AMNA DA SAFNA

Part 13-14

by @zahratulqalam51

بسم الله الرحمن الرحيم. 
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 

🖤AMNA DA SAFNA🖤

Part1️⃣3️⃣▶️1️⃣4️⃣

📱Writing✍🏼
Aisha G Umar 
🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️



SAFNA. 

Tana dawowa daga Makaranta ɗaya daga cikin ma su aikin flower Habu, ya ba ta saƙon Marwan cewa,  "ya ce ki kai masa takalmin sa a wanke masa kan ya dawo, saboda shi zaisa da yamma, sannan...." tsaida shi Safna tayi da cewa  "where is the shoe?"  "ehh?" Ya furta saboda bai fahimci inda maganar ta dosa ba, "ina takalmin yake?"  takalmin mai matuƙar tsada brown colour ya ɗauko, ya miƙa mata yana ƙoƙarin sake magana, sai dai wucewar Safna ne yasa shi ƙunshe bakin na sa.

Safna kuwa, tasan Marwan ya bar mata aikin ne bawai haka kawai ba, ɗan kwanan nan da akayi ba tare da ya mata komi ba, ba daɗi yayi masa ba, tasan hanya ce kawai ta musguna mata da yake son yi, inba haka ba ko kuɗin aikin bai bata ba, sannan ga masu aiki da su ya dace ya bawa amma ya zaɓi ya ba ta.

Shiga gefen su tayi, tana gama dik abinda zatayi ta ɗauki kuɗin ta tafita dan kaiwa wani mai wankin takalmi da yake kusa da gidan, sai dai ta yi rashin sa'a saboda bata tadda shi ba.

cikin rashin jin daɗi ta dawo gida, da tinani meza tayi yanzu, aikuwa sai shawara yazo mata, na ta goge masa takalmin da tsumma da ruwa, wata zuciyar ta ce mata 'inkuma yaga baiyi ƙyalli ba fa?' aikuwa taba zuciyar ta amsa a fili, "sai in sha fa masa Mai".

Nan ta fara goge sa saida ya fita tas sannan ta je kitchen ta ɗibo Man-gyaɗa takoma gyafen ɗaki ta fara shafawa, sai da ta tabbatar yayi yadda ya kamata sannan ta kai wa Habu, saboda ba tason haɗuwa da Marwan ɗin.

ɗaki ta koma ta zauna a kan gado, kusa da Ammu da ke bacci hakan yasa ta jin kewa, ba waya take rikewa ba bere ya ɗau ke mata kewa, ɗauko Alqur'ani tayi tafara karan tawa cikin muryar ta me daɗin sauraro.

Ta ɗau awa uku, ba tare da ta dena ba, Ruki ce ta bankaɗo Ƙofar ɗakin ba tare da ko sallama ba dama al'adar su kenan' saida takai aya sannan ta juya gun Ammu, ganin bata farka daga bacci ba yasa ta sauke ƙaramar a jiyar zuciya, maida kallon ta tayi gun Ruki da ke yi mata kallon banza, tana kallon ta, ta kuma maida kan ta kan Qur'anin tana ci gaba da karatu.

Wani baƙin ciki ne ya bugi zuciyar Ruki, azuciyar ta take faɗin  "wato yarinyar nan girman kanta ne yayi yawa fa, saboda tsaban iskanci ni zata sha re?"  A fili kuwa tace  "to mai girman kan tsiya, Marwan ne ke kiran ki, kuma kina ɓata lokaci zaki sha jibga wallahi"  tana gama faɗin hakan ta fice daga ɗakin.

Zuciyar ta ne ya buga jin Marwan na kiran ta to me kuma? Me zai sa ya neme ta bayan ta gama masa aikin da ya bata? To ko don ba ita ta bashi da kanta bane?.

Ijje Alqur'anin tayi ta sa himar ta fito, ganin fitar Ruki yasa ta yin hanyar fita falon saboda tasan a can yake, domin ta san Ruki sai ta ji dalilin kiran da akayi mata, dan tasan ba banza ba, tsayawa zatayi in ta ga amma Safna abun mugunta sai tayi ta dariya, haka take da ma.

Nufan inda ta gansu tayi zuciyar ta cike da far-gaba, ta ɗaura idanun ta kansa da tin ɗazu yake mata kallon tsana, wanda dukkanin su suke yimata wannan kallon inka ɗauke Dady da kuma Yazeed.

