Chapter 26
by @mrsalkali01
✨ZABI NA ✨
✍️~Mrs Alkali ~
Page 2️⃣6️⃣
~Ammi ce take ta faman jera abinci akan dinning table Abba ne ya ke kallon labaru a TV, kallon Ammi yayi yace nikam ina mama na tashigane tun dazu banji motsinta ba.
Tabe baki Ammi tayi tace tanacan dakinta tana sana"ar tata mana, Abba ne yace wace irin sana'a kuma , Ammi ce tace na tunanin ZABIN ta mana ai tun dawowarmu da ga garin gombe , tasamu wannan sarannan.
Abba ne ya ce kiramin ita inji meyake damunta don naga ke badamuwa kikeyi da damuwar ta ba, Ammi ce tadan girgiza kai jin yadda Abba ya dage sai masifa yake faman mata daga ta fadi dan wannan maganar, to me zatace masa bayan dakanta ta tambayi jawaheer me yake damunta, Amma me sai ce mata tayi tasamu ZABIN ta, Ammi taji dadin jin wannan batu, da ta tambaye ta a ina suka hadu kuma waye shi sai cemata tayi, ai wannan kurman balaraben ne dasuka hadu a mota, wani irin takaicine yakama Ammi jin abunda jawaheer ta ke fada, Ammi ce tace saura inji kinfadawa abban ku wannan maganar, kin tsaya shirmen banza da wofi da habeeb din kika kama da yafimiki ,shima alhajin da yabiyemikin yakusa dawowa daga rakiyarki, in dai yaji wannan zan cen.
Abba ne yace wai nikam Ammin yara me yake damunki ne kwana biyunnan bana ganemiki , kinsa yawan tunani agaba, jin muryan Abba ne yasa Ammi nufar dakin jawaheer, kamar yadda Ammi tayi tsammani, akonce tasameta kamar yadda tayi tsammani,idonta arufe kamar mai bacci.
Ammin ce ta tsaya a bakin kofa ,tace sarkin tunani ki sauko kasa Abban ku yana son ganinki, kinzauna kina tunanin abunda bazai amfane kiba.
Jawaheer ce tabude idanunta kallon Ammi tayi zumbura mata baki tayi tace , nidai Ammi ina son shi wlh, shine ZABI NA Ammi ce tahau salati kama baki tayi tace Ashe duk nasihar da namiki ashe bakijiba, toh Allah ya yayemiki,
Jawaheer ce ta sauqo daga kan gadon sanye take da doguwar riga na wani hadedden material dinkin ya zauna ajikinta sosai, fiskar nan tata tayi fresh bawani make up dan ita batacika yin make up ba, natural beauty ce , kanta sanye yake cikin wani hadedden hula wanda ya hau da rigar jikinta, bin bayan Ammi tayi.
Abba ta samu zaune a parlourn wajensa tanufa hannunsa yamikamata rike hannun nasa tayi , zama tayi agefen sa, tare da kontar da kanta bisa kafadar sa, Abba ne yace nikam meyake damun Mama na ne kwana biyunnan zaman daki ya aureki, jawaheer ce tayi dariya tace Abba ba komai pha , dariya yayi yace a'a Mamana banyadda ba fadamin me yake damunki, kallon Ammi tayi dake tsaye awajen dinning table tana cigaba da shirya abinci, hada ido sukayi da Ammi, Wani irin harara Ammi ta wurga mata, tabe bakinta tayi kamar meshirinyin kuka, saikace wata karamar yarinya Abba kaga Ammi ko, Abba ne ya kalli inda Ammi take yace ,me Mamana tayi akemata wannan hararar, Ammi ce ta tabe bakinta tace bagata akusa da kaiba ai saika tambayeta cewar Ammi da ta,cigaba da aikinta .
Abba ne ya maida dubansa akan jawaheer hannunsa na dan shafa bayanta alamar rarrashi yace Mama na fadamin meyake damunki, namiki alkawari ba abunda bazan iyamiki ba aduniyar nan indai kudi da alfarma na sayanshi, jin kalamen Abba ne ya sa jawaheer sauqe wani wawan ajiyar zuciya kallon Abba tayi, tace Abba ina son shi sosai , shine ZABI NA, hannunta ta daura a saitin zuciyarta tanajin yanda take bugawa da karfi, Abba ne ya kafeta da idanunsa, tabbas jawaheer da gaske takeyi don ya karanci daga cikin zuciyarta maganar take fitowa, sannan bata taba fadamasa tana son wani mutum ba , duk samarin da suke sonta taki ta amince da auren su don tace bazata taba aure ba in ba ZABIN zuciyar ta, duddah wahalan da takesha in ciwon nata ya tashi, lallai kuwa in dai hakane kowaye ne wannan mutumin da ya sace zuciyar tilon yar sa indai yana raye yayi alkawarin sai ta mallakeshi amatsayin mijin aure.
Ajiyar zuciya Abba yayi kallon ta yayi yace Masha Allahu, lallai nayi surki ke nan fadamin wani mai sa'a ne wannan dariya jawaheer tayi,tadaura hannayenta akan fuskan ta irin ta danji kunyan maganar da Abba yayi, Abba ne yace a ina kuka hadu, dangidan waye ne, me sunanshi.
Jawaheer ce ta turo dan karamin bakinta dan abun ya zamomata sabo indai zatayi maga saitayi tabara musamman ma in tana tare da Abba, Abba bansan sunan shiba ,kuma amota mukahadu da shi,.
Nan jawaheer ta labartawa Abba yadda komai yafaru tun farko, Abba ne ya jinjina lamarin, wannan shine ga samu ga rashi yana tunanin matsalar su tazo qarshe , Ashe wannan ne mafarin matsalan, ta ina yasan zaifara neman wannan mutumin da yakasance ZABIN zuciyar yar sa, tilo.
Jawaheer ce ta kalli Abba tace Abba kaima bazaka goyi bayana ba kamar Ammi, murmushi yayi tare da shafa kanta yace namiki alkawari Mama na zanyi iya kokarina innemo shi, koda kuwa ba a wannan kasar yakeba, rungumar Abba tayi tana dariyar farinciki tace shiyasa nake son ka Abba na I love you, dariya Abba yayi yace I love too mama na.
Ammi ce ta girgiza kai tana kallon Abba da jawaheer, tarasa meyasa alhaji yake biyewa shirmen jawaheer dudda shine ya sakaltata, batajin dadin yadda yake nunamata komai zai iya samamata shi aduniyar nan, shiyasa wasu lokutan jawaheer bata fiye sanarmata wasu matsalolin taba sabida tana ganin Ammi bata goyon bayan ta , shiyasa wasu abubuwan da suka shafi jawaheer sai dai Ammi tajisu abakin Abba.