Zaɓi na

Chapter 7

by @mrsalkali01

✨ZABI NA ✨ 

✍️~Mrs Alkali ~


🆓 Page 7️⃣







Jamila ce ta kallah zara'u tace ke meyake faruwane nazaci bakida lafiya shiyasa ba kya zuwa makaranta kwana biyunnan, ajiyar zuciya zara'u tasauke tace kedai bari jamcy, baba ne ya hana wai aure zaimin , Jamila ce tazaro idanunta waje hannunta tadafe a kirjinta tace nashiga uku aure kuma zara'u, to wa zaki aura kinsan yanda Mansoor yadamu kuwa, idanun zara'u ne suka cika da hawaye jin Jamila ta ambaci sunan Mansoor dinta, Allah sarki masoyina nima na damu dashi wlh Jamila ce tace bani labari ya akayi, nan zara'u ta shiga labarta mata yadda baba yace , 
Toh ke zara'u ki yadda da zabin baba mana kinsan Allah Yaya Aliyu yahadu ,tsaki zara'u tayi tace wlh zamu bata dake ina da Mansoor mezanyi da wani Yaya Aliyu mutum sai bakin hali ,ga shegen takama da izza sai kace wani jinin sarauta,ai wlh da Yaya Aliyu me kudi ne da anshiga uku, Jamila ce tayi murmushi tace nikam wlh burgeni yakeyi da zaki hadani da shi da kingamamin komai, hmmm Jamila sai kace bakiji me nace miki ba , nan da sati biyu pha baba yace zai auramin shi kuma wlh sai dai akaimasa gawata ,ni nafara tunanin guduwa ma wlh Jamila ce tayi murmushi tace haba zara'u kigudu kije ina ,
Indai zaki hadani da Yaya Aliyu namiki alkawarin zankaiki inda za a sharemiki kukanki, zara'u ce ta matso kusa da Jamila sosai kamar wacce batason aji maganar tace bangane me kike nufiba Jamila, dariya tayi tace indai kinmin alkawarin zaki hadani da Yaya Aliyu to zanyi kokari afasa auren ki dashi kinga sai kije ki auri Mansoor dinki, wani irin runguma zara'u tayiwa Jamila tace Allah da gaske kikeyi , nataba miki irin wannan wasanne zara'u, akoi wani malam mai almajirai da nake raka mamana wajensa yana mata addu'a kuma wlh mama tace addu'a n sa kamar yankan wuka, ke bakiga yadda nake da farin jini bane , ai awajen sa mama ta karbamini maganin farin jini, zara'u ce tace shegiyar ashe shiyasa kika cin kudin samari yadda kike so, aini Jamila indai zaki cikamin alkawarinnan toh wlh kingamamin komai Yaya Aliyu kuma kaman kin aureshi kingama dariyar jin dadi Jamila tayi, dan ita har ga Allah tajima tana son Aliyu, yaza'ayi tabari zara'u ta aure sa ai ko zatayi yawo tsirara sai tasan hanyan da zatabi ta rabasu batare da zara'un ta ankaraba, don dai zara'un ma son Mansoor ya makantar da ita ne shiyasa tace bata son Aliyu, Amma ina za a hada Aliyu da Mansoor sai dai ance so Makahone, dan ya makantar da zara'u kam.
Zara'u ce tace toh ai ni banida kudin dazamu kaiwa malam na sadaka ko dai ummah zantambaya, karki damu zanbada abun sadakan ai kinfi karfin haka awaje na wani irin dadi zara'u taji ganin yadda Jamila ta ke sonta, 
Jamila ce tadan waiga takallah kofa ganin ba kowa  awajen yasa ta saka hannunta acikin hijabinta wayar da Mansoor yabata taciro mikawa zara'u tayi, zara'u ce ta kalleta tace wannan kuma fa , Mansoor ne yace inbaki zakuna waya dashi dan ya damu sosai kwana biyu da bai gankiba, karban wayar tayi ta rungume a kirjinta , Allah sarki Mansoor dina ashe yana mugun so na haka , Jamila ce ta daka mata duka a baya tace kisa wayar a silent sannan kina boyeta dan wlh in baba ya sanda wayannan kashimmu ya bushe daga ni har ke, ajiyar zuciya zara'u tasauke daukan wayan tayi ta tusa shi a kunkuminta inda daurin  zaninta yariqeshi tamau yadda bazai fadiba , Jamila ce tace yanzu to ya za ayi kifita kinsan yakamata muje wajen malaminnan da wuri kar lokaci ya qure tunda kince nan da  sati biyu baba ya ce za ayi bikin , shiru zara'u tayi alamar tana dan tunani, chan tace karki damu zuwa jibi zan lallabi ummah in baba yatafi kasuwa sai nazo, jamila ce ta jinjina mata kai alamar ta gamsu da bayaninta tashi tayi zata tafi zara'u ce tace toh muje in rakaki,saura ki fadawa ummah cewar Jamila datake shirin fita daga dakin zara'u ce ta ce haba bawanda zan fadawa, 

