GANIN IDO

PAGE 58

by @oumameer2671

GANIN IDO 🥀🥀

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

AMEENA IBRAHIM

OUM-AMEER

*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewapen:@Oumameer2671

FREE-BOOK

PAGE 58

Wani irin matsanancin tsoro ne ya dabaibaye masa zuciya a lokaci ɗaya, domin yanda yaga wani irin ɓacin rai da ya bayyana ƙarara akan fuskar Ya Mohaa ɗin ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba.

Wato a irin wannan mugun yanayin da ake ciki, ko wuƙa a ka ɗora masa akan maƙogoransa yasan cewa ba zai iya faɗar wai dalilin da yasa yake bibiyarta ba.

Cewa zai yi don yana sonta yake bibiyar ta ko me? Ko kuma cewa zai yi yaga shi ɗin bai cancanceta ba sai ga shi? Hmm! Wai aka ce wuya makarantar Kare.

Da ya buga ya buga yaga cewar dai he has no way to escape yasa ya zube akan gwiwoyinsa murya cike da zallar magiya ya ce.

"Sharrin shai ɗan ne kawai...wallahy sharrin shaɗain ne. Dan Allah ka yi haƙuri,wallahy daga yau ba zan sake ba."

Girgiza kansa ya yi yana faɗin.

"A'a kam! Duk tsawon lokacin da ka kwashe kana bibiyar ta, taya ya rana ɗaya za ka ce mini ka daina kawai in yarda da kai. Yan da ka jure ka ke ta wahala haka na zaman bibiyarta dole dai kana da wani dalilin da yasa kake bibiyantan."

"Wallahy tallahy, na rantse da Allah, billahillazy ba komai, kawai sharrin shai ɗan ne..."

"Shi ne wanda yake ƙawata maka matar tawa ko? Hmm! Ka kuwa san rayuwar waye kake bibiya? Duk da da cewa a wannan lokacin ka samu ka kuɓuta da ƙyar wato ashe bai ishe darasi ba. Mata ta itace komai ta wa, duk wanda yace zai raɓeta da wani sharri kuma! To tabbas mutuwa za ta fiye masa alheri a cikin rayuwarsa."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Dan Allah yallaɓai ka yi haƙuri..."

Bai san ya akayi ba, cikin en daƙiƙu kaɗan yaga sojojin sa sun zagaye da bindiga suna jiran umarni.

Cikin gidan ya wuce direct ya bar su a nan ba tare da yi musu wani bayani ba.

Ni kuwa, ina nan na zauna parlour tare da twins ɗina inda muka ci uban gayu sai farin ciki muke. Suna nan na zaunar da su duk da cewa zaman bai gama nuna ba da kayan wasan su wanda Bahrain da Ya Hamza basa gajiya da zuwa kasuwa wurin siyowa, wata haukar ma sai ta baka dariya, yi ni suke wasa da su matuƙar dai suna gida ba su fita ba. Shiyasa Ammie ke cewa da a nan za su ci gaba da zama har su yi wayau da tabbas su Ya Hamza sun haukatar da su.

Ina ganin shigowarsa sai da na ji wani abu mai sanyi ya ratsa cikin xuciyata wanda ya saka na lumshe idanuna sannan na buɗe su a hankali na taka na je na rungume shi na ce.

"Welcome home my LOVE. Na saba yi maka barka da zuwa a duk lokacin da ka dawo gida....yau kuma da ni da yaranmu muke maka barka da zuwa...Welcome home DADDY."

Tun da ya ɗaura ƙwayar idonsa a kanmu, sai da ya ji wani sanyi ya ratsa duk wata gaɓa da jijiyar jikin sa. Wai shi ne a yau ya dawo gidansa ya tarar da matarsa da 'ƴa'ƴansa? Ashe akwai irin wannan lokacin da zai zo a gareshi watarana. Tabbas komai yana da lokaci muddin ka yi haƙuri ka saka Allah a cikin al'amarinka...

"Why are you quite?"

Saukar ɗumin hawayensa na ji a gefen wuyana. Sannan ya ɗago fuskata a hankali ya kalli ƙwayar idanuwana sai kuma ya kalli su Arhaam sannan ya sake kallona cikin wani irin yanayi ya ce.

"farin ciki ne Ya hanani Magana Bibi. Wani irin yanayin farin ciki na ke ji na a ciki wanda ban san ma abin da zance ba...Kin haskaka rayuwata kin sauya mini duniya. You are different Bibi!"

Murmushi na yi masa na ce.

"Alhamdulillah Ala kulli-hal!"

Maimaita kalmar ya yi sannan ya kalle ni a nutse ya ce.

"Bibi...na san Jafaru, nasan irin alaƙarku ta maƙotaka da kuma irin zumuncin da ya ƙulli har yanzu a tsakaninku. Amma ina so ki faɗa mini  da bakin ki gaskiyar abin da yasa yake bibiyar ki daga baya....bai kamata Sam ace zancen sa ya shigo a cikin rayuwarmu a irin wannan lokacin da muke tsaka da farin ciki ba. Amma kamawa ta yi ki yi haƙuri. "

Ban san lokacin da wasu hawayen baƙin ciki suka wanke mini fuska ba. Cike da takaicin sa na yi masa bayanin komai da ya wakana tun wancan zuwan har ranar da akace ya zo nemana a daren suna.

Hmm! Wato wani irin mummunan yanayi ne ya bayyana akan fuskarsa wanda sai da ya saka na ji a raina dama ban faɗa masa ba.

Wani irin zafi ne ya ji yana ratsa ƙirjinsa har zuwa fatar jikinsa tsabar yanda ya ji kalaman masu kama da feshin wuta a cikin kunnuwansa.

Wayarsa naga ya ciro yana faɗin.

