Chapter 3
đź’¦ AKWAI SILA đź’¦
BY AMANARCOOL
YOTA ID/O21
PAGE 5-6
Ya sake lumshe idanunsa, ƙamshin miyar taushe na ratsa masa hanci kamar ƙamshin wani wuri da ya taɓa rayuwa a ciki. Numfashinsa ya ɗan tsaya, ya doke shi da wani irin firgicin da bai fahimta ba. Hannunsa ya ɗora a ƙirji, zuciyarsa na lugude kamar ana buɗe ƙofa daga duhun da ya daɗe a kulle.
Sai ga wasu hotuna kamar inuwa, sautin dariya, ƙamshin girki, murya mai taushi, duk suna ƙoƙarin fitowa, amma suna ɓacewa kafin ya kama su. Ya buɗe idanu da sauri, jijiyoyin kansa na matsewa kamar ana jawo su. Karensa ya matsa daf da shi, yana lumshe ido kamar shima ya fahimci wani abu ya faru.
Zuciyar Joriyya ta fara tayar da wata guguwa ta daban, ta fara É—agawa kowa hankali. A falo ta tsaya tana huci kamar wadda aka ci amanarta.
Momy ta ce “Auta ki zo nan”
Joriyya ta ce “Momy ku dai ku bar ni ku bar ni kawai!”.
Dady ya sauko daga sama a hankali kukan takaici yana barazanar ƙwace masa “Shalele” ya kira ta da murya mai nauyi “Ni fa ba zan yarda ki ɓata mana suna saboda wani mahaukacin da ba mu ma san asalinsa ba, kina ƙaramar yarinya dake da ƙananun shekarunki za ki ɗaga mana hankali!”.
Ta juya masa baya ta ce “Dady ba ku gane shi bane! Shi mutum ne kamar kowa!”
Wannan kalma ce ta huda ransa. Zuciyarsa ta tashi duka. Ya ɗaga murya fiye da yau da kullum. “Ni ki ke faɗawa haka? Ni? Ni na raine ki ne da wannan dabi'ar? Na koya miki ƙaunar kowa ne? Abin da na sani shi ne ban koya miki mugunta ba, wannan abin da kike yi ƙasƙanci ne na fi ƙarfin wannan zancen da kike jawowa!”.
Joriyya ta tsaya cak. Muryarta ta soma rawa. “Kai ka ce ƙasƙanci? Don ina jin tausayin mutum? Don ina son… don ina son…” Numfashinta ya fara birkicewa. Idonta ya cika da hawaye, hannunta ya fara rawa, Momy ta ruga da sauri “Auta ki yi shiru, ki daina” amma hawayen sun zubo. Ciwon ya motsa a ƙirjinta wanda duk gidan ke tsoro, numfashinta ya ɗauke na ɗan lokaci.
Dady ya ruɗe. “Ke Hajiya riƙe ta, bari na ɗakko ruwa!” Sai ta zauna a ƙasa tana haki kamar za ta faɗi, da ƙyar suka samu abin ya lafa mata, gashi dare ya fara yi idan ba'a yi sa'a ba sai ciwon ya hanawa kowa bacci a gidan.
Washegari.
Joriyya ba ta je school ba saboda yanayin jikinta, misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe Anty Zainab ta iso gidan cikin hargagi kamar wadda aka kira ta don kashe gobara, Dady na ƙoƙarin fita suka gaisa, ganin Zainab ta zo ya sa shi komawa ya zauna, zama ta yi bayan sun gaisa ne ta ce
“Dady, Momy tun jiya da kika gaya mini maganar nan hankalina ya tashi, wannan ba abin wasa ba ne. Yarinyar nan tana da neman magana, wannan ai zubewar mutunci ne”. Ta yi maganar tana kiran
“Joriyya zo nan Joriyya”
Fitowa ta yi ta zauna ba walwala.
Anty Zainab ta ce “Joriyya dubi yadda kika fara fita hayyacin ki saboda wani mahaukaci da ko sutura ma bai iya sakawa ba, wane irin rashin hankalin ne da ke? Wannan wane irin abu ne kika ɗaukar wa kanki?”.
Joriyya ta miƙe da sauri kamar an hura ta, ta ce “Ki daina zolayarsa, ki daina faɗin mummunan abu akansa bana so, bana son ana yi masa haka!”.
Anty Zainab ta yi dariya mai ciwo ta ce “Shi fa mahaukaci ne Joriyya, mahau....”
Bata gama ba Joriyya ta katse ta da murya mai kaifi “Ki yi shiru, ba zan bar ki ki zage shi ba, ni fa ban taɓa jin kunya ba kamar yanzu da kuke faɗar hakan, ku duka ba ku gane shi bane wai?" Ta yi maganar jikinta na tsuma tamkar za ta fita hayyacinta.