Ummah ce a tsakar gidan tana kwashe tuwo a kula Jamila ce tace ummah natafi , ummah ce tace aa Jamila muna kwashe tuwo kice zaki tafi ,kitsaya kici mana ,aa ummah nagode zantafi kar nayi dare a hanya in rasa abun hawa, to ki gaidamin da mamanki zataji cewar Jamila,tana kokarin fita kofar gidan , zara'u ce take biye da ita abaya tana mata rakiya,
Aliyu ne zaune a kofar gidan a kan dakalin da akayi a kofar wayarsa yake dannawa yaji alamar an fito daga cikin gidan bai dago da kansa ba amma kuma yana kallon su ta kasan ido, zara'u dasuka fito daga cikin gidan, wani irin bugawa zuciyar Jamila tayi ganin Aliyu a zaune agabanta batare da tayi tsammanin ganinsa ba, hannunta tasa a fiskar ta tana dan gogewa , chanza salon tafiyarta tayi , tawani maqe muryarta harda dan rusunawarta tace Yayanmu inayini, duk abunda Jamila tayi akan idanu Aliyu shi abunma dariya ya bashi , Amma ko a fiska bazaka ce yasan da su awajen ba jin shirun yayi yawane yasa Jamila satan kallon shi, wani irin Zillow zuciyar ta tashiga yi numfashinta kamar zai dauke , Masha Allah, wannan saikace wani aljanin balarabe taya ma za ayi inbar zara'u ta aure sa ai wlh sai dai muyi biyu babu dagani har ita , ni dazansamu ya aure ni ai ko bazaina kulani ba bazandamuba indai zandinga ganinsa kullum, Jamila ce take ta wannan zancen acikin zuciyar ganin bayi daniyan amsawa ne yasa zara'u ta dan bugi Jamila ganin tayi nisa cikin tunani, firgit tayi jin an daka mata duka,  zara'u ce tafarayin gaba ganin haka yasa Jamila bin bayanta sum sum , dan ita ko kwana zata yi anan wajen bazata gaji da kallon Aliyu ba, zara'u ce ta dan tsaya Jamila ce tace ya kika tsaya anan ko rakiyar ta isa haka ,  hmm Jamila kenan kin manta baba yace kar inkara fita yanzunma dakikaga ummah tabarni dan ke ne , Jamila ce tace nikam zara'u Yaya Aliyu kam anya bai hada jini da larabawa ba kiganshi sai kace ba dan Nigeria ba , zara'u ce ta tabe baki tace uhmm kedai narasa me kika gani ajikin Yaya Aliyu kika haukace haka kina ganin mutum sai kace wani nunan rana ni pha wlh banaganin kyawunsa Mansoor yafishi kyau nesa ba kusaba,kuma kinsan ance fararen mazannan basu cika tabuka komai agado ba dariya Jamila tayi tace chap lallaekam bakisan menene kyauba , ke bakiga yanda yake  kama da larabawan da muke gani a cikin  TV ba, zara'u ce tace ai ummah tace maman sa yar gudun hijira ce kuma buzuwa ce kinsan buzaye da shegen kyau bare kuma ya hadu da jinin fulani , fadane ya barke a chan qasar tasu shine pha su kayi gudun hijira har Allah ya kawo su Nigeria toh anan baba Ibrahim yaganta ya aure ta shiyasa zakiga yaya Aliyu kamar ba dan Nigeria ba,
Haba ai biri yayi kama da mutum cewar Jamila, zara'u ce tace zankoma cikin gida kada baba yazo yasame ni awaje kinsan yakusa dawowa, toh shikenan sai da safe karki manta da magananmu  pha, cewar Jamila da ta ke tafiya don tsaida abun hawa,