ZAKIYYA Matashiya mai juyayyiyar Kaddara

10

by @sadiyanasir

ZAKIYYA 

Page 10

      Aliyu na kammala shirin fita zuwa gidan Amaryarsa ya dawo ɗakin Jidda don ya yi mata sallama. A wannan karon, Jidda ta tattara ƙarfin hali ta share hawayen da suka taru a idonta ta saki murmushi mai rauni. Tana so ƙwarai zuciyar mijinta ya huta duk da nata zuciyar cike take da wani irin nauyi. ƙarasowa yayi ya zauna kama hannunta.
“Jidda ta?" Murmushin da yafi kuka Jidda tayi. "Na'am Abban Farra". "Ina sonki Jidda, a duniya ba za'a tab'a samun ta biyun ki a zuciyata ba, in sha zanyi ƙoƙari a komai don Allah ki yarda dani.?” Gyada kai tayi jikinta a sanyaye. “Allah ya sa albarka Abban Farrah. Ka tashi kaje dare nayi.” Lumshe ido yayi na jin daɗin jin kalamanta sun sa mishi sanyi fiye da yadda baya  zato. Gun Y'ay'an ya nufa da suke kwance ya sumbace su ya shafa jikin su. "Allah ya muku albarka, na barku lafiya". Murmushi Jidda tayi da zolaya tace. "Ko dai zaka tafi dasu gun Amarya ce?". Dariya yayi idon sa akansu. "Ai watarana haka zan d'aukesu muje mu kwana abin mu". "Kaji dashi, please dare tanayi". "Shikenan ranki shidade". Ya ambata yasa kai ya fice. Bayan ya fita Jidda ta kasa riƙe hawayen daya taru mata tun d'azu. Ta durkushe ta soma wani irin kuka mai nauyi, wanda ke tashi daga zurfin zuciya, kuka na rashin samun nutsuwa, kuka na tsoro, kuka na rashin tabbas. Tana jin kamar wani ɓangare nata ne ya tafi da shi. Sai da ta gaji don kanta kafin ta shiga toilet ta wanke fuska ta dawo ta kwanta. Ajiyar zuciya kawai take sauk'ewa a haka baccin wahala ya d'auketa.

       Aliyu kuwa da farin ciki mai nauyi ya isa gun masu Kaji ya saya wa Amarya Zakiyya da drinks masu sanyi. Wani 
Abu da zuciyarsa ke ji ba zai iya fassara shi gaba ɗaya ba. farin ciki, alhinin Jidda, tsoron adalci, da fargabar sabon aure. Yana shiga gidan Zakiyya zuciyarsa ta fara bugawa da nishaɗi.

A d’akin kuwa, Zakiyya zaune take tamkar wacce za’a yanke, zuciyarta. Tsoro ne ya rufe ta gaba ɗaya. Hannunta har zufa yake yi kafin ta ji sallamar Aliyu a kofa.

“Assalamu alaikum.”