"Na'am Yaya Mar..."  kan ta kaiga ƙarisawa, ya wanke mata fiska da mari wanda ya sata yin baya baya tana ƙoƙarin fa ɗi,  "ke Safna wai meyasa kikayi mugun raina nine? Saboda ina ragamiki yasa haka ko? Ok Today I will teach you mindfulness".

Ƙollan da ya cika mata ido ta ma tso ya dira ra kan kumatun ta,  "yaya Marwan bansan me nayi maka ba wallahi"  ta ƙarashe tana hawaye,   yace  "ni kike cewa bakisan laifin da kikayi min ba?"  Yafaɗi yana maida kallon sa gun Habu da ke gefe ya cigaba da cewa,  "kai ina ta kalmin yake?"  Jiki na rawa Habu ya ɗauko, saboda bayason yayi a bakin aikin sa.

Ijje Takalmin yayi a gaban Safna kamar yadda Marwan ya umurce sa, ya wuce gefen su, zaro ido waje tayi ganin Takalmin da ta sha gogewa ɗazu ya zama karmar an ciro sa daga bakin Kura, yadda ko ta ina na jikin yake da ƙura harda wani a lamu kamar ansa Wuƙa an caccaka shi, saɓanin ɗazu da yake ta walwalin yadda yaji maiƙo.

Yayin da ita kuwa Ruki kewa Safna dariyar mugunta,  "Saboda tsaban renin wayo, dubi yadda kika mayarmin da shoe to yau zaki san ni Marwan kika raina,  Frog jump zaki fara yi cikin ranar nan kuma sai kinyi one thousand tukunna za ki bari, Is that your punishment"  cikin tashin hankali ta dube shi jin wai tsallen kwaɗo zata yi, abinda ke matuƙar bata wahala,  "Wallahi ba haka na ba Habu takalmin nan ba, ka tambaye sa?"  Ta ƙarashe maganar cike da damuwa.

"Ke banason iskanci za kiyi abinda na sa ki kokuma sai kin ji a jikin ki before? "  Cewar Marwan harda zare mata ido,  share ƙananun hawayen ta tayi, da ma tayi zaton haka daga gare shi, ƙarajin maganar sa tayi yana cewa,  "Ruki ki tabbatar da ta kai adadin da nace sannan ki rabu da ita"  yana gama maganar ya wuce ciki.

Inalillahi wa inna ilaihi raju'un ta faɗi a zuciyar ta, tana mai ƙa ra jin Za fin abu-buwan da yaran hajiya ke mata, Ruki ɗauko abinda za ta zauna tayi, da murmushin mugunta  take bin Safna dashi, zama tayi tana faɗin  "baza kiyi bane sai na kirashi?"  Bata tanka mata ba ta fara yi.

Tsawon wani lokaci, gaba ɗaya ta gaji zufa sai tsatstsafo mata yake idanuwan ta duk sun canza kala, hawaye kawai suke fitarwa, jin Cinyo-yin ta take kamar ana sassara mata su, Ruki kuwa danna wayanta kawai take, inta kalle ta sai ta kwashe da dariya, ta kuma maida kanta ga wayan, domin kuwa ita ta ƙulla mata wannan.

Ana cikin hakan Baba Hambali yaji ƙarar hon, tun kan yakaiga ƙa risa buɗewa Yazeed ya danno hancin motar ciki, yanayin parking ɗin motar ya fito, sanye da wando Black jeans da kuma t-shirt blue ba ƙaramin haɗewa yayi ba, yayo gurin da Hambali yake dan yin masa masifa na rashin buɗewan da baiyi da wuri ba, Saidai ya da kata da zuwa wurin sa ganin abinda Safna take yi sannan ga Ruki gefe kenan ita ta sa ta,

A hasale yafara takawa zuwa inda suke, babu zato babu tsammani Ruki taji saukar Ma ri a kuncin ta, ƙara ta saki haɗi da yin tsallen 'yan China tayi ge fe, itama Safna da katawa tayi tana kallon inda Ruki take, jin ƙarar marin da akayi mata, ba tare da sanin yaushe yazo wurin ba, don hon kawai taji.

"Yazeed mari na fa kayi me nayi maka?"  Ta ƙarashe faɗi tana sakin kuka,  shima amsa ya bata da cewa,  "Saboda ke ga ki shegiya za kisa mara ga lihun nan frog jump akan me?"  Wani irin takaici ne ya cika Safna, ya kira ta da mara ga lihu amma yake cewa akanme aka sata frog jump.

