💔NAUYIN BAKI👄💔 Na Uwar Batoorl
39 _ 40
💔NAUYIN BAKI....👄💔
Na
Uwar Batoorl.
𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍
🅿️ 39 _ 40
⭐️
Khausar ficewa a ɗakin ta yi ta wuce sashin Sadeeq, ganin azahar ta yi tana tunanin ko zuwa sannan ya tashi a baccin, amma ko da ta duba bai tashi ba, hakan ya sa ta ja mishi ƙofa ta fito ta dawo wajan Umma, suka ci gaba da jujjuya lamarin da jimami.
***
Sadeeq idanuwanshi a kan wayarshi ya iso cikin palourn, hakan ya sa bai lura da kowa a palourn ba ya ɗauka ko suna sama.
"Sannu da fitowa Yaya Sadeeq", Khausar ta faɗa tana washe baki.
Maganar Khausar ya sa Sadeeq ya sanya wayarshi a aljihu, tare da ɗagowa yana sakin ƙayataccen guntun murmushi, ya taka a sannu har ya ƙarisa inda Khausar da Umma ke zaune, a wajan ƙafar Umma ya zauna a ƙasa tare da ɗaura kan shi a saman cinyar Umma, cikin haɗaɗɗiyar muryarshi ya ce, "Barka da hutawa Ummanmu."
Idanuwan Umma cikowa suka yi da ƙwalla na tausayin Sadeeq, amma tayi ƙoƙarin mai da su, tare da ɗaura hannunta a kan shi, kwantaccen gashin kanshi mara yalwa ta shafa, tare da cewa, "Barkanmu Sadeeq, barka da dawowa daga asibiti, sannunka da tashuwa, Allah ya maka albarka, Allah ƙara maka lafiya da haƙuri da jumriya, Allah ya tabbatar da abinda yake mafi alkairi a rayuwarka Sadeeq, Allah ya zame gatanka kuma majiɓancin dukka lamuranka, Allah ya tsare ka da tsarewarshi ya kare ka da kariyarshi, Allah ya baka tsawon kwana mu ga ƴaƴanka, Allah ya sa da kai da ƴan uwanka duk ku sanya ni a gidana na gaskiya, ka yi haƙuri Sadeeq, ka bai wa zuciyarka haƙuri ka kuma sanya mata salama, Allah na tare da mai haƙuri, kuma duk abinda ka ga baka samu ba a rayuwa, to dama tun fil'azal wannan abu baya rubuce a ƙaddararka ne, amma muddin Allah ya rubuta maka samun abu, to ko ana ha maza ha mata sai ka samu, ka miƙa lamuranka ga Allah Sadeeq, kuma duk abinda Allah ya yi kai dai ka gode mishi ka kuma sanya imaninka a kai hakan ne alkairi gare ka, addininka da ma zuri'arka."
Lumshe idanuwa Sadeeq ya yi, wani irin nitsuwa ne da ƙwarin guiwa ke ratsa shi, tabbas uwa jigo ce a rayuwa, addu'ar uwa rahama ce ga lamura, duk tsawon shekarun da yayi yana dakon so, bai taɓa jin makamanciyar natsuwar da yake ji a yanzu a zuciyarshi ba, duk da kuwa yana tunatar da kanshi karɓar ƙaddara ko wacce iri ce, amma dai yau da abin yake daga bakin Umma, ya fi sanya shi natsuwa.
Hawayen da Umma ke ƙoƙarin haɗiye wa ne ya gangaro tare da ɗiga a bayan wuyan Sadeeq, hakan ya sanya Sadeeq ɗagowa da sauri, girgiza kan shi ya soma yana faɗin, "Umma kukan me kuma? Dan Allah kada ku mana kuka Umma, khairan da yardar Rabbi."
Umma share hawayen ta yi tare da murmushin ƙwarara guiwa, kamar yadda ya yi magana kuma yake kallonta cikin ƙwarara guiwa, tana murmushin ƙarfin hali ta ce, "Ina matuƙar son ka da auta, na fi kowa baƙin cikin ɓoyewan da ka yi, amma duk da haka ina addu'a muddin ku alkairi ne ga juna to Allah ya mallaka muku junanku, idan ba alkairi ba kuma to Allah ya ba ku haƙuri."
"Amin Umma", Sadeeq ya faɗa yana duƙar da kai tare da shafa bayan wuyanshi.
Khausar da ke gefe ita ma tana share ƙwallan cewa ta yi, "In sha Allah ma su alkairi ne ga juna Umma, wallahi Yaya Sadeeq ya fi dacewa ya auri small Mum, Allah dai ya iya mana da abinda ba za mu iya ba."
"Amin Khausar", Umma ta amsa.
Sadeeq ta wutsiyar ido ya kalli Khausar, ya ɗan murmusa tare da cewa, "the cry don't fit you, so ki bar wa jikokin Abba su yi", a taƙaice yayi maganar, kuma da sigar raha duk da babu hakan sosai a fiskarshi, sai dai a zuciyarshi kawai wanda ke cike da ƙaunar mahaifiyarshi da tilon ƴar uwarshi.
Umma ta ce, "Ai kuwa ta bar wa masu jajayen kunnuwa su yi, ita ta girma ai."
Sadeeq a taƙaice ya ce, "Afuwan Umma."
Murmushi Umma ta yi tare da shafa kan Sadeeq, saboda ta gane a kan maganar Sadiya yake bata haƙuri, hakan ya sanya ta ce, "Allah ya yi albarka ya shige mana gaba Sadeeq."
"Amin Umma", ya amsa yana miƙewa tsaye, tare da sake duba agogon da ke maƙale a rantsattsiyar hannunshi, sai da ya numfasa sannan ya ce, "Masallaci zan wuce Umma, daga nan zan yi gida na gai da Mama."
"Ya kamata kam ka leƙa Mamarka, dan yau saboda kai har da asubanci, ta bugo mana sammako, wannan Mama taka kana bata wahala Sadeeq", Umma ta faɗa tana ƴar murmushi na yaba soyayyar Mama ga Sadeeq.
Shi ma Sadeeq murmushin ya yi, bai kuma cewa komai ba ya musu sai ya dawo, ya juya ya fice cikin ingirman tafiyarshi mai burgewa, masallacin ya wuce kai tsaye, kamun a ta da sallah ya dinga gaisawa da jama'a, waɗanda suka san Sadeeq ba lafiya, suka dinga mishi jaje tare da fatan ƙarin sauƙi, dan Sadeeq mai jama'a ne sosai, mutuntawa da girmamawa da kuma gaisuwa su ne tsakaninshi da kusan kowa a anguwar, duk dai wanda suka san juna.
