Zaɓi na

Chapter 28

by @mrsalkali01



✨ZABI NA ✨ 

✍️~Mrs alkali ~

Page 2️⃣8️⃣ 

Abba ne zaune a parlourn bayan yagama cin abincin zama yayi tare da su Khaleed, shidai Aliyu ya gagara sake jikinsa duddah ya fahimci iyayen Khaleed suna da kirki musamman Abba yana ta jan su da hira, har tambayansu yakeyi yanayin karatun nasu, shi dai Aliyu sai dai yayi murmushi baicika maganaba, shi kanshi Abba ya fahimci hakan ajininsa yake.

Kiran sallah ne yasa su tashi dakin Khaleed suka nufa alwala sukayi suka sauqo parlourn kasa Abba sukasamu yana jiransu, masallacin cikin gidan su kanufa don yin sallah ,don acikin gidan akoi katon masallacin da makwafta da yan anguwa suke shigowa yin sallah.

Ammi ma dakinta tanafu dan yin sallah bayan tagama tattare dinning table din dasukaci abinci.

Jawaheer ce konce a makeken gadon ta hannunta ne daure a saitin zuciyarta, sallah takeson yi amma takasa tashi,zafi sosai zuciyar ta takemata,a hankali wasu irin hawaye masu zafi suka gangaromata.

Wannan wace irin kaddara ce, zuciyar ta ta kamu da son wanda ma baisan tanayiba, da alama ma shi ya manta ta da suntaba haduwa ma, ashe ita kadai take ta haukarta.

Tun randa tahadu dashi zuciyarta batasake samun nitsuwa da sukuniba kullum a cikin tunaninsa take kullum burinta Allah yasake nuna mata shi saigashi har gidansu yazo baima shida fiskar ta ba, wasu sabbin hawayene suka qara silalowa daga cikin idanunta .

Wani irin zafi da ciwo zuciyar ta kemata jitakeyi kamar zata kumbura ta fashe, sake dafe saitin zuciyartar tata tayi da karfi jin yanda numfashinta yake mata barazanan daukewa, a hankali idanunta suka fara lumshe wa yayin da takejin hankalinta yana kokarin barin jikinta, idanuntane suka rufe ruff.

Su Abba ne suka shigo parlourn zama Abba yayi akan sofa, Khaleed ne yaja Aliyu suka wuce dakinsa.


Ammi ce ta sauko parlourn wajen Abba tanufa zama tayi agefen sa, Abba ne ya ce ina Mama na ne , Ammi ce tace tana can dakinta , Abba ne ya ce kirawomin ita, na lura dazu takasa sakewa taci abinci da kyau Ammi ce tace haba alhaji kadinga rage irin wadannan abubuwa da kake nunawa jawaheer, wataran fa aure za'a mata kuma gidan wani zata tafi.

Abba ne yace zaki kirata ne ko zakiciga ba da min wa Azi kinga sai natashi nakirata da kaina,tunda ke ban isa dakeba .

Allah ya huci zuciyarka cewar Ammi da tashi tanufi dakin jawaheer.

Tura kofar dakin Ammi tayi, ganin jawaheer tana konce kuma da alama bacci takeyi, rufe kofar dakin tayi ta juya, Abba ne ya ga Ammi ta dawo ,ita kadai,tambayanta yayi ina maman tawa ne naga kindawo ke kadai, Ammi ce tace naje nasamu tana bacci.

Abba ne yace bacci kuma da wannan sakaliyar la'asar din, ai da kintashe ta tunda kinsan baccin la'asar din bashi da wani amfani.

Ammi ce aranta tace ni Zainab a hakanma ban tsira ba, tunanin ta ne ya katse lokacin da taga Abba ya nufi dakin jawaheer dakansa, jinjina kai tayi, tana tunanin wannan wace irin kauna Abba keyiwa jawaheer,baya wasa da duk wani abu da ya shafeta.

Abba ne ya bude kofar dakin hangota yayi konce akan makeken gadon ta shiga cikin dakin natan yayi, wajen gadon ya nufa, hannunsa ya daura asaman goshinta wani irin zafi yaji , hankalinsa ne yayi mugun tashi, Mama na haka Abba ya hau kiran sunanta, Amma ko alamar motsi batayi, hankali Abba in yakai kololuwa to yatashi.

Hannunta dayagani dafe da saitin zuciyarta ya taba Amma me zaigani hannun ne ya yafadi yaraff agefe wani irin gumi ne ya yankowa Abba sake kai hannunsa yayi abakin hancinta jiyayi bawani numfashi da yake fita, wani irin sarawa kansa yayi take yaji wani irin hajijiya tana kokarin dibarsa zama yayi abakin gadon nata yafara salati.

Ammi dake zaune a parlour ne taji muryan Abba ya buga salati, da hanzari ta tashi ta nufi dakin jawaheer dan tana da tabbacin chan ne yashiga dazu , shigar ta dakin ta samu Abba zaune abakin gadon jawaheer sai uban gumine yake yankomasa bakinsa dauke da salati da alama ma baisan yanayin da yake cikiba.

