chapter 29
***
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*****
BOOK 1
PAGE 2️⃣6️⃣
SADIYA
"Innalillahi wa inna ilaihi raji,un" Sadiya ta furta a fili tana miƙewa tsaye ta shiga dudduba wajen tamkar dai jakar za ta gani gabanta yana faɗuwa ta shiga dubawa amma bata gani ba duk hanklinta ya tashi saboda kuɗinta ne da take son fita kunya idan ta haihu duk wani tanadinta yana cikin kuɗin amma ta rasa yadda aka yi ta rasa jakar, tun da ta tabbatar a lokar ta saka tun da kafin ta fita ma ta saka kuɗi a ciki. Da sauri ta janye ƙaramar bedside ɗin daga wajen ta duba bayan bed side drower ko ɓera ne ya ja don ra fara tunanin ko lokar a fashe take daga baya amma sai ta ga babu wani waje da yake da alamar fashewa a jiki.
Lokar saman ta janyo tana birkicewa wai ko dai a ciki ta saka duk da Sadiya bata da mantuwa komai nata a nutse take, ma,ana ta san a lokar da ta saka kawai dai tana dubawa ne amma wayam babu ko alamar jaka bare a je batun kuɗi.Birkice ta shiga yi a ɗakin amma babu jaka babu alamarta haka ta fito falo kamar zautacciya domin ita ta san irin wahalar da ta sha a kuɗin tun da halaliyarta ce duk wani mai neman halal kuwa ya san neman halak da wuya!.
Duk hankalinta ya tashi sai da ya dawo ta ga kuɗin da ta karɓo na curry da sauransu sai ta yi tunanin wancan kuɗin ne da take nema amma sai da ta zo ta tuna haka ta dawo ta zauna tana ta ambaton Allah a zuciyarta har dai ta samu nutsuwa a zuciyarta. Tana iya jiyo ƙaran TV daga ɓangaren Meenal kuma ta san shi ma mai gidan ya dawo amma ko leƙo ta bai yj ba domin ta ji zuwansa.
Ita dai ta san ɗakinta a kulle kuma ko ma ba a kulle ba abu sabo abu ne da ba a taɓa.yimata ba wato sata, saboda ta san in har ba ita ta yi niyyar yin alheri ta ba mutum kuɗinta ba babu mai ci sai dai ko Nasir idan son kuɗinsa ya tashi ya ce ta bashi don kawai taƙamar tana matarsa bayan kuma shi ba bata yake ba. Haka ta jure ta haƙura ta kwanta tun da babu wanda za ta tunkara da maganar, haka ta yi addu,a ta kwanta tana ta tunani da ciwon rai ya ishe ta kawai sai hawaye ne suke zuba, ta jima tana hawayen nan har da sheshsheka kafin daga bisani bacci ya yi awon gaba da ita bata falka ba sia wajen ƙarfi biyu da kwata haka ta tashi ta yi alwala ta yi nafila bayan ta idar ta zauna ta yi karatun qur,ani sannan ta karanta sunanyen Allah tare da salatin annabi S.A.W ta ɗaga hannu ta ce
"Ya Allah kai kake ƙaddara komai a lokacin da ka so, ya Allah na san kai kake bayarwa kuma kai kake hanawa Allah ka san damuwata a kan jakata da na rasa ya Allah idan rabona ce ka bayyana min ita idan kuma babu rabona ka sauya min da abin da ya fi alkairi, na yarda da duk wani abu da za ka ƙaddara min" Haka ta gama faɗawa ubangiji tana hawaye tare da jero wasu buƙatub nata sannan ta ƙara yin salatin annabi S.A.W ta shafa addu,ar Ta koma takwanta sai ta ji zuciyarta ta yi wani irin sanyi duk damuwa da nauyin da zuciyar ta yi babu shi!.
Da asuba ta yunƙura dakyar ta yi sallah ta sake karatun qur,ni da yin addu,o,in ta.