Falon ya yi shiru. Idanun Momy sun cika da hawaye. Anty Zainab ta ce “Ke Joriyya, ni kike mayar wa magana haka? Mu gane shi a ina? Waye shi ɗin? Ni anya Joriyya ba iskokai ne suka shige ki ba kuwa? Ko dai ba mutum ba ne mahaukacin?”.
Zuru ta yi musu da manyan idanunta, tare da rasa abin da za ta gaya musu, domin su fahimce ta. Fuu ta bar musu falon gaba ɗaya, su duka suka bita da ido har ta haura sama, Dady ya maida kallonsa ga Anty Zainab ya ce “Kin ga dai yadda muke fama da ita, gabaɗaya ta rikice, ita ba abin a yi mata magana ba wannan ciwon nata ya tashi, da haryanzu shi ma ba a san kansa ba, sai lalube kawai da ake yi a dubu. Anty Zainab ta ce “Lallai Dady wannan abin babba ne dole a san matakin da ya kamata a ɗauka, kafin abubuwa su rikice fiye da haka, Momy kin gaya wa Anty Na'ima ne?”. Girgiza kai Momy ta yi ta kasa magana saboda ta fara tsorata da lamarin yarinyarta ta, Dady ya miƙe ya yi musu sallama ya fita, ranar a gida Zainab ta yini su na tattauna lamarin Joriyya, sai bayan la'asar ta bar gidan.
Da yamma Jiniyo ya zo gidan da nufin ganin Joriyya kamar yadda ya saba yi da ƙaunar da ta wuce misali, yau saboda halin da Momy ke ciki ya sa ba ta tsaya sunyi hira da shi ba, Joriyya na jin maganar Jiniyo ta fito da sauri, ba don shi ba sai don tana son yi masa zancen mutumin nan, babu sallama ba komai ta ce
“Jiniyo” tana tsaye hannaye a ƙugu, “akwai wani mahaukacin wanda nasa muka kai masa abinci jiya ni da Dady, ka ga yadda yake cin abinci? Ka ga yadda idanunsa suka yi?”
Da farko Jiniyo ya yi dariya da tunanin soyayya ce kawai. Sai ya gane ba soyayyarsa take faÉ—a ba, sautin wani mutum daban take faÉ—a.
Nan take ƙirjinsa ya buga da ƙarfi, zuciyarsa ta yi masa nauyi mai girman gaske, ya ce “Ke kina jin zancen da kike yi? Kin manta kina da ni?”.
Cikin ko in kula ta ce “Ka yi haƙuri Jiniyo ban da lokacin hakan yanzu”.
Wannan kalmar ba ƙaramin ɓata ransa ta yi ba, ya juya cikin fushi ya bar gidan, zuciyarsa na tafasa da kishin wanda bai san ma asalinsa ba.
Yau ma kamar kullum Joriyya ta je makaranta, sai dai gabaÉ—aya yanzu ba ta mai da hankalinta wajan karatu, idan aka zo tambaya game da karatun da aka yi musu sai ta yi shiru tana tunani kamar wadda ta yi nisa da Duniya.
Malam Musa ya ce “Joriyya me ke damunki?” Bata ba shi amsa ba ta sunkuyar da kai ta ci gaba da jan biro tana zana layi ba tare da ma’ana ba.
Momy ce ke video call, da yarta da take zaune a can Dubai, cikin damuwa ta ce “Na'ima kina jina Joriyya ta shiga wani hali. Wani mahaukaci ne ya shige mata rai, ni ban ma san wace irin alaƙa ce tsakaninsu ba, ni na fara zargin ko dai aljani ne ya fito a suffar mahaukaci, yake son shafarta.
Na'ima ta yi shiru na ɗan lokaci cikin jimami ta ce, “Babbar magana, Momy kuna zaman me? Wannan ba abin wasa bane, lamari ne da yakamata a ɗauki matakin gaggawa tun da wuri, kafin al'amarin ya wuce tunani. Amma abin da tsoro a ce rana tsaka kawai ta haɗu da mahaukaci a ce tana shiga shirginsa kamar ta san shi"
"Wallahi Na'ima na rasa abin yi, da na ɗauki abin nata wasa, amma yanzu na fuskanci da gaske akwai matsalar da take buƙatar matakin gaggawa"
Na’ima ta yi ajiyar zuciya ta ce "Amma Momy ku faɗa min gaskiya wane irin mahaukaci ne haka? Me ya haɗa ta da shi? Waye shi? Ya aka ? Yaya ma take jin shi?”.
Momy ta jingina da kujera, hannunta ɗaya na riƙe da wayar, ɗayan kuma tana goge zufa duk da sanyin AC dake ɗakin, muryarta ta yi ƙasa-ƙasa kamar wadda aka sare wa zuciya ta ce
"Wallahi Na’ima tun jiya hankalina bai tsaya ba. Joriyya ta canza, ina jin tsoron kada ta faɗa cikin wani abu da ba zan iya fitar da ita ba”
"Kin san mai zai faru, zan duba idan da yiwuwar ki bani ita ta dawo nan gurina mu gani"
Momy ɗan waro ido ta ce ta ce “ Kina nufin ta koma wajanki da zama?”.
