ABUNDA KE 'BOYE...

44

by @surayyahms

ABUNDA KE ƁOYE💫
arewabooks@surayyahm.


⏯️4️⃣4️⃣
ibaad yana karasowa ta wajen motar zainab Arifah tay sauri ta sauka ta fito waje dan karma yagane a buge da kwaya take sosai..

tana sauƙa daga jeep din tay leaning back dinta to stand firmly wasu irin mayun idanu ta zuba masa ayayinda yake tahowa lokacin kwakwalwrta yakasa auna mata yadda zatay tafara ma rabuwa da wannn hadadden gayen wanda duk duniya ta zaga haryau bataga namijin da ya balain dacewa da ajinta kamarshi ba.

idanunta taji ya ciko da ruwan hawaye zazzafa, tuna nasihan iyayenta da kuma dalilinsu da suka bata kai koma ba dan haka ba, kwana nan fa tay kisan kai snn babanta ya rufa mata asiri kai tsaye, bayan nan kuma yadau arzikinsa me bala'in daraja ya dorata akai babu shakka kodan hakan ya canci ace ta iya sadaukar masa da komi na rayuwarta saidai kuma batajin soyayyar ibaad abune wanda da zata iya binnesa cikin saurki, dan duk jimawan datay acikin tunani kwakwarlwrta ya kasa bata wata mafita, abu daya kawai tasan she is very sure of inhar ta rabu da ibaad to karshen rayuwarta ne yazo dan akan abun duniya kam sam sam bazata taɓa iya tsallakeshi ta auri wani namijin ba...

sosai ta shirya daukar mataki but she has to ask him few questions kafin tasan me zatayi nan gaba.

muddiin ibaad zai aureta ta amince zata aje musu komi nasu da suka bata ta rabu dasu tabi ibaad a musu aure, idan kuma bai amince ba...she has a good  secret plan for all this eida ways tasan dai rasa ibaad a rayuwarta baya cikin options dinta gabaki daya.

idanunta nakansa bata ko kiftawa har ya iso gabanta yay mata sallama bataji ba cos she was soo lost in her tots har saida ya kira sunanta snn tadawo cikin hayyacinta suka gaisa...kai tsaye yace "u wanted to see me...wani irin gyara tsyuwarta tay tareda sauke ajiyan zuciya tace "yes..

cikin gyada kai yace okay go on kinga ankusa a kira sallah..

cikin lumshe ido da budewa tace.. a farko dai i wll like to apologise gameda abunda mummy sukayi ma sisternka ayaanah kusan a nitse yace its unfortunatez But thanks..dan shiru tay can kuma muryanta na yar rawa ahnkli tace ibaad? yadago ya kalleta da kyau baice komi ba, da wani irin yanayi akwayar idonta tace" dama akwai wasu yan tambayoyine da nake so na maka but pls answer me sincerely its very important to me..girarsa na sama a dage yace "i am all ears..go on..

cikin sace ajiyan zuciya tace and pls keep ur answers short..

yace" Enuf of this rules na gayamaki zan wuce masallaci soon ko

tace ok..uhm...dama inaso nasani ne what is actually going on betwn us kagane like inason nasani are we in a real rlshp?

kai tsaye yace "No..next question pls..

cikin hadiye bakin cikinta tace "okay, have u ever felt sumting for me? like in ur hrt baka taɓa jin kana kaunar ace nazamo matarka ba?

..yace "Bantaba ji ba.

cikin lshe ido da budewa tace "but u're aware that i cant even breath witout u ryt? nd kana nufin dagaske ne you cant marry me saboda kana da wata macen daban??

yace "hold on. where are we getting at with this boring cnversation

da karsashin bruise ego a muryanta mekama dana izza da fushi cikin tsimewa tace i just want to knw.. bcos i want us to get married next week kaga ynxu i am settled kaima ure almost free. you dont have to love me now, ni inasonka. kuma bazan iya rayuwa batare da kai ba ai anayin aure ahaka.. magana tay masa kamar na asalin yar kwaya

shiru yay harta gama magananta ya kalleta yace" zainab uve got to leave cos seriously banda wann lkcin..

da taurin kai a idonta tace but i am not leaving here untill u come to ur sense nd agree with me. nide aure kawai nake so muyi, bazan iya auren kowa ba saikai, tana gama furta hakan ta bude motarta ta jawo jakarta ta ciro cheque book na apex bank of america ta yaga leaf daya aciki ta miƙa masa lkcin hannunshi na cikin aljihu sai bai karba..

desprately tace pls take this,write any amount of money nay alkwari i will compensate the girl ure obsessed with kuma i will sponsor our weding inma shiri ne bakayi ba, ive got a house nd everything..U have nothing to think abt

kwayar na wainata ba acikin hayyacinta ba tafara kkrin cusa masa cheque din a aljihunsa da wani irin sauri,

shikuwa yana zare hannunsa daga aljihun ya wanka mata wani irin gigitaccen marin da dawuri tafasa ihu tabi ta dauke hannunta ajikinshi ta ja baya tana maidafe wajen kusan a rude .

