Chapter 13
by @mrsalkali01
✨ZABI NA ✨
✍️~Mrs Alkali ~
🆓 Page 1️⃣3️⃣
Washe gari da safe Aliyu ne yafito dauke da jakansa rataye akafadansa sanye yake da farar t-shirt da bakin wondo na jogger kafansa sanye cikin snickers bakake ya daura bakin p-cap akayinsa, bakin sajennan nasa ya kwanta yayi luf luf akan fuskarshi , inkaganshi zakace bayajin Hausa a bakinsa ko kadan,
Dakin ummah ya nufa sallama yayi baba ne dake shan kunu ya amsa masa , shigo mana gadanga saikace wani bako, Aliyu ne yashigo sai dai ya cire p-cap din kansa tsuguna wa yayi ya gaida baba, amsawa yayi tare dacewa badai har angama shirin ba, dan sosa kansa yayi yace ehhh baba tunda bansan wajenba nace gara intafi da wuri kuma naga wajen akoi dan rata,
Baba ne yace ehhh kaima kayi gaskiya baba ne yasa hannu a aljihun wondon sa kudi yaciro dubu hamsin yamikawa Aliyu yace ungo rike wannan ka kara a hannunka, Aliyu ne yace dakabari baba akoe wasu kudi a hannuna, aa Aliyu karmuyi haka dakai bakaji nace ka karaba ainasan bazaka rasa wasu kudin a hannukaba Amma na dau wannan nabaka, maza karba , amatsayina na uba hakki ne a wuyana Aliyu ne yasa hannu biyu ya karba , godiya yayi yace Allah amfana da ameen baba ya amsa ,
Ummah ce tafito daga uwar daka tace kaima malam akoika danaci mutum yacemaka akoi kudi a hannunsa sa Amma sanda kamasa dole ya karba haba, ace wannan zabgegen saurayin ne akebawa kudin mota abun ai da kunya, wlh.
Kul kul Hadiza kar na kuskura nakarajin makamancin wannan maganar abakinki, daga yau in ina magana da dana bana son inkarajin bakinki, cewar baba da ransa yagama baci sabida maganar ummah.
Ummah ce ta tabe baki tace to ai shikenan, tunda haka kazaba, Aliyu ne yace ummah antashi lafiya, nizan wuce, amana addu'a , ummah ce tace to Allah ya sa karatun yamaka amfani,
Baba ne yawurga mata wani kallo shiru tayi ba shiri, baba ne yace toh gadanga Allah ya tsare hanya ,inka isa lafiya sai ka sanarmini dan hankalina ya kwanta Aliyu ne ya ce insha Allahu baba tashi yayi ya rataye jakansa a kafadan sa ,yace ummah natafi, Allah ya tsare tace masa batare da tasake kallon inda yakeba, don ita haushi suke bata da ga Shi Aliyu n har baban.
Aliyu bai tsaya ko inaba sai tashar Motar da take lodin kano kudin sit yabiya ,ya shiga ajiye jakansa ,yayi a booth din motan, zagayawa yayi yashiga sit din tsakiya ,baijima da zamaba motar tacika hanyan kano suka kama sunyi nisa cikin tafiya wani dattijo yayi magana akan yanaso atsaya zaikama ruwa driver ne yace bari su dan wuce wannan motar sai su samu gurin parkin wata bakar jip ce kirar SUV take parke agefen titin da alama tasamu matsala ne don ga drivern motar awaje yanata faman dubata ,motar su Aliyu ce tayi parking a gaban SUV din dattijon ne yafito tare da sauran masu bukata kowa yanufi inda yake ganin yafimasa sirri domin biyan bukatarsa,
Cikin bakar jip dinnan wata mata ce dawata yarinya budur wa, bazata wuce 17yrs ba fara ce sosai tana da manyan idanu gashin idonta bakakene zarazara , idanunta farafe ne tas kamar madara akoe Wani bakin layi dayazagaye kasan idanunta kamar wacce tasa ka kolli,hakan sai yakara wa idanunnata kyau sosai gashi inka kalli idanunnata kamar maijin bacci sai wani irin lumshe wa sukeyi da kan su ,Amma haka Allah ya halliceta,tana da dan karamin baki mai dauke da lips pink colour maihade da surkin baki ta dan kasan lips din zakace kolliyace ,daga saman goshinta kuma bakin gashine a konce kamar na jariri yayi luf dashi har kan girarta ,yan giranta sirara ne yan madaidaita kamar wadda aka zana su awajen , bata fiska yarinyar tayi tace nidai nagaji wlh , dan Allah Ammi kicewa Abba ya turomana wata motar, tun dazu baba idi yagagara jara motarnan, matar da aka kira da Ammi ce tace nidai zanga randa zaki girma jawaheer , kuma ba Abban ku da zankira barinyiwa baba idi magana in ba a shawo kan matsalar ba sai ya roka mana motar da ta tsaya dinnan agaban mu su karasar damu, wani irin daure fiska yarinyar da aka kira da jawaheer tayi tace haba Ammi ai ba girmanmu bane shiga waccar motar, dan Allah ko yaya Khaleed ki kira tunda munkusa isa , amma nikam bazan shiga waccar motar ba, Ammi.