Chapter 23
by @mrsalkali01
✨ZABI NA ✨
✍️~Mrs Alkali ~
Page 2️⃣3️⃣
*CIGABAN LABARI*
Amarya Zara'u zaune take akan kujeran parlourn ta taci uban kolliya fiskarnan tasha foundation da powder gawani jagira da taja , bakinnatannan yasha jan jambaki sai kamshin turaren emergency takeyi,
Tadaura kafanta daya kan daya sai tauna chewingam takeyi kana ganinta kaga amarya mai capacity 😂 dagani kasan jiran dawowan ango akeyi dan wannan uban kolliyan shi akayiwa, tunawa tayi da wani magani mata da jamcy takawo mata tashi tayi tashiga uwar dakanta daukan goran tsumin tabaje tayi tabude marfin, kwankwada ta hauyi sanda tasha yadda ya isheta sannan ta rufe, ajiyewa tayi, jin ana sallama a bakin kofar dakinta ne yasata fitaowa parlour n tayi ganin mama ce ke rafka sallama wato mahaifiyar Mansoor dake a family house suke ,ganinta ne yasa zara'u ta dan daure fiskanta sabida ta lura tunda aka kawota gidan mama irin surakanai masu shegen sa idon nanne kafin ma tayi magana hajiya mama harta zauna akan kujera one siter, amarya ansha kyau wannan uban kwalliya haka,sai kace mai zuwa gasan kyau zara'u ce ta tabe bakinta tana tauna chewingam dinta harda wani hurashi takeyi tace eyyi wlh , "hajiya Mama ce ta tabe baki aranta tanacewa Yayan zamani ba kunya,
Sallaman Mansoor sukaji , zara'u ce ta tashi da dan gudunta tanufeshi daleshi tayi tana dariya, shima cikin farinciki ya dagata sama yayi yana dan juyi da ita sai dariya sukeyi, hajiya Mama ce tayi jaran murya Mansoor ne ya dago kansa jin kamar muryan mutum acikin parlourn karaf suka hada ido da hajiya Mama dake leko su ta window parlourn ai Mansoor baisan sanda ya sake zara'u ba shiriba duk rashin kunyarshi bazaiyi agaban hajiya Mama ba, dan yasan ta ba kanwan lasa bace zara'u ce ta karbi ledar daya shigo da ita wucewa tayi gaba shikuma yabita abaya, parlourn suka shiga , zara'u ce ta wuce hajiya Mama zata shige uwar daka da bakin ledan da Mansoor ya kawo, hajiya Mama ce tayi charaf tace ke zara'u me aledar ina kuma zaki wuce da ita, Mansoor ne yace hajiya Mama barka da gida ko kallon sa batayiba ta karbe ledan hannun zara'u , budewa tayi taga balangu ne me zafi sai kamshiyakeyi yasha albasa da cabbage, wani irin hadiye yawu hajiya mama tayi tace, Masha Allahu kace balangu muka samu, daukan yanka daya tayi tasa abakinta, zara'u dai jitakeyi kamar ta shako wuyan hajiya Mama, shi kuma Mansoor sunkuyar da kai yayi kasa, don yasan ko giyar hauka yasha bai isa yayi magana ba.
Hajiya Mama ce tace maza dauko kwano in ibi rabona , zara'u ce ta tashi tanufi kitchen plate ta dauko , takawo hajiya Mama karba tayi ta raba balangun biyu ta ibi rabi mikawa Mansoor sauran tayi tace ganaku hannu biyu yasa ya karba ledar mikawa zara'u ledar yayi amma taki ma ta kalleshi barema yasa ran zata karba, tashi yayi yanufi cikin dakin hajiya Mama ce tace masa ahuta gajiya,
Zara'u ce ta tashi zatabi bayanshi hajiya Mama ce tace ina kuma zakije daga dawowan shi ai dai Kya barshi ya huta , ku yaran zamani ba kunya agaban uwar miji zakibishi , komawa zara'u tayi tazauna haka hajiya Mama tacigaba da cin balangunta tana yima zara'u tadin da ba fahimtar komai takeyiba,
Zara'u ce ta daga kanta ta kalli agogon bangon dayake makale ajikin ginin parlourn karfe 9:30pm na dare, kallon hajiya Mama tayi tayi wani rashe rashe bata da ma niyan tafiya, wutan NEPA ne ya dawo , hajiya Mama ce tace yauwa kaga yan albarka, maza kunnamana TV, zara'u ce tatashi ta kunna TV,
Wani Indian film akeyi a tashar star plus hajiya Mama ce tajara zama taci gaba da kallon film din India hankali konce , wani waje aka hasko inda jarumin film din yake koqarin yiwa jarumar kiss da sauri zara'u ta dauko remote ta chanza channel din , hajiya Mama ce tace yakika batarmana mayarmana mugani irin wannan soyayyah haka ,haka zara'u tasake mayarwa hajiya Mama tacigaba da kallon ta tun zara'u na fahimtar film din har bacci yayi awon gaba da ita akan kujera,
Mansoor ne yagaji da jiran zara'u, lekowa yayi ta jikin labulen dakin hada ido sukayi da Mama tace ashe bakayi bacci ba kaida yakamata ka huta kawuni kana aiki, me kake jira haryanzu baka kontaba ,
Mansoor ne ya dan sosa kansa yana dan satan kallon zara'u da ta kishingida tana bacci akan kujera daganin baccin kasan saceta yayi batare da ta shirya ba, Mama ce tace aida ka je kayi konciyarka innagama kallon film din nan zantashi zara'un ta rufe muku kofar, sosa kansa yayi yace toh Mama saida safe, Allah bamu alheri, cewar hajiya Mama haka tacigaba da kallon ta har misalin qarfe 12:00 sannan akagama haska film din tashi tayi ta tada zara'u tace maza zoki rufe muku kofa, zara'u ce tatashi tana ta gigin bacci haka taje ta rufo kofar bayan hajiya Mama ya fita,
Daki ta wuce tasamu Mansoor a baje akan gado yayi rashe rashe sai buga gortin sa yakeyi, gefensa tayada hakarkarinta ita ma ,tacigaba da baccinta batare da ta cire kayan jikinta ba bare ta goge fiskarta datasha foundation da powder.
Toh amarya Zara'u sai dai muce asuba ta gari😂😂😂