri zara'u ta dago kanta jin kamar muryan qawar ta Jamila, wani irin rugowa zara'u tayi ,dagudu ta rungumi jamila, me yahanaki zuwa makaranta kwana biyu cewar Jamila, zara'u ce tasaketa ,sanda ta waiga taga ba kowa a tsakar gidan tace kedai bari kawai akoe damuwa mushiga daga ciki zakiji komai ,dakin ummah suka wuce ,
Ummah ce zaune akan sallayarta ta idar da sallan la'asar tana lazumi ,su zara'u ne sukashigo, Jamila ce ta gaida ummah amsawa tayi tare da nade sallayarta hijabinta ta tacire, kallon zara'u tayi tace kingama tankaden ne , aa ummah ai nasan za'a rina dole kubarmin aikina tunda kinsamu qawar ki, ummah ce tafita tana dan mitan ta kitchen tanufa dan karasa aikin.