Da safe da ta fito sai take jin duk babu daɗi yadda babu nepa a ɓangarenta ita bata san ma wanda za ta faɗawa ba, ɓangarenta basa son ta kai ƙaransa shi kuma nata ɓangaren basu damu da ita ba basu san muhimancjn ta ba, sai dai kawai ta san akwai sakayya. Tsakar gidan ta nufa, da yake wajen ƙarfe bakwai ne ruwan zafi za ta ɗora saboda yunwa take ji kasancewar mace mai ciki akwai jin yunwa, ga shi kuma ita bata da nepa bare ta jona a nepa. Tana zuwa ta buɗe kicin ɗin sai lokacin ma ta tuna gawayin nata ya kusa ƙarewa, a haka ta ɗauke na ƙasan buhun duk da ya zama ƙareci duk ƙanana ne, ta samu ta hura da ya kama ta ɗora ruwan. Waje ta samu ta zauna a kicin ɗin tana jiran ruwan ya tafasa tana zaunen tana kallon kayan sana,ar da suke gefe a cikin kicin ɗin aajiye manja farin mai da sauransu tana tuna yadda jakar kuɗinta ta ɓace jiya, tunaninta ɗaya yanzu idan suka ƙare yadda za ta haɗa kuɗin ta saro wasu domin ba lallai ta haɗa kuɗin ba kasancewar asarar da ta same ta duk da ta san Allah ne ya ƙaddara mata.
Da ta dama kokon, sai ta ɗauki sauran fulawar da ta rage mata wacce ita ta saya ta kwaɓa ta musu waina ta saka a fulas ta gaa sai ta ɗora ruwan zafin wanka wanda ta san ma ba lallai gawayin ya isa dafawa ba. Kicin ɗin ta janyo bayan ta ɗakko jug ɗin kokon da kuma kwanon wainar. A falo ta ajiye sai ta koma ta ɗakko plate da kofi da cokali ta dawo ta zuba wainar da kokon da ta saka sugar ta zauna tana ci bata ma ra,ayjn ci da ya ji sai da ta ji ta ƙoshi ta rufewa Kalifa sauran. Tana jin lokacin da su Husna suka buga gidan aka buɗe musu wajen ƙarfe takwas kuma Meenal ce ta buɗe tana jin yadda take musu masifa wai sun ɓata lokaci ba su zo da wuri ba, haka ta ji suna bata haƙuri kamar wata uwarsu.
Har suka gama suka tafi bata fito ba Kalifa kuma har lokacin bacci yake kasancewar jiyan ya yi ta gijifgijiftu a gidan kaka, saboda gajiya shi ya sa bai tashi da wuri ba. Bayan tafiyarsu sai ta gyara ɗaki ta share tas ta yi goge goge sai ta kunna turaren tsinke, tsakar gidan ta shiga sharewa, sai ta ta je tana tattarawa sai kawai ta ga wani abu da ya bata mamaki, da sauri ta kai hannu ta ɗakko tana juya shi a hannunta gabanta ya buga da ƙarfi domin tabbas ko tantama babu zip ɗin jakarta ne, abin da ya sa ta game shi zip ɗin jakarta daga aarshensa a ɗan lanƙwashe yake ba komai ya lanƙwasa shi sai wani lokaci ya cije ya ƙi ziguwa shi ne ta maƙala shi jikin ƙofa ta cisga da ƙarfi shi ne ya lanƙwashe daga wajen kamawar, abin da ya bambanta wannn da nata shi ne wannn baƙiƙƙitin da shi kamar wanda aka ƙona shi.
Tsaye ta miƙe tana aara ƙare masa kallo fitowar Nasir da Meenal daga ɗaki ya sa ta yi saurin juyowa, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai kamar ya ga kashi sai dainita ba wannn bane a gabanta saboda yanzu abinnda yake gabanta na mamaki da al,ajabi ya danne komai. Ba ta san lokacin da ta ce
"Wallahi wannna ƙarfen zip ɗin jakata ne" Dududdummm gaban Meenal ya harba da ƙarfi amma saboda ƴar bariki ce sai ta basar tana mayar da kallonta kan Nasir tana wani kashe murya shi kuma yana biye mata bai ma damu da maganar da Sadiyar ta yi ba sai da Sadiya ta ankara da abin da ta ce sannan cike da sanyin murya ta ce
"Ina kwana Abban Kalifa, an tashi lafiya" Ta faɗa a tare don gabaɗaya ta shiga ruɗu da tunanin yadda aka haihu a ragaya.
