46
by @surayyahms
ABUNDA KE ƁOYE💫
arewabooks@surayyahm.
⏯️4️⃣6️⃣
tunda hajiya hajara ta gama tsige aminiyarta hajiya mairo akan batun maganan auren zaidu da fatima sai bata sake cewa komi ba, suna zaune anan suna yan hira har ammi karama ta kawo musu abin taɓawa albarka suka saka mata da har zata wuce dakinta taje tay wanka hajya hajara ta zaunar da ita ta dinga mata nasihohi masu ratsa zuciya da shiga jiki, nauyi da kunya duk yabi ya hana hajy mairo cewa kowa ba har hajiya hajara ta sallameta ta fita.
ata fannin bappa zaidu kuwa gabaki daya daren ranar juyi yakeyi akan fankacecen gadonsa da tunanin yadda zai iya bullowa al'amarin aransa saida yasamu cikakken nitsuwa yay tunani me zurfi snn ya iya sake ransa yayi hakuri.
washe gari da safe as usual suka fita sallahn fajr ibaad ya jasu bayan an idar suna shigowa cikin gidan ya kirawo shi sukaje private palonsa acikin sashen sa. ibaad yana daga kasa shi yana sama.
kai tsaye yafara sanar dashi abubuwan da ya farun jiya, dan yasan da wuya ne inyana da masaniya dake tun asubah jiyan ya fita kuma bai dawo ba saida yamma lisss.
har saida ya gama fayyace masa halin da ake ciki snn yay masa nasiha, ya kuma sanar dashi bada son ransa bane daya zo yana dawo masa da wnn maganan. su dauka kawai duk wannn abun qaddara ce dan haka umarni yake bashi da yay hakuri ya amince ayi auren, inyaso daga baya in komi ya lafa sai ya aure duk wacce yakeso ya hadasu su biyu.
tunda bappa zaidu ya furta masa wnn maganan saiyaji kamar iska ya dauke masa baya shaqar numfashi ganin yakasa amsawa yasa bappa zaidun yace masa yaje yay tunani zuwa yamma ya bashi amsa yay masa nasiha ya kuma bashi hakuri sosai..
jikin ibaad a sanyaye ya tashi ya bar wajen bai masan sanda yakai kansa dakinsa ba he laid on his bed for a while yanajin kamar baya duniyar ne gabaki daya, sai can ya jawo wayarsa yafara kkrin danna lambar mum dinsa ganin bata dauka ba kawai ya miƙe ya shirya kansa duk sonsa da tsafta yau ko kula wanka baiyi ba, karfe 7 dede saigashi ya shigo cikin gidan idonsa a rufe kai tsaye dakin amminshi ya nufa hanklinsa a tashe sosai...
tana gama gyara koina kenan zata fito ta shiga kitchen yay sallama ta amsa masa yashigo gani tay kawai ya zauna kasa jikinshi a mugun sanyaye yayi shiru baice komi
throw pillown dake hannunta ta aje ta karaso wajensa tace "rayyan ya naganka da sassafe haka lafiya kuwa? ko bakajin dadin jikinka ne...
jin kamar idan ya budi bakinsa zaiy kuka yasa ya sunkuyar dakansa can kasa gwanin ban tausayi baice komi ba saida yadan samu nitsuwa taciki. shirun dayay yasa atake jikinta ya bata, waje ta nema ta zauna kusa dashi akasan da sanyin murya tace rayyan pls talk to mummy, kunyi magana da bappanka ne ko?
yana dago kansa taga idanunsa yay jaaa zai magana cikin katsesa tace "honey, Its for the best" Dan Allah kayi haquri none of us wanted this for u. musmn ma kawunka wallh jiya ya bani tausayi dan inda anbita nashi da ya gwammaci hajiya mairo ta tsine masa akan daya maka wann auren..pls look at it as ur destiny...kay hakuri...
cikin girgixa kai hawayensa tsilli daya ya sauko murynsa na rawa yace "Ammi wallah bana kaunarta, kuma bappa bai taɓa bani umarni akan wani abunda banaso ba sai wann karon, iyakan zamana da shi a gidansa he always defended me har sama da farin cikin matarsa, ni ynxu bansan me zance masa dan banason saɓawa umarninsa kuma harga Allah banason na aure zainab sabida bana kaunarta kwata kwata banajin zan iya kallonta a amatsyin matata..
da tausayinsa a idonta tace "nasani..dama kuma ba auren soyayya muke nema agareka ba rayyan...inada yaqinin cewa zainab wata bangare na jarabawa da kuma qaddarar kace, hala wani gwaji ne da Allah ya aiko maka dan ya jarabce rayuwarka snn karkamanta tun tana karama sosai ta fara wann abun. gashi har yanxu ta girma dashi yaxo yanaso yay sanadiyar rayuwarta, toh da ace ka bijire ka wargaza zumunci akan rashin haquri kuma zaonab tazo ta rasa ranta sanadiyarka gara ace kay musu biyayya kay hakuri ya zamo kaine aka zalunta bakaine ka zalunce kowa ba..if ure patient Nothing evil will ever happen to u addua ta kullum yana tare da kai, nide hakuri nake dada baka dan Allah ka rufa mana asiri yazamo nan gaba baza'a a kalleka ace kaine kayi sanadiyar tarwatswer zumunci da kimar gidan al-mansur gabaki daya ba. pls dont think as her a matsayin zainab da baka kauna, just look at her as a fragile life dat needs ur company to be able to dream nd breath again, nd i know my son wudnt be the reason for sumones grieve, or life lost..u wont be the reason to tear this family apart, kaduba girman abunda zakayi a idon Allah, this is a huge secrifice for the entire family nasan mahaifinka zai yi alfahari dakai..pls keep ur desires aside rayyan, nd do this for sake of Allah... besides babu wanda zai hanaka auren wacce kakeso anan gaba
...kawai kay hkuri ka ansa wa kawunka, shima ya samu nitsuwa kaima ka samu nitsuwa gidan nan duka a samu kwanciyar hankali...inda mahaifinka na raye you know he will prefer to keep the peace too, kuma shima da abun da zai roka awajenka kenan.. duk wani walwala da farinciki da zumuncin gidan nan yanxu haka yana wuyanka ne, be the bigger person pls nd think abt it..amma koma miyene nidai dan Allah karkace ma kawunka a'a zaka kunyatar dashi, just let it go..nd let god see u throu. inma taruwa akayi agidan nan duka aka cutar da kai kabari kawai Allah zai saka maka. kuma in sha Allah zaka cinye wann jarabawar
hawayen dayake zuba a idonsa yasaka hannunsa yashare ahnkli muryansa a sanyaye yace toh shikenan ammi tunda kema hakan kike gani bakomi zanje na sameshi in sanar dashi na amince zan aure zainab din..
