TUN RAN GINI

Chapter 1

by @maryamlitee

DA SUNAN ALLAH MAI RAhMA MAI JIN ƘAI.

SANIN GAIBU

PAGE ONE*

MARYAM LITEE

"Ki bar ma Halima wanke-wanken ki tafi zuwa zancen ai ya fi muhimmanci."

Kalaman da na tsinkaya kenan daga bakin mahaifiyata tana faɗa ma ƙanwata A'isha da aka aiko ana kira a waje.

Na dubi tulin wanke-wanken na dubi igiyoyi biyu da na cika da shanya kayana da na mahaifiyar tawa da na ƙaramar ƙanwata Bilkisu, gabaɗaya na gaji so samu na samu wurin da zan yada haƙarƙarina na huce tarin gajiyar da ta yi wa ilahirin jikina ƙawanya tare da ciwon marar da ke murɗa mini akai-akai da nake tunanin na mene ne don baƙona lokacin dawowar shi da saura.

A'isha ta yi fara'a jin an raba ta da wanke-wanken sai dai tana cira ƙafa na ce

"Idan kin dawo kin yi abin ki a gajiye nake."

Wani kallo Mamanmu ta feso mini kafin ta furzo mini maganar da ta haddasa ma ƙirjina riƙewa.

"Har wata gajiya gare ki Halima? Mu ba mu faɗi gajiya da ke ba muna zaune da ke shekaru har ashirin da biyar, kai

wannan baƙin jini Ubangijin rahma ka yi mana tsari da irin sa.

Kar ta je zancen ita ma ta bi sahun ki ku taru ku kashe ni da baƙin ciki a......

Ban jira sauraren ƙarashen maganar ta ta ba na miƙe cikin sauri na isa rijiya na ja bokiti na fara janyo ruwa.

Ina fara wanke-wanken A'isha ta fito cikin kwalliya ta burgewa ta yi waje, har kuma lokacin Mama mita take mini na zama na har yanzu ba aure.

Mai bi na namiji ne Abdallah mai shekaru ashirin da uku, A'isha ita ce ƙanwata ta biyu shekaru ashirin ne da ita, sai Amina mai sha bakwai, Bilkisu ce ƙarama mai shekara sha ɗaya.

Kukan zuci nake har na kammala wanke-wanken ga ciwon marata da ke ƙara gaba ina ta addu'a cikin raina Allah ya taƙaita mini shi don ba ni da maganin da nake haɗiya don samun sauƙi ya ƙare, ta'azzarar ciwon kuma na nufin sai Mama ta saya mini magani sayen kuma zai haifar mini da maganganun da sai na gwammaci zafin ciwon da su.

Na miƙe tsaye na ja ƙafata zuwa ɗaki A'isha ta shigo ɗauke da manyan ledoji guda biyu a hannunta, hakan ya ja Mamanmu da ke haramar talge sakin muciya ta ce in je in talga mata suka shiga ɗaki.

Ina zaune gaban murhun ina gyara itacen Bilkisu ta shigo kitchen ɗin tana rufe ido saboda hayaƙi, na goge idona sannan na miƙa hannu na karɓi lemon ɓawo guda ɗaya da yankan abarba mai ɗan girma sai ayaba ɗaya, na ajiye a gefena na yi talgen.

Mama ba ta fito ba hakan ya ja mini jiran ya dahu na tuƙa sannan na tashi zuwa ɗakinmu.

Daki ne babba falle ɗaya mai ɗauke da gado mai rumfa irin na mutanen da sai family bed six by six, ƙasa rubber tiles ne sai wardrobe da muke adana kayanmu sai kujera doguwa ƙwaya daya.

Na tsallake Mama da ya'yanta da suka yi rashe-rashe a filin dakin suna bidiri kan tsarabar saurayin A'isha sai sannan na tuna da wanda aka kai mini, na ture wani tsalelen less sai atamfa da aka fitar anko ta yarinyar makotanmu da ta zamto ƙawar A'isha sai wasu ubansun takalmi a bisa gado mai rumfar na kwanta.

