Zaɓi na

Chapter 8

by @mrsalkali01

✨ZABI NA ✨ 

✍️~Mrs Alkali ~


🆓 Page 8️⃣






Duk abunda su zara'u suke fada ita da qawar ta Jamila Aliyu yana jin su , zara'u ce tazo zata shige cikin gida ba zato taji saukan zazzakar  muryarsa cikin izza da daki ya, yace ke zonan juyowa tayi tazo ta tsaya a gaban sa baisake ce mata uffan ba yaci gaba da danna wayarsa, tun zara'u na tseye da dadin rai har kafafun ta sukafara rawa tsabaragen ta gaji gashi ko giyar wake tasha bata isa ta tafiba , gajiya tayi da ysayuwan , tace Yaya Aliyu gani , nanma shiru yayi, yakusan minti biyar kafin yadago kansa wadannan mayun idanunnasan ya zuba mata su  zara'u ne ta sunkuyar da kanta kasa dan duk iskancin ta da sakalcin ta tana shakkar yiwa Aliyu sabida baya wargi ga idanunsa masu ladabtar da mara kunya inyana kallon ka dasu,
Har tacire tsammanin , zaiyi mata magana, taji saukar muryansa , wace ce wacchan yarinyar, ko bai fadaba tasan Jamila yake nufi , don haka ne yasata cemasa qawata ce ,
Akaron farko ya maida wayarsa aljihun gaban rigan sa batare da ya kalleta ba yace wato ita ce me  koyamiki rashin kunya da fitsara ko, toh kar in kuskura insake ganin kafarta agidannan ,wuce kibani waje, zara'u ce ta wuce cikin gida tana qunquni sai kumbure kumbure takeyi ta tura bakinnan gaba kai kace dukanta yayi,
Ko sallama batayiba tana shiga cikin gidan gun da ummah take zune tanufa tare da fara murza idanunta tana diddirka kafafun ta akasa ummah ce tace meyafaru kuma auta, me yasameki waya taba minke zara'u ce tace ba Yaya Aliyu ba ne yace kar Jamila tasake zuwa gidannan wai inyasake ganinta saiyamana duka nida ita , ummah ce tafara salati tare da tafa hannayenta tace ni Hadiza da wanne zakiji to bayan malam ya hanaki zuwa makarantar ma hakan bai ishesu ba shine zaice kar qawar ki tasake zuwa gidannan nan tsabaragen samun waje, ehhh lallaekam ko da yake ba laifinsa bane laifin malam ne dayake daure masa gindi ,Share hawayenki bari malam din yadawo , zai zo yasameni.

Da dere misalin qarfe 8 00pm malam ne zaune akan tabarmar sa a tsakar gidan yana kishingide kansa akan pillow radion sa ne a hannunsa yana sauraran labaran BBC muryan amurka, Aliyu ne yashigo bakinsa dauke da sallama Ibrahim ne a bayansa, malam ne ya amsa sallamar tasu tare da tashi ya zauna, Aliyu ne yazauna agan baba tare da tonkwashe kafafunsa , Ibrahim kuma gefen baba yazauna tare da daukar radion baba yana qoqarin kasheta baba ne yace ingo naka Ibrahim haka nace maka kazo kasameni inajin abuna kace zaka kashe , Ibrahim ne ya shafa kansa yace , Yaya Aliyu ne yazo maka da labari mai dadi, baba ne ya washe bakinsa yace Masha Allahu,
Gadanga me muka samune ai tunda naga kunshigo tare nasan akoi wani abu, Aliyu ne yasake jara zaman sa , hannu yasa cikin aljihun sa wayan sa yaciro budeta yayi ya mikawa baba , babane yakarba hoton wata takadda yagani baigane komai ba ajikin takardan, ingo karba wayan ka kasan bawani ganewa zanyi ba wannan abunku na yan bokon imin bayani kawai, murmushi Aliyu yayi jin abunda baba yace, sake gyara zamansa  yayi, yace,
Dama na samu admission ne a Nigerian Law School kano (Bagauda Campus), Allah ya nufa sunana yafito achan, cewar Aliyu, dayake yiwa baba bayani ,Masha Allah yanzu sai shirin tafiya kenan ko cewar baba, zuwa yaushe ne tafiyar taka , nan da sati uku ne , Masha Allahu kaga faduwa tazo dedai da zama bayan daurin auren ku sai katafi tunda kace shekara daya ne makarantar,kaga itama zara'u sai ta qarasa tata makarantar kafin kadawo sai ayi maganar tariyar, bikin naku.
Sake sunkuyar da kai Aliyu yayi, a hankali yace Allah ya kaimu baba ne yace ameen, Allah yamuku albarka, tashi yayi yace sai da safe baba , Allah ya kaimu 
Part dinsa ya wuce Ibrahim ne ya kalli baba yace wlh baba sai naga kamar Yaya Aliyu basu dace da zara'u ba haba ai inni ne nake da kyau irin na yaya Aliyu wlh bazan auri yar Nigeria ba ma ,sai dai in auro yar India, baba ne ya ce ingo naka Ibrahima tashi kaban waje da wannan shegen shirmennaka, yo da zara'u da Aliyu ai duk cikin su daya kaga bawanda ya isa ya guji dan uwan sa ,ita ma zara'u n shirme takeyi Amma nasan dazaran anyi auren zata natsu nasan gadanga zai saita ta, Ibrahim ne yayi dariya yace chap wayaga , Yaya Aliyu ya auri zara'u aikuwa zai sha shirme, tashi yayi yace barin dubo ummah cewar Ibrahim daya nufi qofar dakin ummah,
Ummah ne zaune akan sofa zara'u ce konce akan cinyan ummah tana shafa mata kitson ta Ibrahim ne ya harareta yace wlh ummah ke kike qara sakalta yarinyar nan, dubi yadda ta haumiki qafa sai kace wata jinjira, aa Ibrahim barmin auta ta tahuta da wanne zataji nekam duk kunsakota gaba agidannan, zara'u ce ta turo bakinta gaba , hannu Ibrahim yasa zai buge bakin ummah ce ta rikemasa hannu tace kul karkafara wlh, toh ma ina ruwanka da ita, hararan zara'u yayi yace zakigane ai bari ki auri Yaya Aliyu wlh sai ya saitamana ke , zakigane bakida wayo , zara'u ce tafashe da kuka tace ummah kinga Yaya Ibrahim ko , ni wlh bazan auri Yaya Aliyu ba sai dai akasheni ni Mansoor ne ZABI NA, Ibrahim ne ya ce dallah rufewa mutane baki ke inbanda ma baba ne yahada auren nan ke kin isa kimatso kusa da yaya Aliyu ai ko me wanke wanken gidan sa baki kai ba, harkina batun ke bakya son shi, har kina hadashi da wani wai shi Mansoor, to wayagayamiki kedin ZABIN Yaya Aliyu ne shima biyaiya ce kawai inba haka ba ke kin isa ne ,
Dallah rufemin baki saikace Aliyu n ubankane sai wani godashi kakeyi ,sai kace shine autan maza , ai duk namijin da bashida kudi ai shida banza duk dayane wayake maganar wani kyau , ai kudi sune rayuwa shi Aliyun me yake dashi, cewar ummah data dage tana zazzaga wa Ibrahim masifa,  Ibrahim ne yabata rai yace haba ummah wacce irin magana ne , to ubana dake ni nace tunda antaba dan gwal, ma ubanme kazo mini adaki a wannan daren , wuce kaban waje, in ji ummah data nunawa Ibrahim hanyar fita daga parlourn,juyawa Ibrahim yayi yafita ransa amatuka