AMNA DA SAFNA

Part 19-20

by @zahratulqalam51

بسم الله الرحمن الرحيم. 
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 

🖤AMNA DA SAFNA🖤

Part 1️⃣9️⃣▶️2️⃣0️⃣

📱Writing✍🏼
Aisha G Umar 
🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️




Fannin baiwar Allah SAFNA. . 

Ammu ce ta tashi da rashin lafiya duk magun-gunan da take sha Safna ta bata amma jikin sai ƙara zafi da yayi, tinanin yadda zatayi take amma ta rasa, Dady baya nan bere ya kai su Hospital, Hajiya kuwa tasan ko ji tayi Ammu suma take yi ba bu abinda zai sa ta ko kalle ta bere ayi maganar taimako.

Ganin jikin na ƙara zafi sosai yasa ta tashi tayi waje da sauri, turus tayi bayan bangazan Hajiya da tayi,  'ke!"  Hajiya ta furta da tsawa da yasa jikin Safna rawa, "dan Allah, dan Allah Hajiya ki gafarce ni, wallahi ban lura bane, Ammu na ce ba lafiya jikin ta ya ɗau zafi sosai"  ta ƙarashe faɗi cikin rawar murya.

Wani irin gigi taccen mari Hajiya ta sauke mata da yasa ta yin gefe goshin ta ya bugu da gini, durƙusawa tayi haɗi da saurin sa hannun ta kan goshin na ta, ta rintse ido jin yadda yake mata zugi, tana sauke hannun taga ya ɓaci da jini, ashe fashewa yayi.

Duk da ganin hakan bai sa Hajiya taji tausayin ta ba, sai ma jan tsaki da tayi tana wucewa, hawaye mai tsananin zafi ne ya koranyo daga cikin manyan idonuwan ta, dama fitan da tayi dan zuwa gurin Baba Hambali ne, ko zai bata wayar sa ta kira Dady ta sanar da shi halin da Ammu ke ciki.

Miƙewa tayi zuwa wurin sa, hannun ta da pe da goshin ta, zaune ta sami Baba Hambali kan kujerar zaman sa, ya ka ra Radio a kunnen sa yana sauraron shirin Inda Ran Ka, isa wurin sa tayi duk da tana jin zugi a goshin na ta,  "Assalamu alaikum Baba ina wuni"  ta gaishe sa,  "Lafiya..... subhanallahi Meya same ki haka 'yata?"  "Ba wani abu bane Baba, dan Allah ko zan samu waya in kira Dady?".

Tayi masa maganar tana sauke hannun ta a goshin na ta, sai dai jinin bai tsaya ba, sai ma ɓata mata kaya da yayi,  "haba 'yata duba fa jinin yaƙi tsayawa ya kama...."  Cewar Baba mai gadi cike da damuwa, sai dai katse sa tayi da faɗin  "please Baba Hambali dont worry a bout this, kawai waya zaka bani ka ji dan Allah".

Ciro wayar sa burin ɗan garuwa yayi, irin ƙaton wayar nan mai bottle, ya miƙa mata, da sauri ta amsa tana tambayar sa wani suna yasa?"  Dialing tayi bayan sanar da ita sunan da yayi saving numbern da shi, a kira na Uku ne ya ɗauka yana faɗin,  "sorry I'm meeting now".

ganin cewa bai ma san numbern da aka kira sa da shi ba, yasa Safna cewa  "Dady it's me Safna Ammu na ce ba lafiya Dady dan Allah ka taimake ni"   ta ƙarashe faɗin tare da fitar da hawaye a idon ta, cikin tashin hankali yace  "what happen with her?"  Babu ɓata lokaci ta sanar dashi,  "ok I'm coming right now".

Kashe wayar tayi da tinanin, da ma ta san indai Dady yaji to zai yi gaggawan zuwa,  miƙa masa wayar tayi haɗi da yi masa godiya  "Safna kan ki na zubar da jini sosai"  kan ya ƙara yunƙurin wata maganar tace,  "zanje in wanke yanzu"  ta faɗi tana sharar ƙolla,  ita fa da so samu ne, in mutum zaiyi mata magana yayi mata kalma ɗaya ko biyu ya wadatar.

Zuwa ɗaki tayi ta shiga toilet ta wanke jinin da ke zuba, ta ɗaura ƙyalle à wurin, bata tsaya canza kaya ba, ta nufi inda Ammu take  "Hasbunallahu wa ni'imal wa kiil"  ta faɗi lokacin da zafin jikin Ammu ya ratsa hannun ta bayan ta ɗaura à kan ta.