Amsawa ya yi kamar an masa dole ganin haka sannan kuma ta ga alamar Meenal ba za ta bari su yi maganar ba sai ta ce
"Wallahi jakata da nake ajiye kuɗin cinikina ne ta ɓata rasa ta na yi kuma abin mamaki yanzu da nake shaarar nan sai na ga ƙarfen zip ɗin a can" Ta faɗa tana nuni da inda ta ga zip ɗin. Meenal kai ta kawar gefe domin kar a hango jirginta shi kuma tamkar ta faɗa masa saƙon mutuwa ya gaɗe girar sama da ƙasa ya ce
"To ko ni ne na ɗauka?" Ya tambaya cike da gatse. Kai ta girgiza alamar a,a ganin yana neman ɗora mata jakar tsaba kaji su bi ta sai ta ce
"Kawai dai ina mamaki ne wallahi abin kamar almara"Hankalinsa ya mayar kan Meenal da take magana cikin muryar ɓaci duk ta wani shagwaɓe fuska.
Meenal tana ta mamakin yadda aka yi da ta ƙone jakar bata ɗauke da ƙarfen zip ɗin ba.
Ya fara tafiya Sadiya ta ce
",Ina da magana "
Ya ce
"Za ki iya faɗa tun da babu bare a nan" Kallon fuskar Meenal ta yi wacce ta murmusa fuskarta ta nuna alamar murmushin ƙeta wato da alama ta zama ƙarfen ƙafa komai ma a gabanta za a faɗa. Daurewa ta yi tana danne takaicin da suke ƙunsa mata wanda watarana sai zuciya ta zuga ta a kan ta rama sai kuma wata zuciyar ta ce ta ƙyale watarana saj labari!.
Tana kallon yanayin fuskarsa ta ce
"Gawayina ne ya ƙare ɗazu ma dakyar ya isa na yi amfanj da safe... Numfashin ta ya tara da faɗin
"Sadiya ni ba na son almubazzaranci ta yaya za a yi gawayjn a ce har ya ƙare to ni ba ni da kuɗj yanzu sai dai ko in bada itace a kawo miki" Ƙwalla ta taru a idanunta bayan da gawayi take amfanj Meenal tana amfani da gas sannan kuma tana cancantawa amma kuma yanzu a mata maganar ita ce jin hakan Meenal ta ce
",Gas ɗina ni ma fa ina ga ya kusa ƙarewa" !Wani irin washe baki ya yi ya ce
"Tohm zan saka miki idan na dawo" ,Tana masa bye bye ya fita ya tafj Sadiya kuma ta kasa motsawa ma daga wajen, wannan abubuwa ne masu tarin yawa da suke nuni da cewa Nasir ya gaji da ita, sai dai tana jiran ranar da Allah zai kawo mata mafita a lamuran nan. Tana jin yadda Meenal take dariya har da ƙyaƙyatawa da ta ga ta nufi ɗaki, ko da ta shigo ɗakin zaman dirshan a falon tana tunanin ƙarfen zip ɗin da ta tsinta ta rasa ta yaya haka ya faru ta rasa kalar tunanjn da za ta yi, iya hasashe da tunanin ta bata samu amsar ba da a ce a buɗe ɗakinta yake za ta zargi komai ma sai dai a rufe yake sannn da mukulli ta fita idan ba aljannu ba waye zai ɗauka?. Kukan da Kalifa ya saki ne ya dawo da ita daga tunanin da take.
Zuwa can aka zo sayen manja ganin babu ƙullal ne a leda saj ta buɗe jarkar ta tsiyaya a za ta ƙulla saj ta ji warin kananzir cike da faɗuwar gaba ta kai hancinta jikin ƙofar amma sai ta ji warin tamkar ta shinshina jarkar kananzir, da sauri ta saki murfin jarkar ta nufi ɗayan ta farin mai gabanta yana faɗuwa ta buɗe amma cikin ikon Allah sai ta ji babu warin hamdala ta yi a ranta tana ta kissima abubuwa a ranta duk da an ce zato zunubi amma kam tana ta zargi a zuciyarta.