kusan dede nan kalmomin nasa suka dira acikin kunnen ayaanah datazo kofar dakin da sauri da niyyar zata gaisher da ammi dan yau exams na IRS zasuyi karfe 9am dai dai tanaso ne taje tafara shiri dan tuni tagama duk wani bitan karatu da zatayi.
tana dada jin muryansa aciki ta tsaya cakkkk dan har wani yaam yaam taji kunnuwanta na neman toshewa tafara jin jiri jiri ne ko faduwar gaba ne duk ta rasa me takeji, she instantly frozed har ta gama jin conversation dinsun na karshen yadda yake tabbatar ma mum dinsa zai hakura kawai ayi aure. ita iyaka nan kawai taji..yau yaa ibaad din nata ne dakansa yake cewa zai aure anty zainab arifah??
batasan how many minutes tay a daskare ba ita bata bude kofar ta shigo ba ita bata iya jan jikinta daga shock in datake ciki ta koma room inta ba, jim kadan sai taji inuwar mutum agabanta,
kirjinta na bugawa da balain karfi ta daga idanunta sama taga shine har ya fito, suna hade ido dashi hawayen da batasan daga ina suka taho ba suka fara sauka a idon ta jikin ta na rawa rawa ta juya da uban gudu zata koma daki yay saurin biyota yana furta "ayaanah, ayaanah..
...amma inaa bata tsaya ba tana shigewa dakin idonta a rufe kamar mai aljanu tanufi bayan gidan tay sauri ta kulle kanta aciki tareda rusunawa akasa da wani irin mtsanancin kuka me daga hankali sosai, hanklinsa a mugun tashe ya shigo dakin yana kirar sunanta safiya tay marmaza ta sauka akan gado ta fice basu waje.
kirjinsa kamar zai amon wuta ya tarwatse ya tsaya daga bakin bayin yana jin sautin kukanta yana cewa "ayanaah pls come out..is not what u think..dan Allah ki fito..kinji?? kukan kawai takeyi jikinta na rawa rawa dan ita kanta bata sanma me takeji a dukkan ilahirin jikinta ba, ji take kamar she just cant take it..gashi Allah yadora mata wani irin matsanancin kishinsa musmn ma akan zainab arifahn...
rokon duniyan nan yay mata ta fito amma taki fitowa har kukan ya lafa, muryanta na fita ahankli cikin sheshhka tace masa kawai ya tafi ita bata so tay magana dashi ne yanxu sabida batajin dadi. tun 7.30am yana tsaye har saida 8am ya wuce ayaana bata fito ba, dakyar ya hakura ya fita agidan dan kawai ta samu ta fito ta shirya taje exams dinta.
fadin tashin hanklin daya shiga wann rana bazai kiyastu ba musm da yasan ayaanah taji komi daga bakinsa nd he knows bazai taba samun nitsuwa aransa ba kuma yanxu..
tsabar kansa ya dau zafi yana komawa gida saida ya fada wanka da ruwan sanyi mai sanyi sosai, haka ya bar ruwan showern ya zuba akansa sosai, so that his muscles will calm down and relax, wnn ne karo na farko da yarasa yadda zaiyi da rayuwarsa everthing bcome so intense musmn da yaga reaction din ayaanah dan yasan yarinya kuma zaisha wahala kafin ta fahimce shi.
cikin danne abun aransa ya shirya ya wuce harkokin gabansa he tot abt it all day, yana yi yana gwada lambar ayanah amma har yanxu ji yake akashe, da yamma liss daya dawo bayan sallahn isha'i nan ya gaya ma bappa zaidu cewa "ya amince zai masa biyayya kawai dan haka yabar masa komi ahannunsa...bappa zaidu was very proud of him daya cika dan halak ya masa wann halaccin, nd for the immense secrifice nd respect for the family, duk dama baiji wani dadi ba dan haka nasiha yakara masa, yace masa wann abun jarabawar rayuwarsa ce, Hala haka Allah ya qaddara zai hadashi da wani abunda baya kauna dan yaga iya level din imaninsa da hakurinsa da juriyarsa da kuma biyayynsa ga dokokin Allah,...yace masa bama su kawai yay biyayya ba ya dinga tuna Allahn daya jarabce shi shima zaiy alfahari dashi in yay hakuri, snn zai samu ladan hada kan ahalin sa, da ladan yin hakuri da wnn mummunan qaddara, snn kar dan baya son zainab aransa yay amfani da wnn daman ko ikonsa na mijinta ya cutar da ita, dan a sanadiyar haka sai Allah ya shigar da ita aljanna shikuma rashin hakuri da rashin sauke haqqin aure akanta sai ya kaisa wuta. haquri ya bashi sosai yace masa duk yadda ake ciki shizai kasance tare dashi bazai taɓa kyalewa a cutar dashi ba, snn kowa cece yazo yace yanaso nan gaba zasuy kkri su aura masa, dan haka yay hakuri karyace komi ynxu har sai anyi aurensan zainab ta samu lafiya zasu san yadda zasuyi.