"To ai bani na sata ba, Marwan ne kuma yace sai tayi sau dubu sannan ta bari"  nanma ta ƙara faɗi tana zunɓuro Ba ki, yadda ta zunɓuro baki yasa shi ƙara kai mata tagwayen maruka, yana ce wa  "ni kike zunɓurowa baki, yanzinnan sai in tattakaki anan stupid, shi kuma Marwan ɗin baida hankali ne da zaisa mutum frog jump kuma yace sai tayi thousand? Se kace dabba yasa".

Ruki kuwa sai rusan kuka ta keyi na zafin marin da yayi mata, ba'abin ta mai da mai ba, ya tattaka ta kamar yadda ya faɗi ƙaramar aikin sa kenan,  "me sunan ki ma?"  Cewar Yazeed yana kallon Safna da ke masa kallon ɗar-ɗar, azuciyar ta kuma tace  "wai me suna na, koda yake zai iya mantawa tunda ba kiran sunan yake ba".

"wuce ciki" kawai ya faɗawa Safna, shima yana yin hanyar shiga,  "to mezan cewa Marwan ɗin"  Ruki ta tsaida shi da faɗi cikin muryar ta da ke nuna kukan da take bai ƙare ba,  kallon da ya jefa mata ne yasa ta yin shiru,  Shiga falon yayi Safna na rufa mai baya, tana tafiya da ƙyar sabida yadda ƙafafuwan ta ke yi mata zugi.

Yana shiga bai tsaya a ko ina ba sai a ɗakin Marwan,  zaune gefen Bed ya tadda shi yana latsa waya da alama chat yake, dago idon sa yayi dan ganin wanda ya shigo Masa ɗaki, bazai yi mamakin rashin sallama ba saboda dukan su haka suke, sai dai kaji ƙarar dirar su.

"What kind of person you are Marwan? Akan me zaka sa yarinyar nan punishment me wahala?"  Yayi masa maganar cikin ɗagun murya, Miƙewa Marwan yayi yana kallon ƙanin na sa da yaba shekara biyu da haihuwa cikin ɗagun murya shima ya fara magana,  "Yazeed be careful with me! Har zaka zo kana ɗaga min murya akan kuca kan yarinyar nan akanme?"

Jin alamun masifa a ɗakin Marwan yasa Hajiya yo wa wurin,  itama antayawa kawai tayi tana faɗin,  "ku meyasa koda yaushe kuke sa'insa tsakanin ku ne?"  "Hajiya wai ni Yazeed ke ɗagawa murya akan Safna"  mayarda duban ta tayi kan Yazeed,  shima cewa yayi,  "Hajiya saboda tsaban mugunta sa Safna tsallen kwaɗo yayi, harda cewa sai ta yi thousand sai kace ba mutum ba? Kinga yadda ta gala-baita kuwa?".

Kallon Yazeed kawai Hajiya keyi, tana ƙara jin haushin Safna, ita tsoronta ɗaya kada wata rana Yazeed ya bijiro musu da maganar yana son Safna fa, saboda ganin abubuwan da yake wani lokaci anya kuwa? Ta tambayi kanta,  afili kuwa tace,  "Yazeed intambaye ka mana? Wai me ruwan ka da sheɗaniyar yarinyar nan ne?".

Kallon ta yake da mamakin tambayar,  "Hajiya me kike nufi ne?"  "Gani nayi kana yawan shishshigewa lamarin ta ne"   "tambaye shi dai Hajiya"  Cewar Marwan,  a hasale Yazeed yace,  "wai me kuke nufi ne?"  Kawai ya furta haɗi da ficewa daga ɗakin cike da haushin abinda suka ce, daga yin magana akan musgunawar da Marwan yayi wa Safna sai su ɗauki wani tinani a ransu, nufi ma suke ko yana Son ta, to mema zaiyi da ita mtsww

Da ƙyar Safna ta iya ƙarisawa ɗaki, jikin ta Sam baya sabo da wuya, inba haka ba abinda Hajiya da 'ya'yanta suke mata tun tana ƙarama ai yaci zuwa yanzin ta dena jin zafin duk wata wahala, a ɓangare guda kuwa, tayi mamakin yadda Yazeed ya taimake ta duk da shima zai iya sata fiye da hakan saida ta ma tse Cinyo-yin ta da ruwan ɗumi tukunna taji ɗan dama dama, ga shi gobe weekend ranar Aikin ta.


------------------------‐----------‐--------


Hmm lallai, to nima dai nace Yazeed anya kuwa?
To koma dai menene zamuji a gaba.

Kukasan ce dani a part na gaba. 


🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️