Page-14
*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
(*F.W.A)*©✍️
⭐⭐⭐
Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد.
❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁
Free book📓
By
*Aisha G Umar*
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_
Page1️⃣4️⃣
Da saurin gaske na yunƙura kafin ya sauke ƙafar shi, na sanya hannayena da niyyar wai ya taka hannuna ba tare da ƙafarshi ya taka kwalbar ba, wai don in tare shi ban yi ma tunanin ba zan iya tare shin ba, tun da shi babban mutum ne.
Ƙara na saki mai ƙarfi saboda azaban da na ji ya shige hannuna sakamakon taka hannuna da Dady ya yi ba tare da ya ankare ba, kwalaben da ke ƙasan suka shige bayan hannuwa, sai lokacin Dady ya farga da abun da ya ke faruwa, kafin ya gama ijje ƙafar ya yi saurin janyewa idonsa a kaina.
Ni kuwa bayan ya ɗage ƙafar ta shi na yi saurin ɗauke hannuna ina kallon bayan hannun na wa da fasassun kwalabe su ka shige, sai jini da ke da ya fara fita wannan ma wai ba taka ni sosai Dady ya yi ba. Hannuwana suka hau rawa take na fara kuka saboda zafin da na ke ji sosai.
Cikin tashin hankali Dady ya saki wayarsa ta faɗi ƙasa tare da zuwa inda na ke da sauri yasa hannu ya kama na wa hannayen, sai kuma ya kai idonsa gurin kwalaben ya kuma dawo da idonsa kaina, ni kam idona na kan hannuna kawai da ya ke fitar da jini.
Jin ihun nawa ne ya fito da Momy da sauri, daidai lokacin Dady ke ƙoƙarin fitar da ni daga falo, don ya kaini asibiti. Momy kuwa zuciyarta ne ya tsinke domin ta yi zaton ko duka na ya yi sannan ya ke son fitar da ni daga gidan, duk da zuciyarta ya ƙi amincewa da hakan.
"Dadyn Abba lafiya?me ya..." kafin Momy ta ƙarisa maganar ta yi shiru haɗi da zaro ido waje, saboda arba da ta yi da jinin da ke kwance a kan tayis, sannan kuma ga kwalaben da su ka haddasa hakan, zuciyarta ya tsinke ko da ganin haka da sauri ta fice domin lokacin har Dady ya fitar da ni a falon yana nufar inda motarsa ta ke, da gudu Momy ta isa inda mu ke Dady na ƙoƙarin sa ni a motar, sai a sannan ta ga hannayena da ke ta faman tsiyar jini.
Momy ta cire gelen da ta ɗaura a kanta ta yafa, cikin ruɗewa ta shige motar inda Dady ya sa ni, Dady bai yi magana ba sai wucewa da ya yi ya shige mazaunin driver, ni kuma sai kuka na ke yi domin kamar zafin ƙaruwa ya ke yi min, Momy tana min sannu.
Lokacin da Dady ya ja motar Zulai ta fito, zuciyarta na bugawa, saboda bayan ta zo zata share ta ga jini a wurin alamar wani ya taka, sannan ga hayaniyar da ta ji, dafe zuciyarta ta yi da tsoro ta ce, "na shiga uku!" Ta faɗi zuciyarta na tsinkewa, da sauri ta koma don ta kwashe.
Bayan mun isa asibiti aka fara min tritment ɗin hannayena, na sha azaba sosai gurin cire wannan kwalaben saboda sun shiga sosai, jikin Dady gaba ɗaya ya yi sanyi ko magana ba ya iya yi, sai kallona da ya ke cike da tausayi yadda na ke hawaye da rintse ido a duk sanda za a cire kwalbar, Momy ma cike da tausayawa ta ke ta yi min sannu, ta ma ƙi bari ta ga yadda ake cire min, saboda yadda ta kawar da kanta gefe, sai jakar Abbana da ke hannunta.
Haka har aka gama muka dawo gida. Muna zaune a falo hannayena duk an zagaye da bandage, fiska da idanuwana a kunbure saboda kukan da na sha, idon Dady na kan hannayena domin kuwa ya san saboda shi ne na shiga wannan halin, saboda kareshi kada ya taka kwalbar ya ji ciwo shine ni na sanya hannuna, juyawa ya yi yana kallon Zulai da ke zaune kanta ƙasa.
Nan ta fara ba da haƙuri akan kuskure ta yi ba da gangan ba ne. Sauke numfashi Dady ya yi ba tare da ya ce mata komai ba, lokacin Momy ta fito da abinci a hannunta, ta zo kusa da ni ta zauna tana cewa Zulai ta je kawai amma ta rinƙa kula sosai, "taya zata je kawai bayan ga abun da kuskuren na ta ya ja?" Cewar Dady fiskarsa na neman fito sa ɓacin rai, ya kuma cewa, "maza yanzun nan ki ba Nuriyyah haƙuri!"
Da sauri na juya ina kalonsa jiin ya kira suna na, Momy kuwa da mamaki ta ke kallonsa ganin kamar abyn da ya faru da Nuriyyah ya dameshi, duk da ta san shi mutum ne mai tausayi d kulawa, amma yadda ya yi mata magana ɗazu, ba ta yi zaton zai damu da yarinyar ba, ba ki na rawa Zulai ta ce, "don Allah ki yafe min Nuriyyah, wallahi ba da gangan ba ne, ki yi haƙuri".