Ko da ya tafi ko ƙeyarsa babu bare a samu wanda zai kawo mata itacen da ya ce, da rana dai gari da madara da sugar ta haɗa musu suka sha, tana tausayin Nasir ranar da haƙƙi zai tambaye shi musamman haƙƙin ɗansa Kalifa domin shi yaron ko kaɗan bai san daɗin uba ko kulawarsa ba ga shi koyaushe daɗa wayo yake, ita damuwarta ma yadda yaron idan ya ga ana mata abu yake nuna rashin jin daɗi ta hanyar kukansa ko kuma yake goge mata hawaye yana ambaton Momma Abba ne? Duk da tana iya yinta don ganin bata kuka a gabansa.
Tana tsakar gida lokacin almajirin Meenal yana mata sharar baranda, ita kuma ta kinkimo jarkar man mai warin kananzir sai kawai suka yi ido huɗu da Meenal ta mata dariya, hakan ya sa a ƙufule Sadiya ta ce
"Wai mai kika mayar da ni ne Meenal sai kike kallona kina min dariya kamar wata mahaukaciya kika gani?" Dariyar ta ƙara yi a karo na biyu sai Sadiya ta ce
"Ko mai mutum ya yi ya je shi da Allah domin yana can a madakata yana jiransa duk daren daɗewa akwai mutuwa sannan akwai hisabi shi dai ubangiji ba ya yafe haƙƙin wani a kan wani" Ɗan dum Meenal ta yi sai ta ji ta kasa cewa komai domin zuciyarta ta fara raya mata ko dai Sadiya ta gane ita ta mata sata kuma ita ta zuba mata kananzir a cikin jarkar manja, domin yanayin furucinta ya bayyana kamar dai akwai wani abu.
Ɗakinta kawai ta wuce ba tare da ta ce komai ba. Da yamma Sadiya ta masa waya tw ce za ta je gidan Hajiya bai musa ba don ya san wani neman wajen ne za ta je tun da Hajiya dai ba ra,ayinta take yi ba, sannan kuma ya san tana zuwa za ta dawo a kan sawunta tun da ba ma lallai a ƙara mata magana daga gaisuwa ba.
Ko da ta je gidan Hajiya ta samu Hajiya zaune a gindin murhu tana tuƙa tuwo, sai goge ido take saboda hayaƙi, ta amsa mata babu yabo babu fallasa don su Hibba ma ba sa gidan sai ita kaɗai. Tabarmar da aka shimfiɗa a wajen ta zauna, ko Kalifa Hajiya bata wa magana ba. Sai da ta rufe tukunyar bayan ta gama tuƙawa ta taso ta shiga ɗaki ta jima sannan a shelaƙe ta fito ta zo ta zauna daga can bakin barandar
Sadiya ta ce
"Dama wata magana na zo da ita... Hajiya ta tari numfashin ta da faɗin
"Sadiya ni ba na sin kinibibi da gutsiri tsoma, wace irin magana ana zaune ƙalau dama duk mace ai sai ta yi haƙuri a gidan miji sannan dama idan kika san ma ba ke kaɗai ba ce sai dai ki kauda kai saboda wani namijin idan ba ya ra,ayin ɗaya ya fi ra,ayin ɗaya a cikin matansa sai dai wacce ba ya ra,ayi ta ɗauki dangana, idan ma ta ce sai ta ga yadda take so tabbas iska tana yawo da mai kayan kara ne!" Ɗago kai Sadiya ta yi suka yi ido huɗu Hajiyar ta kauda kai gefe, sai Sadiya ta ce
"Ba a kan wani abu ba ne dama, kin san ina sana,ar kayan sanyi to shi ne ƴan nepa suka cire wutar ɓangarena shi kuma ya ce sai ina biyan kuɗin wuta ... Hajiya ta tare mata numfashi da faɗin
"Ai ya yi daidai! Kina neman kuɗi kuma a ce sai ya biya kuɗin wuta? Ko shi kike ba kuɗin cinikin yake sakawa a aljihunsa" Girgiza kai Sadiya ta yi daman ta san ba za a mata adalci ba hakan ya sa ta ce
"Yanzu ai na ce zan ke biya amma kuma bai san an mayar mini ba, ana zuwa neman kayan sanyin ina cewa babu kada kasuwar ta mutu shi ya sa dama na ce bari na zo na faɗa miki ko za ki masa magana"
Hajiya ta ce
"Sai ki ɗauki na annabawa ki jira lokacin da idan ya gama busar iska zai sa a gyara miki, abin da sana,ar da kike ta fi goma ko kin ɗauka ba sani ba ne, tun da laila ta ƙiya sai a koma caca, ai a yadda kike caskar kuɗina wannan gidan da ke matan da suke son miji ne da ko aikin hajji ne ma kin biyawa Nasir tun da ta dalilin zaman gidansa da albarkarsa kike samun kuɗi" Shiru Sadiya ta yi ta ma rasa mai za ta ce sai kuma ta daure ta ce
"Yanzu gawayina ya ƙare kuma na faɗa masa ya ce ba shi da kuɗi ita kuma ta ce babu gas ya ce zai saya mata..
