Kamar da wasa pg 14
by @mrsomar
KAMAR DA WASA💘
Fatima Isa (mrs Umar)
Page 14
Katsina state
Lamari kamar wasa sai gashi wannan watan har ya kare sam babu labarin Papa babu dalilin shi sam yaki tura mana kuÉ—in abinci daga karshe ma sai ya cewa Ummie an rufe masa account sai bayan wata biyu za'a buÉ—e wannan dalilin yasa ko Ummie bata sani ba naje office domin bincika naji dalilin da yasa aka rifewa mahaifina account wane laifi ne ya aikata haka mai muni da har haka ta faru dashi sai dai kash.
Wai ana zaton wuta a makera sai aka risketa masaka babu abinda na dawo dashi gida sai kayan bakin ciki da ban haushi ji nake kamar na yi aman zuciyata ko hakan zai sa na samu sauki a cikinta a yau ji nake duk duniya babu wanda nake jima haushi irin Papa na, ji nake na tsani maza duniya ganinsu nake duka halin su É—aya tunda har Papa na zai iya cin amanar Ummie duk irin soyayyar dake tsakanin su ai ko wane irin namiji ma zai iya.
Kai maza duka sunan su É—aya ne babu bambanci.
A cikin wannan tashin hankali na iso layin mu a kan mashin É—in mu da nake tukawa wanda Allah ne kawai ya kawo ni gida, dan sam bana ganin gabana da kyau.
Kamar daga sama Ummie taga na faÉ—o cikin É—akin ko sallama babu na fara cewa.
"Wallahi Ummie, komai ya ƙare! Everything is messed up! Do you even know what Papa did?"
Numfashi Ummie ta sauke kafin ta ce.
"Hmm ina jinki meya faru"
Abayarta ta cire ta jefar cikin zafin zuciya ta ce.
"Ummie meye ma bai faru ba kina da labarin duk abunnan da Papa ke mana aure ya ƙara a wajen duty ya sake aure a Batsari ya aure mai sayar da tuwo tuwo shi yasa Papa ya sauya lokaci ɗaya. Ummie, Papa keeps lying to us!he keeps pretending there's no money he knows exactly the nonsense he's been doing there! Wai me yasa maza suke haka ne baya ganin irin faman da ake bazai tsaya ya bamu ilimin daya kamata ba haba dan Allah"
Tunda ta fara magana Ummie ke kallonta har sai data lafa kafin Ummie ta saki murmushin daya fi kuka ciwo ta ce.
"Kin gama to idan kin gama zauna muyi magana ta fahimta"
Duk da jannat na cikin ɓacin rai haka ta zauna saman tsohuwar kujerar ɗakin su cike da bakin ciki tana dafe kanta.
"Jannat kenan tun ba yanzu ba na fahimci babanku aure ya ƙara dan zan iya bada shaida baya neman mata sannan baya shan giya baya shan taba ke ko goro baya ci kin ga ko sauyawar shi lokacin ɗaya dole zanyi mamaki. A binciken da na yi na gane ya yi aure shi yasa yake turo mana kuɗin da duk yaga dama. Na ɓoye maki wannan maganar ne dan nasan baki da hakuri. Amma ko yanzu hakuri zamu yi komi yana da lokaci haka Allah ya nufa mahaifinku sai ya ƙara aure.."
"Kut*b*chan waye ya ƙara aure badai Papa ba?,"
Sadiq ne da wannan kalma dawowar su daga makaranta kenan suna shigowa Amina na bayan su.
"Idan bashi ba to wa ake magana ai wannan tsohon ya gama damu mtss"
Jannat ta sake faÉ—a tana sakin tsoki.
Amina ce ta iso wajanta da sauri yarinyar da bazata wuce shekara 10 ba amma sai shegen wayau ta ce.
"Haba aunty Jannat shi yasa biri yayi kama da mutum shi yasa Papa ya cire mu daga Naowa ya mayar damu Natsinta duk dan ya kara aure saboda ya kuntata mana to wallahi baza mu yadda ba ko Ummie ta hakura mu baza mu hakura ba sai mun dauki mata ki"
Murmushin Ahmad ya saki yana mai aje jikanshi ya zauna kusa da Ummie yana cewa.