"Ku yi masa mugun dukan da sai kamanninsa sun sauya sannan ku rufe mini shi..."

Wayar na karɓe jikina na wata irin ciccira na ce.

"Ku harbe min shi! Ku saka bindiga a tsakiyar kansa ku harbesa, kafin ku aiwatar ku faɗa masa cewa saƙo ne daga Beenafah..."

Da sauri ya fisge wayar yana mai mini wani kallon mamaki ya yi sauri ya ce.

"No, don't kill him. Kui masa duka sannan ku rufe mini shi..."

Wasu zafafan hawayene suka biyo saman kumatuna domin sam ni wannan decision ɗin bai mini ba, na so ace an kasheshi domin sam na san har abada ba zai daina bibiyata ba tunda shi ɗin jahili ne, munafuki mai fuska biyu. Jin da gaske ya sauya hukuncina yasa na karye wuyana still da hawaye a fuskata na ce.

"To don Allah kada a bar mini shi a cikin gidannan, domin idan har ya kwana a nan to burinsa ya cika na kwana a inuwa ɗaya da ni. A yi nesa da shi dan Allah."

Jinjina kansa ya yi ya ce.

"Idan kuka gama dukansa..take him to police station, ayi masa azaba mai tsanani."

Yana kashe kiran ya je ya ɗauki Arhaam wanda yake wasa da kuka a lokaci ɗaya alamar ya gaji da zaman, Aryaan na ɗauka nima na fashe da dariya ganin da yake ta wani diri yana dariya na kalli Arhaam na ce.

" Kaga Aryaan yafi ka wayau, domin dariya yake yana welcoming Daddy kai kuma sai wani taɓe baki kake kana kuka.."

Dariya ya yi tare da ware ɗayan hannun sa muka shige ya zagayemu yana faɗin.

"Shi ma ai haka ne a wurinsa. Alhamdulillah! Da sabuwar rayuwar da zamu shiga. Allah ya amintar damu ya bamu zaman lafiya."

"Amin yah ubangiji."

Haɗa masa su na yi sannan na je na kawo mana kayan abincin na baje su a nan,muka zauna muka ci. Bayan na dawo ne ina haɗa musu madara yana ta kallona na yi murmushi na ce.

"Ya dai?"

Jinjina kansa ya yi yace.

"Kin yi kyau sosai. Ban ga wata mace mai kyaunki ba a duniya Bibina.."

Dariya nayi sannan na ce.

"Duk Mazan duniya haka kuke cewa..."

"And every man Idan kika ji ya faɗi haka, to ki yarda cewa shi abinda yake hannun sa, yake zuciyar sa kaɗai ne ya yarda da shi."

"Uhmm! To na gode. Kai ma ka yi kyau sosai..."

"Yanda kika ce kenan."

Bowl ɗin na miƙo ina faɗin.

"Na baka ka ciyar da su.."

Zaro ido ya yi sannan ya yi dariya ya ce.

"What! No...kada na shaƙa musu a hanci."

Dariya na yi ina jinjina kaina na ce.

"Hardai Aryaan, wallahy idan ba ka yi da gaske ba, sai ka shaƙa masa a hanci saboda gadauniya da rashin zama wuri ɗaya."

Matsowa ya yi a kusa damu ya taimaka mini ina basu yana ta dariya ganin yanda muke ta drama, Idan na yi da wannan kafin in waigo wannan ya kama wani abun na daban, a haka dai har muka gama sannan na gyara musu muka wuce ɗaki domin yi shigar da su bacci.

Dariya na yi tuna abinda na faɗawa Suwara ɗazu na ce mata maganin bacci zan ba su domin kada su shiga rayuwata da ni da mijina a yau. Da haka na yi ta addu'a a raina ina roƙon Allah yasa idan suka yi baccin nan kada su farka a yanzu sai na gama bai wa mijina farin ciki da na ƙudurta da shirya masa a wannan daren.

Shi dai yana tsaye tun ɗazu yana kallona ganin yanda nake ta lallaɓa su suna shan Nono har na samu Allah ya taimakeni suka yi baccin.

Bayan na gama tofesu da addu'a na taso ne na ji ya rungumeni a hankali ya ce.

"Thank you for everything Bibi...you are the best mother ever. Allah ya baki lada akan duk wata hidimarki akan su da kuma ni..."

Murmushi na yi tare da saƙalo hannuna cikin wuyansa ina kallon idonsa na ce.

"And thank you for being the best Husband and Super Daddy. Allah ya ci gaba da kare min kai a duk inda ka shiga a faɗin duniyar nan. Allah ya ci gaba da baka halal ɗinka komai ƙanƙantarta ya kuma kare daga sharrin haram komai yawanta..."

"Amin.."

Saukar da hannuna na yi na saƙala a cikin nasa ina masa wani kallon na ce.

"Can we?"

"Anything special?"

Lips ɗina na kai a hankali na goga a nasa sannan na janye tare da kashe masa ido na ce.

"We are gonna burn in fire today..."

Cikin wani irin yanayi ya jinjina kansa yana mai riƙo kwankwasona ya ce.

"And Dayaa is ready to burn in fire..."

"Let's go..."

Tun a wurin wanka ya tabbatar da kalamaina domin na bashi mamakin da sai dinga kallona yana jin na koma masa wata Bibin ta daban a yau. Bayan mun fito muka shirya inda a gabansa na ɗauko wata fitinanniyar Nighty wacce tun ɗazu na gama jiƙeta da sihirtaccen ƙamshin da na shirya masa. Bayan na saka na zare ribom ɗin kaina na zubo gashina kamar yanda na san yana burgesa.

Kallona yake yana mai jin duk wata gaɓar da ke jikin sa tana amsar saƙona yanda ya kamata.