Maida kallon ta tayi kan jawaheer dake konce kamar mai bacci da sauri ta qarasa bakin gadon hannunta tadaura akan na Abba tace alhaji lafiya me yasameka, da kyar Abba ya iya daga ido ya kallah Ammi, kamar wani karamin yaro mai koyan magana yace zainab shikenan munrasa jawaheer, Zainab jawaheer ta mutu.

Wani irin duum gaban Ammi ya yanke ya fadi, ai batasan sanda ta zabura tayi kan jawaheer da ke konce ba azatonta bacci takeyi, girgiza ta Ammi ta hau yi Amma ina tariga da tagama sakewa ba inda yake motsi ajikin.

Tashin hankalin da Ammi tashiga bakaramibane dan bakaramin kaunar jawaheer takeyiba duddah tana dannewa bata nunawa afili, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un kawai shine abunda Ammi take iya maimaitawa wani irin zufa ne yake yankomata,,

Abba ne yayi karfin halin ciro wayansa a cikin aljihun sa , number n Khaleed ya kira , kira daya Khaleed ya dauka, jin abunda Abba yace ne yasa shi zabura aibaisan sanda yayasar da wayar ba hanyan kofa yanufa.

Aliyu ne ya tashi yana tambayarsa ko lafiya ko takan Aliyu baibi ba yanufi hanyar da zata sadashi da dakin jawaheer, ganin hakane yasa Aliyu ma ya rufamasa baya ganin Khaleed din bayama cikin hayyacinsa don daganin yanda ya yi wurgi da wayarsa ya fita kasan bayacikin hayyacinsa.

Khaleed ne yafara shiga cikin dakin ganin yanda Ammi da Abba suke ta rusa kuka yakara tabbatar wa da Khaleed maganar da Abba ya fadamasa awaya ,inda jawaheer ke konce ya nufa, tabata yashiga yi Amma ina ko ina ya sake ajikinta,
Aliyu ne ya shigo ganin halin da familyn sukashiga ne acikin kankanin lokaci abun ya dauremasa kai kallon Khaleed yayi dashima har yafara hawaye ,
Yace meyake faruwane kam, Abba ne ya yi jarumtar fadamasa , wani irin bugawa zuciyarsa tayi , wani jiri ne ya debeshi jikin ginin dakin ya dafa , innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Aliyu yake nanatawa, ahankali ya matsa kusa da gadon da ya hango jawaheer, idanunsa ya daura akanta kamar maison gano wani abu a hankali yadau hannunsa ya daura a saitin zuciyarta, wani wawan ajiyar zuciya ya sauke jin zuciyar ta tana harba wa Amma a hankali sai mutum ya natsu ne zaigane hakan.

Da sauri yakalli Khaleed yace guy zuciyar ta na bugawa haryanzu amma a hankali, ai baigama rufe bakinsaba yaga dukansu sun nufoshi Khaleed ne yasa hannu yadauki jawaheer kamar wata jinjira, kofar fita ya nufa da ita, Aliyu ne ya rufamasa baya , sai Abba da ya bisu, Ammi kuma taje dauko hijabinta a dakinta zatasame su a mota.

Gun motar da sukazo da ita Khaleed ya nufa yana isa ya bude kofar baya yasaka jawaheer, key din motar yaciro ya wurgawa Aliyu, chafke key din Aliyu yayi bude bangaren driver yayi, Khaleed ne yashiga gefe mai zaman banza Aliyu ne yayi rivers yaja motar security ne ya wangale gate din cillah hancin motar yayi akan titi su Abba kuma shida Ammi wata motar suka shiga baba idi driver ne yajasu, bin bayan motar su Aliyu suke yi.

Khaleed ne yashiga yiwa Aliyu kwatance har suka iso wata hadeddiyar private hospital, da sauri sukayi parking, Aliyu ne ya kashe motan kafin yafito har Khaleed ya shiga cikin hospital din ya dawo  da nurse's mata guda biyu,daukan jawaheer sukayi akan dan gadon da ake tura marar lafiya,
Dasauri suka nufi cikin asibitin da ita su Abba ne su ka iso asibitin suma binbayan su Khaleed din sukayi,
Wani daki nurses din sukashiga da ita, Khaleed ne yake kokarin binsu cikin dakin dakatar dashi sukayi sukace musu sujira a waje doctor ne zai dubata,
Dukansu ba wanda ya iya zama kowa yana tsaye yayi jugum jugum, suna jiran fitowar doctor.

Aliyu ne ya kalli fuskokinsu ganin yanda damuwa ta bayyana qarara akan fuskokinsu yasa shi jin ba dadi, Allah kenan baruwanshi da lafiyanka kalau inyaga dama yanzu sai ya karbi ranka, ji yanda wannan familyn suka shiga tashin hankali da damuwa acikin mintuna kalilan kamar basu suke wasa da dariya ba dazu .