Ta dago kanta a hankali.
“Wa’alaikumus salam,” ta amsa, muryarta na rawa. Aliyu ya shigo da sallama da murmushi mai taushi. “Amarya, kina lafiya?” Ta gyada kai. “Lafiya, sannu da zuwa.” Ya ajiye ledar da kazar daya zo musu dashi “Kinji yanda nake jin gajiya kuwa? Tashi ki d'auko mana plate.” To Zakiyya tace ta mike ta d'auko plate. Umurni ya bata ta juye Kazar cikin plate, zaunar da ita yayi yace taci, babu musu take tsakurar Kazar tamkar magani take ci. wani irin tunani ya tsinkayo zuciyarta kamar wuka. Tunawa da tsohon mijinta Mahmod.
Lokaci guda idonta ya cicciko da hawaye. Hannunta ya faɗi daga saman farantin.
“Zakiyya?” Aliyu ya matsa dab da ita cikin damuwa. “Me ya faru? Kina jin wani ciwo ne?”
Kai ta girgiza, hawaye suka fara sauka a hankali. “Ba komai… kawai… nayi tunani ne kawai…” Aliyu ya kama hannunta a hankali.
“Kin sha wahala sosai. Ki bani lokaci, in sha Allah zan mayar miki da takaicin ki farin ciki.”
Share hawayen tayi numfashi na rawa. “Nagode sosai nagode.”
Bayan sun kammala alola sukayi Aliyu ya jasu sallah na farko a matsayin ma’aurata. Bayan sun idar hanu Aliyu ya d'aga  “Ya Allah ka sanya albarka, ka kawo nutsuwa, ka hana fitina. Ina rokonka ka bani alkairin da wannan baiwa taka tazo dashi. Sharrin dake bibiyarta ya Allah kayi mana maganinsa” Ya shafa Addu'a ya juyo ya kalleta sosai. A cikin idanunta ya ga wani irin tsoro mai zurfi, wanda ya sosa masa zuciya. "Zakiyya?” "Na’am…” "Kin yi sanyi sosai baki da lafiya ne?.” Ya dora hannunsa a goshinta. Zafi yaji na zazzabi yana dukan jikinta. "Subhanallah, kin sa tsoro na a ranki ko?” Yayi maganar da zolaya
Kai ta girgiza da sauri. “Tun safe nake jin babu dad'i”  Paracetamol ya mika mata da ruwa . “Sha kisamu ki kwanta. Allah ya baki lafiya.” Ameen ta amsa ta karb'i  magani tasha ta kwanta. Cikin mintuna kaɗan bacci mai nauyi ya dauke ta saboda gajiya da tsoro.
Aliyu ya tsaya yana kallon fuskarta na mintuna kafin ya tashi ya d’aura nafilar neman sauƙi da albarka ga sabon gidansa. Ya roƙi Allah ya ba shi ikon adalci, ikon jurewa rayuwar biyu, da ikon kare zuciyoyin matan sa biyun. Ya koma ya kwanta dab da ita a gefen gado.
           Wajen ƙarfe 5 saura, Zakiyya ta farka da wani irin razana kamar an tasheta daga sama. Numfashinta na sama-sama. Ta kai hannunta ta taba Aliyu a nan ya bude ido da sauri.
“Lafiya..? Zakiyya?”
Ta sauke ajiyar zuciya mai karfi. "Alhamdulillah… mafarki nayi.” Ya shafa gashin kanta a hankali.
“Kinayi addu’a kafin ki kwanta?” “Inayi. Amma yau…” ta lumshe ido. “Sai na kasa saboda Zazzabin nan.” “Idan kika tashi da tsoro, ki ambaci Allah. Shikenan, bakomai da zai sameki in sha Allah.” "Na gode.”
Ya duba agogo. “Asuba tana kusa. Bari in yi alwala.” Ya shiga toilet ya d’aura alola yazo ya tada nafila, ita kuma ta tsaya tana kallonsa da nutsuwa mai sanyi tana shigarta. Lokacin kiran shiga sallah ya fita zuwa masallaci. Itama ta tashi ta yi nata sallar. Sai wajen karfe shida Aliyu ya dawo ya same ta zaune a parlor tana lazimi. "Amarya, barka da safiya.” Ta dago da murmushi. "Barka dai ya ka tashi?” "Alhamdulillah. Ya jikinki?” "Bana jin komai yanzu.” Ya yi murmushi kadan. “Tsoro na ko? To ki daina?” Ta yi murmushi tana sunkuyar da kai. “Zan dan kwanta wallahi, idanun nan sun yi nauyi.” "To kayi bacci lafiya.” Ya shiga d’aki ya kwanta, ita kuma ta cigaba da lazimi. A haka bacci ya sake daukarta tana zaune.

     Karfe 09:23 Zakiyya ta farka jin nishin da Aliyu keyi  kamar mai fama da ciwo. Gabanta taji ya fadi ta mike da sauri ta yi d’akin.

“Aliyu!!” Tayi kansa da sauri ganinsa durkushe rike da ciki yana numfashi da wahala. Idanunsa sun jazur saboda azaba. “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Zakiyya ta fada tana durqushewa kusa da shi. “Aliyu me yake damunka na shiga uku?!” Jiki a wahale ya ce "Wayata, d’auko security 2 guda 4, ki kira Abbas yazo muje asibiti don Allah…” A rude ta d’auki wayarsa,  hannunta na rawa ta kira Abbas ta sanar dashi halin da suke ciki. Ba a jima ba Abbas ya iso suka d’aukesa cikin gaggawa zuwa asibiti.