da muryan kuka ta dago zatay magana ya hade ransa ya nunata da yatsarsa yace ive heard enuf of ur insults keee ya isheki haka.. nd for ur information daga ke har ubanki bakuyi kudin da zaku saye soyayyata ko na macen da zan aura kwanan nan ba..ke a tunaninki har wani rufin asiri kike dashi da zaki zo nan ki kirani kina gayamin wannan kalar maganan banzan?who did u think u're zainab cos to me u're nothing jst a regulat spoil brat with no self worth.. wato dan jiya andoraki akan arzikin da bakisan zafinsa ba, wanda tun kafin kizo duniya aka gama ginasa shine har kin samu audacity da zakizo kimin burga dashi ko?toh ai ke karamar yarinyace wallah infact ure classless nd very stupid..i ques dis shud be ur last time talking to me naga raini tsakanina dake yafara yawa. ya girgiza kai "...youre just lucky ure my cousin sister today da wallh sainaci ubanki anan wajen naga waye gatanki, bana son raini nd if ur empty skull have failed to comprhend that then dats ur misery, my life is already moving on without you inkinga dama karki nemi mijin auren dazaki siyeshi da kudi ki aura ki tsaya kina hauka wata rana kuwa zan miki abunda baki tsammani inkika sake kulani...

hannunta dafe da kuncinta hawayenta ya fara zuba tace son da nake maka ne hauka??
then u have no idea what love is..u have no idea what i did bcos of ur love da har kake cewa hauka, wallah karya kake bakasa isa ka rabu dani ba...

yace thank goodness i dint ask you to do all those things... ur life ur choices ryt?? ke da Allah kiwuce..uve got to go.. nace bazan aureki ba kije kinemi wani ki bashi kudin.

dacan hawayene ke sauka akan fuskarta kamar ruwa tanata kallon bakin ibaaad din amma dataji dirin shigowar jeep din bappa zaidu cikin compound in da wani irin karfi ta fashe masa da kuka kamar dukanta akayi....

baice mata komi ba ya kama hanyarsa yay cikin gidan yabarta atsaye, da karfi take kukan har bappa zaidu yaa karaso yay parking car insa ya taho wajen da mamakin irin kukan fitar rai datakeyi.. yace zainab meyafaru ne what is happening? da wani irin gunjin kukan makirci tazo jikinshi tace uncle zaid bansan meye nay ma ibaad ya tsaneni ba, if he cant like me atleast i am a human being he shudnt be hurting me with his words.."

dan jawota bappa zaidu yay dan yadda take kukan sosai tabashi tausayi da muryan lallashi yace "kiyi hakuri doter its okay..kidena kuka...duk lallashin nan sai batace masa komi ba ta rungumesa saida har tay kukan makiricinta na kusan minti biyar ta kara daga mai hankli sosai snn ahnkli ta kwace kanta sounding depressed tana hawaye gwanin tausayi tace "shikenan uncle zanyi hakurin tunda abunda yake so kenan, amma uncle kace masa shima yana hakuri nimafa ba yin kaina bane nake sonshi dayawa haka...dede nan ta kara fashewa da kuka wani irin tausayi tabashi sosai tace' i will like to go home now kaina namin ciwo kaima inna taba maka wani abu kayafe min dan Allah.

tana fadin hakan ta juya cikin sauri ta bude motar ta shiga within few minutes ta waina shi ta fice a compund din da sauri..

hanklin bappa zaidu a tashe ya shigo cikin gidan yanamai kwalawa ibaad kira daga kasa wanda tun be sauko ba ammi babba tay maza ta fito dan tasan bai taɓa kwalawa ibaad kira ahaka da tsawa ba

'yaa zaidu lafya kuwa naga ranka a bace

bai amsa ba saiga ibaad din ya sauko kasa cikin ladabi yace
sannu da dawowa bappa naji kamr kana kirana..

bappa zaidu yace "yes..inaso ne insan meyafaru yanxun nan awaje tsakaninka fa zainab Arifah? and why are you treating her like this ynxu idan wani ne yay haka ma kannenka zakaji dadi?u dont like her nd so what..dat doenst mean u shud keep hurting her with ur words gaskiya ban ji dadi ba..

kan ibaad na kallonsa kasa yace "Kay hakuri bappa..nayi kuskure. saidai bansan me tace maka ba nidai zuwa tay tacemin wai tanaso muyi aure next week snn ta ciro cheque na dollars ta bani wai she wll sponsor the weding shine nace mata karta sake min haka. nd beside bappa...nifa bance zan aureta ba

jin hakan yasa bappa zaidu yadan sauko da tempernsa da mamaki yace zainab dinne ta gaya maka haka nd she gave u a dollar cheque???

ahnkli ibaad yace eh kuma hakane kawai ya faru tsakanina da ita...

da mamaki bappa zaidu yace "toh?? ikon Allah indai hakane kam toh ai bata kyauta ba dan ba a siyan aure da soyayya da kudi. but kaima ai da kayi amfani da hanklinka awajen tunda kaga ka girmeta kuma ita mace ce u shud have mind ur words amma bakomi kaje kawai zan nemeka anjima

..cike da girmamawa ibaad ya amsashi snn ya haura sama

yana wucewa Ammi babba ta kalle bappa zaidu da tsananin haushi a muryanta tace amma wallah kabani kunya yaa zaidu
...toh wann wani irin danyen hukunci ne me kake nufi da bin bayansa dakayi dan kawai yarinya ta kawo masa kudi dan tsabar tsiya na bibiyarsa shine zai ki karba?? kudin gadon dayake juyawar yake burga dashi wallah ya kusa karewa cutar kansa ma zaiyi inbe aure zainab arifah ba dan wallah rufa masa asiri zatayi.