godiya ibaad yay masa suka bar maganan anan, sai ya shiga motarsa adaren yazo gida..kai tsaye ya wuce sashen amminsa zuwa yay yasamu wai ayaana tana bacci, ammi tace masa ai yau batay ma exams dintan ba a hall din taje ta fadi ta suma aka dawo da ita da zazzafan zazzabi tasha maganin kenan tay bacci..
lahawla wala kuwwata ya rika nanatawa acikin zuciyarsa hanklinsa gabaki daya baya jikinsa he stayed beside her for a while ko zata farka suyi magana ya lallabeta amma bata tashi ba, har sai wajajen 11.30 na dare kafin nan ya hakura ya koma gida.
washe gari ma sassafe haka ya dawo gidan, still ayaanah ta kulle kanta a daki taki sam ta kulashi, she missed 2 of her exams ma wann kwanakin, both IRS nd geogrphy dan wani irin kishi mai balain rufe ido yahanata numfashi ta kasa jin sauki aranta kona minti daya, duk sukabi suka dagula ma ammi karama tunani har tasoma gane cewa dole ne kawai da akwai wani abu special atsakaninsu...
ita bata san cewa ayaana taji cewa zai aure zainab arifah ba, so she cant really conclude cewa rikicin kishi da soyayya ne, shikadai yasan da hakan, arana sai yazo gidan sau hudu sau biyar duba jikin ayaana saitaga ita kuma ayaanan batason tana kulashi, sam taki su kebe suyi magana, taki sam yazo kusa da ita.
wann yanayin suke ciki har na tsawon kwana biyu lamarin auren bai hanashi bacci kamar tsnanin fushin da ayaanah takeyi dashi ba.
daga dayan bangaren kuwa aranar da aka kan shirin sallame zainab arifah da safe around 8:30am bappa zaidu yasha manyan kaya yay kyau ya shigo asibitin kai tsaye dan dama shi bai taɓa zuwa ba. koda security suka ga spitting kamannin da sukey da prof da kuma irin kwarjininsa na babban mutum mai ji da naira wata mayyar sky blue shadda ya saka garensan nan taji aiki me aji, sai maza maza suka bashi hanya, infact har ciki securiry suka rakosa ana masa fadanci har private room din da ake monitoring zainab din aciki...
her life line has increase with 50% chance of recovery saidai haryau bata magana kullum idonta a lumshe da hawaye aciki, prof yadan fita yana waya da lawyer dinsa kenan hajy hamida taji sallama a kofa...
dake ma har muryansu yana dibi sai tay zaton mijinta ne da mamaki ta amsa dan tasan mijinta baya yin sallama in zai shigo waje...
wani irin sanyin qamshin
turare taji me tsada da kuma dadi dayasa ta juyo da sauri suna hade ido da bappa zaidun atake fuskarta ya wani sauya tamiƙe tsaye da raini tana yatsinawa...
muryanta kasa kasa tace 'ohh ashe kai ne..
sama da kasa ya kalleta a dakile bai tsaya sun gaisa ba yace hamida ya mai jiki??
kafin ta amsa taga ya dauke kai ya wuceta wani irin zafi taji akan kirjinta dan tarasa wani irin jiji dakai wann mutumin yake ji dashi mutum ne da bata isa ta zageshi ko ta rainashi ba sbd kwarjininsa kuma da alama taga kamar rashin mutuncinsa da walakncinsa yafi wanda ka kanta yawa.
kai tsaye ya karasa gadon da zainab take ya zuba mata idanunshi for a while kafin yace.."Doter Zainab arifah are u awake? ya jikin naki.
..jin ance doter zainab yasa tay firgit tabude ido da sauri hawayenta na zuba ahnkli tana ganinsa tace"uncle zaid??
dan karamin murmushi yay yace "how are u feeling? ya jikin naki..bata amsa shi ba ta langwane tareda fashe masa da kuka sosai ta motsa kadan ta matso jikinsa tarike masa hannu ta dora kanta akan hannun nasa tana kuka a agajiye...
da muryan kukan tace 'uncle zaid i am sorry dan Allah kar kace banyi hakuri ba...i jst cant take it anymore,.pls help me. amugun makirce take furta hakan da zimman takara cusa masa tausayi dan tasan shine bbn mtsalar yanxu dan taji sarai lkcin da akace shine yahana auren..
she was just crying nd begin him yayi shiru da tausayinta a idanunsa yana shafa mata kai yana sassaita ta
..aka bar hajy hamida tana kumbura fuska kamar zata tashi sama wato ma zainab tana da muryan yin magana shine su bata musu ba take ma wann mutumin
da tsananin bacin rai ta sabule ta fita a dakin ta samu prof a gefe yana waya tana isowa tana huci muryanta kamar zatayi kuka tace alhaj alhaji alhaji.. da sauri ya katse wayar yace "meyene? da bacin rai tace "wancan mugun dan uwankan ne yazo nd u cant believe it zainab is now talking to him...tsabar ta kufula hawayenta na zuba tace "for good 3 days muna nan muna wahala zainab bata mana magana ba sai shi? nikam wallah kazo karya kara juya ma yarinya kanta i am sure he is using magic nd charms on her..