Ana idar da sallah, bayan shafa addu'a, Sadeeq ya fito masallaci ya nufi gidan Mama, cikin wannan takun nashi mai kama da na izza da ƙasaita yake tafe har ya isa ƙofar gidan, wanda ke da madaidaicin ƙaramin gate dan motar Umar, da kuma ƙaramar ƙofa ta shiga.
Ƙaramar ƙofar Sadeeq ya tura da bismilla ya shiga da sallama a ƙasan maƙoshin shi, sai da ya ɗan tsaya jim a madaidaicin filin tsakar gidan, murmushi yayi cike da kewar gidan da yake ji tamkar shi ne nasu, saboda yadda yake ƙaunar ahalin mamallakan gidan, son da yake yi wa Amininshi Umar, da kuma son da yake yiwa Mama da ya ɗauketa tamkar mahaifiyar da ta haifeshi, waɗannan soyayyar ne suka haɗe suka rikiɗe suka koma ƙauna a kan Sadiya, ƙauna yake yi wa Sadiya irin wadda baki ba zai taɓa iya furta adadinshi ba, shiyasa ya zaɓi yin shiru, domin duk kalmomin duniya ba za su faɗi kwatan-kwacin yadda yake jin ƙaunar Sadiya ba, amma yana da tabbacin muddin Allah ya nufa kuma ya mallaka mishi ita, zai shayar da ita madarar ƙauna da zumar soyayya, zai yi ƙoƙarin fayyace mata dukkan ƙaunarshi a bayyane kuma a aikace, ba tare da ya wahalar da kunnuwanta wajan saurara ba, a jikinta da kuma zuciyarta za ta ji hakan ta kuma yarda ta aminta ya fi kowa son ta.
Wani irin murmushi mai taɓa rai Sadeeq ya saki, murmushi irin wadda idan wani aka yi wa, to zai ɗau shekara da shekaru bai mance da murmushin ba, a yanayi na natsuwa da kamewa ya ƙarasa har bakin ƙofar palourn, knocking yayi tare da yin sallama.
⭐️
SADIYA POV
Baccinta take yi har aka yi azahar, sai da lokaci ya gota sannan ta tashi, toilet ta wuce kai tsaye ta watsa ruwa sannan ta ɗauro alwala ta fito, mai ta shafa kawai da turare, ta zira dogon riga mara nauyi ta sanya hijabinta ta tayar da sallah, tana cikin sallah Mama ta shigo ɗakin, ganin Sadiyar na sallah sai Mama ta juya ta fice.
Sadiya ko da ta idar da sallan, dogon addu'a ta yi sosai tana kuka, roƙon Allah ta ke ya sanyaya wa kowa zuciyarshi, ita dai a barta da Haidar nata shi take so, ba za ta iya zaman aure da Sadeeq ba, ta ɗau lokaci tana addu'a sannan ta shafa tare da lafewa a kan darduman ta kwanta tana mai da numfashin kukan da take yi, yunwa take ji yana nuƙurƙusarta, amma ba za ta fita cin abinci ba, domin ba iya Umma da Abba take kunya ba, har Khausar tana kunyarta, kuma tana tsoron Mama da Yaya Umar tunda ta fi kowa kwana da sanin irin yadda suka ɗauki Yaya Sadeeq nata, "Allah ka mini mafita ka barni da Haidar", ta faɗa cikin muryar kuka, tana nan a kwance a wajan har aka ƙira la'asar, bata tashi ba sai da masallaci suka idar, sannan ta tashi cikin rashin ƙwarin jiki ta tayar da nata sallahn.
Mama ko da ta fice a ɗakin Sadiya, samu ta yi ƙanwarta Hauwa Kulu na ƙiranta a waya, hakan ya sa ta ɗauka suka yi magana, ƙanwar tata ke sanar mata suna hanya sun kusa isowa, a iso lafiya Mama ta musu sannan ta katse wayar, ta shige kitchen dan ƙara sanwar dare tunda baƙin yau za su fara zuwa.
Bayan Mama ta kammala an ƙira la'asar ta wuce ɗakinta ta yi sallah tare da masallaci, tana idarwa ta shafa addu'ointa, sannan ta miƙe ta fito ta nufi ɗakin Sadiya cikin taƙaicin rashin fitowan Sadiya tun da jimawa, balle ta ci abinci.
Da sallama Mama ta shiga ɗakin, yanzu ma samun Sadiya tayi tana sallah kamar dai ɗazu, guntun ƙwafa tayi tare da cewa, "Maza kina idar da sallahn to ki fito ki ci abinci, yunwa dai ba ƙanwata ba ce kuma ba ƙanwar babanki ba", daga faɗin haka Mama ta juya ta fice, dan ta koma ɗaki kar su Najla su mata ɓarna.
Knocking na ƙofa Mama ta jiyo, da kuma sallama wanda ba ta jiyo muryar sosai ba, hakan ya sa ta dakata tare da amsa sallamar tana faɗin, "A shigo."
***
Sadeeq sai da ya lumshe ido ya sauƙe numfashi, sannan ya buɗe ya tura ƙofar ya shiga da wata sallamar, kan shi a ƙasa.
Mama washe baki ta yi kamar gonar auduga, ko wacce aka yi wa bishara da kujerar makka, har ta ma rasa abinda za ta faɗa saboda farin cikin ganin shi da kuma murna.
Sadeeq ƙarasawa yayi cikin palourn tare da zama a ƙasa, da haɗaɗɗiyar muryarshi ya ce, "Barka da rana Mamana."
Sai sannan Mama ta samu abun faɗa, zama tayi a kujera tana kan murmushi, ta ce, "Ma sha Allahu, alhamdulillah, barka babana, sannu da jiki, Allah dai ya ƙara sauƙi da ƙarfin jiki, Allah kuma ya sa kaffara ne, Allah ya tsare gaba, Allah kuma ya yi albarka mai babban suna."
"Amin Ya Rabbi Mama, fatan an wuni lafiya?"
"Lafiya alhamdulillahi sai godiya mai babban suna, ni da nake batun zuwa duba ka, sai kuma ka zo da kanka kenan, to Allah ya maka albarka babana."
"Amin Ya Rabbi Mama", Sadeeq ya faɗa yana duƙar da kai ƙasa.
