Zaɓi na

Chapter 11

by @mrsalkali01




✨ZABI NA ✨ 
✍️~Mrs Alkali ~

🆓 Page 1️⃣1️⃣






Rana bata karya saidai uwar diya taji kunya a yau jumma'a ne za a daura auren zara'u da Aliyu bayan sallan jumma'a a babbar masallacin unguwar su,
Zara'u ce zaune akan katifarta sai dirzan kuka takeyi Jamila ce zaune a gefen ta tana ta bata hakuri, haba zara'u karki damu insha Allahu baza a daura auren nan ba nina fadamiki ,don bakisan aikin malam ba ne tunda yace ba za ayi auren nan ba Dan Allah ki kontar da hankalinki,
Zara'u ce ta dago kanta dayake kife a kan cinyar ta fuskar nan tata duk hawaye, sai jan majina takeyi,
Kallon Jamila tayi tace haba Jamila kinaganin anjima za a daura auren kice na kontar da hankalina da nazaci aikin malam zai sa baba ya fasa auramin Yaya Aliyu Amma kingani shiru har yanzu, kina ganin satin chan Mansoor ya turo iyayen sa Amma baba yaki amince musu , yace aure na da yaya Aliyu ba fashi,
Ni wlh akan na auri yaya aliyu gara in gudu, Jamila ce taja wani dogon tsaki tace haba zara'u nace miki ki kontar da hankalinki ai dasauran lokaci, cigaba da rusa  kuka zara'u tayi Jamila ce tadau wayan zara'u Mansoor ta kira , hello beb ykk ,cewar Mansoor daya daga wayar, Mansoor ba itabace jamcy ce , ina ita zara'u n gatanan sai kuka takeyi taki tayi shiru , bata wayan , mikawa zara'u wayan tayi karba tayi tasa a kunnenta, haba tawan ya zakina mini asarar hawayenki, yakamata ki adanamin su sai ankawoki gidana , anjima , Zara'u ce taja ajiyar zuciya tace Mansoor na karaya kanaganin baba yana kan bakansa anjima za a daura min aure da yaya Aliyu, shine kakecewa kar na damu anya kana sona kuwa,
Mansoor ne yayi dan murmushi yace haba tawan kema kinsan ina mugun son ki inkinga ban aureki ba sai dai in mutuwa nayi, kar ki damu akoi shirin dana ke mana wani irin ajiyan zuciya zara'u tasauke tace toh shikenan Allah ya sa , ameen ya ce , kashe wayan yayi abunsa.

Misalin qarfe 2:30pm bayan an idar da sallan jumma'a daurin aure akafarayi babane zaune agefe sanye da babbar riga yasha hula akansa , kallo daya zakamasa kagane yana cikin wani yanayi kaikace bashine uban amaryar ba, gefensa kuma Aliyu ne zaune shida Ibrahim, sanye yake da farar jamfa da bakar hula wacce yayiwa kari biyu , sai sheki yakeyi kana ganinsa kaga ango, don yasha kyau iya kyau, Ibrahim ma jamfa yasaka sai dai shi tashi milk color ce,
Sanda aka daura auren mutum 5 kafin aka shiga kiran waliyan ango da amarya wanda za a daura su ne na 6 , lasfikar masallacin ne yadauki muryan me shelan inda yake ambatan sunan malam Amadu Kalam amatsayin waliyin amarya, nan baba yatashi jikinsa ba wani karfi yanufi inda ake kiransa ko inda Aliyu yake yaki ya kallah mai shelan ne yasake cewa ananeman alhaji jauro waliyin ango da ya matso gaba domin nemawa dansa aure, nan wani alhaji dan dottijo da shi , kallo daya zaka masa kasan yahada jini da Mansoor,haka ,ya matsa wajen su baba ,
Waliyin ango ne ya nemawa Ango auren Amarya, baba ne yace ya bayar ya amince,Nan danan aka shafa fatiha aure ya dauru tsakanin fatima Ahmadu kalam(zara'u )da Mansoor alhaji jauro, nan akashiga rabon minti da goro, baba ne yake ta gaisawa da jama'a sai barka akemasa , da kyar yasamu ya zame , acikin mutanen inda su Aliyu suke zaune ya nufo , ahankali baba ya riqe hannun Aliyu hanyar fita daga masallacin yanufa da shi batare da yamasa maganaba haka Aliyu yabi bayan baba batare da yace masa uffan ba don jikinsa yariga da yayi sanyi, shikenan zara'u tazama matar wani , Ibrahim ne ya take musu baya, don shi harga Allah baiji haushin yanda aurennan ya chanzaba, murna yakeyi da faruwar hakan.
Bayan sun danyi tafiya mai nisa baba ne yasaki hannun Aliyu juyowa yayi ahankali ya kira sunan sa baba ne yafara magana cikin sanyin jiki, Aliyu kagafarceni nasan ban kyautamakaba , amma ni kaina bansan me yasa na amince da wannan auren ba bayan alhaji jauro yazo nemawa dan sa Mansoor auren Zara'u ne wanchan satin, nanuna musu nayiwa zara'u miji haka sukabani hakuri suka tafi, ban san me yasameniba haka kawai nakejin auren ka da ita yafita a raina na kasa fadawa kowa , kwasam yau da safe saiga alhaji jauro yasake dawowa wajena  ya na roqona akan aduba lamarin yarannan tunda suna son junan su, kar su shiga wani hali, ganin yanda ya damu ne yasani cemasa in har da gaske sukeyi sun shirya , to yau suzo masallacin jumma'a a daura musu aure, haka mukayi sallama dashi ya tafi aganina suntafi kenan bazasu kara dawowaba, kwasam dazu saiga alhaji jauro da tawagarsa a masallaci, banason su maidani karamin mutum  tunda ga alkawarin da na masa , shiyasa nace nabasu auren Zara'u,
Kayi hakuri Aliyu, Allah ya sa zara'u ba matar ka bace , 
Allah ya sa hakan shi yafi alkhairii, Aliyu ne ya amsa da ameen, cigaba da tafiya sukayi shida baba ba mecewa uffan kowa da abunda zuciyarsa take saka masa, bazaka iya tantance yanayin da Aliyu yake cikiba, 
Haka suka qaraso gidan cike yake da baki sai hidimar biki aketayi Aliyu ne yafara shiga gidan nan abokan wasan shi suka fara tsokanansa suna cewa ga ango ga ango , ango yasha kamshi murmushin da bai isa zuciyaba yayi musu da kyar yasamu suka barshi yawuce part dinsa, don shikadai yasan halin da zuciyarsa take ciki.
Jin irin hayaniyar da akeyi ne ancewa ango yasha kamshi yasa zara'u kara fashewa da kuka tace nashiga uku Jamila shikenan tafaru ta kare ,an daura aurena da Yaya Aliyu,wayyo Allah na wlh piyapiya zansha in mutu ,inyaso akaimasa gawata shikenan kowa ya huta.