Bilkisu ta iso gaban gadon ta ce mini "Aunty kin ga kayan da saurayin Aunty A'isha ya kawo mata da lemo da ayaba da abarba har da kwakwa.

Ta ƙarashe faɗi tana ɓantarar kwakwa, na lumshe ido

"Na gani Bilkisu."

Ba ki da lafiya?

Ta tambaye ni

Kai na ɗaga mata

Ta juya cikin sauri tana fadi ma Mamanmu

"Aunty ba ta da lafiya.

"Allah ya sawaƙe."

Ta faɗi daga inda take .

Juyi na ci gaba da yi cikina na daɗa tsananta har abokiyar zaman Mama ta leƙo ta ce tuwo na ƙauri, Mama ta dubi inda nake kwance ta ce

"Wane irin iya shege ne za ki bar mini tuwo ya lalace?

Na ja ajiyar zuciya

"Marata ciwo take Mama."

Uhumm! Watan ya yi kenan sai ki tashi ki haɗiyi maganin."

Na kai hannuna na dafe goshina na ce "Ya ƙare."

Ta zabga ƙwafa kafin ta ɗaga duka hannuwanta sama

Allah na roƙe ka ka yanke mini zaman Halima ka kawo mai kwashe ta.

To ki sani ni yau ba ni da ko ƙarfanfana."

Na dube ta sai na lumshe ido ina jin wani abu na tasowa daga ƙasan zuciyata.

Ta fita ta bar dakin .

Ban tashi ba sai da na ji kiran sallah na sauka gadon na fita kewayawa na yi ganin har na gama tsugunno na ba alamar zuwan baƙona sai balain ciwon marar da ke ƙara ta'azzara na miƙe da kyar na fita.

Kowane ɗaki a gidan sun fito da tabarmarsu sun shimfida yaran kowane daki da uwarsu suna zaune .

Na yi alwala na koma daki cike da ƙarfin hali na gabatar da sallar kamar kullum bayan yi ma iyayena addu'a na roki Allah ya iyakance mini wannan zama ya kawo mini miji.

Ina nan zaune lokaci-lokaci ina share hawaye har aka kira isha'i na gabatar da ita na miƙe zan hau gado auta Bilkisu ta shigo

"Aunty, Mama ta ce ba za ki fito ki ci tuwo ba?

"Na ƙoshi. Na furta na haye gadon, juye-juye na yi ta yi har lokacin kwanciya ya yi duk suka shigo A'isha da muke kwana tare ta wuce bayana tun ina jin hirarta da saurayinta ta waya da take yi ƙasa-ƙasa har Allah ya kawo mini sauƙi na shiga barci.

Da asuba ciwon ya farkar da ni na fita na kewaya a fatar da nake baƙon nawa ya zo ko na samu sauƙin wahalar da nake ciki sai dai addu'ar tawa ba ta ci ba na miƙe na fita na yi alwala, ina idar da sallah gado na koma maimakon sharar tsakar gidanmu da na wajabta ma kaina yin ta ganin yadda matan uku na babana kowacce ke jin ƙyashin sanya ya'yanta su yi .

Marar ta ci gaba da ciwo kafin ta lafa na fara barci sama-sama muryoyin Mama da abokiyar zaman ta wadda mu yaran gidan ke kira Ummi ita ce mata ta uku wurin babanmu, Mamanmu ce babba sai Haj murja mu yaran gidan na kiranta Umma.

Sai da na saurara da kyau na gane kan hayaniyar da suke tun da safe don abin da na ji Ummin na faɗi

"Sai maigidan ya bayar da kuɗi ki dama mana koko mu sha mu warware hanjinmu sai ki haɗa mu da ɗumame, a soke kuɗin don kin ga ba ya nan .

E hakan ma matsayi ne ke ki soke mana, tuwon na ga damar ba kowa wanda bai ci sai ya bar shi ."

Ai kam shi ya sa bukatar kowa ta biya ta bar ta mutum.

Wace buƙata ce tawa ba ta biya ba Bilki?

An bar ki da ɗiya a daki kuma duk sakamakon abin da kike aikatawa ne."

Mama ba ta ba da amsa ba daki ta yo

Ai sai ki tashi Halima ki ji har an fara yi mini gorin rashin aurenki."