Mama tana murmushi ta ce, "Tunda mun gaisa ai sai ka tashi ka zauna a sama ko, wannan sanyin ƙasan kuma dama lafiya bata ishe ka ba."
"Babu komai Mama", faɗin Sadeeq a taƙaice.
Sai da ya numfasa sannan ya ce, "Mama a mini afuwa."
Murmushi Mama ta yi, dan ta fahimci a kan me yake nufi, hakan ya sanya ta ce, "Ba komai mai babban suna ya wuce ai, amma dai sam-sam bamu ji daɗi ba har Ummanku, Babana kana da iko da Sadiya yadda Umar ke da iko da ita, amma bamu ji daɗin wannan abinda ka yi ba sam, abu ne wanda ya fi komai sauƙi amma ka mayar da shi mai wahala, abinda ni ya mini rashin daɗin shi ne har kana cikin damuwa a kan haka, amma muka kasa fahimta kai kuma ka kasa sanar mana, duk sai ina ganin laifin kaina da gazawa a matsayin uwa a gare ku, tunda na kasa fahimtar me ke a zuciyoyinku har abu ya kusa lalacewa, amma godiya ya tabbata ga Allah da abun bai ida lalacewa ba, muna da sauran dama, kuma in sha Allah za mu taya ku da addu'a da komai har wannan abu ya yiwu."
Sadeeq kan shi a ƙasa ya ce, "Allah ya saka da alkairi Mama, Allah kuma ya ji ƙan magabatanmu, Allah ya tabbatar da abinda yake mafi alkairi."
"Amin Ya Rabbi mai babban suna."
"Ayoyo big uncle", Najla da Nayla suka faɗa lokacin da suka iso palourn, a shirye suke tsaf dan dama Mama ta musu wanka ta basu abinci ta shiryasu da suka tashi bacci.
Sadeeq buɗe musu hannu ya yi suka faɗa jikinshi, sannan ya amsa gaisuwansu har Nayla me gwalanti(tsamin baki irin ta yara masu ƙananun shekaru).
Mama gaba ɗaya mancewa ta yi da wata Sadiya, akan bata fito cin abinci ba, hirarsu suka dinga yi da Sadeeq, sai da Najla ta dubi Mama ta ce, "Granny where's mummy and small Mum?"
Mama ta ce, "Mamanku tana gidan Abba, Sadiya kuma tana ɗaki."
Da Nayla da Najla duk ɗakin suka nufa da sauri wajan Sadiya, sun shiga sun same ta a kwance a kan darduma, Nayla ta kwanta a jikinta tana mata rigima, Najla kuma wajan fiskarta ta je tana leƙawa, da sauri ta ce, "Small Mum you're crying, what's wrong? Did granny hit you?"
Sadiya bata ba wa Najla amsa ba, ƙoƙarin tsagaita kukanta ta yi da kuma hawayen, saboda Nayla na ƙoƙarin leƙo fiskarta, ga shi Najla ta kyaɓe fiska, ko kamun Sadiya ta yi wani yunƙuri har Najla ta miƙe ta fice da gudu ta dawo palourn, kai tsaye wajan Mama ta nufa, tana ɓata fiska ta ce, "Granny you beat small Mum ko? Granny ba a dukan babba fa."
"Ai ko Khausar bata wuce duka ba balle Sadiya."
Najla da ta ɓata fiska har da guntun hawaye, juyowa ga Sadeeq tayi tare da cewa, "Big uncle kazo mu rarrashi small Mum, she's crying."
Mama girgiza kai ta yi, domin ta san za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya, "yanzu kukan me Sadiya ke yi? Me aka mata? Yarinyar nan dai bata iya samun waje ba, idan ta ga ana lallaɓata baza tijararta take har da salo, to Allah zai dawo da Umar lafiya shi ne daidai ita", Mama ta ƙarishe zancen zucin tana ƙwafa.
Sadeeq da tunda Najla ta ce Sadiya na kuka, wani iri ya ji a ranshi sosai, ji yayi zuciyarshi na mishi zafi da ciwo, sai dai fata yake da addu'an kada ya zama shi ne sanadin kukanta, domin wannan kawai ma ba zai yafe wa kanshi ba, a sanyaye ya ce, "Mama me aka yi mata?"
Ƙwafa Mama ta yi tare da cewa, "Wa ya san me aka mata babana, ita dai ta san me aka mata ko me ta ƙirƙira, sam-sam Sadiya tana da abun haushi da abun cika ciki, amma duk samun waje ne shiyasa, bari Umar ya dawo."
Marairaice fiska Sadeeq yayi tare da sassauta murya ya ce, "A yi mana afuwa Mama kar a haɗa ta da Umar, a dai tambayeta da farko me ke damunta, wataƙila akwai abinda ke damunta shiyasa take kuka, kuma dan Allah Mama in dai saboda magana nane, dan Allah a bari na yafe, a barta a mata abinda ranta ke so, abinda za ta yi farin ciki da shi", ya ƙarishe faɗa cikin jin kunyar Mama.
Numfashi Mama ta sauƙe sannan ta ce, "Babu ta yadda za a yi maganarka ta sa Sadiya kuka, kawai taɓarattace ta motsa, da ma idan ba kai ba waye ma zai iya da halin Sadiya? hali dubu babu na zaɓe duk abun taƙaici gare su, daga taɓara sai rigima, sai shagwaɓa sai shirme da sauransu."
Ƴar murmushi Sadeeq yayi tare da cewa, "A dai yi mana afuwa Mama."
"To, ta ci albarkacin babana, an yafe ba dan halinta ba."
Sadeeq murmusawa ya sake yi, duk da zuciyar shi a cike yake da son gani ko jin me ke damunta, amma rashin sanin a wani hali take ba ƙaramar cunkushe ran shi yake yi ba, a haka suna hira da Mama da raha har aka yi sallama aka shigo, manyan mata ne da yara, kana ganinsu ka san shatar mota suka ɗauko suka taho.
Mama da Sadeeq amsa sallamar suka yi, Mama na murmushi ta ce, "Lale marhabun da mutanen Minna, isowar yamma kenan."
Duk waje suka samu suka zauna, tare da amsa wa Mama sannun da ta musu, Sadeeq cikin mutuntawa ya gaishe da manyan matan, yaran kuma suka gaishe shi, ya amsa, sannan ya miƙe tare da yiwa Mama sallama, ya fice tana jaddada Allah ya ƙara mishi lafiya.