Hajiya ta katse mata hanzarin wajen faɗin
"Ya isa Sadiya na gaji da jin ƙorafinki ai dama tun da na ga kin ɗakko ƙafafu da ciki tirtsi tirtsi ke ga kaza sarkin haihuwa san sai dai ƙorafe ƙorafen ne zai kawo ki Allah na tuba gawayin me duk neman kuɗin da kike ma ai ke ya dace kike ciyar da kanki, kuma da kike maganar gas ni baki ga da abin da nake amfani ba tun da gas ɗin ya ƙare sai kawai mai baro na gani da itace Nasir ya aiko, tun da ya haɗu da mace mai jan akala da ragamar rayuwarsa sai dai mu zuba ido"
Sadiya ta ce
"Amma ni ma ai haƙƙina ne ya saya mini, kuma duk arziƙin da mace take da shi Allah bai ɗora mata ɗawainiya da kanta ba, ko da ta fi mijin nata kuɗi haƙƙinta na komai yana wuyansa sai dai idan ita ce ta ga dama bisa kyautatawa!"
Hajiya ta ce
"Yi min wa,azi Sadiya kin san ai ni kidahuma ce babu abin da na sani"
Sadiya ta ce
"Ba haka ba ne Hajiya, wallahi jiya da na fita gidan Kaka na dawo na rasa jakata da nake saka kuɗaɗe a ciki, sannan jarkar manja na tarar da kananzir a ciki...
Tun bata kai aya ba Hajiya ta ce
"Bakya fitar da zakka ne, ai dama wanda ba sa fitarwa da dukiya zakka su asara take faɗawa" Kallon Hajiya kawai take sai kuma ta ce
"Ai sana,ar tawa bata kai munzalin da zan fitar mata da zakka ba, ina sadaka dai"
Hajiya ta ce
"Ke kika sani da yake matsaloli ne suka baibaye ki shi ne kika zo kina zana mini kamar mai biya mini karatun hadda, to sai ki ɗauki ƙafarki ki koma inda kika fito, ko a tunaninki zan zaɓe ki ne in ajiye ƴata Meenal a kan maganar siyan gawayi da gas ai wata kusar ta fi wata kinnga tafiyata" Hajiya tana kaiwa nan ta tashi ta shiga kicin ta ɗakko robar da za ta kwashe tuwo ta yi ajen murhu, Kalifa sai kallonta yake abin takaicin ko uffan bata ce masa ba wai yana jikanta ɗaya tal duk duniya.