Saurin tashi tayi ta ɗibo ruwa a kwano ta ɗauko ya di mai laushi ta fara tsomawa tana matsewa sai ta ɗora kan Ammu tana mammatsa mata, da addu'an Allah yasa dabarar yayi kafin zuwan Dady.

Ta ɗau 30 minute ba ta tsaya ba, amma zafin jikin ya ragu, sai à lokacin Dady ya zo cikin manyar kaya, irin na hamshaƙan masu kuɗi, ɗaukar Ammu sukayi zuwa Hospital,  Safna ma akayi mata bandejin goshin ta, Dady ya tambaye ta me yasame ta haka, sai ta bashi amsa da bugewa tayi, dan sanar da shi gaskiyar babu abinda zai amfane ta da shi.

Doctor ne yake sanar musu da,  "ba wani babban abu bane yasa ta kasancewa a yadda take yanzu  face rashin motsa jiki sosai da ba'a sa ta, kuma ya kamata a rinƙa kula da ita wurin fitar da ita waje ta rinƙa shan iska, saboda kasancewar ta kullum à ɗaki guri ɗaya zai kawowa da jinin ta rashin jin daɗi gurin kewayawa a jikin ta, kuma hakan zai haifar mata da wani abun daban, ku sai mata keken guragu zai tai maka muku wurin tura ta ba tare da ta sha wuya ba"  Bayan sun gama jin abun da likita yace Dady yayi masa godiya, da kuma sanar da shi za'a kiyaye.

Bayan fitowar su suka nufi ɗakin da Ammu take,   "shirya ta mu koma Gida Safna"  Cewar Dady, to ta amsa masa dashi sannan tace  "thank you so much Dady"  "No my daughter akan me zaki yimin godiya? dama kula da ku a wuya na yake, so don't thank me"  ƙasa kawai tayi da kan ta, da roƙon Allah ya bata abun da zata sa kawa Dady da shi, saboda shine mai kula da matsalar su à ko da yaushe.

AMNA.

Koda isan su gida Ummee suka shiga tashin hankali dan ganin Raunuka a jikin Ɗan su, duk da anyi masa tritment, tambaya suka shiga yi musu, sai dai har yanzu Amna batayi magana ba, sai ma wucewa ɗaki da tayi.

A hasale cikin ɗagun murya Ummee ta fara magana,  "har yaushe zaki bar abubuwan nan da ki ke yi Amna? Tun da ki kayi shiru nasan bai wuci ke kika haddasawa Mubarak wannan raunin da yake jikin sa ba, ke wace irin Mutum ce wai, baki da aiki sai neman rigima?"  Rintse idanun ta tayi yayin da taji magan-ganun Ummee a gare ta.

  "a ah Ummee ba yadda ki ke...."  katse sa Ummee tayi  "rufamin baki dama duk san da zata kwaso rigima ai a bayan ta kake, kai ga ka mai 'yar-uwa"  "Biba kada kice haka saboda baki san dalilin da yasa faruwar hakan ba, domin nasan Amna baza tayi abu ba tare da dalili ba"  Cewar Mamma dake zaune gefe tana ƙara kallon Mubarak cikin tausayawa. 

Ummee ce ta ƙara cewa,  "haba Mamma dubi abin da ta jawa Ɗan-uwan ta, ita kam koda yaushe bata san haƙuri ba ne, ita kinga jikin ta da ko ƙorzane ne? Duk abun da ake faɗawa Amna a kan haƙuri ba ta ɗaukar sa, sai kace ita tafi kowa zafin zuciya" Ta ƙarashe maganar cike da masifa.

"Mubarak meya faru a makarantar?"  Mamma ta tambaye sa,  sanar da ita komai yayi, babu ƙari ba ragi, sallallami suka hauyi  cikin tashin Hankali,  "yanzu abun da ya faru kenan, Lahaula wa la ƙuwwata illa billah, Amna wani irin abu ki kayi haka? ba ku zuwa ku sanarwa da mahukuntan makarantar su ɗau mataki da kansu?"  Cewar Mamma cikin tashin hankali da tinanin a binda zai biyo baya.