Mama da kan ta, ta ɗauko musu ruwa sannan ta zauna suna gaisawa.
Wacce ke matuƙar kama da Mama a cikinsu ne ta ce, "Ina amaryar ban ga gilmawarta ba? Ko tana gidan Abban nata ne?"
Mama girgiza kai ta yi, tare da cewa, "Sadiya tana ɗakinta, kawai bata jiyo hayaniyarku ba ne."
Ɗaya matar ta ce, "Kulu ƙyaleta ta huta, kin san Sadiya sarai da son jiki, yanzu ga gajiyar hanya sai ta nemi ƙara mana wata gajiyar."
Mama dariya tayi kawai, daga haka suka ci gaba da gaisawa da hirar ya bayan kwana biyu.
**
Sadeeq riƙe da wayar shi a hannun shi ya fito a palourn, yana ƙoƙarin amsa ƙira sai ga Umar ya shigo, hakan ya sa ya fasa amsa ƙiran, ya sanya wayar a silent ya maida aljihu daidai Umar ya iso inda yake.
"Assalamu alaikum bro", Umar ya faɗa yana miƙa wa Sadeeq hannu.
A dake Sadeeq ya amsa tare da miƙa mishi hannu suka yi musabaha, sannan ya janye hannun shi tare da sanya su a aljihu.
"Ka zo zance kenan?", faɗin Umar yana dariya.
Sadeeq taɓe baki yayi tare da cewa, "Da yake yau na fara zuwa gidan ai."
Ƴar murmushi ta nemar magana Umar ya yi tare da cewa, "Ba yau ka fara zuwa ba, kuma ko a baya da walakin goro a miya kake zuwa, amma dai zuwar yau ta daban ce, ina fata kun gama sasanta kan ku?"
"A a jira muke ka sasanta mu."
"Yo ai ba komai a ciki, kai ka sani, na sasanta ku shi ya fi komai sauƙi a wajena, sannan na ɗaura muku aure, na kai maka ita har ɗakinka."
"Za ka aikata", Sadeeq ya faɗa a taƙaice.
Dariya Umar yayi tare da cewa, "Abba ya ƙira ni ɗazu ina office, wai idan an yi sallahn isha'i mu haɗu da ni da kai da shi a sashinka, ina ji dai za mu ƙarisa tattauna yadda shirye-shiryen za su tafi ne."
"So zan jira ka a waje, idan ka kammala sai ka fito."
"Yanzu-yanzu ma kuwa ba ɓata lokaci", Umar ya faɗa tare da ƙarisawa ƙofar shiga palourn, da sallama ya shiga, ya kuwa gaisa da su aunty Kulu cikin fara'a da girmamawa, sannan ya wuce ɗakin shi, a gurguje ya watsa ruwa ya sanya ƙananan kaya kamar dai irn shigar da Sadeeq ya yi, sannan ya fito sai baza ƙamshi yake yi.
A ƙofar gida ya samu Sadeeq, ya hakimce a saman booth na motar shi, ƙarisawa yayi ya tsaya tare da jingina a jikin motar, ya ce, "Bro, ina fata ba za ka jima ba za ka dawo aiki?"
Sadeeq da ke danna wayarshi ya ce, "Tunda an sallamoni a asibiti me ya rage? Zaman me zan yi kuma a gida?"
"Zaman angwanci mana, wannan sati na bikinka ne, after bikinka kuma amarci za ku ci tukunna, dan haka kar dai ka jima."
"Hmmn!", Sadeeq ya faɗi yana girgiza kai, alamar Umar ya yi nisa sai addu'ar Allah ya taro shi.
Suna tsaye a wajan, suna hira jefi-jefi har aka ƙira magrib, hakan ya sa suka nufi masallaci, a can suka yi alwala sannan suka shiga suka bi jam'i aka yi sallah, bayan an idar, suka fito suka koma wajan motar Umar, tattaunawa suka shiga yi a kan abinda ya shafi company, sannan ne Sadeeq ya buɗe baki da kyau yake magana.
Sai da aka ƙira isha'i suka yi salla, sannan suka shige gidan Abba, kai tsaye sashin Sadeeq suka wuce dan ba kowa a palourn, ko da suka shiga sashin, sun samu abinci an kawo an jere, suka zauna suka ci, Umar ya tattare kulolin ya mayar kitchen na Umma, ya fito a kitchen ɗin kenan sai ga Abba na sauƙowa daga bene, hakan ya sa Umar ya dakata har Abba ya sauƙo, cikin girmamawa ya ce, "Barka da dare Abba."
"Yauwa Umaru barkanmu, ina shi Abubakar ɗin?"
"Yana sashin shi."
"To muje, dan wajanku za ni dama", faɗin Abba yana mara bayan Umar da yayi gaba.
Da sallama suka shigo sashin, Sadeeq da ke danna wayar shi, amsawa yayi tare da ɗan muskutawa ya gyara zama saboda ganin Abba, a ladafce ya ce, "Barka da shigowa Abba."
"Yauwa Abubakar, barkanmu dai, ya ƙarfin jikin?"
"Alhamdulillah Abba."
"Ma sha Allah, Allah ya ƙaro sauƙi da ƙarfin jiki."
"Amin Ya Rabbi", Sadeeq da Umar suka haɗa baki wajan amsawa.
Abba gyara zama yayi tare da yin gyaran murya ya ce, "Da farko da kai zan fara Abubakar, ina son naji dalilin da ya sa ka fidda wannar magana da naji a bakin Mamanku da kuma Umar, meyasa ka fidda maganar?"
"Kayi haƙuri Abba", Sadeeq ya faɗa a taƙaice a gajarce yana mai lumshe idanuwanshi.
Abba girgiza kai yayi tare da cewa, "Ba na buƙatar ban haƙurin ka Abubakar, domin ko ma menene kanka ka yi wa, ba wa ni ba kuma ba wa kowa ba, kanka ka cutar, shiyasa ban tambaye ka me yasa ka ɓoye ba, ban kuma tambaye ka me yasa ka yi ruwa da tsaki a lamarin Aliyu ba, bayan ka san kai ma kana son ta, damuwana ɗaya kuma shi na tambaye ka, me yasa ka yi maganar a yanzu?, so kake ka mayar da ni ƙaramin mutum? Ko so kake mutane su zage ni da wanda bai riƙe amana ba ya so kan shi? Tukunna ma ina hankalin ka da tunanin ka da ilimin ka? Ina ka kai su?"
