Zaɓi na

Chapter 16

by @mrsalkali01




✨ZABI NA ✨ 

✍️~Mrs Alkali ~

🆓 Page 1️⃣ 6️⃣





A kofar wani narkeken gate motar yaya Khaleed tatsaya horn yayi security ne ya wangalemasa gate din cillah hancin motar sa yayi cikin katon gidan parking yayi acikin wata rumfa mai dauke da manya manyan motoci masu numfashi,
Ammi ce ta bude motar tafito , haka yaya Khaleed ma fitowa yayi, jawaheer ce kawai ta rage acikin motar 
Yaya  Khaleed ne ya kallah Ammi yace kinga yarinyar nan ko don iskanci ta jara zamanta acikin Motar taki fitowa ko, wlh in na je wajen sai na tattakata , Ammi ce tanufi bangaren da jawaheer take zaune bude marfin motan tayi tana cewa, kedai naga sanda zaki girma ace mutum kullum sai ne man magana ganin jawaheer bata kula ta bane , tana zaune bayanta jingine jikin sit din Motar idanunta a lumshe kamar mai bacci yasa Ammi tace , toh wani sabon iskanci ne haka yaushe kikafara yin bacci amota jawaheer, shiru Ammi taji hakanne yasa ta daka mata duka a kafadanta nanma shiru ba motsi Ammi ce tasa hannunta a hanci jawaheer taji bata numfashi, wani irin salati Ammi tasake,
Jin irin salatin da Ammi keyine yasa Yaya Khaleed matsowa yana cewa Ammi lafiya kuwa meyake faruwa,
Ammi ce tace Khaleed inaga ciwon jawaheer ne yatashi , dagata mushiga daga ciki , matsawa Ammi tayi gefe Khaleed ne ya matso nade hannun jamfansa yayi daukan jawaheer yayi, baban parlourn gidan ya nufa da ita,
Abba ne zaune a parlourn yana Karan ta jarida fiskar sa sanye da farin glashi, Ammi ce tafara shigowa , sallama tayi Abba ne ya amsa tare da rufe jaridar datake hannunsa, marmushi yayi tare da tashi yanufi Ammi dan rungumar ta yayi ta gefe , kiss ya mannamata a gefen kumatunta, Ammi ce tadan yi murmushi itama, tace alhaji barka da warhaka, barka dai Ammin yara har andawo ya hanyan, lafiya kalau, ya kuka baro mutanen gombe, lafiya su baffah suna gaisheka, Masha Allah, gaisuwa ya iso,
Bayan Ammi ya shiga lekawa alamar akoi abunda yake dubawa ,Ammi ta famci me yake nufi kallon sa tayi cike da tausayi , da so , shikuma haka Allah ya dauramasa tasa kaddarar akan jawaheer,kafin tacemasa wani abu 
Yaya Khaleed ne ya turo kofar dauke da jawaheer a hannunsa, sai kace wata marar rai,
Abba ne ya nufeshi hankali tashe yana cewa me ya faru da ita Khaleed, Ammi ce tace inaga ciwon ta ne ya tashi, 
Abba ne yace subhanallahi, yi maza kidauko alluranta kimata, Ammi ce ta nufi bedroom dinta wasu allurai ta dauko guda biyu jawaheer ta nufa dake konce bisa kujerar parlourn Abba da yaya Khaleed na tsaye akanta Abba ne ya kemata fifita da babbar rigarsa, kai kace parlourn ba AC gani yakeyi kamar AC bayazai wadacetaba, duk yabi ya rude ,Ammi ce ta matso tace alhaji barinmata alluran, Abba ne ya matsa gefe kallo daya zaka masa kaga rauninsa abaiyane, akan jawaheer,
Ammi ce taja ruwan alluran a cikin syringe cire mata  abayan jikinta tayi yarage daga ita sai riga da wondo, dan jan wondon Ammi tayi ta sama yadda jikinta bazai fito sosaiba, ahankali ta sokamata alluran, wani wawan ajiyan Zuciya jawaheer ta sauke , bata ko motsaba bare ta bude idanunta, sai ma wani irin gumi da yake shiga karyomata,
Ammi ce tajaramata konciyarta, Yaya Khaleed ne ya kalli Abba shima jikinsa duk yayi sanyi dan ba qaramin so yakeyiwa Yar uwar sa ba duddah ba sa shiri azahiri,
Abba ni zan wuce yanzu danyakamata in shiga school din da wuri cewar Yaya Khaleed Abba ne yace to Allah ya taimaka, Ammi ce tace Allah ya tsare da ameen ya amsa.
Ammi ce tasauqe ajiyar zuciya zama tayi agefen Abba, daura hannunta  tayi akan hannun Abba, kallon ta yayi cike da damuwa, cikin sigan rarrashi Ammi  tace alhaji a koi matsala fa indai akacigaba dayiwa jawaheer wa dannan alluran, kasan abunda doctor yafada, Abba ne ya kalli Ammi fiskar sa dauke da damuwa, yace , haka ne nasani kullum da wannan abun nake kwana nake tashi, bansan ya zanyiba, Ammi ce tariqe hannunsa da kyau tace alhaji hakuri zakayi, kawai kamata aure da habeeb din,  Abba ne yace Amma kinsan munriga da mungama maganan habeeb agidan nan ko tunda mamana tace batason sa kinsan dai bazan mata auren dole bako, 
Alkawari nayi bazan yiwa mamana auren Dole ba tunda tace batason habeeb, abarta takawo ZABIN ta mana , kamar yanda zuciyar ta take so.