Rigar da ke jikina da ita da rashin ta duk ɗaya, maimakon shi da ya saba fara kawo mini far miki, ni ce nan yau na nemi na zautar da shi da wata kalar zazzafar soyayyata wacce ya ji ta a yau har can cikin ƙololuwar birnin ransa.

Zallar madarar ƙauna muka zuba mai matuƙar daɗi da sanyaya zuciya. Bayan mun kambala mun yi wanka ne na je na ƙara duba su Arhaam wanda duk tsawon lokacin nan suna nan suna bacci abin su sannan na juya na koma a hankali na kwanta a jikinsa tare da ɗora kaina a ƙirjinsa.

Ji na yi ya rungumeni tare da kissing lips ɗina a hankali ya ce.

"Thank you for the Love we made today...kin bar ni wani tarihin da har abada ba zai goge mini ba kamar yanda farkon tarayyarmu ta kasance a tunanina...you promise us to burn...and we burn Happily...thank you."

Shiru na yi tare da ƙara narke masa  ba tare da na ce komai ba. Sai dai kalamansa sun yi tasiri a zuciyata sosai, da wannan farin cikin na yi ta murmushi a raina har na yi bacci.

Shi kuwa, gabaɗaya baccin neman sa ya yi ya rasa a wannan daren tsabar yanda ya ji duniyar ta yi masa daɗi.

Bayan ya tabbatar ta yi baccin da gaske, nan ya lallaɓa ya zame ta gefe tare da lulluɓa mata Duvet ya saka pillow ya tare da kada ta ji ta ita kaɗai.

Sai da ya jima yana kallon fuskar twins ɗinsa yana ta zubo da hawayen farin ciki sannan ya tashi daga ƙarshe ya je ya yi alwala ya zo ya duƙufa yana ta nafila yana godiya ga Allah da kuma neman albarka da fatan cika da kyau da imani.

Yana nan zaune yana karatun Qur'an ya ji motsawarsu. Koda ya duba agogo ƙarfe huɗu saura ne na dare.

A hankali yaje ya tasheta taje wurin ta ji da su wanda sai da ya dawo masallaci yaje ya tarar ina ɓingire a nan na ci gaba da baccina tare da su.

Murmushi ya yi sannan ya tashe ni a hankali yace.

"Kin yi sallah ne?"

"A'a! An yi ne?"

"Ƙarfe shida da rabi fa..."

Dirowa na yi a raina ina faɗin ai yanzu salla ta daman sai wuraren ƙarfe shida zuwa bakwai nake yinta, duk yanda Ammie ke tashina sai na yi da gaske sannan nake iya miƙewar tsabar yanda bacci ke dagula lissafina.

Bayan na yi sallahr na kambala na kira Bibi domin ta yi musu wanka ta shirya su, sannan na wuce kitchen na duba mai girki, wacce ɗaya daga cikin chefs ɗin Ziza ne na Eatery ɗinta. Ɗayar kuma ita ce mai share-share.

Wanka na yi na shirya cikin wasu English wears na riga da skirt da hula sannan na je na gyara mana table muka je muka karya.

Haka muka yi ta mu huɗu muna ta rayuwarmu inda a nan muke ta ƙara sanin wasu abubuwan dangane da juna tsawon kwanaki uku.

Ina ɗaki da Arhaam a bayana ina duba wasu ayyukan Daddynsu Arhaam da ya nuna mini yace an kawo musu talla na duba na gani kafin ya mini bayanin yanda abun yake sai ga kiran Ammie ya shigo.

Hankali a tashe ba ta ko bari muka gaisa ba ta ce.

"Beenafah Jafaru ya ɓata, tun ranar da ya iso ya ajiye jakarsa ba'a ƙara sanin ina yake ba. Wayarsa kuma a kashe."

Kai tsaye na ce.

"Ni da Mijina ne muka kulle shi a police station...ni tun a ranar ma na so a kashe shi amma Daddynsu Aryaan ya hana...."

Cikin wani irin tashin hankali ta ce.

"Mi kika ce Beenafah? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Miye ya yi muku haka da zafi..."

"Ammie Jafaru bai da mutunci....kuma a can zai ƙare rayuwarsa har ya mutu."

"Dan Allah Beenafah ki yi haƙuri ki rufamin asiri,...kinga...ina shi Hammodin yake??"

Daga haka na ji ta kashe wayar wanda daga nan ban san mi ya faru ba, sai gashi ya shigo saɓe da Aryaan a kafaɗarsa ya kalleni ya ce.

"Ki shirya mu tafi police station ɗin. Ba dole sai na je ba, amma zan tafi domin wani dalili."

Sauke shi na yi na shirya cikin wani Lace da mayafinshi sannan na sauya musu kaya, sai da na gama duk shiririta ta sannan muka fito a tare muka shiga mota. Na yi mamakin ganin Convoy ɗinsa domin in dai a cikin gari ne daga ni sai shi muke fita a mota. Sai dai idan garin ne zamu bari zamu fita a irin wannan yanayin.

Koda muka isa mun tarar da su Ammie har sun Iso da su Maman Fakiha da Baba.

Tuni duk mutanen da ke wurin suka ɗauki saiti sai ya yi musu umarni da a fito da shi.

Ganin yanayinsa kaɗai sai da ya sanya su Ammie fashewa da kuka mai tsanani. Domin baka ma gane fuskarsa muddin ba ka yi masa kyakkyawan sani ba.

"Jafaru! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Wai miye yake faruwa ne??"

Cewar Ammie tana mai kallona da ni da Daddynsu Arhaam.

"Kowane irin laifi ya aikata muku ai bai cancanci wannan hukuncin ba. Shi fa tamkar ɗan uwa yake a wurinku..."

Wani kallon ya yi masa sannan ya ce.