Sadeeq ƙasa yayi da kai, zuciyarshi na zafi, domin ko Abba bai ƙarishe maganar shi ba, to zuwa yanzu ya fahimci makomar shi, hakan ya sa duk bai amsa wa Abba ba, "Kayi haƙuri Abba", haka ya kuma faɗa a taƙaice.
Ƙwafa Abba yayi tare da mayar da kallon shi ga Umar, sannan ya ce, "Kai ka bani amasar da ya kasa bani, me yasa sai yanzu ya ta da maganar?"
Ƙasa da kai Umar ya yi, tare da cewa, "Ka yi haƙuri..."
Dakatar da shi Abba ya yi, ta hanyar ɗaga mishi hannu, ran shi a ɓace ya ce, "Ba na son haƙurin da kuke bani, idan haƙurin mai muhimmanci ne kuma na gaske, me yasa ku baku yi haƙurin ba kun bar wannar magana? Me yasa za ku ta da wannar magana bayan kun san kwanaki kaɗan suka rage a ɗaura aurenta da Aliyu?"
"Abba ka yi haƙuri, amma laifi na ne ba na Sadeeq ba, ɓoyewan da yake ta yi shi ya sa har ya kwanta ciwo, wallahi ko da na fara zargin lamarin, da na same shi da maganar faɗa muka yi da shi sosai, ya nuna mini ba komai a zuciyar shi, idan kuma ina musawa to na nemo hujja, ni kuma hakan ya sa na duƙufa na dinga yi mishi bincike, gida da office da motar shi duk ba inda ban bincika ba, har sai ranar da Khausar ta zo, ta tayani muka bincika muka samo hujja, ko sannan ma ya so musa mini sai da na nuna mishi na san komai sannan yayi shiru, ko da ya faɗa mini dalilin shi na ɓoyewa, na ce zan muku magana, amma yace ba zai auri Sadiya ba muddin bata amince dan raɗin kanta ba."
"To bata amince ba, dan haka babu wannar magana, tun ran gini tun ran zane, ko ma menene to Abubakar shi ya saya da ƙudin shi", faɗin Abba yana aika wa Sadeeq mugun kallo, dan ko shi da kan shi yana jin haushin abinda Sadeeq ya yi, ai babu wanda ba zai so auren Sadeeq da Sadiya ba.
Umar ɗagowa yayi da sauri tare da kallon Abba, ya ce, "Abba wai ita Sadiyar ce ta ce haka da bakinta? Ita ta ce bata amince ba?"
"Sadiya bata faɗa da bakinta ba, amma yanayinta da halin da take ciki ya nuna haka, dan haka bana son takurawa ko tsawwalawa, sannan daga yanzu kuma a nan nake so wannar magana ta mutu kamar ba a taɓa yin ta ba, Aliyun da take so shi zan aura mata da yardar Allah."
Wani irin mashi ne, wani irin kifiya ne mai matuƙar kaifi da dafi ya daki ƙirjin Sadeeq, ya huda har ya isa ga zuciyar shi ya soke shi, a take idanuwan shi da suke a lumshe suka rine da raɗaɗi da zafin da ke a zuciyar shi, hakan ya sanya ya sake runtse idanuwan shi tare da taune leɓen shi, kan shi na wani irin sara mishi, abinda ya guda kenan tun farkon fari, da a kan ya amshi tabbacin Sadiya bata son shi daga bakinta, ya gwammace ya mutu yana ɓoye soyayyarta, wannan son da take mishi na Yaya da ƙanwa ma ya wadace shi, amma yanzu me Umar ya ja mishi? Zai iya jure ciwon nan kuwa?
Umar idanuwan shi a kan Sadeeq, yana kallon reaction na shi, hakan ba ƙaramin sake hasala shi ya yi ba, tare da sake ɓata mishi rai, Sadiya ba? Lallai zai saɓa wa Sadiya abinda bai taɓa yi mata ba.
Abba yana ta faɗan shi da surutu, Sadeeq da Umar duk ba ji suke yi ba, dan kowa ya yi nisa a abinda yake ji a zuciya, da kuma abinda yake lissafasawa, hakan ya sa, sai da Abba ya ƙira sunan Umar, sannan Umar ya ɗan yi fiska kamar da ma yana saurara, a hankali cikin girmamawa ya ce, "Mun ji Abba, in sha Allah kuma shikkenan ya wuce."
"Yauwa haka nake son ji, yadda ka dage ka binciko ka tono maganar, to ka dage ka binne maganar."
"In sha Allah Abba."
"Allah ya yi muku albarka, Allah ya shige gaba a lamuranku, Allah ya baku abinda yake rabon ku, ya tabbatar muku da dukkan alkairai na rayuwa da bayanta, kai kuma Abubakar, ka sanya salama da haƙuri a zuciyarka, tun farko dama a kan turbar haƙuri kake tafiya, dan haka sai ka sake ƙawata turbar da haƙuri fiye da a baya."
Murya ƙasa-ƙasa kuma can ciki, Sadeeq ya amsa, domin babu ma wanda ya ji abinda ya faɗa, kawai sun ga leɓenshi ya motsa ne.
Sai da Abba ya sake yi musu faɗa da nasiha, tare da sanya musu albarka, ya kuma yi wa Sadeeq addu'ar ingattacciyar lafiya, sannan ya miƙe ya fice.
Abba na ficewa Umar ya miƙe tsaye rai a ɓace shi ma ya nufi ficewa a sashin, Sadeeq da ke kule da Umar, murya ciki-ciki ya ce, "What did you think you're going to do? Did you want to make another mistake? Ko baka fahimce mu ni da Abba bane? I told you very clear, ba zan aure ta ba idan bata amince ba, Abba ya maimaita maka ba zai aura mini ita ba tunda bata amince ba, so after all this what are you going to do? Ka wani tashi a zafafe a fusace kamar mayunwacin zaki, abeg malam ka koma ka zauna, kai ka ja komai ai, you already know the truth, ignoring nashi kawai ka yi, but the word «some secrets are meant to be secrets forever» gaskiya ne, wani abu idan an ɓoye shi, a bar shi a ɓoyen shi ya fi alkairi."
"What's said in the room, stay's in the room, right?" Umar ya faɗa yana kallon Sadeeq.
