Chapter 22
by @mrsalkali01
✨ZABI NA ✨
✍️~Mrs Alkali ~
Page 2️⃣2️⃣
Doctor ne yace alhaji binciken ya nunamana tadan jima da laluran kuma tana shan magani dan haka yanzu immune system dinta baya karban manin sai dai mu daurata akan alluran shima zuwa gaba zaidaina karban jikinnata, solution dayane shine a gaggauta mata aure dan in anbari yaje matakin da system dinta bazai karba alluran ba toh pha akoe matsala, Abba ne yamikawa doctor n hannu yace mungode doctor zamu iya tafiya in ancire mata drip din, yes of course inji doctor n, Abba ne yatashi fita yayi yanufi dakin da aka kontar da jawaheer,sunsameta ta tashi tana zaune akan bed din,
Idanunta sunyi zuru zuru, fiskar ta tayi fayau da ita Abba ne ya matso yace sannu Mama na ,ya qarfin jikin, da sauki Abba, to Allah ya kara sauki ameen ta amsa, Ammi ce ta taimakamata ta tashi mota sukashiga da ita driver ne yajasu sai gida,
Tun wannan lokacin alhaji Adamu waziri yashiga cikin damuwa shidai baya son ya yiwa jawaheer aure awannan lokacin sabida tayi yarinya gashi kuma doctor yace nangaba kadan ciwon zaizama barazana ga rayuwar ta,
Ammi ce ta lura da Abba samunsa tayi damaganan auren jawaheer din, toh inma auren zamumata ina jawaheer take da wani saurayi, inji Abba,, Ammi ce tayi shiru can tace alhaji me zai hana kayiwa abokan aikinka magana inyaso su turo yaran su duk wanda ta zaba sai a musu aure kawai, shiru Abba yayi, ajiyar zuciya ya sauke jin zuciyar sa ta gamsu da bayanin Ammi, hakane kinkawo shawara , saimu jarraba mugani.
Hakance ta kasance Abba dakansa yayiwa abokan sa magana , suma ba bata lokaci su ka amince ganin Abba babban mutum ne a kasarnan gashi da dukiya maitarin yawa , haka suka turo yayan su kowa na fatan jawaheer ta zabi dansa , Amma duk cikin su jawaheer tace ba ZABIN ta, Ammi ce tashigayimata fada Amma Abba ya dakatar da ita yace shibazaitaba yiwa jawaheer auren dole ba , Ammi tashiga damuwa sosai sabita ita nurse ne tasan hadarin irin wannan cutar, haka jawaheer tacigaba da zuwa makaranta har tashiga SS 3 anan ne suka hadu da habeeb shima dan abokin Abba ne yana karatu a Spain, yanzu yakammala shine yadawo gida,
Yazo ziyara gidan su Ammi anan yaga jawaheer,atake yaji yasamu matar aure dan bakaramin sonta Allah ya doramasa ba asanda ya koma gida ya fadawa baban sa bakaramin dadi yajiba ganin ga dama tasamu, baiyi kasa a guiwaba yasamu Abba da maganar Abba yayi murna yayi farin ciki saidai yace yaje yaga jawaheer inta amince dashi bawani matsala,
Bayan zuwan habeeb ne jawaheer tace sam ita baimata ba shi ba ZABIN zuciyar ta bane haka Abba yabawa su hakuri, amma duddah haka habeeb baidaina mata naciba,
Jawaheer ta kammala makarantar secondary sai dai Ammi taki yadda ta jona jami'a sabida tana tsoran kartaje tahadu da kawayen bazanza gashi tana dauke da wannan laluran ta muguwar sha'awa,shiyasa taki amincewa duddah daga farko Abba baiyarda ba Amma haka ammi ta tsaya kai da fata harta fahimtar da shi irin hadari da kuma illolin da zasu'iya fiskanta in har aka bar jawaheer tatafi jami'a,
Jikin Abba ne yayi sanyi jin Ammi tafi shi gaskiya shiyasa suka hakura da cigaba da karatun jawaheer harsai tayi aure sai tacigaba agidan mijin ta suma hankalinsu zaifi konciya.