Kamar da wasa pg 13
by @mrsomar
KAMAR DA WASA💘
Fatima Isa
Page 13
Cikin abinda bai gaza minti 45 ba jirgin su ya sauka cikin airport ɗin Murtala Muhammad international Airport dake cikin babban birnin Lagos.
Kasancewar su Anas basu ida isowa ba yasa Khalid kiran ɗaya daga cikin yaran S.Y Shattima ya ce su same su a Airport yanzu kafin ko jirgin ya sauka har sun iso saboda sanin waye ogan nasu sam baya son ɓata lokaci idan akwai abinda ya tsana to African time ne.
Sai da komi ya dai-daita kafin suka fito yanzu ma haka hannunsa rike da yaransa Naana na take masu baya Khalid a gaba.
Motace suka shiga wanda tazo ɗaukar su ta alfarma da sauri wadda yazo ɗaukar su ya fito yana salute ɗin S.Y shattima yana faɗin
"Morning Sir"
Kun san dai gaisuwar soja dare rana safiya duka morning ne.
Kai kawai ya ɗaga mashi tare da kama hannun Minal ya tura cikin mota suka zauna dai kamar lokacin da zasu dawo.
Khalid dashi yaron suka saka kayan a bayan mota.
Sai da suka ɗan yi nisa kafin Khalid ya ce.
"I think everything is normal kayi duk abinda ya dace ko? Waziri"
"Yes everything is normal. Yanzu haka na saka anyi duk abinda ya dace sannan aikin nan na sojas club har yanzu basu ƙarasa shi ba da alama yanda suke jan aikin zai iya kai one month basu gama ba"
"Ka faɗa masu nan da zuwa jibi nake son su gama aikin idan kuma basu gama ba su tabbatar sun maido min kuɗina"
S.Y shattima ya faɗa cike da ƙasaitar nan tashi.
Da sauri wanda aka kira da waziri ya ce.
"Ok Sir an gama"
A haka suka isa wata unguwa wanda ta amsa sunanta unguwar masu faɗa aji duk wani shege daya tada kansa da naira zaka samesa a victoria island.
Har suna gab da shiga gate ɗin babban gidan, wani mai gadin da yake sanye da uniform ɗin soja a jikinshi da jar hula ya buɗe gate ɗin da girmamawa.
Shattima bai ce komai ba, har suka shigo cikin katafaren gidan, wanda ko daga bakin titi zaka hango cewar ba talakawa ke rayuwa a ciki ba. Tsabtaceccen muhalli, ƙamshin flowers, fitilun bango masu shape, da bututun ruwa da ke fesowa da sauƙin gaske.
Waziri ya yi parking a wuri mai kyau, Khalid ya fita da sauri ya zagaya motar, ya buɗe masa kofa yana cewa "Welcome back home Sir"
Shattima bai amsa ba, sai kawai ya kamo hannun Iman, ya ce da Milal,
"Tashi mu shiga ciki."
Naana ta fito a hankali kamar mara gaskiya idanunta na yawo kowane ɓangare na gidan. Babu abinda ya sauya na gidan. A hankali ta bi bayan su da kaya a hannu.
Waziri ya ce da Khalid. "Ka shiga da kayan ni zan ida fito da sauran"
"Yes Oga"
Khalid ya faɗa yana hararar Waziri. Dariya ya yi yana faɗin
"Sorry Sir"
Komi Khalid bai sake ce mashi ba.
Suna shiga ciki da Mama Binta suka ci karo tana masu sannu da zuwa duk ta gyara duk abinda ya kamata.
Cikin minti goma, komai ya daidaita. Yaran sun shiga dakin su. Shattima ya zauna a babban parlour da ke facing garden, hannunsa rike da phone. Ba tare da ya yi magana da kowa ba, ya tura glass ɗin window gefe yana kallon flowers.
Naana ta tsaya a bakin kofa kamar wadda aka sallama daga lefi. Tana tsaye, tana jiran izini, amma ba a furta komai ba.
A ƙarsashe, murya mai sanyi da amo amma cike da ƙarsashi ta fito daga bakin Shattima
"You can take the guest room at the left. Don't go beyond there"
Naana ta girgiza kai da ladabi, ta ce
"Nagode"
Ta ɗauki jaka ta nufi ɗakin da ya nuna mata. A zuciyartarta take faɗin
"Gani a Lagos amma sai dai kash.."
Bata ƙarasa ba ta yi shiru..
Gidan shiru kamar ba mutum a ciki. Fitilun bango na kunne da launin mai kyau da ƙawata waje ga sanyi mai kama da sanyin damina. Naana tana zauna a gefen gadon dakin baƙi, ta cire takalminta cikin natsuwa, ta zuba ido jikin ƙofa kamar tana kallon wani da take tsamanin zuwa.
Numfashinta bai daidaita ba. Tana jin kukan zuciyarta
“Na shiga gidan da babu iyaye, babu yaya, babu soyayya. Gidan da kallo ɗaya zaka gane ba gidan wasan yara bane”
A gefe ɗaya na dakin, ta ajiye jakarta. Bata buɗe ta ba. Bata cire hijabinta ba. Bata kwanta ba. Sai dai.. tana ji kamar cikin sabon gwaji ce da zuciyarta ke shakku da karfi.