"So, what can you possibly do to him now that it's already too late? Ko me zaku yi fa yanzu a banza dan lokaci ya riga daya kure Papa ya yi nisa yanzu baya jin kira"
"FaÉ—a masu dai Ahmad wannan fushi nasu duk bashi ne mafita ba addu'a kawai zamu dage"
"Haba dan Allah Ummie ki daina faɗin haka dan Allah kamar abin bai dame ki ba. Wallahi sai dai idan Papa ba cikin barrack ɗin nan zai kawo ta ba dan idan har ta yi kuskure ƙafarta ta shigo cikin barrack ɗin nan wallahi sai ta yi dana sanin sanin wani soja a rayuwarta"
Tun kafin Ummie ma ta sake magana ta tashi ta shige bedroom duka da kallo suka bita. Dan zuciyar Jannat dukan su tsoro take basu.
Shiga ta É—aki sai data jerawa Papa kira biyar bai É—auka ba sai a na shida ya É—auka yana faÉ—in.
"Ke kam Jannat meke damunki kin kira mutum É—aya biyu bai É—aga ba ai sai kiyi hakuri idan ya gani ya kira maybe yana wani uzuri"
Kukan da nake ɓoyewa ne na saki lokacin ɗaya murya ta na fita da sauti na ce.
"Papa kace haka mana tunda kaje can ka aure wata shegiya yar tuwo tuwo ka manta damu har kana mana karya an rufe maka account"
"What is wrong with you? Are you mad? Ni kike faÉ—awa maganar banza dan ina wasa dake dan ubanki. To idan ma uwarki ta sakaki ki faÉ—a mun maganan banza, bata isa ba kuma zanzo gidan zanyi maganin ku"
"Wallahi Papa babu abinda ka isa ka yi wa Ummie mu akan wannan ƙaruwar banza kuma wallahi sai na yi maganinta..."
Wayar kawai taji an zare an kashe saboda sam bata ji shigowar Ummie ba.
"Baki da hankali Jannat ai komi babanku ya yi baici ace kina mayar mashi magana ba shi É—in mahaifinki ne"
Kuka na share tare da jan majina na ce.
"Ummie dan mahaifin mu ne sai kuma ya shiga hakkin mu. Ya hana mu abinci dan ya yi aure.
Wallahi Ummie idan da ban yi niyyar shiga aikin soja ba to yanzu zan shiga kuma Papa sai yasan ya wulakantamu dan wallahi bazan taɓa taimaka mashi ba Allah dai ya bamu lafiya da tsawon rai"
Ajiyar zuciya Ummie ta sauke tare da girgiza kai ta fita dan tasan ko ta tsaya ranta ne kawai zai ɓaci.
Bayan kwana biyu
Magana fa har ta gama zaga bariki matan layinmu sun samu abin faɗa har takai ana mana habaici a kaikaice wannan batu ko ya ƙara zafafa mun rai shiyasa yau na tashi a shirye da ko wacce shegiya ina jira, rabon ayi maman Jamila ta watsa habaici dai-dai ina shirin zuwa toilet. Hahaha dama mai nema cikin duhu balle ya samu sarari.
"Bakin wasu fa ya mutu aure dai anyi shi shi yasa shiru kake ji babu rashin kunya"
Dariya nayi ina ajiye bokitin da zanje wanka na kwashe da dariya ina faÉ—in.
"Gara mu nahaifin mu aure ya ƙara ya kuma raya sunnan ma'aiki. Alhmadullillah tunda bai aje karuwa ba kuma muna saka rai ko ya haihu da ita ya'yan yaran sunna ne ba yan gaba da Fatiha ba"
"Sai ki faÉ—a min ubanwa ya aje karuwa"
Dariya na sake saki ina mai taɓe baki sam babu tsoro a cikin idanuna na ce.
"Kira mijin ki shi zai baki wannan amsa amma ba Aisha Adam Ruma ba"
Na bata amsa ina mai dukawa na É—auki ruwan tasha gabana tana shirin kai hannu jikina da sauri na rike hannun ina faÉ—in.
"Kul na raba ki koda wasa kar ki yi wannan kuskure dan wallahi zan baki kunya ne a cikin jama'a zaki yi dana sanin zama block É—in nan. Kuma idan kina ganin wasa ki gwada kiga aiki da cikawa wallahi"
ÆŠayan hannun take shirin kaiwa mijinta ya daka mata tsawa kuka ta fashe tana faÉ—in...
#Son zuciya
#Soyayya
#Yaudara
#Makirci