tanakan maganan yaja tsaki da mamaki yace kina nufin zaidun ne yazo nan duba jikin zainab?? kafin ta amsa azafafe yafara kiran security babbansu na zuwa kawak ya daukes da mari yace how dare u let anyone come in here witou my permission? security ya fara bashi hakuri masifa ya ke ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, dakyar hajiya hamida ta janye shi suka koma daki suka samu bappa zaidu har yadaga zainab daga kwance ta zauna ya saka mata pillow ta jingina bayanta dashi
bai mata wani dogon nasiha ba,sama sama kawai ya gaggaya mata makomarta inta koma wajen Allah a matsayin wacce ta kashe kanta snn ya bata hakuri yace mata sunyi magana da ibaad karta damu. intay masa alkwarin zata cire komi aranta ta warke toh shida kansa zai tabbata anyi auren su da ibaad batare da anja lokaci ba, amma sai ta masa alkawari bazata sake yunkurin kashe kanta ba no matter what. .
tunda aka fara case dinnan zainab arifah bataji wani sanyi aranta ba face yau. da sauri ta amince masa, tare da masa alkwari cewa bazata sake yin haka ba.
yace mata shikenan shima zai cika mata alkwarinta zai ma babanta magana azo ayi maganan aure kawai
babu shiri yaji ta fado jikinsa ta rungumesa da karfi tana hawayen murna tace thank you sir thank u uncle zaid ure the best uncle in this world...
cikin haka sai ga su prof din sun bankado kofa sun shigo kamar wasu mayaka, he was dumpfounded dayazo yaga zainab ta rungume bappa zaidu tana kuka tana murna tana masa godiya
hajy hamida taji kamr zata fashe, fushi ya debe prof ya karaso tare da fincike yarsa
ajikin bappa zaidun yana cewa "how dare u show ur face here zaidu?uhhh kazo harnan zaka karasa min ita ko?to wallh ka fita kafin na maka abunda har ka mutu bazaka manta dani ba
wani irin kallo bappa zaidu yamasa yace" kai wai yaushe zaka girma ne kabar wann shirmen...as u can see ur doter is fine nd happy only bcos i came. i am not the monster u think i am zayyanu, kaine dai da kajima kana kokrin raba kanka damu kaine kake da matsala da kowa, zainab is like my doter too, i care abt her happiness.. anyways na gama duba jikintan ni zan wuce sauran bayani zakaji a bakinta
ya kalle zainab yace" doter Allah ya baki lafiya..
da wani irin murmushin jim dadi tace "thank you so much uncle zaid i love u soo much uncle..
bappa zaidu yana fita bakinsu a sake suka juyo kanta ganin tsananin farin ciki dake shimfide akan fusrkta kafin ya budi baki tace"Daddy, he said yes"
in unison suna kallonta kusan adaskare sukace "whaaaaaat?
share hawayenta tay da sauri ta sauko kamr ba itace tay kwana uku bata ko motsi ba.
tana kallonsu duka tace 'uncle zaid yace inhar na masa alkwari bazan kara memeta haka ba zai min auren,..nd i told him i promised..nd he said he will get us married..yace min he has told ibaad alredy nd kaima zakuyi magana kuje ayi maganan ranar auren.
wani irin tsaki hajiya hamida tay a mugun kufule tace nd "is that why ure fucking happy u bloody ingrate???
a daskare prof yake kallon zainab da mamaki yadda yaga tamike zaune garau
yace hamida is enuf karki sake mata tsawa, cant u see how this news has make her happy??yaushe rabonki da kikaga princess dina haka
...ohh my baby come here
..tana karasowa ya rungumeta yace i am so happy ure back okay? zo ko zauna ki gaya min duk abinda yace miki
tana murna tace thanks daddy..i know u love me nd i love u too...but, wil u go and meet him?
yay dariya yace 'sure princess, zanje mana. amma ai sai kin cika masa alkwarinsa
...since we have two more days in this hospital. prove it to me dat u want to get better. take all ur medications, deep sleep, don't cry..alwys talk to u daddy.
murmushi tay yana karasowa jikinta ta kara rungumesa tace 'i will do just that for u daddy.. da tsananin kaunarta aransa yay kissing inta slihgtly akan forehead inta yace dats my girl. snn ya jawota sula zauna tare akan gadon.
wani irin tsaki hajy hamida tajaaa tana masa kallon mahaukaci da sauri ta fita waje tana huci me zafi..
sam sam ranta baiyi dadi da aka gama case din nan da wuri har haka ba, dan koba komi taso ace an hada case dinnan yay zafi, dan prof yayi amfani da powernsa yaci mutuncin familynsa ya tagayyara zaidu da hajiya mairo ita babban burinta kenan taga yaci mutuncin ahalinsa musmn ma uwarsa snn yahada harda tsinannen yaron nan ibaad ya karar masa da rayuwarsa a lkci guda.
she stayed outside for a while, har saida abun ya wuce mata kafin tazo ta samu zainab arifah da babanta, this rush of emotions yasaka har line inta yatashi daga 50- yakai 68% kamar ba ita take kan langwabewa ba, tana ta hira da babanta, ya aji komi aransa yanakan lallabarta dan ta warke sosai..
fannin ayaana kuwa kwana biyun nan gabaki daya takita kula ibaad dan koyazo gidan bata sakewa ta fito inya kira kuma wayarta yawanci zaiji a kashe text message dinsa gabaki daya bata amsa ko guda daya ba. he explained most of the situation to her tru text amma haryau baiga ta sauko ta amsa shi ba, sai dai ta karanta tay ta kuka danji take kamar itama mutuwan kawai zatay in ya aure zainab arifah ba ita ba.