"Wannan dalilin ne yasa har kika iya ganinsa a nan Hajiya. Ba don hakan ba da yanzu wani zancen ake na daban....Kai! Ka buɗe baki ka faɗa musu laifin da ka yi, komai da ka aikata bana so ka rage musu, idan ba haka ba, zan saka ka a motana na tafi da kai wata duniyar da har abada ba za ka taɓa mantawa dani ba."

A somaye ya buɗe bakin sa tsabar yanda ya sha baƙar wahala ya ce.

" Zan faɗa! wallahy zan faɗa dan Allah ka yi haƙuri na tuba."

Yawuna na tofa masa ina mai yi masa kallon tsana na ce.

" Ashe kai ɗin marar kunyar ƙarya ne matsoraci. Ba ka ce a shirye kake domin akan son da kake mini ba koda za ka mutu ba? Miyasa kake magiya kana bada haƙuri a yanxu?"

Hannu Mama ta ɗora a ƙirji tana mai doka wata irin taslima sannan ta ce.

"Yanzu ashe duk tsawon lokacin nan ba ka ji maganata ba Jafaru? Duk yanda na tsawatar maka akan wannan shashancin baka saurare ni ba ashe?..."

Kallon Police ɗin ta yi ranta a ɓace tace.

"Yallaɓai! Ni ce nan mahaifiyarsa, wannan kuma mahaifin sa. Ku ɗauke shi ku mayar da shi cikin Cell ku yanke masa duk hukuncin da ya dace da rayuwarsa mun baku dama.."

Jinjina kai Baba ya yi ya ce.

"Wallahy ni ma nan na baku dama! Marar mutunci wanda bai san harkar girma ba..."

Rai babu daɗi Ammie ta ce.

"Kayya! Dan Allah ku saurara Haba..."

Kuka Jafarun ya fashe da shi sannan ya ce.

"Dan Allah ku yi hakuri, wallahy daga yau har abada ba zan ƙara kallon ma inda take ba..."

"Sai fa ka buɗe bakinka ka yi musu bayanin irin cin zarafi da toxarcin da ka bi ta da shi. Bana so wani ya riƙe ni a rai ya yanke min hukunci da cewa saboda ina da kuɗi ina iko na ci zarafin ka. Na fi ƙarfinka ta kowace fuska, waɗanda suka fika komai sun buga dani sun bar ni ballantana kai wanda ko a silifas ɗina ban kawo ka ba. "

" Ai zan faɗa musu. Wallahy zan faɗa..."

Daga nan ya zayyane musu duk irin yanda ya yi ta bibiyata da irin nasarar da ya samu ta haɗamu husuma da kuma bibiyata da ya riƙa yi a waya, har zuwa wurin bokan sa bai rage komai ba.

Kuka sosai Mama take tana faɗin.

" Allah ya isa tsakaninmu da kai Jafaru! Allah ya wadaran rayuwarka. Abin da kake yi kenan ashe bayan duk nasiha da jan kunnen da na yi maka. Mi kake da shi mi kuka kake taƙama da shi da har ka sanya kanka a cikin wannan masifar ka nemi rabata da gidan auren ta? Ashiru ma da ya fi ka sanin zafin ta ya turo neman aurenta Allah ne bai yi ba, sannan yana da sana'arsa yana da madogararsa, ya haƙura da ita ya yi mata fatan alheri ballantana kai...maimakon ka ɗauki maganar iyayenka ka haƙura ka je ka yi karatu ko don gobenka, shi ne kaje ka lalata karatun ka cinye kuɗin registeration har sau biyu, kana ɗaukar kuɗin kana kai wa wani ƙaton boka ƙaton mushriki saboda shafewar basira. Allah ya isa ban yafe maka ba duniya da lahira, ka je tunda ban isa da kai ba shi ke nan. Zumuncinmu kuma tunda ba kai ne ka haɗa ba, wallahy ba ka isa ka raba mana shi ba."

Daga haka ta miƙe daga kan bench ɗinda take zaune ta yi tafiyarta. Duk kiran da Ammie ke mata bata tsaya ta waiwaye ta ba.

Itama Ammien jiki a sanyaye ta kalle shi ta ce.

" Jafaru ba ka kyauta ba. 'ƴar tawa ka ke ta bibiya ashe kana bin ta da sharri? Yanxu kai ba ka ji kunya ba? Da ace Fakiha ce ko Farisa wani ya dinga mata haka ya za ka ji a ranka?"

Ajiyar zuciya Ya Mohaa ya sauke sannan ya ce.

"Ku zama shaida...dukkanku ku zama shaida..idan har ya sake bin koda inuwar inda matata ta taɓa, to lallai ba zan tsaya tunani na biyu ba a kansa."

Daga haka ya ja hannuna muka fice wanda a lokacin har an fara kiran sallar Magrib. Gidan Hajiyarsa muka wuce inda sai da muka shiga bakin Main door ya ce na yi musu sallama domin gobe zamu tafi, kuma asuba zamu yi.

Ina jin haka na ce masa Allah ya kaimu rai da lafiya. A raina kuma nace ni dai Jafaru ka ja mini salalan tsiya, bukin Fakiha da Ya Ashiru da nake buri da saka ran a ɗan jira na yau ka gwanɓale mini shi.

Ina shiga muka gaisa ya fita masallaci ni kuma na tsaya nan inda Hajiya wacce ta cika da farin ciki ganin Abeer da Mima suna yi wa su Aryaan wasa. Wurin Munira na zagaya muka gaisa, nan ta shaidamin cewa na aurar da Haulatu tana Mafara aka kaita. Allah sanya alheri na yi mata sannan na fito shaf-shaf na shiga sashensu Aunty Ziza ita da Suwara.

Zaune na tarar da su da paper da Biro a hannun Suwara.

"Miye kuke yi?"

Dariya suka yi sannan Aunty Ziza ta ce.