Ummee kam kasa magana ma tayi saboda tsaban tashin hankali, sai da ta sauke babban ajiyar zuciya sannan ta fara kiran Amna,  fitowa tayi har lokacin bata cire kayan ta ba, kuma fiskar ta ko alamar fara'a babu, sai lokacin suka ga jinin da ke kayan ta,  "wannan kenan duk jinin mutanen ne, na shiga Uku  Amna zaki kashe ni da raina, wannan wani irin masifa ne? Yanzu waya san abun da zai faru, bayan abinda kika jawo mana"

Sai lokacin ta buɗe baki tace  "Ummee ku duba raunukan da suka yi masa fa"  ta faɗi tana nuna inda yake, kan ta ƙasa  "munji sun yi masa rauni, to kuma babu wata hanya da za kiyi sai na ramawa?"  Cewar Ummee,   Mamma ma tace,  "Amna nakan goyi bayan ki a ko da yaushe, duk da abin da yaran sukayi ba daidai bane, amma hanyar da ki ka bi bai dace ba, yanzu Allah kaɗai yasan abun da zai faru gaba, dan nasan iyayen su baza su bar maganar ba".

Miƙewa kawai Amna tayi ta wuce dan yin wanka tayi Sallah,  bin ta da kallo su kayi  Mamma tace,  "babu ruwan ta fa"  "ai kin san ta Mamma duk abinnan da tayi ganin dai-dai take masa"  faɗin Ummee tana girgiza kai cike da takai ci, shima Mubarak miƙewa yayi da ƙyar,  "sannu Mubaraka bari in tafasa ruwa in mammatse maka jiki, baka zauna haka ba",  Mamma ta faɗi hakan tare da miƙewa.

DARE. 

Su Ummee sun kasa sanar da Baba abun da ya faru, dan ko yanzu daya kira su hira kawai sukayi, ba tare da kawo maganar ba.

BABA.

Bayan ya gama magana da iyalan sa, ya ijje waya kenan kiran Zilla ya shigo wayar sa, dagawa yayi da mamaki,  "ka yi mamaki ne? To ba abun mamaki bane beautiful, kawai naji ina son jin muryar ka ne, na ƙosa gobe yayi in haɗu da kai, saboda ina da abubuwa masu ban sha'awa da zan ba ka, amma kamar wani lokaci zamu haɗu?"  Ta faɗa masa yana ɗaukar wayar.

"Da ma wai haka take da surutu ne ko me? Danni banga jan ajin n'a ta ba"  Cewar Baba a zuciya,  sannan ya amsa mata da,  "kamar da yammaci"  "kashsh gaskiya banji daɗi ba, yammaci yayi nisa, amma ba komai sai lokacin i love you beautiful"  kashe wayar yayi ba tare da ƙarasa jin abunda take faɗa ba,  wani takaici ya rufe sa, dan shi ƙyamar ta ma yake,  "Allah ka bani sa'a akan wannan aikin da na ɗauko" kawai ya faɗi a fili.

WASHE GARI, ASABAR RANAR HUTU. 

SAFNA. 

Duk da abin da ya faru jiya bai sa ta hutawa ba, sanin cewa yau ranar Aikin ta ne, cike da juriya ta fara aikin har ta gama, ɗauko keken da Dady ya kawo wa Ammu tayi ta ɗora ta a kai, dan fitar da ita tsakar gida dan shan iska.

Tasa Ammu à gaba tayi tana kallon ta, bayan ta fito da ita waje, ta zauna akan kujera ita ma,  "sannu Ammu, na san dai yanzu kin ɗan ji sauki ko?"  Lumshe ido Ammu tayi sannan ta buɗe alamar eh taji sauki,  "yauwa Ammu na haka nake so, insha Allahu nan bada daɗewa ba, zaki samu lafiya daga dukkanin Matsalar ki".

murmushi Ammu tayi mata dayin mata alama da  "Allah yasa hakan, nima abinda na keso kenan"  ta ɗago hannun ta da ƙyar alamar  "matso kusa dani"  murmushi ita ma Safna tayi, ta sauka kan kujerar da take, ta tsugunna haɗi da ɗaura kan ta a saman ƙafafuwan Ammu, tana mai jin farin ciki a ranta,  rabon da Ammu ta fito ko ƙofar ɗaki ta manta bere waje.



--------------------------------------------


To fah,  shin iyayen su Jalo zasu bar maganar kuwa?.

Ya Baba zaiyi idan yaji abunda autar sa tayi? Zai goyi bayan ta ko kuwa?.

Baba zai ci nasara ko daiii?. Nifa har na fara tinanin wani abu😁

Fitar da Ammu waje shan iska zai ɗore kuwa?.


🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️