haka rayuwa ya kasance, 4 days later zainab arifah ta dawo cikin hayyacinta prof yana tsare da ita kome tace masa tanaso sai kaga ya mata, baiyi fushi ko ya mata fada ko sau daya ba, instead wani irin sakalta ya cigaba dayayi har likitotin abun yana damunsu aransu
everything she says shi ake ji, and everything she want komeyene shi kawai yake mata. akwana na hudun dayaga tana bada hadin kai sosai anaata jinya her ECG has reached 98% yanxu kuma tana cin abinci sai kawai aka sallamesu da dare suka dawo gida
ranar gabaki daya he was with her a room inta yana gaya mata kalamai masu tsananin dadi har tay bacci tana murmushi tareda jin matsanancin son babanta aranta sosai
the moment ya koma room dinsa kuma ya sauya fuska suka zauna sukayi magana da matarsa hajya hamida dan yasan yanxu babu yadda ya iya dolene kawai yaje family house again ayi magana asaka ranar daurin auren nan, all this while bai taba fitowa fili yagaya ma matarsa hajiya hamida boyayyen qudurinsa akan zainab ba sai yanxu.
wanda tunda ya fara fayyace mata yadda ya tsara rayuwar zainab din itama saida taji tsoro ta hau sara mashi.
cikin dare ya gaya mata dokokin da zai saka ma zainab, na farko kuma mafi muhimmanci shine babu wani hidimar biki na yar gata da zasuyi dan ko sisin su bazasu sake su kashe a auren nan ba, everything will be within the family, shine kawai zai gayyato manyan bakinsa maza aje daurin aure dan a shaida ya aurar da yarsa shikenan.
na biu kuma ya riga yagama shirinsa da likita, yace mata daga gobe, zai bata wani magani da zata rika zuwa ita dakanta tana bawa zainab arifah tana sha agabnta dan maganin hana haihuwa ne, snn zaa mata small surgery a mahaifa zaa toshe hanyar da sperm zaibi yana shiga, wata nurse zataso har na tsawom wata guda tana kulawa da ita in ayi surgeryn dan baiyasone kwata kwata zainab ta haihu a gidan ibaad, cos he still suspect that in ya hada jini da su zasu kashe masa yarsa snn suyi amfani da abunda zata haifa a kwashe mata dukiya...
doka na uku shine zasu cigaba da yin duk yadda zasuyi suga auren zainab din baiyi lasting har abada ba ta hanyar sponsoring da providing rayuwar ibaad da komi daya shafi financial freedom, yace mata zai bawa ibaad kujeran MD a kamfanin da zainab din take jagoranta, sabida su san samunshi da rashinsa, da komi dayake ciki finances dinsa ya zama a tafin hannunsu yake.
nd he believe zainab will come back to her sense one day, cos no woman want a weak man, intaga ibaad yana karkashinta ne baida arxikin kansa sai nata zata rainashi, on the long run zasu cusa mata ra'ayin da zata ji bai dace da ita ba idan kuma aka kai matsayin da auren zai tarwatse then they will snatched their wealth frm him, disgrace him, locked him up and make him miserable nd poor forever. yarsu kuma sai ta aure wanda ya dace da ita ta haifa masa jikoki da miji within her class cikin salon alon, wai ahakan kuma gani suke sunyi maganin yan hassada da yan son amfani dayarsu dan su gaje arzikin yarsu anan gaba
hajiya hamida kamar zata zuba ruwa akasa tasha tsabar farincikin dirar plans din nan, 100% ta goya ma mijinta baya. tace masa yabar mata part din cusa ma zainab ra'ayin tsana da raina miji..cos she knw extly when to begin tace masa lokcin obsessive soyayyar ya fara gushewa dats when she will start her own.
perfectly suka hada plan dinsu, washe gari akwana na biyar they behave normal agaban zainab basu ce mata komi ba. har saida akaci one full week snn sukazo room dinta da dare zasu mata goodnite.
anan ne prof ya sanar da ita cewa gobe ne zaije suyi magana a saka ranar auren nata, but...he has his writen rules on paper like a contrct, inhar ta amince ta tasaka hannu akai toh maganan aure angama dashi.
tsabar zumudi tace masa ai koma miye dokar zata bi inde she wll get to answer mrs ibaad a rayuwarta,duk dama arazane take da reaction din nala, ta lura kamar nala is scared da maganan matarcan boka datace aurensu bazaiyi ba,but she is still counting on the fact that rukky tace mata "ko da yayu it will be her karma" meaning zai iyu faruwar kenan,. oh well then, fuck the karma, ta riga ta sa aranta tunda har akwai tiny chance na yuwar auren duk wani mummnan qaddara da zai biyo baya zata iya dashi
infact she will create her own destiny ai anty saferea ta taba cemata bokayen nan mugayen makaryata ne
tay tunanin duk dokokin babanta bazai wuce akan kudi ba, well, daya bata papern taga abubuwan daya shafi kudin, da yadda zai dauki nauyin rayuwrta dana mijinta an all that, batun rashin haihuwar ne ya mata bambarakwai kuma ya mugun daga mata hanklinta sosai..but she quickly discard it, cos is better to lose a child than the father.
ranta baiso har can can ba tay ma babanta biyayya tayi signing komi snn tace masa bazata taɓa karya dokokin sa tamasa alkwari.
tunda suka gama da wann fannin shi ya fita yaje family house, hajy hamida kuma daga safiyar ranan ta fara dura ma zainab arifah kwayoyin hana haihuwa
dagata dayan bangaren kuwa tunda aka fara maganan Auren ibaad komi ya lafa gidan sai kananan gulma dake tashi here and der msammn daga wajensu ammi babba da su anty safeera, ga hjy mairo ma inzaty magana babu sirrii sam sai kowa yaji, wanda duk dama ayaanah tana fushi da komi acikin satin nan gabaki daya saida behaviours din mutanen gidan yasaka ta gane cewa komi na dole akayi ma ibaad snn yana cikin wani hali gashi wainashi data dingay yasa yadan kyaleta dan shima yaji dakansa cos he is hurting soo much msmn dayaga ayaanah taki ta fahimceshi.