"Girke-girke ne nake koya mata Theoretically, kafin mu fara practical.."

Jinjina kai na yi ina murmushi na ce.

"Mun yi mubaya a domin kujerar ki ce,kuma mun bar miki kayan ki. Allah ya ƙara basira da zaƙin hannu. Gaskiya na yi farin cikin ganin yanda kuka haɗe kanku haka. Allah ya ƙara muku zaman lafiya ya ƙara buɗe Ya Emraan hanyoyin arziki..."

Hannuna Aunty Ziza ta riƙe tana wani irin murmushi ta ce.

"Ina mai ƙara baki haƙuri Beenafah. Muma ɗin nan muna alfahari da samun ki kuma muna gode miki, domin shigowarki rayuwarmu ce wasu abubuwan da yawa suka sauya. Alhamdulillah da irin samun mijina a lokacin da yake Naval officer, a yanxu ma Alhamdulillah zan ce domin samun sa da darajarsa sun ƙara yin sama, ta dalilin ki da yarjewar ubangiji ga shi zamu ƙara yin gaba muma zamu koma UAE da zama,... "

Cikin wani irin farin ciki na ce.

" Dan Allah da gaske kike? Yaushe?"

Dariya Suwara ta fashe da ita ta ce.

" Ni fa daɗina dake azarɓaɓi Aunty Beenafah."

"Wallahy kin ji na rantse miki bani da wannan labarin.."

Aunty Ziza na dariya ta ce.

"Sai Suwara ta haihu tukun.."

"Wayyo Allah daɗi. Allah ya nuna mana ya sauketa lafiya. Mu gobe zamu tafi in sha Allahu, sai kunxo. Don dai kam, nasan abun da zai dawo damu ƙasar nan ba kusa ba."

"Allah ya kai lafiya. Idan kin je muna gaishe da Mijinmu..."

Dariya na yi sannan na ce.

"To a nawa?"

"Ko nawa kike ce."

Cewar Suwara tana dariya.

Waje na nufa ina faɗin.

"To ba za a faɗa ɗin ba. Ku da yanzu haka ma baku fi minti biyar da gama magana da shi ba, shi ne za ku wani aike ni da saƙon renin hankali. In ƙulle gaisawa ta fatar baki daga nan har Dubai saboda ga Beenafahr iyayi."

Dariya suka bini da ita har muka shige sashen Hajiya sannan muka sallar Isha muka fito har mota suka rakamu.

Bayan mun fito gidan Ammie muka wuce itama na yi mata sallama. Ta ji mamaki da ta ji zancen tafiyarmu wai gobe-gobe. Amma kuma tuna irin abin da Ya Jafaru ya yi sai ta ga cancantar hakan, duk da cewa an kai ƙarshe da shi kuma yayi alƙawarin ha zai ƙara ba. Sannan aka sake shi Baba ya riƙa shi shi da Ya Hamza suka kai shi asibiti.

Kallon yanda Bahrain yake ta wasa da su Aryaan na yi ina murmushi na ce.

"Za su yi kewar ka Uncle Bahrain..."

Hawaye na gani a idonsa sai kuma ya yi murmushi ya ce.

"Tun ranar da kuka tafi gidanku na ke kewar su ai."

Dariya Ammie ta ce.

"Ai a ranar kasa bacci ya yi, sai ga shi ya dawo ɗakina ya kwanta wai kewar yaransa ta hana shi bacci."

Dariya na yi na ce.

"Allah sarki uncle Bahrain! To ko dai na bar maka su?"

"A'a, ki dai bari idan lokacin cire su a Nono ya yi ni zan je da kaina na dawo da su."

Fira muka ɗan taɓa sannan daga ƙarshe Ya Mohaa ya shigo suka gaisa da Ammie, haƙuri ta ƙara ba shi sannan muka fito zamu tafi.

Kallon sa na yi na ce.

"Dan Allah ina neman alfarmar 5M"

Jinjina kansa ya yi ya ce.

"Cash kike so ko transfer?"

Kallon sa na yi da mamaki na ce.

"Ba za ka fara tambayata mi zan yi da zunzurutun kuɗi har haka ba?"

"Har abada ba zan tambaya ba, ai daman tun da muke baki taɓa tambayata kuɗi ba. Yau ɗin ta kasance mini rana ta musamman. Duk abinda kuma za ki yi da su,na san mai muhimmanci ne..."

"To na gode, Allah ya saka da alheri ya ƙara arziki."

Ya Hamza na ce ya bini ya karɓa kuɗin sannan na koma ciki na cewa Ammie.

"Ammie zan ba ki kuɗi dan Allah ki ba wa Ya Ashiru hannunki da nasa."

Jinjina kanta ta yi tace.

"In sha Allahu kuwa. An gode, Allah ya amfana."

"Amin Ammiena, sai da safe."

Bayan mun fito sai da muka biya ta gidan Daddy ya yi wa Mummy gaisuwa sannan muka biya gidan Aunty Labiba sannan bayan mun koma gida Ya Hamza ya zo tare da Bahrain suka karɓi kuɗin suka wuce.

Washegari tun asuba kuwa muka fita har da Biba a wannan karon. Kaduna muka yada zango inda muka kwana ɗaya gidan Aunty Nadeeyah kamar yanda na roƙi alfarma sannan shi kuma ya je ya duba aikinsa sannan muka wuce Abuja muka wuce.

*******

Su Ammie kuwa, sai da ta tsaya aka yi bukin Fakiha da Yaya Ashiru wanda ya ji matuƙar farin ciki na zuwa bukin sa da ta yi sannan ga kyautar kuɗi har 10M daga gareni wanda ni ma kaina ban san 10m ɗin ba ne, ni dai kuɗi na tambaya kuma na ɗauka su aka bani ashe ashe an ninka mini.