“Eh Momy idan har ba ku samu mafita ba, ina ga a nesan ta da shi, nesantawa sosai yadda za ta daina ganinsa gaba ɗaya mu ga abin da hali zai yi ”.
"Mummy gaba ɗaya wannan ba abu ne da za a jira dogon lokaci, ana nazari ko tunanin mafita ba, Joriyya yarinya ce ƙarama, babu yadda za a yi a ce rana tsaka ta tsiri alaƙa da mutum mahaukaci da ba a san daga inda yake ba, idan ya cutar da ita fa?"
Momy ta katse ta cikin ruɗewa, “Na’ima ki yi mini shiru! Kar ki kara tsoratar da ni, don tuni tsoro ya ƙara cika zuciyata”.
Na’ima ta yi ajiyar zuciya. “To Momy ki nutsu. Mu za mu nemo mafita. Ina da ra’ayi ɗaya kuma ina jin shi ne zai iya tsayar da wannan abu”.
Momy ta ɗaga kai duk da ba ta ganinta ta ce “Me ne?”
“Ki bar Joriyya ta zo nan wurina. Ki turo min ita Dubai. Ta yi zamanta a nan, sai taci gaba da karatu a nan. A nisanta ta da wannan mutumin kafin lamarin ya yi nisa”.
Kalmar ta fito a hankali amma ta huda zuciyar Momy kamar ƙusa mai zafi.
Hawaye suka cicciko a idonta. “Na’ima ke kina magana kamar sauƙi ne a raba uwa da yarinya. Yaya zan hana ta ganin iyayenta? Yaya zan bari ta tashi daga nan ta tafi tsakiyar wata ƙasa saboda wani mutum da ba mu san ko waye ba?”.
Na’ima ta ɗan yi murmushi mara annuri. “Momy mafita fa ake nema, kada ki manta ba gurin wasu bare za ta zauna ba a gurina ne. Momy ba fatana nake ba yau idan babu ke a Duniya nice zan zama uwa a gare ta, zamanta zai dawo a gurina”.
Momy ta kasa magana.
Wani abu kamar ƙwallon dutse ya maƙale mata a maƙogwaro.
Na’ima ta ci gaba da cewa, “Ki saurare ni Momy wannan yaron da kuke kira mahaukaci ban san waye shi ba, amma wani abu a jikinsa yana jawo hankalin Joriyya fiye da misali. Idan ba ku yanke wannan abin yanzu ba, zai iya kai ta ga wani hali da ya fi wannan nisan”.
Momy ta dafe goshinta. Ta tuna yadda Joriyya ta yi kuka har ciwonta ya so tashi, yadda ta mayar wa Zainab magana, yadda idan ta ambaci wannan mahaukacin sai idonta ya cika da wani haske da ba a saba gani ba. Ta runtse idanu, hawaye suka sauka a kumatunta. “Na’ima zan yi tunani. Amma zuciyata na tsoro. Yarinya kamar Joriyya an fara ɓata ta. Ina jin wani abu zai faru da ita, amma ban san me ba”.
Cikin tausayi Na’ima ta ce “Momy ki kwantar da hankalinki. Idan Nazir ya dawo zan gaya masa komai, idan kun amince sai mu ɗakkota, ba don mu raba ta da ku ba sai don a ceci hankalinta”ci gaba da tattaunawa suka yi.
Suna gama magana Momy ta kashe wayar tana mai jin idonta ya ɗauki nauyi. Ta jingina da kujera ta saki wani huci mara ƙarfin rai, zuciyarta na bugawa a hankali kamar na mace mai jiran hukunci.
Joriyya na zaune a gefen gado ta takure kanta cikin hannaye. Idonta ya kafe gilas ɗin tagar da ke kallon ƙofar gidan su.
Tun da suka dawo daga makaranta zuciyarta ke faÉ—aÉ—a da wani zafi mara suna, wannan murya, wannan fuska mai datti, wannan idanu da ke rikita mata tunani duk sun mamaye ta, ta yi wani lumshe idanu mai zurfi. Gabanta na faÉ—uwa kamar tana jin shi a wajan.
“Me yasa nake jin shi kamar na san shi?” ta furta cikin ƙasa-ƙasa da murya kamar wadda zuciyarta ke ƙoƙarin tuna abu mai nisa.
Momy na jin ƙarar shigowar motar Dady daga waje zuciyarta ta ƙara harzuƙa da sabon tashin hankali. Ta san dole ta yi masa bayani. Dole su zauna su yanke hukunci.
Zuciyarta ta yi nauyi, saboda duk hanyar da take gani duk akwai ciwo.
Sai ta dafe ƙirjinta ta furta a hankali
“Ya Allah Ka tsare Auta.”
By Amanarcool ✍️
***