Haka ta baro gidan ranta yana ƙuna, tana tafiya tana ta addu,a da karanta sunayen Allah a kan ya kawo mata mafita, ƙaran wayarta ne ya katse mata tunani ta ɗaga ganin sunan ƙawarta Noor tana ɗagawa ta ce
"Albishirin ki"
Sadiya ta ce
"Goro fari ƙal"
Noor ta ce
"Sunanmu ya fito a wannan tallafin da muka cike an ce gobe za a je a karɓi 75k "
Sadiya kawai sai ta ce
"Alhamdulillah, Alhamdulillah" Sai da ta faɗa sau uku Noor ta ce
"Wannan hamdalar fa?" Ta faɗa tana dariyar tsokana
Sadiya ta ce
"Wallahi kawai wata hikima ce ta ubangiji Allah maji roƙo ne, duk wanda ya dogara da shi zai kawo masa mafita, na san wannan sakamakon addu,a ta ne da na yi da yaƙi ni" Noor duk da bata san komai ba sai ta ƙara mata ƙarfin gwiwan na ta ce idan sun haɗu goben za su yi maganar.
Ko da Nasir ya dawo ta faɗa masa cewa ya saka a mayar mata da nepa za ta biya kuɗin sai ya nuna mata ba yanzu ba, ai kuwa ta ƙyale shi. Washe gari suka je suka karɓo kuɗin duk da sun samu layi, dama NIN no da BVN ne ake buƙata da aka cike aka muau hoto sai aka basu ATM mai ɗauke da kuɗin suka cire suka taho gida Sadiya ranta fari ƙal.
Lokacin da ta dawo sai ta ga ƴan nepa su biyu a ƙofar gidan wani maƙocinsu daga can gaba suna mayar masa da wutar da suka yanke, ai kuwa ta musu magana ta biya suka mayar mata da tata wutar ɓangaren nata.
Meenal ta fito daga ɗakinta sai kawai ta ga hasken ƙwan ƙofar ɗakin Sadiya ya kawo hakan ya tabbatar mata da cewa an mayarwa da Sadiya nepa ranta ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, ta ƙufula tana jiran ya dawo don a tunaninta shi ya sa aka mayer da wutar.
Lokacin da ya dawo Sadiya ta fara jiyo hayaniya sosai ana ta tafka faɗa, sai dai bata san abn da suke faɗa ba, tana zaune tana cin farar da ta siyo sai gashi kamar an jefo shi yana shigowa ya ce
,"Wane shegen ne ya mayar miki da nepa?" ,Ya tambaya ransa a matuƙar ɓace kamar zai hau ta da duka.
Ko gizau bata yi ba ta dake ta ce
"Ni ce nan na saka aka mayar mini, saboda na ga baka da niyyar sakawa a maida, ni kuma ina da buƙatar ta, tun da dai ba ni da galihu a matsayjna na matarka da zan aamu wutar nepa a ɓangarena duk da na ce zan biya shi ya sa da na gansu a unguwar suna mayarwa da wasu na ce su zo su mayar mini na biya su kuɗinsu" Kallonta kawai yake yana kissima yaushe Sadiya ta zama haka har take mayar masa martani ko ɗarɗar babu.
Meenal da take laɓe a ƙofar ɗakin Sadiya don son jin ƙwaƙwaf domun ita bata yarda da maganarsa ba da ya ce ba shi ya sa aka mayar ba sa ga shi kunnuwanta sun jiye mata.
Da yatsa ya nuna ta ya ce
"Har ni zan saka doka a gidan ke ki ƙetara?"
Tsaye ta miƙe ta ce
"Ka sa an yanke min wuta na ce a mayar ka wofantar da maganar bayan ka san sana,a nake, na faɗa maka na rasa jakar kuɗina amma ko a jikinka, bayan fitarka daga gidan na samu jarkar manja na ɗauke da kananzir saboda na san ma ba ɗaukan maganar za kamyi da muhimmanci ba ko faɗa maka ban yi ba, na ce maka gawayi ya ƙare ka ce baka da kuɗi, na je na faɗawa mahaifiyarka amma bata goyi bayana ba, ka ga kenan ni idan na biye maka zan dawwama ne babu ƴanci shi ya sa na saka aka mayar mini saboda wannan sana,ar da ita nake tallafawa kaina" ,Tana kaiwa nan ta ɗauki ledar farar ta ta ci gaba da ci.
