Part 1
by @chefmuaysh
BADAƘALA ✍️
NA A'ISHA HAMZA
2025
Bismillah
Wannan littafi Mai suna BADAƘALA na rubuta sane domin fadakarwa da abubuwa masu tarin yawa akwai soyayya akwai tausayi akwai badakalar kuma kamar yanda sunan littafin yake kai wani abun har ma da ban haushi inshaa Allah kuma zakuji daɗin sa kudai kawai ku biyoni a cikin wannan littafi sai daku 🤟
Sai daku masoyana
💜☘️💜☘️💜☘️
✍️ A'isha Hamza (CHEF MUAYSH)
Kwance take saman gadon ƙarfen da katifar sa gaba ɗaya a shamile take saboda lalacewar da tayi tunda tadawo daga talla ta kwanta ko sallar maghrib bata samu tayi ba saboda gajiya
Wata tsohuwa ce zaune saman abin sallah da fitilar kwai a gefenta wadda ita ce ta haskaka dakin da suke a ciki addu'o'i takeyi bayan ta idar da sallah tadau kusan minti ashirin kafin ta shafa su
Saida ta kammala ta mike ta nufi inda yarinyar nan take kwance dan bubbuga bayanta takeyi a hankali tana kiran sunanta
Ayrah ayrah ki tashi mana kiyi sallah ga abinci nan barira ta kawoman kici kinsan dai yanzu inno zata aiko kiranki ko dare yayi zaki kai tuwo dandali
Taɓe baki tayi ta tashi zaune tasa hannu biyu tana murza idanunta da sukayi mata nauyi saboda baccin da takeji
Ƙafafuwan ta tafara zirowa ƙasa kafin tayi mika tana faɗin kai Gwaggo wai anyi sallah ashe baki tasheni ba tun ɗazu
Tsohuwar da aka kira da gwaggo ta nufi wani kwano tana ƙoƙarin buɗe sa da alamu abincin da aka kawo mata ɗin ne tace to ai yanzu tunda na tasheki saiki maida hankali ko naga kingaji ne da yawa shiyasa ban tasheki ba amma ke sai kinyi man tsogumin da kika iya
Butar da take cikin dakin ta nufa tana zuba ruwa tace to yi hakuri gwaggo bari inyi sallar menene barira ta kawo maki ne
Gwaggo tace idon matanbayi ne Ayrah karki maida hankali kinji tafada tana aika mata harara
Sumsum ta ɗauki butar ta fice tana yar dariya ƙasa ƙasa ta nufi banɗaki tafito tayi alwala tadawo ta tayarda sallah
A guje ta shigo gidan ko sallama babu tana kiran Ayrah ayrah inno tace yau ko ita zata fitar da tuwon dandali ne bazakije ba
Gwaggo ce ta tari numfashin ta tana faɗin to yar iya ko sallama babu ja'ira kika fado min daki
Gatsine tayi tana wurwurga idanu to ai inno ta aikoni in kira mata Ayrah zata kai tuwo dandali
To gatanan jarababbiya sallah take yanzu zata taho gwaggo ta faɗa tana neman karan da zata zunguro ta dashi
ƙara murguda baki tayi kafin tayi waje tana gunguni gwaggo tace Allah yasa dai ba zagina kikeyi ba marar kunya kawai
Tunda taji an aiko nemanta hankalin ta ya rabu gida biyu ga yunwa tanaji gashi tana gudun masifar inno
Sauri ta mike dama hijab ɗin tace a jikinta data idar da sallah waje tayo tana ƙoƙarin saka sidaddun takalman ta da suka gama shan wahalar duniya
Gwaggo tace haba Ayrah badai tafiya zakiyi bakici komai ba ina lura dake fa duk yau babu abinda kika saka a cikin ki
Bata tsaya ba tayi waje tana bata amsa gwaggo zandawo ki ajiye man banaso inno tamin faɗa
Ganin ta tafi yasa gwaggo mikewa ta dauko wata robar ta dibar mata ita kuma ta cigaba da cin nata