******
A gefe guda, Jidda bayan kuka mai tsawo da tayi  har bacci ya d’auke ta sai jin idar da sallah tayi. Bayan ta idar na nata sallah ta had'a shayi wa Farra ta koma ta kwanta, amma babu nutsuwa, zuciyarta cike da wani irin nauyi.

******
A asibiti likitoci sun karɓi Aliyu cikin gaggawa. Zakiyya kuka take tamkar ranta zai fita. tunda ta shiga d'akin taga halin da yake ciki ta fito, don zuciyarta ba zata iya d'auka ba. A wajen daga inda take zaune tana jin yadda numfashin Aliyu ke rikicewa. Sai da Abbas ya gama da doctor kafin ya kira Hajiya ya sanar da ita. Innalillahi wa'inna ilaihi rajuum tacigaba da furtawa ta kira y'an uwan Aliyu a waya ta sanar dasu halin da ake ciki. Mayafi ta d'auka sai asibiti. Da sauri Hajiya ta iso cikin gudu, hawayen tsoro na zuba. "Ina Aliyu?". Da hanu Zakiyya ta nuna mata d'akin ta shiga da sauri. Tsayawa tayi cak tana kallon halin da ɗanta ke ciki.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! Aliyu!!! ? Na shiga uku menene haka ya sameka? Ta durƙusa kusa da gadon tana kuka. Aliyu kuwa bai san wake kansa ba saboda rayuwarsa ta soma yin nisa. Isowar su Rabi'a d'akin suka shiga, ganin yanda Aliyu yakeyi yasa  Rabi’a ta kamo Hajiya ta fitar da ita zuwa kujerun waje tana rarrashi.  Zakiyya Jidda ta san halin da yake ciki kuwa?”
Muryar Zakiyya na rawa. “Don Allah ki kirata… wallahi bata saniba.”
Rabi’a ta dauki wayarta ta kira Jidda.

*****
A d’aki Jidda na zaune ta zuba tagumi tana jin wani irin sanyin zuciya. Sai ga kiran Aunty Rabi’a. Ta sauke ajiyar zuciya ta d’aga:

“Assalamu alaikum Aunty, barka da safiya.”

“Barka dai Jidda ya kwanan yaran?”

“Alhamdulillah… lafiya lau.”

