Zaɓi na

Chapter 30

by @mrsalkali01



✨ZABI NA ✨ 

✍️~Mrs Alkali ~

Page 3️⃣0️⃣

 Doctor ne yafito daga cikin dakin da aka shiga da jawaheer,, da sauri duka familyn suka nufoshi tashin hanakalin da suke ciki bazai barsu sujira qarasowarsa garesuba,

" Abba ne ya ce doctor ya ake ciki Mama na ta tashi,, kallon su doctorn yayi ganin yanda gaba dayan su suke cikin matsanancin tashin hakankali yasa ya fahimci ba qaramin so sukeyiwa yarinyar da sukakawo ba,,
" Ammi ce tayi karfin halin cewa doctor kodai jawaheer tarasu ne,, kallon su doctorn yayi cikin sigar kontar musu da hankali yace tana raye bata mutuba,, ahalin yanzu tana bacci sai zuwa anjima zata farka,,
Atare suka furta alhmdullah tare da sauke wani nannauyan ajiyar zuciya,
"Doctor ne yacewa Abba alhaji ina son ganinka a office kai kadai,,
"Wucewa doctorn yayi Abba ya rufa masa baya, bayan sunshiga office din ne doctor yace wa Abba yazauna,,
" Bayan Abba ya zaunane doctorn yakalleshi yace alhaji munyi duk wani gwaje gwaje da yakamata , sannan munsamu munceto yarinyar da ga critical condition da tashiga,,
" A gwaje gwajen da muka mata yabbatarmana da tana dauke da ciwon Zuciya, domin a halin yanzu zuciyarta tafara kumbura shi ya haifarmata da shiga wannan yanayin, da alama akoi wani abu da yake damunta ko kuma take so bata sameshi ba, dan shine zai iya jefata a cikin wannan mawuyacin halin,,
"Hankalin Abba inyayi dubu to ya tashi, ciwon Zuciya 🫀 kuma , suda suke kokarin magance mata waccan laluran saikuma ga wata ta bullo wacce tafi wanchan,
"Doctor ne yakatse wa Abba tunaninsa , yace alhaji shawaran da zan iyabaka shine, ayi kokari asan mene matsalarta sannan ayi kokari adinga kontar mata da hankali, don shine matakin farko na dakileh wannan cutar don inba ayi kokarin magance mata matsalanta ba toh ko mun daurata akan maganin bazaiyimata aiki ba,
"Kuma ayi kokarin ganin bata sake samun wani attack makamancin wannan ba,,
" Abba ne ya ja dogon numfashi yace nagode doctor,mika masa hannu yayi sukayi musabaha, fita Abba yayi yanufi inda su Ammi suke zaune dan jiran dawowansa,
"Abba ne yakaraso jiki a sanyaye zama yayi a gefen Ammi, Khaleed ne dake zaune agefe shida Aliyu, sai kokarin kontarwa da Khaleed hankali yakeyi, tashi Khaleed yayi yanufo inda su ammi suke zaune, Abba ne ya kalle shi yace zamu iya shiga muganta , Khaleed ne yace Abba me doctor n yace maka, sauke ajiyan Zuciya Abba yayi kallon fiskokin su yayi yaga duk shi sukejira yayi magana, Ammi ce tace kodai da matsala alhaji, Abba ne yace bakomai karku damu in munje gida zamuyi maganar, jinjina kai Ammi tayi tana nufan dakin da aka kontar da jawaheer din, Abba ne ya take mata baya,
" Jawaheer ce konce akan gadon asibitin drip ne daure a hannunta, sanye take da kayan jinya na asibitin dan gown ne pink colour da kadan ya wuce kasan guiwanta kanta ba dan kwali gashinta ne kwance akan pillow duk ya barbaje akayi,tayi wani irin haske na marasa lafiya ,
" Abba ne ya qaraso zama yayi agefen gadon, Ammi kuma jan kujera tayi ta zauna ata gaban gadon zuba mata idanu sukayi kamar masu irga numfashinta, ba me cewa dan uwan sa wani abu,,
Khaleed ne ya turo kofan dakin shigowa yayi, gun Abba ya je ya tsaya , shima jawaheer din ya zubawa idanu yana jinjina lamari na uban giji,
" A hankali ta dan motsa hannayenta , Abba ne yayi saurin matsawa kusa da ita, a hankali take bude idanunta da suke mata dishi dishi, saman dakin ta kurawa ido kamar maison yin nazarin inda take ahankali ta juyo da kanta ta inda taji alamar motsi Abba ne zaune yana rike da daya hannunta ,da sauri Abba yace alhmdullah Mama na kintashi,, jinjina kanta tayi alamar ehh, amma batace masa uffan ba,,
" Dakin tashiga karewa kallo idanunta ne suka sauka akan Ammi da yaya Khaleed dasukayi cirko cirko akanta sai hamdala suketa zubawa,,
"Ta fahimci a asibiti take, shin me yasameta, shin ina kurman balaraben nan , abokin Yaya Khaleed,shin ko dai mafarki takeyine, shin meyake damuntane,,
"Kenan ya kubucemata akaro na biyu,, inko hakane ta tabba ta mara sa a arayuwarta, akaro nabiyu ta rasa ZABIN ta,
Wani irin zogi taji zuciyar ta nayi, a hankali ta daura hannunta a saitin zuciyarta da take mugun bugawa da karfi,,