A bangaren S.Y. Shattima, yana zaune a babban falo. Bayan ya gama karanta wani takarda daga military base, ya danna wayarsa, ya kira Khalid.
"Ka tabbata duk abinda zaku mana order ya kasance ba mai nauyi bane"
“Yes, Sir. Minal da Iman. Da Madam ma duk abu iri ɗaya xaka amso masu"
Ya katse kiran nan take. Ba tare da sallama ba. ya miƙe, ya nufi bedroom ɗinsa.
Ƙarfe tara da rabi na dare.
Naana har yanzu zaune take ba ta yi barci ba. Sai dai ta lumshe idanu kadan, taji ana kwankwasa ƙofa.
“Yes?”
Ta amsa cikin dauriya.
Tana buɗe ƙofar Khalid ne. da leda a hannu, yana cewa
“Oga ya ce a kawo miki dinner. Bai san ko kin ci komai tun safe ba.”
Naana ta gyada kai kawai. Bata iya cewa komai ba.
“Nagode.”
“Okay ma. Goodnight.”
Ya fita cikin girmamawa, ya rufe ƙofar a hankali.
Ciki ta koma ta zauna tana mai buɗe ledan.
Ta kalli abincin. White rice da chicken stew da bottle water a gefe. Tana jin yunwa, amma zuciyarta ta cika da takaici, ta rasa inda zata soma.
A ɗakin Shattima, ya kwanta ne ba barci yake ba. Idanunsa a rufe, amma jikinsa da hankalinsa na can, cikin duhu. Bai san me Naana ke ji ba kuma bai damu ya sani ba. Amma wata zuciya a ransa tana sake faɗa masa
“Ka cika alƙawarin Jamilah. Ka kula da yaran nan. Kuma... ka tsare duk wanda ke tare da su komai soyayyarsu”
****
Asuba ta gabato, gidan ya cika da hasken wutar corridor suna walkiya.
S. Y. Shattima ya farka kamar yadda ya saba da cike da ƙasaita nan tasa. Tamkar kullum kiran sallah farko ke farka dashi daga barcin da yake.
Sai da ya shiga bathroom ya watsa ruwa ya ɗauro alwala kafin.
Ya fita zuwa masallaci na gidan, wanda aka gina. Bayan sallah, ya ɗan ja lokaci a cikin masallacin yana azkar, sannan ya dawo gida yana ɗaure fuska kamar wanda ke da hari a zuciyarsa.
Naana kuwa, tana sallah a cikin ɗakin baƙi, tana addu’ar Allah ya sauƙaƙa mata sabuwar rayuwar da ta shiga cikin gidan da babu iyaye ko soyayya, sai jarabawa.
Bayan sallah asuba AB ( Ibrahim) ya shirya breakfast. Babu hayaniya a gidan. Minal da Iman suka farka. Naana ce ta taimaka musu da brush da wanka. Duk da cewar akwai mai aikin dake kula dasu amma haka tatashi ta tayasu, kamar yanda ta saba duk lokacin da take tare dasu dama can akwai shakuwa tsakanin su, nutsuwar ta ya sa yaran ke bin umarninta da sauƙi.
Shattima yana zauna a dining table, yana duba laptop. Naana ta kawo yaran suka zauna. Ab ya kawo tea da butter bread da fruit salad chicken breast and potato egg roll da sauransu dai .
Bayan sun gama ci, Shattima ya ɗaga kansa ya dubi Naana kallon kai tsaye ba tare da jin nauyi ba.
“Prepare their uniforms. School bus will arrive by 7:30. Don’t make them late.”
Naana ta gyada kai.
“Toh.”
Khalid ya zo da jakar Shattima. Yana cikin full uniform. Sai ya juya ya dubi Khalid, daya shigo tun ɗazu
“You’ll drop me at the office before 8. I want you to pick me again by 6pm. Kasan akwai abubuwa da yawa a gaban mu”
“Yes, sir.”
Yaran sun gama shiryawa. Naana ta yi musu gyara. Minal ta saka takalma, Iman ta ɗora jakarta. Dukansu suna da wayau da natsuwa.
Har cikin zuciyar Naana, ta ce
“A ganina yaran nan ba sai mahaifiyarsu na raye ba zasu samu kulawa nima mahaifiyarsu ce. Wannan mutumin idan ina kula dasu tabbas zan samu soyayyar shi.”
Yaran suka fito suka tsaya a gefensa.
“Bye Daddy.”
Shattima ya ce
“Take care. Be good.”
Sun shiga bus. Shattima da Khalid suka shiga motar. Saboda su Anas har yanzu basu iso ba.
Gidan ya koma shiru.
Naana ta koma ɗakinta, amma zuciyarta tana cike da tambayoyi da tsoro. Wannan gida, wannan sabuwar rayuwa komai sabo ne, komai tsanani ne, amma har yanzu zuciyarta na ƙoƙarin daidaitawa.
#Son zuciya
#Soyayya
#Yaudara
#Makirci