karkada kansa yay kawai bai amsa mata ba ya kama hanya zai haura sama tabi bayansa tana masifa "aikin banza aikim wofi yaro bakomin komi ba amma ana gani yana cutar da yarinya ana zuba masa ido, waikomi ya furta sai ahau kai a zauna ahau bashi gaskiya kuma fa munsani fa dan dan ba'aso ran uwarsa ya baci ne ake nonnokewa ba ason masa fada waishi dan gwall
..mmtswwwww

wani uban tsaki taja suna dede gabar sashensa tay kwana ta wuce dakinta da sauri ta dau wayarta tafara kirar anty safeera dan ta shafa mata gulma.


dagata bangaren zainab arifah kuwa tana ficewa agidan ta share makirtaccen hawayen datay ma bappa zaidu dan dama bana gaske bane so take kawai ta hada wani zazzafan plan wanda shine take gani amatsayin mata chance dinta na karshe na samun cikar burinta akan ibaad..

tana kuma sane da maganan ruqqy ranar da zata mutu na cewa aure tsakaninta da ibaad wundt be posbble, even if it will be, then its going to be her bgst karma..but damn all this magic nd astrologies...damn her parents..duk tay banza da su.

yanzu lokaci ne da zata cire batun iyaye da kawaye ta dauki kwakkwrar mataki a hannunta koda mutuwa kuwa zatay in ankaita gidan ibaad wallah saita aureshi....

da wann maganganun aranta
ta isa gidansu, tana gama parking ta sauka ta samu hjy hamida a falo suka gaisa kamr ba abunda ke damunta

hajya hamida tace ur dad will soon be home for dinner we wll be expecting you at the table by 8pm

babu yabo babu fallasa tace okay mummy, daga haka ta haura sama tana shiga room dinta ta kore dukkan maids dinta tace suje can can waje sai ta kirasu..suna ficewa ta kulle kofar da key ta ciki

snn ta wuce gaban drwarta dake cikin mega walk in closet dinta tajawo wata jaka ta ciro piles of cocaine ta fasa ledan kadan da zuka zukan farshem kantinta takamfato a paper tazo dakin tazauna tasha sosai yahaura mata kai taji ta fice ahayyacinta dan abunda take shirin yi ba abu bane da hankali zai dauka ita kanta tsoron karta mutu ahaka takeji but is her one nd only last chance batada wani mafita kusan dole ne ta aikata.


kayan jikinta ta cire ta saka wani mekyau,snn ta zauna akan chair ta dau scissors me kaifin gaske ta rage tsayin gashinta dakenan dede kafadarta sama sama bata yankeshi duka ba, just enuf to prove that she is mentally tortured nd unstable, nan ta zubar da gashin kasa snn ta
jawo paper da biro ta fara rubutu kamr haka.

Daddy, mummy...Ban san ko me zaku ce ba, amma ina fatan a karo na farko zaku saurare ni da kunnen basira ba tare da kun kalle ni kamar wata yarinya marar hankali ba. najima ina kokarin yin murmushi saboda ku amma wallahi na gaji... Na gaji..da jin kamar babu wanda yake ganin zafin da nake boyewa kullum game da rayuwr soyayyata.

tana gama rubuta wann ta aje papern akasa snn ta sake dauko wani fresh ta rubuta

Dearest Ibaad, masoyi na..Kai ka fi kowa sanin cewa ban taɓa roƙonka komai na duniya ba abu ɗaya kawai nakeso kabani wato zuciyrka da kulawarka da lokcinka amma Sai ka guje ni kamar ni wata mummn abace, Na san baka sona, na sani tun tuni. Amma da zafi sosai dayau ka fito ka nuna min kamar ban cancanci komai daga gareka ba.

tana kaiwa nan ta sake yagewa pagin ta jefar akasa
..ta dauko final paper ta rubuta..

the three of you shud knw dat i respected ur decisions, kuma shiyasa zan yanke ma kaina wann hukuncin bawai dan na saɓa muku ba sai dan bazan iya saba maka ba daddyna.ina rokonka kayafemin amma bazan iya rayuwa babu ibaad ba, na yi iya ƙoƙarina, na yi kuka, na yi haƙuri amma babu wanda ya kula da damuwa ta. Idan wannan rubutun nawa ya dameku ko ya taɓa ku, to hakan kaɗai ya nuna cewa akwai ɗan ƙaramin wuri na fahimta a zuciyarku da ya rage min. kada ku damu dani. inna mutu komi zai wuce mana, kowa zaiyi rayuwarsa cikin sauki..ni kuma kabari na zai zamo wuri ne da babu wanda zai iya tambayana me nake ji aciki, nide dan Allah ku yafemin!

yours zainab arifah..

tana gama rubuta last part din tay wani irin darriyar mugunta sann shima ta yarda dashi kasa ta dauki wayarta taduba internat tay dan browsing sai tay maza ta maida hoton ibaad a screen inta tay setting maid alarm 10min sai dau scizzors ta yanka wani karamin jijiya a hannunta atake jininta ya fara zuba along with the effect of drug alarm dinta na bugawa ta wuce uncounsious.