"You already know", calmly Sadeeq ya faɗa yana lumshe idanuwan shi, cikin jin zafi da raɗaɗin da yake har yanzu a zuciyar shi, ko maganar da ya yi kawai ya yi ne saboda Sadiya, he definitely knows muddin Umar ya tafi gida a yanzu, to duka ma zai iya yi wa Sadiya, and Mama won't stop him, tunda duk suna kan ra'ayi guda ne, he's the cause of everything dole ya taushi Umar, duk da nashi ran ma da ciwo.
Umar murmushin gefen baki ya yi tare da cewa, "Ba irin wannan ake nufi da sirrin da za a bar shi a sirri har abada ba", iya haka Umar ya faɗa ya hanzarta ya fice ba tare da ya bi ta kan ƙiran sunanshi da Sadeeq ke yi ba.
Sadeeq kuwa tun yana ƙiran sunan Umar a hankali, har ya ɗaga murya, amma ko waiwaye haka Umar ya fice, hakan ya sanya Sadeeq dafe kan shi, ba ya ganin laifin kowa sai na shi, ko me ya faru shi ne sila, shi ya ja komai kamar yadda Abba ya faɗa, ko ma menene to shi ne ba kowa ba, hakan kuwa bai sanya Sadeeq yin da-na-sani a kan soyayyar Sadiya ba, balle kuma ɓoyewan da yayi, da-na-sani ɗaya ya yi shi ne na gaza haƙuri har ya faɗi ciwon da ya yi silar fallasa komai, lallai ba iya magana ba ce zarar bunu idan ta fito bata komawa, hatta da wasu abubuwan da mutum ke yi, to kamar amai ne ta yadda idan ka yi ba za ka lashe ba, ka yi su kenan kuma ba ta yadda za ka mai da lokaci baya balle ka goge su, amma da ana yi to da ya mai da lokaci baya ya goge wannan ciwo da yayi, ya daure dan kar a zo wannan gaɓar ma.
**
Umar sai da ya shigar da motar shi harabar gidan, sannan ya ƙarasa ciki, lokacin ba kowa a palourn, Mama tana ɗakinta da su aunty Kulu, Sadiya kuma tana ɗakinta da sauran yaran, dan Khausar ta zo ta ɗauki Nayla da Najla sun tafi gidan Abba a can za su kwana.
Sadiya ta daure ta fito ta yi wa su aunty Kulu sannu da zuwa sun gaisa, amma ba raha kamar yadda aka saba, hakan kuwa ya sa su aunty Kulu suka tambayi Mama dalili, amma ta ce musu ba komai kawai rigimar Sadiya ce ta motsa, suka yadda a kan haka suka ƙyale ta.
Haidar ya ƙira Sadiya a daidai domin tana tare da su aunty Kulu, yana sanar mata za a kawo lefe gobe talata, ita kuma ta sanar wa su aunty Kulu, sannan ta miƙe ta koma ɗakinta, suka ci gaba da wayarsu, in da Haidar ke tambayar ko lafiya ya ji muryarta haka, amma ta ce mishi lafiya ba komai, juyin duniya ya yi ta faɗa mishi menene ya sanya ta kuka, dan ya ji alamar haka a muryarta, amma Sadiya ta ce nan duniya ba komai, hakan ya ɓata ran Haidar, ya kuwa kashe wayarshi, ta ƙira ta ƙira bai ɗauka ba, ta yi saƙo bai yi reply ba, hakan ya sake dagula mata lissafi ƙwarai, ta sake fashewa da wani kukan ciki-ciki, saboda kar yaran da suka zo da su aunty Kulu su ji kukanta, sai dai ta makaro dan masu wayon sun fahimci kuka take yi, amma ba wanda ya ce ƙala.
Umar kai tsaye ɗakin Mama ya nufa da sallama, ya yiwa su aunty Kulu barka da dare, sannan ya ce da Mama ta ɗan zo, ba musu Mama ta taso ta fito, tana kallonshi ta ce, "Umar me ya faru? Lafiya na ga kaman ranka a ɓace?"
Ƙwafa Umar ya yi tare da cewa, "Mama kina jin abinda wannan yarinyar ta yi ba, wallahi Sadiya ba ta da hankali, har za ta nuna wa Abba bata son Sadeeq, bata yarda da maganar shi ba, yanzu ga shi Abba ya ce ba zai aura wa Sadeeq ita ba a bar maganar.....", ya ƙarishe tare da labarta mata yadda suka yi da Abba.
Ba iya Umar ne ran shi ya ɓaci ba, don na Mama ya fi na shi ɓacuwa, hakan ya sa ta ce, "Wato munafurcin dai da Sadiya ta je ta ƙulla ya hana ta fitowa yau, ta wuni a ɗaki kamar mace mai jego, ni Sadiya za ta watsa wa ƙasa a ido ta bai wa kunya? Ni dai?"
Umar ba tare da ya ce komai ba ya nufi ɗakin Sadiya, dan ya sake hasala ne, yana shiga ya yi da yaran magana su tashi su fice, sumui-sumui suka fice a ɗakin daidai Mama ta shigo.
"Sadiya", Mama ta ƙira sunan Sadiya rai a ɓace, tun kamun Umar ma yayi magana.
Sadiya da tun shigowar Umar hantar cikinta ta kaɗa, wani kukan ta fashe da shi mai ƙarfi lokacin da Mama ta ƙira sunanta, musamman da ta ji ran Mama alamar a ɓace.
"Za ki haɗiye kukan nan ne ki tashi ki bai wa mutane amsa, ko kuwa sai na zo wajan na yi ƙasa-ƙasa da ke, shirmammiya kawai wacce bata san ciwon kanta ba, wato ana miki gata kina botsarewa", Umar ya faɗa a ƙufule.
Ƙwafa Mama ta yi tare da cewa, "Ka dai haifi yaro ne amma sam baka haifi halinshi ba, idan ba haka ba yo Sadiya har in ba ki misali da kai na, amma ki ƙeƙeshe idonki ki je ki barbaɗa abin kunya, ke yanzu baki ji kunyar cewa Abbanku ba kya son ɗan shi ba?"
Sadiya da ta tashi ta zauna tana kuka, ƙasa da kanta ta yi bata ce komai ba.
"Keee! Ba da ke ake magana ba ne da ba za ki amsa ba?" Umar ya faɗa yana daka mata tsawa tare da aika mata wani mugun kallo, yau ba dan ta ci albarkacin maganar Abba da kuma Sadeeq ba, da sai ya sauya mata kamanni, har sai ta gane gata ake mata."
Jiki na rawa cikin muryar kuka, Sadiya ta ce. "Da..da..da ni ne...."