Ya yi matuƙar farin ciki da shi iyayensa da en uwansa ba kaɗan ba. Sai godiya yake yana faɗin dan Allah ta isar da saƙon godiyar sa zuwa gare ni.

Bayan an kammala bukin da kwana biyu suka juya suka koma gida tare da su Ya Hamza har da Aunty Hussaina wacce ta dinga kuka akan cewa ta tafi da ita kamar yanda ta saba a da.

Cikin dangi aka binciko yara guda biyu aka kawo wa Mummy Zaliha, sannan kuma aka kai Kayan auren Ya Hafiz wanda za'a yi nan da wata uku.

Wanda idan an yi auren ne yace zai kai ta gidansa domin matarsa ta ci gaba da kulawa da ita.

Nan ne Ammie ta bashi shawara akan cewa ya sake komawa makaranta tun da wancan da ya yi ya riga ya zama wasted. Amma idan ya jona in sha Allah ba jimawa zai ga ya kambala.

*******

Muna komawa da sati ɗaya ya koma aikinsa wanda ya dawo fita sau uku a sati, Monday, Wednesday da kuma Friday.

Rayuwa muka sake shimfiɗawa sabuwa mai cike da zallar farin ciki muna renon yaranmu.

Muna nan tsawon wata uku wanda a lokacin ne su Aryaan suke watan su na bakwai a duniya. Ina kitchen tare da Madam Amima tana haɗa breakfast ya kira ni a waya.

Ina shiga na gansu yana kwance su Aryaan na ta hawansa suna tsalle-tsallensu na ce.

"Miye wani gani ga gaka amma sai ka kirani a waya?"

Murmushi ya yi mini sannan ya ce.

"Because. Tomorrow, is going to be special. Very, very special."

Cikin farin ciki na ce.

"Wow! Tun ban ji ko miye ba na ji cewar something special ɗin ya yi deeping in to mah heart..."

Kinkimar Aryaan na yi na kashi wurin Biba da sauri sannan na dawo na tallabi Arhaam shi ma na kai shi tare da buge mata warning na ce kada ta kira a waya da sunan suna kuka. Dariya ta yi sannan ta ce shikenan to.

Ɗakin na dawo na kulle ƙofar na jinjina a jiki ina masa wani kallon ina murmushi.

Tasowa ya yi yazo ya yi trapping ɗina tare da matso da fuskarsa ya ce.

"No questions..just trust your Husband."

Maƙalƙale wuyansa na yi tare da haɗe bakinmu wuri ɗaya na bashi wani zazzafan kiss Sannan na janye ina kallon ƙwayar idanunsa na ce.

"Da wannan daddaɗan albishir...Let's get down to bed...i promise to feed you with the best breakfast..."

"And I will for ever be grateful BibiLove."

Kan gado muka faɗa na kashe sa da zazzafar ƙauna sannan muka yi wanka a tare muka fito.

An yi mini albishir ɗin da ban san ko miye shi ɗin ba. Sai da gari ya waye yace mu shirya zamu tafi.

Sai da muka hau jirgi sannan na kallesa na ce.

" Wai dan Allah ina ne muka nufa haka?"

Pcap ɗinda ke kansa ya cire ta ya ɗora a kaina yana murmushi ya ce.

"we are travelling to the world for you...just you only...trust your Husband,  I assure you za ki ji daɗi sosai."

Murmushi na yi tare da jinjina masa kai na nace.

"Thank you Dayaa. Thank you for loving me."

Tafiya muka yi mai ɗan nisa sannan muka sauka a wani Private island resort. Kyakkyawan farin yashi ne malale a wurin, ga pure Crystal blue water suna ta tsalle gwanin burgewa. Haɗaɗɗen wuri ne mai daddaɗan yanayi wanda ban taɓa zuwa ba.

Kallon sa na yi cike da farin ciki na ce.

"Farin cikina, wannan wace duniyar ce muke?"

Hannuna ya sumbata yana murmushi ya ce.

"Where every queen deserves to celebrate her birthday...Maldives...The land of blue waters. Romantics nights...and unforgettable Love."

Hannuna ya ja ganin yanda na sanƙame ina ta murmushi yayin da wani irin tsabar daɗi ya ƙumeni.

Ya ce.

"Mu huta tukun."

Haɗaɗɗen lounge muka shige wanda ya kama mana na musamman, bayan an gama shigar mana da kayanmu, mukayi wanka muka ci abinci, muka yi sallah sannan muka zauna zaman hutawa.

Sai da dare ya yi misalin 11:30pm, wanda resort ɗin ya ɗauki wani haske da sheƙi gwanin burgewa sannan muka shirya cikin wata shigar da ban taɓa ganin irinta a jikin sa ba ya ja hannuna zuwa wani kewayayyen wuri da aka ƙawata na musamman. Ga wani romantic music da yake tashi a hankali wanda ke saka zuciyoyi amsawa da kuma zama yardajjin juna.

Fireworks ne suka tashi sama suna tartsatsin wuta a lokacin da 12:am dot tayi clocking.

"Happy birthday my queen BEENAFAH..."

Kallon sa na shiga yi babu ko ƙyaftawa yayin da rai na da ruhina suka amsa da wannan farin ciki mai sa kuka. Hakan yasa ban san lokacin da wasu hawayen suka shiga wanke mini fuska ba wanda ban ɗauke idona ba har saida rubutun ya ɓace a hankali wani ya fito da zanen.

"Happy Birthday Bibina....I love you."

Ji na yi ya ɗoramini kanbu a kaina sannan ya kama hannayena ya sumbata. Ya sumbaci goshi na zuwa lips ɗina zuwa wuyana Sannan ya yi mini murmushi ya ce.

"Wish you many many wonderful years ahead sarauniyata."