Muryar Rabi’a ta canza.
“Jidda don Allah ki taho asibitin Gateway  yanzu yanzu fa?". "Aunty Rabi'a meke faruwa?". "Kizo kawai Jidda". Ta kashe wayar. Da ido Jidda take bin wayar da kallo kaman tana neman karin bayani daga garesa. Da kyar ta mike tasa mayafi ta d'auki yaranta suka fita.
     Ganin yanda numfashin Aliyu ke rawa yasa doctor d'aura mishi oxygen don taimaka mishi. Shesahekar kuka da salatin Hajiya cika d'akin. Jikin Aliyu ne ya soma rawa na'urar oxygen ya soma canza lissafi. A rikice Aunty Rabi'a ta fito tana kwala kiran. “Nurse! Doctor!!” da karfi take magana muryarta na rawa.
Kafin kace me, likitoci uku suka shigo a guje, kowanne da kayan aikin gaggawa a hannu. Nan da nan suka kewaye gadon Aliyu suka sallami su Hajiya zuwa waje. Suka cigaba da danna kirjin sa suna kiran sunansa, suna gyara mask ɗin numfashi. Sautin umarninsu da hanzarinsu ya cika dakin. Sun d'auki tsawon lokaci suna jiran komai ya daidaita, amma motsin da suke nema ya ki bayyana. 
      A daidai lokacin da ƙofar dakin ta bude doctor ya fito, Jidda ta shigo da sauri, hijab ɗinta ya kusa zamewa saboda fitowar damuwa da tayi. Ta tsaya cak tana kallon su musamman Hajiya, don tayi tunanin itace ba lafiya, amma jin Kalmar Aliyu a bakin Hajiya yasa taji zuciyarta ta karye. Da sauri Aunty Rabi'a tayi gun Doctor fuska a kame. "Doctor… lafiya? Don Allah meke faruwa?” Doctor ya kalli Rabi'a da dukkan wanda suke wajen, sannan ya sauke numfashi mai nauyi. “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un… Aliyu Allah ya karɓi abinsa.”
Kalmomin sun yi tsawa a kunnen Jidda. Wani irin duhu ya lullube idanunta. Kafafunta suka yi sanyi, bakinta ya bude amma muryar ta ki fita. Ta faɗi ƙasa tas! Tamkar ƙarfe ya bugu da dutse. A gefe kuwa, Zakiyya tana tsaye kamar mutum-mutumi.
Babu kuka. Babu motsi.
Numfashinta ya tsaya cak, idonta ya cika da hawaye amma ba su gangaro ba. Lokacin da zuciyarta ta gane kalmar “Mutuwa” a kan Aliyu…
Sai hawaye suka kafe zuciyarta tayi tauri, wani Abu ya shaƙe mata makogoronta. Girman bala’i daya sameta yasa ta kasa sarrafa kanta
Ta kasa jan numfashi, ta kasa komai. Tamkar gunki haka ta kame, motsi kwakkwara ta kasa yi. Kamar zuciyarta ta daina bugawa gaba ɗaya. Kukan da ke cikin kirjinta ya makale ya gagara fitowa. Idanunta sun cika da hawaye amma sun kasa zubowa, wani irin nauyi ya rufe dukkan jijiyoyin jikinta.
Gaban ta ya dinga yi mata nauyi, kamar an dora dutsen duniya a kirjinta. Hannuwanta suka soma rawa, numfashinta ya soma yin sama-sama, kamar wanda ake ja da karfi daga zuciyarta.
“Zakiyya ki zauna kin ji?” Abbas ya matsa kusa da ita cikin tsoro, ganin yadda take rikicewa, idanunta na kallon wuri daya kamar mai ganin wani abu da ba’a gani. Ta girgiza kai a hankali, tana kokarin furta kalma guda, amma muryarta ta makale.

      A gefe guda kuwa nurses na ƙoƙarin farfaɗo. Hajiya kuka take kamar ranta zai fita, kuka na mace da ta rasa ɗanta a idon ta. Kuka mai tauri, kuka mai nauyi, wanda ba shi da magani.
“Ya Allah ka bani hakuri… Ya Allah ka bani ikon jurewa…” Hajiya take furtawa tana jijjiga jikinta. Babu mai iya lallashin juna tsakanin su ko wacce da abinda take ji. Abbas ne ya samu karfin zuciya ya soma kiran wanda suka dace ya sanar dasu.
           A hankali Jidda ta farfaɗo. Idanunta suka sauka a d'akin da take kwance, Kalmar karshe da doctor ya furta ta dawo mata. Wani irin sauk'a tayi a gado ta fito. Cikin tsananin firgici tayi kan Aunty Rabi'a dake kuka sosai
“Aunty Rabi’a… me doctor ya ce? Ki karyata min don Allah ki karyata min!” Hannunta na rawa, murya ta karye tamkar ta yanka. Aunty Rabi’a ta durƙusa ta rungume ta, kuka ya ci karfinta. “Jidda… ki yi hakuri… ki yi hakuri  Aliyu… ya tafi.” Kamar an jefa ƙaton wuka tsakiya zuciyar ta Jidda ta sake wani irin ihu, ihu mai tsananin radadi da ya sa kowa ya runtse ido. Ta riƙe kirjinta tana ƙoƙarin miƙewa, amma jiki ya ƙi biye mata. Wani irin amai ya taso mata, ta durƙusa tana huci kamar mai neman numfashi a ruwa.
“Aliyu… mijina… mijina… ka tafi ka bar ni? Ka tafi ka bar yaran nan… ka tafi ba tare da ka kalle ni na ƙarshe ba…?” Ta fashe da kuka mai sauti......