"Za ki haɗiye kukan nan ne ko sai na sa kin haɗiye da duka?"
Da sauri Sadiya ta girgiza kai, tare da toshe bakinta da tafin hannunta, tana ƙoƙarin haɗiye kukan.
Mama ta ce, "Ke baki ji kunyar cewa ba kya son mai babban suna ba? Da me kika fi mai babban sunan? Ko kuwa akwai abinda yake da naƙasu a kai? In dai na kintata daidai to sai dai shi ya gwada miki abubuwa da dama, ba dai ke ki gwada mishi ba ko wani ya gwada mishi."
Jinjina kai Sadiya ta yi, cikin muryar kuka ta ce, "Ha...ha..ha ka ne...., amma..wal..wallahi..Allah..ni ban ce wa Abba..Abba..ni ban ce wa Abba ba na son Yaya Sadeeq ba", ta ƙarishe faɗa tana sakin marayan kuka a cikin cikinta.
"Shi Abba naku ne ya miki ƙarya ko kuma Yayanki Umar?"
"A..a, Mama."
Umar fiska a haɗe ya ce, "To, uban me kika ce wa Abba idan ba nuna mishi kika yi baki yarda da batun Sadeeq ba."
Sadiya ƙasa ta yi da kanta, murya na rawa ta ce, "Ni kawai ce mishi na yi, na bar mishi zaɓi, na san ba za ku zaɓar mini abinda zai cutar da ni ba", yanzu kam da kuka mai sauti ta ƙarishe maganar, dan Allah ya gani hakan ba ya nufin a zaɓar mata Sadeeq, ita Haidar take nufi, kuma ta san Abba ya kintata daidai, amma su Mama ba za su fahimce ta ba.
Wani kallo Umar ya wurga mata, tare da yin ƙwafa yana kaɗa kai, kana ya juya ga Mama, ya ce, "Tunda ita ishashshiya ce, sai ta kuma komawa ta sanar da Abba Sadeeq take nufi, idan ba haka ba haɗuwarmu na gaba ba zai mata daɗi ba, kuma idan ta kuskura ta ce matsa mata aka yi sai na saɓa mata kamanni, tunda duk dan ita da kuma gobenta ake duk haka."
"Dolenta ma ta koma ta amsa", Mama ta faɗa tana hararar Sadiyar ita ma.
Umar juyawa ya yi ya nufi ƙofa, sai da ya kama handle sannan ya juyo fiska a haɗe ya ce, "Idan kin tabbata wuyanki ya isa yanka to ki kuma faɗa wa Abba abinda kika faɗa, dan wani abu ya samu Sadeeq sanadinki sai kin sha mamaki na", ya ƙarishe maganar yana kallon yanayin da ɗazu Sadeeq ya shiga sanadin maganar Abba, ya san ko maganar da Sadeeq ya tsaya yi mishi kawai ta dauriya ce, ƙwafa yayi tare da ficewa ya banko ƙofar, kai tsaye ya wuce ɗakinta, ba abinda yake yi sai sakin tsaki a kai a kai da kuma yin ƙwafa.
Mama da mugun kallo ta bi Sadiya tare da yin ƙwafa ta ce, "Ki yi abinda kike so kike ganin ya fi miki, abinci kuma ƙin cin shi kan ki kika yi wa, dan ko gawarki ne sai na kai gidan mai babban suna, a matsayin matar shi kamun a wuce a binne ki", iya haka Mama ta faɗa ta juya ta fice ita ma, sannan yaran suka dawo ɗakin, lokacin Sadiya ta shige toilet.
Sadiya kuwa a cikin toilet kuka ta saki take yi bil haƙƙi da gaskiya, da ɓata wa Haidar rai da ta yi ya ƙi sauraranta za ta ji, ko da batun Yaya Sadeeq, da ta fahimci Yaya Umar ya shirya kassarata a kan Aminin shi, Mama kuma wataƙila ta yafe ta a kan mai sunan babanta, "Ya Allah ga ni gare ka, Allah ka sani ka fi kowa sani, Haidar nake so a matsayin miji, sannan duk wannan bai sa na tsani Yaya Sadeeq a matsayin shi na Yayana ba, sam ban ji haushin shi ba, domin ni ba butulu ba ce, na san alkairi, amma tabbas Haidar shi ne mijin da nake buri", ta ƙarishe faɗa tare da ɗaura alwala ta fito, ƙoƙarin saisaita kukanta ta yi, ta buge da nafila a nan bacci ya yi gaba da ita kan darduman tana kukan zuci ga yunwa tana ji.
⭐️
ALIYU HAIDAR POV
Fushi ya yi da Sadiya sosai, domin ƙwarai a kwana biyun nan ba ya gane mata, kuma abinda basu saba ba na ɓoye wa juna damuwarsu, ko yin ƙarya duk ya fahimci yanzu su take mishi, hakan ya sanya ko da ya kashe ƙiran, yana kallon ƙiranta har saƙo amma bai bi ta kan ko guda ɗaya ba, ya ƙarisa shirin kwanciyarshi ya kwanta, ba jimawa bacci ya yi gaba da shi.
Washe gari kamar yadda Hajiya ta ce, da wuri jama'arta suka fara taruwa, zuwa azahar duk waɗanda ta sanar wa sun hallara, danginta da na Alhaji, da kuma abokanan arziƙi da ƙawayenta, suka sako kaya a gaba suka nufo gidan su Sadiya cikin motoci.
Kaya ne niƙi-niƙi a set guda na akwati orange color, da kuma set na handmade gift packaging basket na saƙa, wanda ake wrapping nashi da shining net mai kyau da flowers, kayaki ne masu kuɗi da kyau babu na wasa, duk da a haka sai da Alhaji ya yi ƙorafi ganin set guda na akwati da kuma handmade packaging basket, wanda suka yi da Hajiyar duk set bibbiyu za a haɗa, amma kuma abinda Hajiya ta faɗa, ya sanya shi zuba mata ido tare da girgiza kai kawai bai sake cewa komai ba, lamarinta kullum gaba-gaba yake yi, ga shi dai kamar ta daidaita komai ta bari, amma ashe ba haka bane, shi dai nashi ido, zai kalli yadda komai zai tafi, amma dai yana yi musu fatan alkairi, musannan wa ɗan shi.
