Chapter 15
by @mrsalkali01
✨ZABI NA ✨
✍️~Mrs Alkali ~
🆓 Page 1️⃣5️⃣
Wajen Motar su Aliyu suka nufa kafin su karaso har driver ya fidda mutanen da suke sit din tsakiya wato nakusa da Aliyu,yacire dama su uku ne a sit din tsakiyan dake mutum uku wajen yake dauka , Aliyu kawai yabari a sit din, Ammi ce takaraso ita da jawaheer, drivern Motar ne ya hau gaisheta saikace zai mata sujjada, BISSIMILLAH hajiya cewar drivern sai wani qoqarin kade sit din yakeyi Ammi ce tace jawaheer tafara shiga , kara turo dan karamin bakinta tayi gaba sai kace zaifadi , shiga tayi tazauna a kusa da Aliyu Ammi ce tayi BISSIMILLAH tashiga itama zama tayi agefen jawaheer rufe qofar motar drivern yayi mutum biyunnan ne daya cire suke ta mita haka yasa wanda yake zaune a sit din gaba ya matsa musu haka suka zauna daya akan daya Motar yatayar suka dau hanya mutane biyunnan ne suketa faman mita akan ai yaga basuda kudine yasa yamusu wannan wulakanci , dayan ne yace ai dayake shi wanchan dayan yaga balarabene shiyasa bai fidda shi ba Amma dake anrenawa bakar fata wayo shiyasa, duk abunda suke fada Aliyu yanajinsu Amma baice musu uffan ba haka drivern yayi ta basu hakuri hardamusu alkawarin zai rage musu dari 500 acikin kudin Motar su nan ne akasamu salama sukayi shiru,
Tunda ta zauna awajen wani irin sassanyan kamshi ne yake dukan hancinta, a hankali tadago kai mutumin dayake gefen ta tazubawa idanu, wani irin kallon sa takeyi tunda take bata taba ganin hadedden namiji mai musulmin kyau kamar wannan balaraben ba sake baki tayi tana kallon sa, Ammi ce take ta mata magana jin shiru ba a amsataba yasa ta juyo wani balaraben mutum Ammi tagani zaune agefen jawaheer kansa ajingine jikin sit din Motar ya lumshe idanunsa kamar mai bacci, kallon jawaheer Ammi tayi taga duk hankalinta yana kansa,
Dakamata duka Ammi tayi acinya wani irin firgita tayi tana turo baki hade da sa hannunta tana sosa wajen da Ammi ta bugetan, Ammi ce tace sai ki kiramana Khaleed din yazo ya daukemu atasha in mun sauka, jawaheer ne tasa hannunta a cikin dan madaidaicin jakarta wayan Ammi ta ciro kirar iphone 16 pro max numbern yaya Khaleed ta dannawa kira atake ya dauka , hello Ammi ya hanya kundawo gidane,cikin wata zazzakar muryanta me dauke da wani irin amo mai dadi ne ya karrade cikin motar, yaya ba Ammi bace nice, tsaki yayi yace me katon kai kawai shine kika bari nayi tazuba kamar kurna zamu hadune dake, qara turo bakinta tayi tace Ammi ce tace munkusan isa kazo tasha ka daukemu Motar mu ce tabaci a hanya ,tanagama phadamasa sakon Ammi kit ya katse wayan kallon wayan tayi tace Ammi yakatse kiran ,badai yajikiba to ai shikenan, kara tura bakinta tayi , Ammi ce tace Allah dai yanunamin randa zaki girma.
Jawaheer ce ta zubawa Aliyu ido , duk wani motsin ta tunda tashigo motar akan idanunsa, amma in ka kalleshi zakazaci bacci yakeyi, don idanunsa a rufe suke, itama jawaheer tadauka wannan kyakkyawan balaraben bacci yakeyi shiyasa, tazuba masa ido duddah gidansu fararene kuma suna da kyau sosai amma ita bata taba ganin hadedden namiji mai kyau kamar wannan balaraben ba shi acikin larabawanma sai wanda Allah ya zaba ne zai samu irin wannan kyan, azuciyar ta take maganan ,
Aliyu ne yadan sa hannunsa ya gyara p-cap dinsa yadan rufe masa fiska aransa yanacewa yau naga ta kaina yarinya saikace maiya ita ko kunya bataji dubi yadda takuramin idanu saikace bata taba ganin mutaneba, dan sake kauda fiskar sa yayi, gefe ,
Jawaheer ne tace wannan balaraben Kila irin wadanda ake turosu aiki a Nigeria ne Gashi sai bacci yaketayi, duk acikin zuciyar ta take maganarta,
Shidai Aliyu duk atakure yake tunda wannan maiyar yarinyar tashigo Motar nan, shiyasa ma yaki bude idanunsa,
Jin mota ta tsayane yasa pasinja fara fita wato har sun karaso kano ta dabo tumbingiwa, ko dame kazo anfika, Ammi ce tafara fita, jawaheer ce tace aikafintabar gurinnan saitayiwa wannan balaraben magana, kinfita daga motar tayi jin shiru ne yasa Aliyu bude idanunsa basu sauka ako inaba sai cikin idanun jawaheer wani irin buguwa kirjinsa yayi da sauri ya kawar da kansa gefe , sabanin ita jawaheer da tasake sake baki tana kallon, wani irin yanayi takeji acikin jikinta jitakeyi ina ma ace yacigaba da kallon ta da wadannan kyawawan idanunnashi, a hankali taji yanayin jikinta yana sauyawa bude baki tayi a hankali tace masa hello,ganin yana kallon gefene yasa tayi tunanin bayajin turanci tana kyauta zaton balarabene ,jin baiyida niyarmagana yasa tace masa Assalamualaikum tunda dai musulmine koma daga ina yafito ai dai ya yanajin sallama kam, nanma shiru bai amsaba bare tasa ran yajita, jiki a sanyaye tafita daga motan aranta tanacewa Allah sarki bawan Allah shikuma haka Allah yaso ganinsa dama ance dan adam tara yake baicika gomaba shiyasa Allah yayi sa kurma ,haka tayita zancen zuci harta iso bakin motar yaya Khaleed da suke jiranta tundazu don ummah kam tariga da tashiga bayan motan ita suke jira,
Yaya Khaleed ne ya kalleta yace zaki shigo ne ko muwuce bakinta ta turomasa , shiga tayi tarufe murfin motan ribas yayi yafita daga cikin tashan,