zaizo gidan baifi sau biyu ba, dayaga har yau batako lekowa bata amsa sakonsa bare kira ranar kawai sai yahakura ya dauke kafarsa yau kusan kwana biyu kenan baizo dubata ba, kuma bai kira ko ya tura mata text din lallashi daya saba kowani rana ba..
duk sai taji kuma ta damu, barinma ranar da sukayi waya da sultana sukayi dogon hira duk ta kwashe labarin wasu abubuwan da ake ma ibaad din,da wanda yake ciki duk ta fayyace mata tace mata auren nan fa bappa zaidu ne suka bashi umarni kuma dama kowa yasan hjy tace zata tsine masa, tace ai yanxu ma bata fiye ganinsa yana cin abinci agidan ba nd he look pale nd sick yanata shiri ma zaiyi tafiya kasar waje next week.
duk sai kuma ta rasa meke mata dadi, yau da safe tay tunanin duniya na yadda zata kirashi ta bashi hakuri amma takasa tabuka komi musn inta tuna irin wahala da wainashi datay akwana biyun nan. dake weknd ne ranar ma basuda exams, takira ruthy ta tambayeta me zatasha jikinta yay zafi ruth tace mata ta gwada shan yellow flagyl wasu yana sa jikin su yay dumi.
bayan sunyi breakfast ta sace key tafita da motar ammi karama tajeta chemist nemo yellow flagyl. fitarta bada jimawa ba prof yazo aka kira bappa zaidu aka taru a falo
bai rusuna ba ya gama nanata dokokinsa haka ya kawo batun cewa ai tunda zaidu yaje asibiti ya lallaba zainab a tsayin kawunta shima kenan dan ya bawa ibaad matsayi da gidan zama yakuma dauke masa nauyin ciyar da mata balaifi bane tunda shima ai kawunsa ne so yana da cikakken dama yamasa wann gatar.
haka uncle moh ya goyi bayan prof 100% yadinga maganganu yana yabonsa snn suka saka hajya mairo dole dole ta amince da komi dayazo dede da ra'ayinsu, da sunan wai ana neman sulhu da hadin kan family snn kuma adalci ne akayiwa ibaad shima kar ace ba'a masa gata ba dan ubansa baya raye.
they manipulated his intention behind doing everything suka nuna ma hajiya cewa wai gata prof yake so yay ma ibaad amatsayin shi na maraya kuma kawunshi shiyasa zai dauko nauyin komi kuma zai bashi MD na kamfani.
bappa zaidu yanata kallonsu da mamakin munafurcinsu aransa tunda yaga hajiya ta hau kai hartana wani kuka tana ma zayyanu godiya akan hallaci da gata dayama ibaad
bappa zaidu baice komi akan batun saka ranar ba, dan nan ma prof ne yay babakere akai yace ma hajiya sai nan da wata daya yakeso ayi auren sabida yana so a zainab arifah ta samu kwarin jiki kar akaita gidan miji da rauni bata gama warwarewa ba.
saida suka gama tass snn ta tambaye bappa zaidu ko duk hakan ya masa, ya kyabe baki yace ai dama sune da biki shidai rule dinsa dayane muddin wann ya aure bazai hana ibaad kara aure agaba ba shikenan, tunda wann na dole ne, toh ya zama dole kuwa abashi dama nan gaba yakara aure da wacce yake so. da mamakinsu prof yace shi wann bai damesa ba shidai kawai kar ynxun ayi abunda zai tabbatar masa da cewa ran yarsa ake nema ba auren kare rayuwarta kona zumuncinsu ba.
sosai ya rika jadadda musu muddin ibaad yay wani abunda zainab ta dau ranta wallah za'a fuskance walaknci da tozarci daga wajensa dan bazai taba yafewa ba kai daga ranar ma kawai gara uwarsan ta tsine masa kawai dan zai musu hukunci ne kamar bai sansu ba.
duk yabi ya cusa zcyar ma hjy mairo tsoro, nan akagama magana aka bar auren in four weeks time wanda dede lkcin da zainab arifah zata gama jinya kenan.
suna ficewa bappa zaidu ya kira ibaad awaya office dinsa yace maza maza yana son ganinsa..
lokcin ibaad yana wani important meeting ne shida jamal da farhan da prince hassan a gidan mahaifyar jamal din wata lady diana kirar yazo masa saiya roki bappa alfarma akan yabashi awa guda yanxu zaizo...
Dama kuma auditioning suka hadu sunayi, suna warware cigaban da suke samu, da inda zasu kara pushing dan lady diana ta kawo musu sabbin crude oil patners tanaso each of them ya saya 10% share a wani saudi arabian oil makert da zai na kawo musu return na billion 2 ko wani wata. haka suka tattara files suka har hada suka cire kudi, kowa ya bada nashi, but they need one more person kuma sun rasa wazasu saka, ibaad was thinking abt maheer amma daya kirasa sai maheer din yace masa bai shirya ba dan acikin yan uwansa karankaf maheer ne kawai yasan ibaad yana da wani abu waishi kudi amma haka yay shiru shima bai gaya ma kowa ba ya rike sirrin dan uwansa kmr yadda shima ya taba rike masa, ganin bai samu kan maheer ba kawai saiya siya share din ma bappa zaidu ragowar dayan slot dinsa yacike masa awajensa.
lady diana itace zata processing musu komi next week duk zasu kasance a kasar waje ayi signing duka legal documents acan dama kuma ibaad yana so yaje ya karasa gama furnishing din makaken gidansa da already last week aka gama shi tsafff...