dede nan private maid inta elizabeth ta karaso jin alarm din tay tsammanin hala wanka zaynab arifah take son tay dan baifi minti 30 ya rage babanta ya dawo ba tana isowa tay knocking sai shiru, tun abu na wasa wasa har ta sauka taje ta karbo spare key tazo tabude kofar tana ganin zainab arifah da scizzor a hannu akwance ga jini ga yankakken gashi ga
takardu akasa a mugun razane ta fasa ihu tayo waje

hajya hamida duk ta dauka shirmensu da zainab din ne jim kadan kawai taga elizbeth ta shigo a ruguje tana ihun sunan zainab Arifah kusan arikice hajy hamida ta miƙe ta bita taje ta tarar da halin da ake ciki

da sauri suka applyng pressure a inda jinin yake zuba sosai

kafin kace wani abu gidan ya balain rikicewa marmaza hajy hamida ta kira mijinta kafin ya iso harta riga ta isa emergency da zainab wanda atake aka shige da ita cikin Resuscitation Room batare da tunanin ko zatay rai ko ma ta mutu ba..


acikin tsananin kaduwa da tashin hankli hajiya hamida take jeka ka dawo a ward din sai nanata ta shiga uku takeyi cikin kuka da dukan wasiqun a hannunta tana karantawa tanajin wani irin tsoro da fargaban rasa yarta mai tsanani yana lullumeta

jim kadan ƙofar wajen ta buɗe da wani irin karfin tashin hankali prof ne ya shigo ciki da sauri tareda gaggawa da wani irin yanayi da ko shi baisan wani hali yake ciki ba, yana tahowa kamar iska da sauri sauri gudu gudu jikinsa yana rawa rawa  kamr an zuba masa ruwan kankara kusan a rufe ya damke hajy hamida yana cewa “Ina take? Ina Zainab Arifa? Ina Arifah? kusan a muryar da ba tasaba jinsa ba yake maganan  duk hnklinsa yakai kolowar wajen tashuwa, wani irin kuka hajy hamida ta miƙe tsaye dashi babu hankali ajikinta ta bashi wasiqun jikinta na kyarma tace alhaj yanxu nan suka shige da ita ciki ta zubar da jini yayi yawa na shiga uku alhaji yata kenan kwalli daya na shiga uku

tana maganan idonsa nakan rubutun hannunsa na rawa rawa, har saida ya gama karantawa snn ya ja numfashi, tsayuwar cak yay jin Kalmomin nata namai sare masa zuciya kakkarfan jiri ne yaso ya kwashesa yay saurin  mannuwa da bango ya dafe kansa sosai, snn ya rufe idonsa da ƙarfi kamar yana ƙoƙarin hana kansa amincewa da abubuwan da ya karanta yanxu


kusan a rikice yace “hamiida Me muka yi wa yarinyar nan? Me ta rasa a duniya?”yanxu akan wann tsinannen yaron har zainab zata kashe kanta??ya furta muryarsa ta karye da karfi.

hawayen hajiya hamida na gangarowa tace alhaj ni damuwata da zainab arifah bata nuna min komi ba, bata yi magana ba, she even told me yanxu zata sauko a ci abinci only for her lock her self up and try to take her own life wallah wallah idan yata ta mutu sai dai ayi biyu babu yaron nam bai isa ya shaki numfashi a duniya ba dan da hannuna zan kasheshi


prof ya yi wani dogon jan numfashi ya share fuska da tafin hannunsa ya kara kallon letters din suicide note ɗin nata ya kara memeta karanta kalmomin dake cikinsu cikin natsuwa duk dama zuciyarsa tana farfashewa.


zuciyarsa sai tambayrsa yake wai shin yarsa zainab ce ga rubuta hak  ta rubuta haka kuma a gidansa kuma wai ba lura ba.” ji yay atake hannunsa ta yi sanyi ya kasa numfashi na dan lokaci.

yace lahawla wala kuwwa sam ni na kasa gane kan yarinyan nan i tot zainab is way more evolved than this, batay tunanin halin da  zan shiga ciki ba?? lallai yaron nan ya cuceni


cikin jin zafi hajiya ta ce tana kuka alhaj ai duk shawararka ce, saida nace maka tun tana karama a rabata da wann gurbataccn soyayya ta yaron nan dan Bana son a ce ita ce da matsala kace min sam sai tagirma toh gashnan ta girman babu abunda ya canza saima wanda yay qaru .


baice mata komi ba ya jingina da bango idonsa arufe numfashinsa ya yi nauyi inda dede lokcin ne wata Nurse ta fito dukansu suka miƙe da sauri sukayo kanta


tace sirr maaam kuy hakuri the  Doctor is stabilizing her…amma kusata a addua

atake hajiya hamida ta narke da wani irin kuka prof ya rike kujera saboda tsananin raunin zuciya.

“Zan iya ganinta?” ya tambaye nurse din cikin murya mai taushin da ba a saba ji daga gare shi ba.

Nurse ta girgiza kai tace
“Ba yanzu ba sir… but she’s
fighting…

cikin rutse idonsa ya dafe kirjinsa for hours suna zaune cikin jimami daga su sai masu gadinsu.


daga can gidan kuma babu wanda yasan meke faruwa,
dan tunda uncle moh yay asarar kudadensa da time dinsa ya gama jiran ayaana ransa ya turmusa yay baqi ya dawo gidan yazo zai sauke haushinsa da masifarsa a gida hajiya mairo har tace masa ai ayaanah tun safe ta fice bata dawo gidan ba taje wajen ruthy sai sann yaji dama dama saidai bakaramin disspointed ya zama ba....

dake sosai anty safeera tana lura dashi ynxu sai jikinta tuni ya fara bata, haka tay ta tambayarsa meyasa mood dinsa ya canza, yace mata ai matsalar business ne kawai sai tay shiru ta kyalesa batace mai komi ba.

