Chapter 10
by @mrsalkali01
✨ZABI NA ✨
✍️~Mrs Alkali ~
🆓 Page 1️⃣0️⃣
Jamila da zara'u ne zaune agaban malam, fiskar sa duk acike take da gashi gawani kasumba buzu buzu bakinshi cike da jan goro ga wani uban charbi rike a hannunsa sai ja yakeyi ,almajirai ne ta ko ina wasu suna ta karatu wasukuma rubutu su keyi, wasu na dinka laya.
Kallon Jamila yayi yace ke Yarinya ya maman taki , lafiyanta kalau inji Jamila, toh abu yayi kyau aikoki tayine , aa malam kawata na rako, malam ne ya kalli zara'u yace meke tafe da ke, nan zara'u tashiga labaryamasa yadda su kayi da baba kuma yasha alwashin aurenta da yaya Aliyu ba fashi, malam ne ya jefa katon charbinsa akasa zara'u ya kallah yace maza dau daya ki mikamini, hannu tasa ta dauko guda daya mikawa malam tayi karba yayi ,bakinsa sai motsi yakeyi amma bakajin me yake fada da alama wani abu yake karantawa, bayan yagamane ya daga kansa ya kalle su,
Yace babanki yana da taurin kai sosai shikuma Aliyu taurarin sa masu karfi ne dole sai dai ayiwa babanki aikin da zaisa shi yafasa auramiki Aliyu da kansa, wani irin dadi zara'u taji tace toh malam yanzu ya za'ayi, malam ne yagama yan dube duben sa yace to pha aikinnan naki yana bukatar sadaka sai anzubda jini, ana bukatar bakin taure, kallon Jamila zara'u tayi, ita ina taga dubu dayama bare harwani kudin bakin taure,
Jamila ce ta ce malam bari mudanyi magana awaje, fita sukayi barandar dakin , zara'u ce tace yanzu Jamila ya zamuyi ina mukaga kudin dazamu bayar asayi bakin taurennan, nida bana maganin sisi ,jamilace tace kinsan me za'ayi kikiramana Mansoor tunda dai danshi za ayi abunnan yazo kawai yakawo kudin aikin ko ya kikagani, jinjina kai zara'u tayi,
Yar wayar ta taciro a kunkuminta Kiran Mansoor tashiga yi ringing daya yadauka nan tafada masa halin da ake ciki, kwatancen gidan yatambayeta , Jamila tamikawa wayan nan tamasa ko tancen gidan malam din,
Basufi minti 5 ba saiga Mansoor yaqaraso nan yake tambayar Jamila ta tabbatar aikin malam yana ci , ina , Jamila ce tabasa tabbaci akan kar yadamu indai malam yayi aiki kamar yankan wuka ne, nan ya dau dubu goma yabasu ,haka suka sake shiga turakan malam din shikuma yazauna yana jiran fitowar su,
Bayan sunbawa malam dubu goma ne yace musu kar su damu yau zaifara musu aiki su dai sujira sugani godiya suka masa haka suka tashi suka fito waje , Mansoor ne yace zara'u ta hau machine ya kaita gida, haka sukayi sallama da jamila ta wuce gidansu itakuma zara'u tahau machine din Mansoor suka wuce.
Tunda sukaje wajen malam Mansoor da zara'u suke ta shiryen bikin su atsakanin su, don Jamila taqara tabbatar musu dacewa su kwantar da hankalinsu aikin malam kamar yankan wuqa, jin hakanne yasa zara'u tasaki jikinta kamar ba abunda yake damunta ganin hakanne yasa ummah ma ta kwantar da hankalinta tana tunanin zara'u ta hakurane da batun auren ta da Yaya Aliyu dama ita damuwarta kar ayiwa yarta auren Dole ,
A bangaren Aliyu shima yanata shirye shiryen tafiya Law School dinsa don bayan auren sa da sati daya ne tafiyar agefe guda kuma baba ne yaketa yan gyare gyarensa, ya gyarawa Aliyu bangaren sa anyi sabon fenti inda amarya zata zauna kafin Aliyu ya dawo daga makaranta, dan shine uban amarya kuma uban ango, bikin nasa ne.
Shin kuna ganin asiri zai kama baba kuwa..?
Shin za ayi auren Zara'u da Aliyu..?
Dawa zara'u ta dace Aliyu ne ko kuma Mansoor
Shin zabin zara'u alkhairii ne agareta..?
Shin waye ne Aliyu kam.?
Shin Aliyu yana son zara'u ne kokuma auren biyaiya, zai yi ne
Shin Jamila qawar arziki ce.?
Abunda ummah take yi akan zara'u dedai ne ..?
Jamila tana samun cikan burinta na mallakan zuciyar Aliyu..?
Da gaske aikin malam kamar yankan wuka ne?
Shin da gaske Mansoor yake son zara'u?