Chapter 25
by @mrsalkali01
✨ZABI NA ✨
✍️~Mrs Alkali ~
Page 2️⃣5️⃣
Yau weekend Aliyu ne zaune adaki book din sa yake dubawa Khaleed ne yafito daga toilet daure da tawol a kunkuminsa da alama wanka yayi jikinsa saikamshin sabulu yakeyi kallo daya Aliyu ya masa yadauke kansa ,
Dan yanda bayason akalli jikinshi shi yasa shima bazai iya kallon jikin waniba, gani yakeyi kamar wani sabon abu ne yin haka, shi har mamakin Khaleed yakeyi yadda ya sake dashi cikin lokaci kankani.
Khaleed ne yake dariyar shi , tunda yake baitaba haduwa da mutum mai murdedden hali irin Aliyu ba sai dai inka Zauna dashi yana da sanyin hali inka fahim ceshi,
Haba guy baka ganni nafito bane Khaleed ne yafada cike da zolaya , kamar badashi Khaleed yake magana ba inda sabo Khaleed yafara sabawa da wassu daga cikin halayen Aliyu don haka baya damunsa, ahakan ma duk cikin school din baya shiga safgar kowa sai na Khaleed din tunda yazo makarantar Khaleed ne kawai Abokin sa, dudda yan mata suna rububinsu Amma shi ko kallo basu isheshi ba, suma suna tsoron masa magana kai tsaye sai dai su samu Khaleed tunda yafisa sakin fiska da shiga jama'a,in Khaleed ya same shi damaganan yan matan share shi yakeyi baya ce masa uffan.
Yauma weekend ne shiyasa basuda lecture Khaleed ne yakeson zuwa gida duba su Ammi da jikin jawaheer,ba yadda baiyiba akan Aliyu ya rakashi Amma yaki sanda ya hadashi da Ammi a waya sannan ya amince dake wataran Khaleed yana hadasu su gaisa haka kawai yakejin kunyar matar, shiyasa ya gagara musata, amma in ason ransane ba inda zaije ya fahimci Khaleed dan gidan masu kudi ne shiyasa yake taka tsantsan bayason yafiye zakewa da yawa.
Ganin Khaleed na kokarin saka kayane yasashi tashi kayansa ya dauka yanufi toilet, don shiryawa.
Bayan wasu mintuna fitowa yayi sanye da jamfa da wondo ammasa dinkin half jamfa bakaramin kyau yayi ba gyra fiskarsa yayi, agogo na Gucci ya sanya a hannunsa turaren sa na GK men ya fesa , hulanshi yadauka ya murza akayinsa, Masha Allah shine abunda Khaleed ya fada juyawa yayi ya kallah Khaleed da yazubamasa ido dauke kai yayi, kamar baisan dashi Khaleed yakeba,
Dariya Khaleed yayi yace wannan kyau haka saikace me zuwa zance, ai sai ka hada mata go slow a hanya, kamar ba dashi akemaganaba.
Khaleed ne yatashi yace let's go guy ,kulle dakin sukayi da key, inda motar Khaleed take parke suka nufa duk inda suka wuce sai ankale su musamman Aliyu, Amma shi ko ajikinshi baisan ma sunayi ba wai an tsikari kakkausa tafiyar shi yakeyi cikin izza da korjini , parking space din suka iso shiga mazauni driver Khaleed yayi , shikuma Aliyu yazauna akujera mai zaman banza,
Yanda ya kafse acikin Motar zaka rantse da Allah wani yarima ne, Khaleed ne ya tada mota suka kama hanyanyar cikin gari .
Sundanyi tafiya maidan nisa kafin su shiga cikin garin Kano dan school din tana dan waje ne ba acikin kanon takeba .