Fakare na ƙara yi har ta ƙaraci fadanta ta fita dakin na dubi kwanon da Bilkisu ta ajiye mini kafin su fita makarantar islamiyya gutsure ɗaya ne na ɗumamen tuwo, ban san yadda zan yi in kai shi cikina ba duk da matsananciyar yunwar da ta taso mini rabo na da abinci tun jiya da rana abu mai ruwa na fi buƙata na dafe cikina na juya baya.

Ina nan kwance gidan ya yi shiru alamar kowa ya tafi sabgar gaban shi yaran sun tafi islamiyya kasantuwar yau ɗin asabar ce boko ma ana cikin hutu, mama ma na zuwa islamiyyar safe Umma da Ummi kadai ake bari a gida Umma tsohuwar malamar makaranta ce tasowar kanenta da ya yi kuɗi ya ɗauke dawainiyarta ya sa ta ajiye aikin, Ummi ke zuwa Kano sarin zannuwa.

Shigowar A'isha na gani ɗauke da baƙar leda ta zauna a ƙasa ta haɗa tea ta fara sha tana danna wayarta hira take da saurayinta ta hanyar voice call lallashin ta yake zai zo da yamma su fita su shakata tsoro ta faɗa mishi tana ji tsoron me ya tambaye ta indai ya samu yadda yake so a wurin ta komai take so a shirye yake ya yi mata.

Da daɗin baki ya samu ya samo kanta ta faɗi abin da take so ya kawo mata amma fita ta ce sai ta yi shawara.

Sun yi sallama ta kashe wayar ɗagowar ta sai ta ga ina kallon ta wata irin razana ta yi da ta sa ta yarda cup ɗin hannunta na ja ajiyar zuciya kafin na furta komai ta fara magiya

Don Allah Aunty kar ki faɗa ma Mama."

Na tashi zaune da ƙyar

"Kwadayi ko A'isha? To mabudin wahala ne. Don wannan ƙyal-ƙyal banzan da yake baibaye ki da su suka rude ki kika sayar mishi da mutuncinki za ki yi da na sani, daga karshe kuma abu mai wahala ne ya aure ki bayan ya gama lalata da ke, idan kuma an tafka matuƙar sa'a ya aure ki ba zai miki kallon mutunci ba ko ki kasance kullum abar zargi a gare shi."

Ta jinjina kai cikin kwantar da kai ta ce "Na bari Aunty, ni dai kar ki faɗi ma Mama."

Na mayar da kaina na kwantar cike da tunani, ban san ta fita dakin ba sai da na ji ana ambaton sunana na tayar da kai Umma ce hannunta riƙe da cup, dayan kuma da baƙar leda ta zauna bakin gadon kusa da ni

"Sannu Halima ya cikin?

Na ce "Yawwa Umma ina kwana?

Ta amsa sai ta miko mini cup ɗin

Tashi ki sha tea na san ba za ki iya cin tuwon da Mama ta haɗa mu da shi ba."

Na miƙe jikina har rawa yake na karɓi cup ɗin na kafa kai shayi ne mai zafi ya yi kauri ƙwarai ga kayan ƙamshi.

Ban ɗago ba sai da na shanye na miƙa mata cup ɗin ina furta kalmomin godiya a gare ta ta ciro maganin rage zogi da nake sha a yayin ciwon marata ta miƙo mini na amsa ina jin sanyi da salama cikin raina, a wannan gaɓar godiyar da na yi mata har da ƙwalla da ta cika idona.

Ta miƙe sai ta bar dakin kamar walƙiya.

Na ci gaba da kwanciya ina jiran cikin ya faɗa ina jin dama-dama na tashi na fita don in yi wanka.

A kitchen na samu ruwa mai zafi na surka na shiga wankan har na kammala ba baƙon watana na fito ina ajiye bokiti Ummi ta fito daga ɗakinta, gani na sai na ga kamar ta ji kunya ta yi ƙarfin halin amsa gaisuwata tana tambaya ta jiki, na ce na samu sauki.