Hawayena ne suka ƙaru sannan na rungume shi sosai ina mai jin wani abu na musamman a ƙirjina. Sosai yau ya tuna mini da Abbie...ni mi zance da wannan mutumin da ya wuce in yi ta masa addu'a ta alheri ina faranta masa ransa da ƙaunar duk abinda yake ƙauna a duniyar nan dama lahira inda can ne matabbata.

Wata diamond necklace ce mai numfashi ya fito da ita ya ɗoramin a wuyana yana murmushi ya ce.

"Wannan Gift ɗin mijin ki kenan Bibi..."

So nake in daina kukan in gode masa, amma kuma na kasa dainawa.

Girgiza kansa ya yi tare da saka hannunsa ya share min hawayen yana murmushi ya ce.

"Haba Bibi! Wai miye haka ne? Muna ta abin farin ciki ke kuma kina zubo da hawaye...oya! Maza maza ki haɗiyesu, ko kaɗan bana son ganin hawaye a nan. Ba wurin su ba ne. Farin ciki ne kawai ya kawo mu nan ɗin."

Hannu na saka da sauri na goge hawayen, tare da fatan Allah yasa kada su zama marasa jin maganar mijina, domin idan suka yi yunƙurin ƙara zubowa tabbatas ba zan taɓa gafarta musu ba.

Hannunsa na kamo na yi twisting a nawa, happily na jinjina masa kaina ina murmusawa na ce.

"Ban san waɗan ne kalmomi ne zan yi amfani da su wurin gode maka ba. But...abinda na sani kai ne rayuwata, kai na daban ne a duniyata, ina ƙaunarka..."

Murmushi ya yi ba tare da ya saki hannun nawa ba ya ce.

"Since the day I married you...my life become complete...you gave me peace, you gave me two beautiful souls Aryaan and Arhaam, and...you are my whole world..i will keep loving you , until we grow old together, har abada matsayin ki ba zai canza ba."

Rungumesa na yi tare da fashewa da kuka ina faɗin.

" Please allowed me....dan Allah karka hanani kuka ka ji...wannan na zallar farin ciki ne, I love you."

Wayarsa ya ciro ya kira, ban ankara ba kawai na ji murya su Ammah suna mini Happy birthday. Cikin farin ciki na amsa su sannan ya kashe ya kira su Jadda..da haka haka sai da ya kira kowa da yake namu suka tayani murnar zagowar ranar haihuwata.

Na yi farin cikin da ban taɓa jin irin sa a rayuwata ba, wannan duniyar da wannan ranar sun kasance na musamman a cikin tarihin rayuwarmu. Har abada ba zan daina alfahari ba, domin miji ne wanda ya cancanceni nima na cancancesa.

Sai da muka yi sati ɗaya cif muna nishaɗi sannan muka juya muka koma gida.

Haka rayuwa taci gabar mana da tafiya har sai da Su Arhaam suka ci ka shekara ɗaya cif wanda a lokacin ne shima Bahrain ya zana jarabawarsa ta kambala secondary school.

Nan suka shirya suka zo inda nake a karon farko tun bayan aurena da Ya Mohaa.

Tare suka zo ita da Bahrain, Ya Hamza da kuma Aunty Hussaina.

Bahrain hadda kukan farin cikin yanda yaga su Arhaam suna gudu akan ƙafafunsa ko'ina.

Sai taɓara yake musu shi da ya Hamza su kuma suna dariya.

Kwana biyu suka yi muka shirya a tare muka wuce Qatar wanda shi ne zuwana na farko su kuma Ammie na biyu.

Garin ya ƙayatar dani matuƙa musamman gidan kakanni na da ya kasance na musamman. Abiyh ya yi kukan farin ciki sosai da zuwanmu.

Ni kam muna isa ko kwana ɗaya ban yi a gidan ba na bi Annie muka wuce gidanta ni da twins muka kwana sannan washegari muka shirya har Ammie muka haɗe gidan Noura inda ta yi aure gidan wani bawan Allah mutumin kirki da shi.

Munsha zumunci mun zaga Qatar mun yi yawo mun buɗe ido na tsayin wata ɗaya sannan muka shirya da nufin ƙetarawa zuwa ƙasar Yemen. Sai ranar za mu fito ne naga Aunty Hussaina da Raihab suna magana wanda ni dai jikina ya gama bani cewa akwai wani abu. Hakan yasa ban yi ƙasa a gwiwa ba na tambayi Ammie wacce ke riƙe da hannun Aryaan na ce mata miye tsakanin Aunty Hussaina da Ya Raihab. Kai tsaye ta ce mini ta ba shi ita, aure za suyi daga zaran mun koma gida.

Wallahy sai da na yi kuka saboda murna, Aunty Hussaina tana bani tausayi a rayuwa. Musamman yanda aka yi ta fasa auren ta samari kuma suka janye. Ashe rabon babban mutum ce ita mai babbar harka Raihab Abdulmajeed. Ga kuɗi ga Addini domin babban Ustaz ne bawan Allah wanda idan ya fara kwararo maka karatun Alƙur'ani mai girma sai ka ji kamar ka sume tsabar daɗi da ƙwarewa.

Yemen da muka sauka, Ammie ta yi kuka sosai lokacin da ta yi ido biyu da Ummie wato matar Sheikh da kuma en uwanta su Nina.

Sheikh ya yi matuƙar farin ciki da ganinmu musamman ni da ya gani da yara, wai ni 'ƴar Mulaifa ce har da jikoki.