har saida ayaana ta dawo gidan kafi talura taga duk ya kasa zama yana ta neman hanyar da zai saka akira masa ita amma dake idon da anty safeera tazuba masa yau yawa yasa bai samu wann daman ba


washe gari kuwa da sassafen Allah labarin abunda ya faru da zainab arifah yazo kunnen hajya mairo anty safeera ce tazo tasanar dasu dan itama a bakin wata kawar hajy hamidan taji da safe cewa zainab has tried to commit suicide last night...

wann labari yasaka kaf gidan aka rude hajiya mairo ta fara ihu tana koke koke gida ya zamo kamar na mutuwa.

tun safen ta dinga kirar bappa zaidu dake monday ne wyarsa na falo shikuma yana daki bai gani da wuri ba, ammi babba ne tazo da gurmi ta hau gaya masa..

wayar dan uwansa uncle moh ya kira yaji yana busy yay sauri ya kira hajiyan kawai cewa take masa yazo ataro duka suje asibitin tare yar zayyanu kenan kwalli daya a duniya da kyar Allah ya bashi maza maza aje masa dan batasan wani hali zayyanu zai shiga ciki ba.

the story came as a shock to ibaad ya sha mamaki amma bai nuna a fuskarsa sosai ba kowa ya fara shiri zasuzo family house asan me za'ayi

within 20 min bappa zaidu da ammi babba da ibaad da sultana duka suka sauko kasa jin wani sabuwar tashin hayaniya awaje na tashi tundaga gate kakejin karar shgwan motocin polisawa

mota guda aka turosu maza sunkai sha biyar suka tunkare su bappa zaidu

"bappa zaidu yace officers lafya naganku haka dayawa a gidana?

cike da girmamwa babbansu yace "lafiya kalau sir. nan ya ciro papern arrest warant ya mika ma bappa, yana maicewa sirr we are directed frm above to come nd arrest ur son person of Dr ibaad almansur with immidiete effect...

cikin katsesu da tashin hakali bappa zaidu yace and on what charges...arrest kuma? dis is abslutely ridicoulos!! me yayi?

nan babban cikinsu yahau ma bappa zaidu bayanin wai charges ne akan Intentional Infliction of Emotional Distress (IIED), he is also going to be held in detention for infliction of emotional trauma to zainab arifah leading to self harm..

its just a protective custody detention, some interrogations nd detntion for some hours.

wani officer yana kkrin sakama ibaad handcuf bappa zaidu ya daka mai tsawa yace heys dont u dare... barawo ne, ko kuma kisan kai yay da zaku taru masa


ibaad ya kalle bappa zaidu yace bappa karka damu i will go with them ku kuje gidan 

bappa zaidu yace Dats not ur decision to make young man...

driver ya kira aka saka su ammi babba da sultana zuwa family house hanklin sultana yay bala'in tashi tun a mota take kuka ammi babba kuwa Allah Allah take su isa ta bada kanun labarai


daga nan kuma bappa zaidu bai sake an saka ibaad a motar polisawa ya daukesa dakansa suka bisu police station din, ya zauna a waje suka shiga da ibaad ciki


fadin irin tashin hanklin da family house ya shiga da ammi babba taxo ta gaya musu antafi da ibaad an kulleshi tareda bappa xaidu bazai kiyastu ba hankalin kowa saida  yay mummunan tashi

abubuwan suka taru suka ma ayaana nauyi a kirji musmn ma tunda ammi babba tafara zuba wani irin karya da makirci agaban hajiya mairo..

nan ta kwashe labari a juye ta gaggaya musu cewa ai fada sukayi da zainab din jiya da yamma,kuma zainab din ta bar gidansu tanata kuka basu san me ibaad ya gaya mata dahar taje tay tunanin kashe kanta  tace musu kuma bappa xaidu yaxo yagani yana daure masa gindi duk da ma sunga halin da xainab din ta shiga ciki

labarin take bayarwa tana kuka agaban hajya xaka rantse da Allah agabanta akayi komi dan babu irin karyan da batay akan ibaad ba, kuma ta kwashe komi tace lefin bappa zaidu ne dama tajima tana gaya masa ya sakalta ibaad, baya ganin leifinsa ko yay laifi baya masa fada snn yana nuna fifiko da bambamci, cikin habaici tarinka cewa ai yanayi ne dan ya burge ammi karama bata dai fito fili ta kama suna ba amma babu kalar gori da habaicin da batay ma ammi karama  ba.

tun jin wann batu hajy mairo ta birkice ta fara tsine tsine tana zagin ibaad, ayaana tabar wajen ta koma daki tanata kuka dan tasan bazai taba yuwa yama xainab wani abu me muni da zaikai har haka ba, sultana ne take rarrashinta sai safiya data fice wajen jin gulma..

ammi karama batace komi ba tay shiru musm dataga kowa ne yahaura sama, uncle moh, ammi babba da su anty safeera duk magana daya suka taru suna gayawa hajiya mairo cewa laifin duka na ibaad ne kuma ya samu daurin gindi ne daga bappa zaidu .

cikinsu babu wanda yaso yay bincike ko yasan asalin meke faruwa kusan kowa ya hau dokin xuciya sai tay shiru abunta batace komi ba.

uncle moh ya kira prof yafi sau talatin amma bai daga ba maza maza yace ayi shiri kawai aje asibitin tunda bappa zaidu yana tare da ibaad a police station...