sum shirya in sun gama meeting din kawai lunch zasuyi atare anan gidan su jamal din but due to kiran da bappa zaidun ya masa sai shi kadaine bazauna ba ya wuce office dan ya samesa acan
bayan tafiyarsa ne wajen cin abinci sama sama jamal ya gaya musu halin da ibaad yake ciki na yadda zainab arifah take kkrin manipulating din family dan a aura matashi
prince hassan saida ya fi kowa jin baqin cikin labarin nan dan sosaine ya tsane zainab arifah like everything abt her is just gross to him, farhan yace dama shi ya dan fahimce komi sabida ibaad was not himself musmn a satin nan kuma yasha jin labarin yarinyar she is complete spoilt brat kuma tana da wata kawa tantiriyar yar kwaya.
dukansu sunji tausayin ibaad bana kadan ba gabaki daya mood din prince hassan saiya lalace gabaki daya harma baici abinci ba, suka yanke hukunci kawai cewa zasu jira ibaad din yadawo dan susan wani irin support ya kamata su masa a wann lokacin dan su saukaka masa radadi.
ibaad yana isa offishin bappa zaidu ya samesa yanakan meeting ,gashi yazo da crude oil file din daya saya masa share dan yasashi signing amma baisan ya zai yafara tunkarsa da mgnn ba. wancan karon ma amminsa ya saya share a dubai na clothing line but it wasnt hard for him ya mata wala wala to get her signature and thumprint cikin sauki yasan bappnsa kam bazai signing haka kawai ba
he had been building a quiet business for his mum a kasar waje amma bata sani ba cos he want to really surprise her with it one day.
duk dama wekdn ne still saida ya jira for 10 min kafin suka fito shi ya shiga..
bayan sun gaisa bappa zaidu yahau gaya masa cewa nan da wata daya ne daurin aurensa da zainab arifah snn ya fayyace masa batun gida, lafiya, ciyarwa, kudin sutura da kudin kashewa da kuma MD position da prof yace zaibasa kuma ga yadda suka saka maganan agaban hajya yanxu basu isa suce basaso ba dan haka kar yace komi kawai ya karba.
sann shi asali ba akan wnn maganan yakirashi ba, cos he just want to know, yace he had been wanting to ask him shin wani busines ne yakey, dan ya jima dayace masa yana business kuma yana ganinsa da cars da ababen duniya amma bai taba fayyace masa menene ba, he want to know now sabida kar aje a dorasa akan matsayin MD a kamfanin prof ya zamana iyakan madogaransa kenan na rayuwa, yace masa a matsayinsa na uba bazaifa yarda hakan ya faru ba, inde busines din dayakeyin bai tsaya ba yagaya masa kawai shizai iya sauka a wann kujerar tasa ya dora sa akai shi saiyay retire koma yaya ne dan kar azo ace prof ne ya dora sa akan arziki akarshe yazamo masa kayan gori snn yana da business partners in yanaso zaiyi amfani da sauran kudin gadonsa tunda yana da yawa sai yay investing kawai de shi bayaso ne ace ya zauna shiru prof yana masa komi.
ibaad yay shiru for a while, dan harga Allah yanaso ne dukiyarsa ya cigaba da zamowa anynomous kodan ya gama ganin kalar kowa, baisan ya nuna kansa a fili bare shima ya zama amfara worshiping dinsa a family kamar yadda ake ma prof dan sosai yaga illar hakan a ahalinsu, kusan wanda yake da abun duniya ne kawai irimsu ammi babba, anty safeera,hajiya mairo da irinsu uncle moh suka fi darajawa
..saidai tunda akayi case dinnan ya lura da asalin masu kaunarsa, bappa zaidu, da mahaifyarsa sai brothers dinsa MJ da maheer wanda tunda aka fara case dinnan basu taba juya masa baya ba ko sun nuna masa baida gata ba
sai yaga ma babu amfanin boye ma bappa zaidu komi nasa yanxu tunda har ya tambya, dan yasan mutumin nan yana sonsa tsakani da Allah snn yay masa yaqin da ko mahaifinsa ne ba lallaine ya masa irinsa ba. he tot abt it for a while kafin ya fara da neman alfarman cewa duk maganan da zai gaya ma bappa zaidun yanxu yana so ne su bari atsakaninsu ko mamansa baiyaso agaya mata, he will tell her how wealthy he is when he feel is ryt..
Da mamaki bappa zaidu yace masa toh zai masa alkwarin ne inde har abun bana cutarwa ko haramun bane.
ibaad ya ciro hadadden samsung dinsa da ga aljihunsa, yajona da printer na office din ya ciro 6 business front document ya tattara duka ya aje agaban bappa zaidu sann ya zauna yafara masa bayanin abubuwn dayake ciki, tundaga kan kamfanin Q4 sovereing grp, da su logistic, ga estates, da multinational investm firm dinsu, da private income streams insa na pharmaceuticals da wasu yan kananan tarkacen side busines
sai ya masa bayanin harda wann sabon dayau suka tattauna, snn yahau bawa bappa hakuri sosai nakin gaya makowa sirrinsa dayayi tsawon lkci, yace he just want to do sumting for himself by himself batare daya takura masa koya daura masa nauyin shige masa gaba ba....
tsabar kaduwa da mamaki da bappa zaidu yasha harsaida idonsa ya tara ruwan hawaye
he was soo amazed abun yafara masa kamar a mafarki dan baiyi tsammanin yawan shige da fice da tafiye tafiye da tarayyarsa dasu jamal wani abu babba haka suke ginawa ma kansu ba, he salut the pure power of strong connection da networking, dan kusan shine 70% magic power da yay boosting succes dinsu daya hadu da sudin mutane me masu bala'in jajircewa da saka kai they take any favourable oppurtunity that comes deir way babu bata lokaci nd they trust each other sosai.