Cikin sanyin murya na ce, "ba komai, Allah ya riga da ya nufa hakan zai faru, na yafe miki saboda na san ba da gangan ki ka yi ba", kallona Dady ya yi sannan ya kawar da kai gefe, cikin jin daɗi Zulai ta yi min godiya sannan ta tashi ta bar wurin. Momy ta dubeni cikin kulawa ta ce, "sannu Nuriyyah, amma wai ya aka yi ki ka ji ciwo a hannu haka? Kuma ta bayan hannu, da ma ƙafa ne sai ince takawa ki ka yi" kame-kame na fara yi.
Momy na shirin sa ke yi min tambayar Dady ya ce, "because of me" da mamaki Momy ta ce, saboda kai kuma Dadyn Abba?" "Eh saboda ni Nuriyyah ta ji ciwon nan, ba tare da na sani ba na zo saura kaɗan na taka kwalaben shine ita ta sa hannayenta don ta tare ƙafana, don kawai ta taimake ni kada na raunana" cewar Dady yana kallona.
Har lokacin ni kuwa idona akan hannayen na wa kawai ba tare da na ce komai ba. Itama Momy kallon na wa ta yi fiskarta alamar Allah sarki. Dady kuma yana gama maganar ya miƙe daga kan kujerar da ya ke tare da kallon rigarsa da ke ɗauke da jinina da ya zuba a kai, ya ce, "lokacin sallar azahar ya yi" ya faɗi tare da wucewa don shiryawa zuwa masallaci.
"Yata me yasa ki ka yi haka? Me yasa ba ki yi masa magana ba? Yanzu dubi yadda ki ka ji rauni" cewar Momy tana kai hannunta kan bandage ɗin hannuna, ɗagowa na yi ina faɗin, "Momy lokacin ya riga da ya iso da ƙafarshi wurin, kuma ni ba zan iya bari ya taka ba, saboda Dady mutumin kirki ne" dafa kaina Momy ta yi tana murmushi yayin da idanuwanta su ka ciko da ƙwalla, ta kuma cewa "to amma ina za ki je da jakar da ki ka saƙala a wuyanki?".
Sai da na yi da kaina ƙasa sannan na ce, "Momy ba na son saboda ni kirinƙa samun matsala da Dady, shiyasa dama zan tafi" zare ido kaɗan Momy ta yi ta ce, "ki tafi!? To ina zaki je? Ba na so kada ki sake yin haka kin ji?" Giɗa mata kai na yi da cewa ta yi haƙuri ba zan sake ba. Dady da ya ke tsaye bayan ya canza kayan jikinsa, kuma ya ji abun da na faɗi, ba tare da ya ce komai ba ya zo ya wuce mu.
Abinci Momy ta fara ba ni cikin kulawa, ina ci ina kallonta har sai da ƙwallah su ka ciko a idona, saboda yadda hakan ya ke sani tuno da Ummana, hannu Momy ta sa ta share min hawayen da ya zubo min kan firka, cikin damuwa ta ce, "me ya sa ki hawaye kuma 'yata Nur?" Murmushi na yi mata da jin ta kuma kirana da sunan da Umma kaɗai ke kirana yauma, sannan na giɗa mata kai alamar babu komai.
Bayan ta gama ba ni abincin, mu ka tashi mu da niyyar zuwa yin sallah, Momy ta ce da ni mu je ta taimaka min gurin yin alwala saboda yanayin hannuna......
"Me ya sameki à hannu Nuriyyah?" Cewar Sadiya cikin damuwa bayan sun dawo makaranta. Asma'u ma da sauri tazo tana kallon hannun sai kuma ta kalleni damuwa da mamaki ya wanzu akan fiskarta, murmushi na sakar musu ina faɗin, "à ah kar ku damu fa, kawai ɗan rauni ne kwana biyu shikenan" cikin kulawa da damuwa su ka ce min sannu.
Nan su ka zauna muka fara hira da su kamar 'yan uwana, Asma'u ta na yi min hirar makarantarsu, nima ina ba su labarin makarantarmu har da islamiyya, muna à haka Momy ta zo ta kiramu mi je dining mu ci abinci, na ce na ƙoshi saboda ba ta daɗe da ba ni abinci ba, amma si Asma'u su ka ce dole na je mu ci tare.
WASHE GARI.
Momy ce ke waya tana cewa, "to ba damuwa insha Allah gobe zan kaita, kin tabbata guri ne maj kyau? Na tambaya ne saboda ba na son na kaita inda zata sha wahala, tun da har ta shiga hannuna to haƙƙi na ne in samar mata da wuri mai kyau, saboda inganta rayuwarta, to nagode sai kun jini zuwa goben" abun da ta gama faɗawa matar da su ka yi waya da ita kenan.
Tana sauke wayar idonta ya sauka akan Dady da ke tsaye tun ɗazu, fiskarsa à haɗe saboda ya ji abun da ta faɗi a wayar, sai da ta yi masa murmushi sannan ta ce, "yauwa Dadyn Abba, dama ina son yin magana da kai, don Allah so na ke ka bani wasu 'yan kuɗaɗe in haɗa da nawa, so na ke na yiwa Nuriyyah siyayya 'yan kaya da wasu abubuwan, na samu wani gidan marayu, yanzu ma haka da wata daga cikin manyan wurin na yi magan, gobe idan Allah ya kaimu zai kai Nuriyyah can, shine na le son yi mat siyayya..." Kafin ta ƙarisa Dady ya yi saurin katseta da cewa..
Last page
___________________________________________________
Himm me kuke tunanin Dady zai ce?
Mu kasance a next page don jin me zai faru gaba?
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_