daga asibiti kuwa kusan sabida content na hard drugs ajinin zainab arifah yasaka bata farka akan lokaci ba it took her 6 good hours snn aka samu ta dawo hayyacinta she wake up very weak duk an lakaba mata IV fluids da pressure dressing a hannu

tunda asubah data farkan iyayenta kowa yaxo jikinta kowa da salonsa na nuna mata soyayya amma kuma hawaye take sam sam taki tace musu komi tun suna mata lallashi har suka aje so agefe suka fara mata fada kowa ya harzuƙa yana fadin mata asalin manufarsa akan tarayyarta da ibaad tuntunin nan saiyau suka iya cire so da gata sukahau bayyana mata asalin yadda basu kaunar ibaaad kuma suka tsane tarayyarta dashi kwata kwata..
saidai basu sanar da ita cewa har sunsan an kama ibaad din ba

their words of hatred akan tarayyarta da ibaad din'nt hurt her much sabida ta riga ta jima da lura da hakan musmn ma awajen mummynta hajiya hamida da tasan ko kadan bata kaunar dangin ubanta bare kuma ta haɗa jini da wanda take ganin kamar bai kaisu arziki ba.

duk hargaginsu da lallashinsu shiru kawai tay tana hawaye batace musu uffan ba wanda hakan ya kara daga musu hanklinsu sosai.

strickt security akasa a inda suke, wajajen 10am manyan gidan gabaki daya suka taho asibitin a motocinsu amma haka kememe aka hanasu shiga ciki..

hajiy hamida sosai ta haukace ta haura can sama da fushi da tsana tace Burin yan uwansa kenan dama su kashe masa yarsa kwalli daya, dan shima a cusa masa baqin cikin da zai kashe shi, snn idan ya mutu a dauki dukiyarsa abasu

tana masa kuka ta maimata masa wann maganan cikin bori da fushi yafi sau hamsin..

daga wajen kuwa bakaramin rikici akayi da hajiya mairo ba in kaganta ma daukawa xakay an mata mutuwa, can daga baya saida akazo aka mata wayo akace ai zainab din tana cikin wani hali ne ana kkrin dagata ba asok hayaniya kuma hukuma na ciki ana bincike shiyasa ba ason kowa ya shiga kawai suje gida.

bada son ransu ba ammi babba ta dawo da hajiya mairo uncle moh ne da anty safeera kawai suka tsaya a reception na asibitin.

ammi karama kuma daga wajen ta wuce police station duba halin da su ibaad suke ciki...

tana zuwa station dake ana matukar daraja familynsu sharply aka kaita wani waiting room ta samu bappa zaidu a zaune yana kan waya suka hade ido dan hawayen datake dannewa atake suka fara sauka katse wayar yayi har tagama karasowa gareshi tun basu gaisa ba yace haba Fatima meyasa kema kika zo nan kuma baga ni nan anan ba?

da matsanacin damuwa a kwayar idonta tace "yaa zaid Kay hakuri kawai so nake naga halin da rayyan yake ciki

bappa zaidu yace 'interrogations ne kawai babu komi ba tunda bawani laifi ya aikata musu ba neman fitina ne kawai. the highest they can do is to detain him here kuma insha Allah i wont let that happen.

cikin lumshe ido da budewa da karyayyen zuciya tace Amma meyasa rayyan zai saka kansa acikin wnn matsalar..cikin fashewa da kukan da yazo mata bazata tace kaikuma kamar baka ganin lefinsa. yanxu duk cikin gidan kowa yana fushi dashi, hajiya ta dau abun da zafi dan Allah inde rayyan ya aikata wani abu na cutarwa akan zainab kawai ana gaya masa gaskiya ni wallah banason hakan yaje ya jawo masa karin baqin jini acikin gidan nan dan baida kowa a duniya inbasu ba.

cikin sassauto da muryansa kasa yace haba fatima yau kece da kanki kike furta min wann maganan? i tot kinfi kowa sanin cewa ibaad kamar dan cikina na daukesa meyasa kike tunanin inhar yay wani abi ba daidai ba zan zuba masa ido in kyaleshi...in dis case he is just a victim of circumstances tsaya masa yakamata muyi bamu hau dora masa laifi ba...ita hajiyar tasan asalin meyafaru ne??

ammi tana share hawayenta tace ni bansani ba amma ai maman sultana ce tazo ta gaya mana wai fada sukayi da zainab din jiya shine ya mata wani abu hartaje tay tunanin kashe kanta..kuma tace tun jiya kay shiru baka masa fada ba duk dama agabanka akayi komi

ahnkli yace fatima
ive personally talked with zainab jiya, nazo kam na sameta tana kuka nd she told me they had a fight..da naje na tambaye ibaad kuma yace min tazo tace masa ne akan suyi aure next week, snn ta dau dollar cheque ta bashi claiming wai zatay sponsoring auren...