bappa zaidu yana hawayen murna still yana masa fada yana cemasa i am proud of u at same time still yana cewa baka kyauta min ba..har ya kusa yasa ibaad din dariya
yace "yanzu dama kana da rufin asirin ka zauna anata maka wannan wakalancin ai danasan hakane da wallah gori ma kadai sai ya ishesu kuma bazaka karbi komi nasa ba....
ibaad yana murmushi yace masa kar ya damu shi hakan ma yake so abar prof din yayi tunanin baida shi, sabida ya lura inhar kowa yasani labari zai iya canzawa, is eida shima afara bashi superior treatment sama da yan uwansa su MJ da maheer, ko kuma kawunsa prof din yay amfani da wani dama yafara jawosa kasa kmr yadda yake ma bappa zaidun makirci inyaga zai samu wani abu babba na cigaba sai yay maza yayi shige da fice yasa ayi cancel wasu contract dinsa aboye.
shikansa ibaad saida ya fara shiga duniyan business kafin jamal ya nuna masa wasu sirrikan prof da kuma irin makircin dayake ma bappa zaidu wata rana ma su suke budewa bappa zaidun hanya a sama batare da yasan waya taimake sa ba.
sosai bappa zaidu ya sha baqar mamaki akan haka snn ya gamsu da wannann bayanin nasa har ma yaji kamar cewa ibaad din ma yafisu wayo da dogon tunani, dan ya tabbata inhar akasan yana da wann daukakar babu shakka irinsu hajy mairo zasu nemi su lalata alaqarsa da su maheer da su mujaheed tahanyar shigo musu da bangarenci da fifiko da nuna bambamci..
is true they have to cut the generational curse kar suma wann dabi'an bambamci da fifikon ya bi generarion dinsu nd he is very proud cewa ibaad ya riga ya dau hanyar katse wann mummunan dabiar akansa da yan uwansa.
ranar murnan da bappa zaidu yay ya jima baiyi irinsa ba yasaka ma ibaad albarka yafi sau saba'in musmn daya ga share daya siya masa harda na amminsa duk ya gaya masa, bappa ya masa nasiha ya masa wa'azi,ya masa jan kunne, ya masa godiyaz kai babu abunda bai gaya masa akan ya cigaba da rike sirrin kansa ba. dan ma kar ya aje ppers din wani ya gani by mistake atake ya konasu a incinerator snn yasa masa albarka akan wanda zai fara ynxu.
yasha matukar mamaki dayaji cewa maheer ma yasan komi amma bai gaya masa ba, but he is atill proud of them, ya lura cewa kamar da alama generation dinsu sunfi hadin kai ko sune ma hala zasu kawo sauyi maikyau ma zuriarsu oho.
hirar abubuwa sukayi for like two hours suna magana akan prof, bappa zaidu ya gaya masa salo salo na yadda zai yi wasu abubuwan, da inda zai saka kafarsa da inda bazai saka ba, da irin risk din daya kamata ya guje duk ya kara masa ilimi...
yadda bappa zaidu ya kara masa kwarin giwa koshi aransa he wasnt expecting to get soo motivated nd happy da irin alfahari da kuma yabonsa da bappa zaidu yayi yanxu.
they agree to keep it secret nd just go with the flow, bappa zaidu yace ma ibaad yanxu kam hanklinsa shima ya kwanta tunda yasan goben ibaad din mai kyauce kuma yana da rufin asiri, koda kuwa ya auri zainab yanzu kambaida wani fargaba akan duk wani tsiya da shashancin mhaifinta saboda yasan yafi karfinsu.
ibaad bai bar offishin ba saida suka gama duk wata magana da zasuyi suka fahimce juna sosai ya karbi share yay signing dinsa a takardan,snn ya ma bappan nasa sallama yaje gida yay wanka da azhar ya dawo gidan lady diana ya same abokansa sukaci abinci atare aka tattauna, duk suka bashi hakuri akan abunda ke faruwa dashi, snn suka ce masa komi zaizo ya wuce tunda dai iyayen nasa basuce masa bazai aure wacce yakeso anan gaba ba. they are just hoping it will be soon, sabida duk sunce bazasu zo daurin aurensa da zainab ba amma idan akazo nashi da ayaanah they will personally sponsor the weding on deir own koda anyi kuwa saisun kara yin nasu hidiman special.
kamar da wasa suka yi hirar akayi dariya bai daukesu serious ba baisan kuwa har sun tattauna da lady diana akan hakan ba shide yasan prince ya dau abun har ransa yace ma ibaad sam sama kar ya sake zainab tau wata biyu a gidansa bai mata kishiya ba dan shi ko gidansa bazaije ba inbabu ayaanah aciki.
they spend quality time da abokansa agidan su jamal har yamma suka raka farhan airpot ya wuce gida dan ba'a nigeria yake zama ba shi. su ukun sunje buga snooker kenan a wani joint wayarsa ya fara kara yaga amminshi ne
gabansa sosai ya fadi duk ya dauka bappa zaidu got so excited ya gaya mata wani abu, yana daukawa kuwa yaji muryanta wani iri yace mata mata meya faru? nan tace masa ai ayaana ce babu lafiya jikinta yay dumi kuma safiya tace wai tay amai, tace suje asbiti kuma tace a'a wai saishone takeso yazo ya dubata agida.
yanajin hakan yau murmushi dan yasan mutumiyar tasa tay missing dinsa ne ta sauko takeson ganinsa.....
#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata
*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*
*WATTAPAD @SURAYYAHMS*
*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED*
#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025