FreeArewaPen original
AKWAI SILA
- 1views
- 25chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter 1
💦 AKWAI SILA💦BY AMANARCOOL YOTA/ID/NO21PAGE 1-2Misalin ƙarfe goma na dare, daren ya yi duhu sosai irin duhun nan da yake cinye inuwa ya bar zuciya. Garin ya yi tsit ba ka jin motsin komai, cikin tashin hankali da kaɗuwa take tsala gudu na fitar hayyaci, gudu take irin gudun da ba a iya sarrafa shi, gudun da ba ƙafa ke yi ba, tsoro ne ke tura ta gaba kamar an ɗaure ta da iska. Idonta na kallon gaba amma zuciyarta ta maƙale a baya. Jin sawun ƙartin mazan nan masu kama da samudawa na binta cikin kaifin mugunta. Zuciyarta na bugawa tamkar za ta yi tsalle ta fito daga ƙirjinta. Kowanne mataki da take ɗagawa yana yi mata nauyi saboda tsananin firgici, sai dai duk da haka ƙafafunta ba su tsaya ba, sai ƙara hanzari suke yi.A bayanta take jin ƙarar takun takalmin waɗancan ƙartin nan suna biye da ita kalmomi masu ban tsoro kamar hadari na fita daga bakinsu, “Ki tsaya mana, ba zamu cutar da...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.