i scolded him sabida tace min yagaya mata magana dabai mata dadi ba, but dan yaqi karban wnn qudurintan kuma sai nahau masa fada akan me?an taba siyan soyayya da kudi ne ko ana dole ne?..kuma kekanki kinsan da wuyane in iyayentan ma suna sane da wann abun, wallah inda ya biye mata wani matsala na daban zata jefashi aciki...karshe suce yay manipulating yarsu ya sace musu kudi, ko su masa sharri cewa shi yy influencing maganan aure akan yarsu..na lura kamar kaf kuna yin abune kamar bakusan waye ubanta ba. he will protct his child bazai taba karban laifin yarsa, so why i cant protect mine, badan ganin darajar su hajiya ba da nima fa ina da dama in shigar dakara akansu ai ba a relshp na dole, sun takura ma yaron nan tunda jimawa ohh wato mune bamu iya kaiwa kara ba ko? is not fair mana haba fatima...nayi ma yara na alkawari bazan musu auren dole ba saidai a bisa qaddara kuma kema kinsani, i cant force ibaad ya aure wacce bayaso gaskiya...so wnn kananan maganan raihanatu da hajia kawai kibarsa dukn su basu san asalin meke faruwa ba...kema kiy hkuri ki kwantar da hanklinki babu abinda zai same ibaad in sha Allah..

shiru tay kanta na kallon kasa har ya gama maganan kafin can ta share hawayenta ta dago kai cikin sauke ajiyan zuciya tace "toh shikenan..inde abunda ya faru kenan da sauki
dan wallah hanklina ya bala'in tashi da irin magngnu da ake kanyi akansa acikin gida.

yace "karki damu in few hours zamuje gidan in sha Allah babu komi sai khairan..


daga haka suka zauna awajen har sai kusan 12:30am to 1pm ma rana kafin suka sake ibaad daga interogation room ya fito ya samesu

bappa zaidu da ammi karama suka hau tambayarsa me akace masa bai boye musu komi ba ya gaya musu

after a while bayan sunyi maganan sai hukuma sukazo sukace zasu rikeshi detention sai jikin zainab yay improving out of danger zuwa yamma azo a daukesa

...bappa zaidu ya karkada kai dan tuni ya gane cewa prof ne kawai yake bada oder a case din nan bawai zunzurutun aikin gaskiya akeso ayi ba

dake shima ya kira mutanensa hakanan yasaka adinga saka masa ido, wanda yasa baiwani damu ba yasako ammi karama agaba suka dawo gida

sun iso gidan arnd 3 na yamma tun a mota yake bawa fatima hakuri saidai tunda hajiya ta gansu bataga ibaad ba tafara sabon hauka tana tuhumar bappa zaidu me ake ciki ita kuma ammi karama batace komi ta wuce dakin ta tanata hawaye sosai.

tun a wann lokcin bappa zaidu yafara ma hajiya bayanin abunda ya faru jiyan amma ta nuna masa kamr bata ma gane meyake fada ba, kowani furuci dake fita a bakinsa abaibai take jinshi, gani take bin nayan rayyanu kawai yakey ,zaa kashe mata jikarta zainab arifah, za'a kuma saka danta zayyanu acikin baqin ciki da kunci...

abu kadan saita cemai aibkao zaidu dake kai kana da zuka zukan yaranka ai dolene abun bazai maka zafi ba, mutuwa fa ba wasa ba..inda kai adali ne da kamata yay ma kace ma hukuma akai rayyanu prisona
inyaso yaje can yay muguntr sa, acan yaro shaidani, wallah wallah ubansa baida wann baqin zuciya, mustapa ba haka yake ba dan yafi kankara ma sanyi gashi da hakuri amma kuma yaje yahaihu mugun yaro
aikodan tausayin rai ya kamata rayyanu ya amshe yarinyar nan amma dake kuna goya masa baya toh gashi nan abunda ya jawo..

bappa zaidu dayaga ba fahimtarsa zatay ba hudu na yi ya mike ya wuce masallaci daga nan ya fita ya koma station din dan yajira time na releasing ibaad yay ya dawo dashi gida.


iyaka su maheer ne kawai suke kiransa uncle moh ko sau daya bai kira ba duk dama yaga miss calls din bappa zaidun na tun safe.

shida da anty safeera dakyar aka barsu suka shiga wajen zainab arifah suka duba ta saidai haryanxu taki magana da kowa sai kuka da yamma liss iyayen suka matsa akan zasu wuce da yarsu gida dan abata cikakken kulawa acan

baisani ba already zainab ta riga ta hada plan dinta da nala kafin tay aika aika ta tura ma nala text cewa tazo duk asbitin daka kwantar da ita ta aiwatar mata wani plan....

a fuska zakaga kamr she is too traumarized to even speak, amma tuni nala tazo ta zaga tabiya likita makudan kudi akay abunda zaayi aka faking result dan ta saka iyayenta su rasa duk wani makama.

ana gama processing sallamarsu doctor ya kawo ma iyayen tarin bayani game da Somatic Complaints kamr body weakness + headaches + fainting yace musu yanxu fa inhar zainab bata samu cikar burinta nan kusa ba she wil be attacked by frequent body weakness, headaches har da kuma sumewa on a regular basis.. snn zai iya haduwa mata da Adjustment Disorder me tattare da intensed Emotional Collapse where she will become too sad too withdrawn, too fragile.

in aka kira sunan ibaad zatana firgita, zataki cin abinci, zatana yawan kuka zatana tsaya cak tana kallon bango. nd with time zata samu full emotional damage wanda inbasu wasa ba sai ankaita therapy na watanni shida awani waje.

bakaramin tashi hanklin iyayen zainab arofah yay ba, dan karfin gwiwarsu na batun tsayawa kyam akan batun su na hana auren tun anan ya fara gushewa musmn ma hajiya hamida datake ganin rayuwar yarta ya kare kenan inhar suka kyaleta ta samu cikakken tabu hankli

zainab arifah is busy pretending nd watching them danma ta dada tsoratasu suna kaita gida ta dinga kuka tana kwalla kiran sunan ibaad tana jan zuciya tana suma kamr ba acikin hayyacinta sai can kuma kaga ta farfado gabaki daya sai taki musu magana taki kuma taci abinci..