Rasa ma abin da zai ce ya yi sai kawai ya juya fuuu ya fita, Meenal da take laɓe bata zaci fitowarsa a lokacin ba, sai kawai ta gan shi, rai a ɓace ta sha gabansa cike da ƙaraji ta ce
"Tun wuri ka saka ƴan nepa su zo su yanke wutar nan tun da babu yawunka wajen mayarwa, kana mai gida mace ta yi abu babu izininka kenan ka zama mijin ta ce, nan gaba duk hukuncin da ka zartar ba za ta bi ba" Shiru ya yi yana nazarin maganarta, ya juya kenan zai koma yan saukewa Sadiya ya nuna mata bata isa ba sannan ya saka a yanke mata wutar sai kawai ya ga Sadiya ta fito kamar an jefo ta rai ta haɗe ta kalle su ta ce
"Idan bai zama mijin ta ce ba ai ya zama mai ɗaukan zugar mace!. Wato dama ke kika saka shi aka yanke mini wutar ɓangarena, to wallahi wallahi wallahi ki fita idona na rufe don shiru-shiru ba tsoro ba ne gudun magana ne, kuma wutar nan yadda aka mayat da ita ta maidu in dai kuɗin wuta ne zan ke biyan kayana, amma furucinki ya nuna ba wai a kan kuɗin wutar ba ne baƙincikin sana,ar ne kike...
Hannu Meenal ta ɗaga mata tana faɗin
"Ahir ɗinki Sadiya!. Na fi ƙarfin na miki baƙnciki a kan wannan sana,ar da bata taka kara ta karya ba"
Sadiya tana riƙe ƙugu ta ce
"Guntun gatarinka ya fi sari ka bani," Sai kuwa Meenal ta fara masifa tana cewa ta msta gorin sana,a shi kuma yana tsaye ya kasa crwa komauɓi don Sadiya ta goge masa hadda bai zaci za ta rikice har ta ƙwatawa kanta ƴanci ba.
Faɗa ne ya kacame a tsakanin su amma Meenal ce take ta kumfar baki a dole sai an cirewa Sadiya nepa ita kuma Sadiya ta ce wallahi babu wanda ya isa ya cire mata nepa.
Haka ta koma ɗaki tana faɗin
"Wallahi idan aka cire mini nepa sai na kirawo ƴan nepa sun cire wutar gidan gabaɗaya sai dai kowa ya zauna babu nepa, in kuwa har wani ɓangare na gidan nan zai zauna da nepa to dole ya kasance nawa ɓangaren ma akwai wuta, domin ni ma mutum ce kuma ni ma matar gida ce kamar yadda kike matar gida" Tana jin su suna ta bala,i ita dai gabanta ma faɗuwa yake lokacin da take yin faɗan, amma ta daure ne saboda ta lura matsawar bata ƙwatawa kanta ƴanci to tabbas shan ruwa a gidan ma sai ya gagare ta, ga shi yanzu za ta yi haihuwa ta biyu kenan ita da ƴaƴanta za su rayu babu ƴanci a cikin gidan.
Nasir ya sha masifa a wajen Meenal don tana faɗin ya zaɓi da Sadiya a kanta. Ranar a kan gado ya kwana shi kaɗai ita kuma a ƙasa don kawai ta nuna masa tana fushi, ta ɗauka zai saka a cire nepar washe gari sai ta ga ɗiff bai yi maganar ba ma hakan ya sa ta saka a ranta dole ta je gida domin ta kaiwa Momi kuɗi a je a yi aiki a kansa wato ya dawo sai abin da ta ce masa.
Sadiya kuwa a daren ta haɗa mango juice da zoɓo ta saka a frezer ɗinta. Tana ta addu,ar Allah ya ɗota ta a kansu, tun da ta ga dole sai tana kataɓus wajen ƴancinta tun da babu mai bin bayanta ya ƙwatar mata haƙƙinta daga gidansu har gjdansu Nasir ɗin.