A gidan Mama tawagar kawo kaya suka samu masauƙi, inda aka cika su da ashirin da bakwai na arziƙi, wanda kayan ciye-ciye da sauransu duk daga gidan Abba ne, dan aunty Kulu ko da ta sanar da Mama batun kawo lefe da suka yi magana da Sadiya, Mama shiru ta yi bata kuma cewa komai ba, amma ranta ba daɗi sam, haka ya sa ko da Umma ta shigo su gaisa da su aunty Kulu, sai aunty Kulu ta sanar wa Umma, ita kuma Umma ta sa Khausar ta taya ta suka shirya komai da ya kamata, bayan ta sanar wa Abba za a kawo kaya, kuma yayi Allah sanya albarka tare da bayar da ƙudin da ake bayarwa na tukuicin masu kawo kayan.
Su Umma sun yaba kaya sosai-sosai da su aunty Kulu, cikin mutunci da raha suka rabu da masu kawo kayan, suka kama hanya suka tafi, su kuma suka zauna kallon kaya suna santi, dan tabbas ba ƙarya an kashe Naira a wannan lefe, Mama dai ƙala bata ce ba, maƙota suka ci gaba da shigowa suna kallo ana sanya albarka.
Mama ta ce da aunty Kulu zuwa dare su tattara kaya su mayar gidan Abba, idan ya gani sai a ajiye kayan a can, duk waɗanda suka zo daga baya su je can su kalla, aunty Kulu ta amsa kuma ta yaba da karar da Mama ta yi wa su Umma.
⭐️
Ƴan kai kaya da suka koma, ba abinda suke yi sai yabon irin tarban da aka musu, Hajiya dai tana jin su amma bata ce komai ba, domin ta jima da sanin wani abu ba iyayen Sadiya ke yi ba, maƙotansu ne iyayen abokin Yayan Sadiya, a kan haka kuma ta shirya shirinta daban da za ta ƙaddamar, daga haka aka yi ƴan hira, aka kuma kassafa abinda aka ba su na tukuici, sannan kowa ya kama hanya ya koma gidanshi, Nihal tana cikin masu kai kaya, ta yaba da komai na dangin Sadiya, ta kuma ji babu daɗi da ta nemi ganin Sadiya amma bata samu hakan ba, ita dai fatan ta Allah ya taro Hajiya da batun Husna, su Sadiya da Ya Haidar su zauna lafiya su sha soyayyarsu.
Haidar kuwa yana samun tabbacin isar kayan aurenshi da kuma IV ga Sadiya daga bakin Nihal, ba ƙaramin farinciki da nishaɗi yake ciki ba, ji yake kawai ya mallaki Sadiya, shedu ne kawai suka rage, hakan ya sa ya yiwa Nihal tukuici, yana kuma mai jin kamar ya ƙira Sadiya, amma fushin da yake yi da ita haka kawai yake sake hauhawa a zuciyar shi, sai kawai ya basar da batun ƙiranta, ya tsaya ganin iya gudun ruwanta za ta ƙira shi ko kuwa fushi ta yi ita ma.
⭐️
Ɓangaren Sadeeq da Umar, washe-gari da wuri suka wuce office, bayan Umar ya sake buga wa Sadiya warning da safe a kan, kada ya dawo gidan ya samu wani magana bayan ta Sadeeq, hakan kuwa ba ƙaramin sake sanya ta a damuwa yayi ba, sanin yau za a kawo lefe, shiyasa ta wuni tana ɓoye kanta a ɗaki, ƙarshe ma a sace ta fice ta wuce gidan Umma, ko Khausar da Umma basu san shigowarta ba suna aikin abun bai wa masu kawo kaya, da farko sashin Yaya Sadeeq ta yi niyan zuwa dan sanar da shi gaskiyar irin soyayyar da take mishi, ta san zai fahimceta kuma shi ne kawai zai iya cetonta daga Yaya Umar, amma ta samu Yaya Sadeeq baya nan, haka ya sa ta zauna a nan sashin shi, kawai ta kasa kunnuwa dan taji shigowar Abba ta mishi magana, duk da ɗaya bata san me za ta ce mishi ba, a nan sashin ta yi azahar da la'asar, a kitchen na Yaya Sadeeq ta samu abu ta sanya wa cikinta, dan ji take tsakanin jiya da yau, ulcer na barazanar yi mata mugun kamu, ga shi ta zabge kamar wacce ta yi wata tana jinya, idanuwanta duk sun kumbura sun yi luhu-luhu da su.
Har goshin magrib sannan ta ji motsin shigowar Abba, hakan ya sa ta fito da sauri, yana ƙoƙarin haurawa step's ta tsaya a tsakiyar palourn, kanta a ƙasa ta ce, "Abba sannu da dawowa."
Abba na murmushi ya juyo tare da cewa, "Yauwa auta, sannunmu ko."
Sake duƙar da kanta ƙasa ta yi, tana murza yatsunta, domin ta rasa me ma za ta fara cewa.
Abba da har ya juya, jin shiru alamar bata wuce ta zauna ba ko tafiya, sai ya dakata tare da juyowa, daga yadda take tsaye ya fahimci akwai magana a bakinta, hakan ya sa ya ce, "Yanzu dawowa na auta, bari na yi sallah sai mu yi maganar da ke tafe da ke ko."
Jinjina kai Sadiya ta yi, tana mai jin salama a zuciyarta gefe guda, dama-dama take ji, da Abba ya fahimci tana tafe da magana, sai dai a yanzu ne take jin rashin kyautawarta, da kuma ganin tsantsar gaskiyar Mama da take cewa bata ji kunyar Abba ba, da ta nuna mishi bata yarda da batun yaron shi ba.
Wannan tunani ya sanya Sadiya sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya, tana jin lallai-lallai cikin biyu dole a yi ɗaya, ko ta jure wa ko ma menene daga Haidar, ko kuwa ta jure wa ko ma menene daga Yaya Umar, amma ko ba dan Yaya Umar ba, ko dan su Abba za ta amsa wa batun Yaya Sadeeq a yau, ko hakan na nufin komai gare ta ne, za ta amsa wa Abba cewa Yaya Sadeeq ta zaɓa, da shi ta aminta, ko da zuciyarta za ta fashe ne saboda yankar ƙaunar da ta mata, tsakaninta da zuciyar Haidar.
***
Za ku iya samun littafin a waɗannan manhajoji.
●BAKANDAMIYA HIKAYA.
●WATTPAD
@uwarbatoorl96.
●AREWABOOKS.
@Uwarbatoorl96
***
a kan Naira #500.
Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah.
# Hareeyh
# ***
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