komi a idonsa anty safeera akayi ga ammi babba na kiransu akai akai ana bata labari haka zata kara maggi da gishiri taje gaban hajiya mairo tazauna ta zazzageshi duk saida ta tayar ma tsohowa da ciwon hawan jininta, ranar karshenta itama ruwan drip aka saka mata sai Allah ya isa take jama rayyanu duk dama tasan abunda take furtawa yana ma ammi karama zafi sosai amma ji take kamar ai ɗa baifi ɗa ba

babban damuwarta shine rayyanu zai mata asarar jikarta snn zai jawo gaba ya tsananta atsakaninsu da danta zayyanu dan tasan bazai taba yafewa ba


wajajen 5:30 bappa zaidu ya gama processing release na ibaad, mutanen prof din har wani cewa suke in wani abu ya sake tashi zasu kara nemansa

bappa zaidu yaja tsaki ya sako ibaad agaba bai sake sunje family house tunda ya gama lura da take taken hajiya mairo ba gaskiya take da niyyar bi damuwarta na kasa ya dauki laifi dan kar na sama yay fushi

suna isa gida ibaad yay wankansa yazo masjid yajasu sallah banda da maheer daya kirasa bai sake wani magana da kowa ba after ishai bayan sunci abnci bappa zaidu baice masa komi ba yace masa kawai yaje yay bacci gobe da safen duk zasuje family house a zauna ayi magana

cikin wann daren fake draman da zainab arifah tama iyayenta bana kadan ba, suna bada baya zata sha drugs tay ta wasu abubuwa sukuma hanklinsu duk sai ya hargitsa ya tashi...

ranar haka aka zauna cirko cirko basuyi bacci ba washe gari sassafe prof yagama tunaninsa ya zaunar da matarsa yace mata bazai iya rasa rayuwar yarsa kwalli daya akan wann case din ba tunda haka arifah din ta zaba so be it...amma kuma saiyaje shi can wajen mahaifiyarsa sun tattaunawa ya dawo snn zaizo ya saka ma yuwar auren nasu tsauraran dokoki wanda dolene abi, itama zainab arifah din dole tabi. kusan babu yadda hajiya hamida ta iya itama haka ta goya masa baya dan kawai su ceto rayuwr yarsu....

da sassafen ya shirya cikin manyan kaya ya fito banda tea dayasa acikinsa baisha komi ba shidakansa yadauki babban motarsa as early as 7am da sassafen sai gashi nan a family house fuskarnn tashi a matukar daure kamar wani mala'ikal daukar rai.

yana kammala parking tun awaje yay gamo da uncle moh da jallabiya ajikinsa kowani gaisawar arziki basuyi ba suka karasa ciki, cikin sashen hajiya mairo direct yay dashi wanda tunda tagansa tafara koke koke tana maganganu akan abunda ya faru, mrzamaza tasaka a kira mata zaidu da ahalinsa duka suzo gida ayi magana anan atare...

maheer is already on his way dan da sassafen yabi jirgi zai taho, mujaheed ma tun jiyan yafara neman exit dan abarsa yaxo amma abun baiyu ba

mujaheed ya gama waya da bappa zaidun kenan an taru a dinning za'a breakfast saiga kirar ammi karama wanda da gangan hjya mairo tace lallai ita zata kira musu zaidu ai inyaga kirarta ne zai dauka da wuri kuma yazo akan lkci....

tana kuwa kira dake wayarna hannunsa ya dauka cikin nitsuwa da sanyin murya yace "fatima antashi lafia? da wani irin sauri ammi babba ta aje cupin shayi ta zuba masa wani dan uban ido mai tafe da mugun harara

after uttering few words yace toh bakomi muna zuwa snn ya katse wayarsa ya aje akan table yay banza da batun ya cigaba da breakfast dinsa hankli kwance dan baiga abunda zai sakashi yaqi cin abincinsa akan zuwan prof na

tajira tajira taji ya musu bayani sai shiru kai can dataji abun ya cicciyota sai tace 'yaa zaidu gidan lafya daiko ina dai ba jikin hajya bane ya kara tashi?? a dan dakile yace "a'a kudai kammala breakfast dinku ahankli sai muje muji..

suna gamawa kuwa kowa ya tashi sai ya kalle ibaad yace 'ibaad kai kazo kasameni a dakina yanxu zai aikeka office dina inyaso inka dawo saika wuce can ka samemu

cikin girmamawa ibaad ya amsashi, suna shiga dakin ya bashi aiki da akalla yasan zai dauke sa 2-3 hrs kafin yagama dan kwata kwata baijin yau zai iya zuba ido aje can gidan asako ibaad agaba a dora masa laifin komi snn agaya masa bakaken magana dan yana tabbacin cewa hajy mairo intana gaban danta zayyanu ba lallaine tabi bayan gaskiya ba....

he prefer to face them alone than ya barsu su taru suci ma ibaad mutunci da sassafen nan.


ibaad ne ya fara ficewa da aikan kafin nan suma suka shirya suka fito shida matarsa da yarsu sultana suka wuce family house....

coment nd share ur tots

#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*


*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED*


#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025