Ammie bata san ma mi za ta yi wa Sheikh a duniyar nan domin faranta masa ba. Ya riƙe ta tamkar uba Ummie ma ta riƙe ta tamkar ita ce ta haife ta. A yanxu dai iyayenta suna da hali da zarafin da ba ta isa tace za ta nuna musu wani iko ba, domin sai dai ma ita su bata,domin wannan zuwanma sai da Abiyh ya kawo takardu akayi rubuce-rubucen da ya mallaka musu abubuwa ita da Annie wanda ya ce mallakinsu ne domin shi bai san mi zai yi da wani abu ba a yanzu, rayuwar farin cikin da yake ciki kawai ta ishe sa. Sai dai yace Alhamdulillah.

Tambayarsa ta yi tace mi yake so ya ce mata baya son komai. Shi ganinta ma da ya yi a cikin farin ciki ya wadatar da shi.

Ya Mohaa aka yiwa magana akan ya tsantsara masa gida na musamman wanda zai kasance ita ce wacce ta gina masa a matsayinsa na mahaifin ta. Sannan ta bashi kuɗi da shi iyalansa kyauta ta ban mamaki. Bayan mun gama yin sati biyu muka wuce Canada inda gidanmu yake. A nan muka tarar da Dr. Basheer wanda ya shirya mana zama da mutanen kamfanonan kamar yanda yace a baya.

Nan muka yi zaman meeting ɗin na tsawon sati ɗaya domin har da na Wazeermed da FruitWave. Sannan bayan an akai matsayar komai an buɗe mana account ɗinmu. Sannan aka raba shares ɗinda za su riƙa a cikin account ɗin kowannen mu duk ƙarshen shekara. Sababbin ma'aikata aka sake naɗawa a nan NordicBag da kuma Abuja.

Bayan komai ya kambala muka wuce Sudan muka ziryace su na tsawon sati ɗaya sannan suka koma gida mu kuma muka wuce Saudiyyah Wurin Umrah har da Ya Mohaa inda muka yi ibada muka huta na tsawon wata ɗaya sannan muka koma gida.

Sannu a hankali muna tafiyar da rayuwar har su Aryaan suka cika shekara da wata bakwai. A lokacin ne aka cire su a Nono amma kuma ya ce bai yarda a kai su ko'ina ba a bar shi da yaran shi domin su ne farin cikin sa. Iyaka idan mun tashi mu shirya mu ziyarci su Aunty Ziza ko kuma su ziyarcemu da su Hairiyyah wanda a yanzu duk muka kasance a gari ɗaya.

Bayan wata ɗaya da Yayesu ya zo mini da Admission letter na shiga jami'a, daman ina nan ina classes a online har na samu ya samar mini takardun kambala secondary.

Cikin ikon Allah na fara karatuna a hankali komai yana tafiyar mini daidai, kwatsam sai kuma ga ciki. Sosai ya ɗaga hankalin sa musamman ganin sabon yanayi a tattare dani na tsananin rashin lafiya na laulayin ciki wanda ban yi shi a lokacin cikin su Aryaan ba.

Nasha baƙar wahala ga karatu ga laulayi wanda ban samu wani sauƙi ba sai da cikin ya gota watanni huɗu. Yaso na ajiye karatun nace masa a'a ya bari in sha Allahu zan lallaɓa.

To fa da gatan da yake mini da kuma kulawar en uwa da abokan arziki sai abubuwan suka ɗan sauƙaƙa a gare ni. Inda a kullum kwanan duniya ba na taɓa gajiya wurin godewa Ubangijina akan irin mijin da ya bani sai dai godiya da sambarka.

A haka na lallaɓa ina year two first second semester na samu ƙaruwar wani ɗa namiji wanda da kansa ya saka masa suna Abdallah. Domin yace mini yana son sunan a rayuwarsa.

Nan akayi shagali na musamman inda muka samu halartar wasu da yawa daga cikin dangi waɗanda kuma ba su samu zuwa ba, suka yi ta yi mana fatan alheri.

Haka na ci gaba da tafiyar da rayuwar iyalina wanda nake matuƙar nuna iyakar ƙoƙarina wurin ganin ban gaza musu da komai ba, duk da dai ita rayuwar nan ba za ka taɓa zamowa 100% ba sai dai ka yi abinda kake iyawa kabar wa Allah saura.

Shima Mijina yana iya ƙoƙarinsa a komai, lokacinsa, rayuwar sa da komai nasa namu ne akan gaba kafin shi, inda a yanxu suma su Aryaan an saka su a makaranta. Sannan Hajiya Batula ta dawo nan inda muke zaune kamar yanda na roƙesa, ganin irin albarka da yake ta samu da alheri, yasa ya manta komai, har jin cewa da yake ba zai iya zama da ita ba yanzu komai ya wuce a rayuwarsa.

Duk ƙarshen shekara muke shiryawa muna ziyara duk inda ya dace, birthday na ma da na su Arhaam idan ya tashi baya mantawa, daga zaran an tashi yake samun ƙasa ta musamman domin muje muyi celebration. Ya cika mini duniya ta da farin ciki ya bani dariya da walwala kamar yanda shi ma yake iƙirarin na yi masa.

A yanxu kullum lissafi nake wanda ni ka ɗai na barwa kaina sani sai kuma Allah. Saura kwanaki ashirin da ɗaya mu cika shekaru biyar cif da aure, wanda shi Sam ban taɓa jin ya yi lissafin wannan ba. To shi ne nake so nima in yi surprising nasa da bukin weeding Anniversary ɗinmu wanda zan shirya komai a ɓoye sannan in haɗa da bukin birthday ɗinss wanda a lokacin ne zai cika 52Yrs a duniya.

Ina so in faranta masa, duk da cewa a kullum cikin faranta masa nake, but I want this one to be different. Something that's gonna be special and unforgettable.

Wannan dalilin ne yasa na shiga neman shawarwari a wurin Raihab mijin Aunty Hussaina wacce ke da yarinya mace da kuma Bahrain da kuma Aunty Labiba da sis Noura.

✍️ OUM-AMEER ✍️