Chapter 12
by @mrsalkali01
✨ZABI NA ✨
✍️~Mrs Alkali ~
🆓 Page 1️⃣2️⃣
Zuciyar Jamila ce ta buga da karfi jin abunda zara'u take fada , zuciyar ta ne tashiga mata lugude, ita ba wai Shan piyapiya da zara'u zatayibane ya dameta, ba , jin cewa andaura auren Zara'u da Aliyu shine ya daga mata hankali, wani irin gumine ya karyomata, kallon zara'u tayi tace indai dagaske andaura auren nan wlh gara kisha piyapiyan ,ai inkin mutu kin huta da wannan bakin cikin , ka auri wanda kakeso ma ya kakare bare kuma wanda baka so, wani irin zabura zara'u tayi jin abinda Jamila tace mata faduwa tayi a kasa ta hau birgima, tana ta shure shure , saika ce mai tashin aljanu.
Ummah ce tashigo tace me haka kikeyi zara'u, tun daga daki na nakejin ihun ki, to inkingama sheganta kar taki sai kizo baban ku na kiranki,
Ummah ce tawuce tafita don itama tana cike da haushin wannan qaddarerren auren, inbanda baba da shegen naci me Aliyu yake dashi yaushe zai iya rike zara'u, dayanace sanda aka daura auren, wani irin kwafa ummah taja.
Haka ta karasa parlour tazauna agefen kujeran da baba yake zaune, ta hade fiskarta sosai kamar wacce akayiwa sakon mutuwa ,suna zaman jiran zara'u.
Zara'u ce tashigo dakin Jamila na rike da ita sai sheshsheqan kuka takeyi fiskar nan tata tayi jajur sabida kukan da tasha,
A kasan carpet din dakin tazauna Jamila ce tazauna a gefenta, baba ne ya kalli ummah yace alhmdullah kamar yadda kikasani ayau andaurawa Zara'u aure, a yanzu bata qarqashin kulawarmu, sai dai ina son in sanar daku cewa bada Aliyu aka daura auren ba kamar yadda tace Mansoor ne ZABIN ta to Allah ya nufa shine mijin ta ba Aliyu ba , sai dai inason kusa ni duk wani abu dazaije ya dawo ni Amadu ba hannu na acikinshi, tunda ZABIN ta ne sai tayi hakuri da duk wani abu da zai faru , tunda tace taji ta gani ,dama shi zaman aure zo muzauna zo musaba, sai anyi hakuri dajunah.
Duk wannan bayani da baba yake korowa, zara'u ba fahimtar shi takeyi ba sai dai kunnentane yajiyomata baba yace ba Aliyu ta aura ba ,wani wawan ajiyan zuciya suka sauqe tare da kawarta Jamila, tashi tayi da gudu ta fada jikin ummah dariya ta shiga yi mai hade da kuka kai kace ba ita bane take ta dirzan kuka tun da safe ba tace ummah dagaske ne ba Yaya Aliyu aka auramin ba , ummah ce tace ja'irar yarinya kawai tashi akaina karki ballani , tashi tayi tana cewa baba na gode insha Allahu bawini sabani da zaishiga tsakanina da Mansoor sabida shine ZABI NA kuma yana sona sosai , baba ne ya girgiza kai shi jikinsa ma duk yayi sanyi, gani yakeyi bai kyauta wa Aliyu ba ,tashi yayi yanufi kofar fita daga parlourn ,jamila ce ta ce eyyeh kaga amaryar Mansoor, ai sai ki wuce muje mufara shirye shiryen kai amarya, dama nafadamiki , Mansoor ne mijin ki, wani farrrr zara'u tayi da idanunta tace hmm yau kwana saigidan Mansoor dinah,
Ummah ce tafara salati tare da tafa hannayenta tace ni Hadiza yau inaganin rasarkunya agurin ya'yannan zara'u ce tafita dagudu tana rufe fiskanta da hannayenta ,
Da yamma saiga motocin daukan amarya haka akafito da amarya Zara'u taci kwarass abunta saikace ba itace take ta bore dazu ba , ayanzu da za akaita gidan mijin ta ko hawayen rabuwa da iyayenta batayiba, don tace kukan me zanyi bayan ZABI NA na aura , haka a ka sada amarya da gidanta dayake anguwar tudun wada, ba laifi gidan su Mansoor yana da dan kyau dan mahaifinsa dan kasuwa ne ,acikin gidan su zai ajiye zara'u wato family house dinsu aciki ne alhaji jauro ya gyaramasa ciki da falo da bandaki sai dan baranda da dan kitchen dinsa agefe, a daya bangaren kuwa hajiya Mama ce mahaifiyar Mansoor, take zaune a dakunan.
Ankai amarya an watse anbar amarya da angonta, sai dai mumusu fatan alkhairii.
Aliyu ne zaune agaban baba yace baba inaga yakamata intafi campus gobe sabida akoi takaddin dazan cika achan sannan akoi shirye shiryen da zan karasa in na je chan , baba ne ya sunkuyar da kai gani yakeyi sabida abunda yafaru ne yasa Aliyu yakeson tafiya tun kafin lokacin tafiyan yayi, gadanga ina mai kara baka hakuri akan wannan abu da yafaru komai kagani muqaddari ne daga Allah wani baya auren matar wani, kayi hakuri kaji ko,
Bakomae baba kawai dai ina son injene kafin lokacin kaga akoi abubuwan daya kamata nayisu, to shikenan tunda ka matsa yanzu yaushe ne tafiyar taka,
Gobe da safe insha Allahu to Masha Allahu, Allah ya kaimu goben ameen baba cewar Aliyu, ummah ce tace saikace wani zunubin ka aikata malam kabi ka damu kanka , akanshi akafara fasa aure ne dama chan Zara'u ba tsarar sa bace, baba ne ya girgiza kai dan ba zai biyemataba su raba hali ba tunda wanda akeyi akanta tanachan gidan mijin ta aikingama ya gama ,
Aliyu ne yatashi jin abunda ummah take fada inda sabo ya riga da yasaba da wannan halin nata tun yana yaro yasan ummah akoi yawan fada musamman akansa , kullum gani takeyi baba yafi sonshi akan su Ibrahim da zara'u da ya haifa acikin sa, shiyasa take yawan fada akan sa.
Barin je incigaba da shiri cewar Aliyu baba ne yace to Allah ya taimaka, ummah ce tayi charaf tace nidai naga randa wannan qaddarerren makarantar zata qare ace shekara da shekaru bata kareba, yanzu ma ana tunanin takare gashi ka tsiro da wani abu wai shi law school ne kome ne ma dai ohoo , kai baka tsaya kayi sana ah ba bare ka tai make mu ,sai ma kudin da ake kashemaka wai dasunan karatu, babane yace Hadiza bana son irin wannan abunda kikeyi , in Ibrahim ne zakifadamasa hakane ,kuma kisani da Aliyu da Ibrahim duk daya ne awajena kwafa tayi tawuce daki.
Yanzu ne wasan zaifara, kubiyo ni don jin yanda labarin zai kasan ce.
In kuna son update anjima, to kuyi comment, da like, insha Allah, ni kuma zanyi kokari anjima, zakuga update.