Tuni kasuwar kayan sanyi ta dawo, bayan kwana biyu aka sake kafe sunayen ƴan tallafi Allah da ikonsa sunan Sadiya ya sake fitowa amma wannan karon ban da Noor dama an ce wasu hsr sau uku ma sunan su yana fitowa haka ta je ta karɓo kuɗin nan, tana ta al,ajabi duk da ba a mamaki da lamarin ubangiji ga shi dai ta yi asara amma da yake Allah maji roƙo ne ya mayar mata a lokaci ƙanƙani, sai ta sauya wajen ajiya kawai ya zamana ƙananan kuɗi take ajiyewa a gida, su manyan kuɗin kawai sai ta ba almajirinta ya je pos ta rubuta masa acc no ta a je a tura mata, ya zamana ba ta ma ajiye cash ɗin bare a ɗauke.
Meenal kuwa wuni ta tambaya zuwa gidansu, ta haɗa kan kuɗin wajen Sadiya wanda ta sata, da na wajen Nasir da take masa sata yadda ba zai gane ba, ko ya ce zai sauke ta a gida sai ta ce masa ya je za ta hau napep. Waya suka yi da wani Alhajinta cikin wanda suke holewarsu kafin ta yi aure sannan suna shirmensu a waya ma, haka suka haɗu a hotel ya kama musu ɗaki suka sheƙe ayarsu, ya mata alƙawarin za ta ji alert mai nauyi domin a lokacin wai bankinsa ya samu matsala kuma ba shi da cash.
A ƙofar gidansu ya sauke ta, dama ta yi wa Momi waya haka suka fito Momi ta tare musu wani mai napep, su biyu ne a ciki mai napep da kuma wani a gefensa a zaune, Momi ta kwatanta musu inda za su kaisu, don sosai sai an fita ma daga gari wani ɗan ɗauye ne haka suka yi ciniki, sai suka yanka musu kuɗi da yawa Mominta dage tana neman ragi buɗar bakin Meenal tana dariya ta ce
"Momi akwai kuɗi fa, kuɗi ba matsala ba ne kawai mu je ai biyan buƙata kawai ake so, ai tun da Nasir har ya fifita wanann ƙazamar matar tasa marar aji sai ya gwamamce kiɗa da karatu"
Momi ta ce
",Yaushe ta zama ƙazama bayan na ji ana cewa tsaftar masifa gare ta"
Meenal ta ce
",A,a kawai na faɗa ne"
Haka suka ci gaba da tafiya suna tafiya su Meenal da Hajiya suna ta tattauna zancen kuɗin da yake a jakar.
Momi ta ce
,"Wallahi gwara da kika raba shegiya da kuɗin ai da sannu zaman gidan zai gagare ta,"
Meenal ta ce
"Ai bokan nan ko nawa ya buƙata zan basho, dama akwai ma wani alƙawarin kuɗi da aka mini" Sun saki baki suna ta zuba, basa lura da cewa basu san su waye masu napep ɗin ba, kawai mutane in suka shuga napep ko motar haya sai su saki baki suna ta zance, wani ma sirrinsa zai ke faɗa abubuwa dai barkatai ba a takatsantsan.
Duk abin da suke masu napep ɗin suna jin su, sannan suna ta yi wa juna magana da ido don sun gama shirya komai ba tare da su Meenal sun sani ba. Sai da suka yi nisa a tsakiyar daji gaba babu kowa haka ma baya sai kawai mai napep ta taka birki ya tsaya Momi ta ce
"Ya dai?"
Sai ya ce
"Mai ne ya ƙare shi ne zan zuba wani"
Meenal ta ce
"Don ma kana da akwai da yanzu a nan ina za a samu wani mai"
Mai napep ta ɓangaren Momi ɗayan da ya fito ta ɓangare Meenal dama majiya ƙarfi ne, hasali ma ba masu napep ba ne arowa suka yi a wajen abokinsu don su yi damfara sai kuma tsautsayi ya faɗa a kan su Momin.
Duka suka yi wa su Momin suka ƙwace jakar Meenal da wayoyin su, sai da suka musu lilis sannan suka shiga napep ɗin suka kwasa a guje, suka bar su yashe a nan tsakiyar hanyar tsakar daji, kowacce tana murƙususu don hatta bakinsu da hanci ya sha naushi, basu ma da ƙwarin gwiwar hadda ce lambar jikin napep ɗin!
Yau Sadiya kawai muka taɓo ina da uzuri ne.
MAMAN AFRAH
***