Na wuce ina tunanin abin da ta ce ma Mama a kaina wanda ko kaɗan ban ji haushin ta ba ita Maman ita ta samar da ƙofa ita ke mini gorin aure kafin kowa ya fara har ga shi ita ma yau abokiyar zaman ta ta yi mata.

Kwanciya na yi bayan na sanya doguwar riga ta wani yadi mara nauyi.

Ƙarfe sha ɗaya Mama ta dawo tsakar ɗakinta ta miƙe ƙafa bayan ta yaye hijab ta ajiye.

Kuɗaɗe take ta famar cirowa cikin jakar makarantarta kasantuwar ta uwar adashe, rana irin ta yau kuma ake kwasa.

Sai ƙirgawa take tana warewa ita ɗin uwar adashe ce ta gaske tana yin babba da karami har da na maza.

Ta amsa sannu da zuwan da na yi mata hankalinta na kan lissafin da take zuciyata na ta kai ka wo ta yadda zan faɗa mata halin da A'isha ke so ta tsoma kanta amma ina jin wata irin fargaba na lulluɓe ni.

Karshe na yi amfani da hadisin Manzon rahma da ya ce wanda ya ga wani abin ƙi ya hana shi da hannunsa, idan ba ya iyawa ya hana shi da bakinsa idan ba ya iyawa to ya ƙi abin a zuciyarsa.

Amma wannan shi ne ma fi raunin imani.

Addu'a na yi ta jera ma A'isha a zuciyata Allah ya tsare ta ya kare ta daga faɗawa ɓarna kowace iri ce.

Ranar ma dai a kwance na wuni da kuma ciwon marar, hankalina ya tashi don bai taɓa yi mini haka ba.

Karfe takwas da minti biyar na dare aka aiko kiran A'isha ta amsa tana zuwa don dama ɗakin daga ni sai ita sai Mama sauran yaran suna ɗakin Haj don ita ke da kayan kallo suna kallon shirin Daɗin kowa.

A'isha tana zaune ta fito wanka tana tsala kwalliya wani ƙayataccen less ta daura da ɗinkin ya zauna dam a jikinta, kyakkyawan dirinta da ya fito ya tuna mini da shekarun da suka shuɗe lokacin da nake da shekarun ta har ma na zarta ta ban sha'awa amma yanzu fa?

Na tambayi kaina siririn hannuna na ɗaga na kalla ikon Allah mai mayar da sarki bawa. Tun da na gama cikar budurcina a hankali na yi ta zaizayewa ina tsotsewa har na koma wata irin siririya ƙannena duka sun fi ni.

Katse tunanina na yi na dubi A'isha saboda wani daddaɗan ƙamshi da ya daki hancina turare take feshe jikinta da shi, na lumshe ido ina jin wata irin fargaba ta fitar ta ta na rufe ni.

Ban yi azarɓaɓin tunkarar Mama ba har sai da ta je taɗin ta dawo ƙarfe goma saura mintuna bakwai ta shigo na dubi agogo sai na dube ta tana sunce kayan da ta fita da su bayan ta miƙo wa Mama tsaleliyar waya da saurayin na ta ya gwangwaje ta da ita.

Mama sai juya wayar take cikin farin ciki "Mijin aure ya zo A'isha, ni dama Sabi'un nan da kika ƙwallafa rai a kansa ban ga abin a gaishe ku ba, wani yaron shago a ka yi me na sama ya ci ballantana jeho mini.

Sai an ce ba shi da abin yi ki tattare ki ce a shagon yayansa yake.

Ai nan bakina ya suɓuce na ce

"Mama ki kula da A'isha ki tuhumi shi wannan da ya zo yake ta famar kashe mata kuɗi da wacce ya zo, ko wata ba a yi ba dubi dukiyar da ya kashe mata. Ki ja mata kunne Mama ta kula da mutuncinta kar ya yaudare ta da abin duniya.

U'uhum, ni Hanne."

Mama ta fadi tana dafe haɓa gabana ya yanke ya fadi don na san na yi katoɓara.

"Ai ba sai kin yi haka ba zan san kina baƙin ciki da A'isha za ta yi aure ta bar ki!

Baƙin ciki! Na furta kalmar da ƙarfi hawaye na wanke fuskata.