Sauri sauri gudu gudu ta shiga gidan nasu duk mutanen gidan suna zazzaune a tsakar gida ga botikin tuwo da kuma na miya nan kusa da inno sun zuba wani a farantai suna ci itada yaranta guda biyu zainaba wadda taje kiran Ayrah sai kuma Ameerah ƙarama ce bazata wuce (6 year's) ba shekara shida
Sai Halima tana gefen dakinta itama da nata yaran guda biyu itama ɗaya zata kai sa'ar Ameerah sai kuma ƙaramar bata wuce shekara biyu babbar itace Hindu sai qaramar kuma hauwa
Har ƙasa ta duka tace umma halima barka da dare Barka dai Ayrah kina lafiya ko lafiya kalau ta amsa kanta na ƙasa kafin ta mike ta ƙarasa kofar dakin inno inda suke zaune suna cin tuwon
Barka da dare inno Ayrah ta faɗa tana ƙoƙarin jan bokitin tuwo dana miyar ko kallo bata isheta ba saida Ayrah tagama haɗa kayan tuwon zata ɗauka kafin tace wallahi idan akayi min ɓata irin na jiya sai na lahira yafiki jin dadi
Buɗe baki Ayrah tayi zatayi magana inno taqara katseta da faɗin to uwar yan gardama me zakice ko ƙarya namiki jiya baki satar min kuɗi na ba ko kuma ƙarshe ma kika bawa ƙattin banzan da kike tare dasu tuwona
Shuru tayi ta kama hanya zata fita tana musu sallama saita dawo Halima tace to Ayrah adawo lafiya ki kula da kanki Allah ya tsare
Inno ta watsa wa Halima harara tare da taɓe baki tana faɗin yenyenyen uwar gulma munafuka kawai tana watsa mata harara
Halima dai ko ci kanki bata ce mata ba taja yaranta suka shige daki gudun kar zaman yasa Inno ta ci-gaba da aika mata da maganganu don suyi faɗa
Bata wani sha wahala ba yau a dandalin yan mata da samari sai rakashewar su sukeyi wasu na fira anata siye siyen abubuwa ana ci
Duk yanda Alolo yaso ta bashi dama suyi fira Ayrah tayi kicin kicin ta haɗe rai dole ya hakura dukdan ya burgeta Saida ya siya tuwo shida abokanan sa
Kafin Akira isha'i ta haɗa kayanta domin ta siyar da tuwon saidai cikinta da yake ta yimata wani ƙurƙurr saboda azabar yunwar da take ji
Bata ɓata lokaci ba tayi gida tun a kofar gidan tafara jin hayaniyar su ta tabbata fitinar gidan ce ta taso Saida tayi addu'a a zuciyarta domin gudun kada abin ya shafeta kafin ta shiga gidan
Wallahi malam bazai taɓa yiwuwa ba nagaji nagaji wannan ai masifa ce ka kawo mana cikin gida nagaya maka Halima ce take daurewa yarinyar nan…… har take abinda taga dama
Inno ce keta faman zazzaga bala'i halima na tsaye kofar dakinta ta rike qugu da alama dambe suka gama sha inno kuma ta daku don Halima irin matan nan ne karfafa bata cika biyewa inno ba saboda tanada hakuri amma yau Saida ta kaita ƙarshe harta mata duka
Malam ne yace haba halima wannan ai iskanci ne uwar ƴaƴan nawa zaki daka saboda ke baki da ta ido ko
Halima tace to malam aini naga ba matanka bace ba ko kuma baxaka tsaya kaji abinda yafaru ba zaka fara yanke mana hukunci duk hakuri na cikin gidan nan amma kai baka gani tana kai karshen maganar ta shige daki don zuciyar ta a kusa take zata iya yin abinda za'a yi dana sani baki ɗaya
Inno ta ci-gaba ai dama nasani malam kaima ta rainaka bare kuma ni na lura tsoron Halima kakeji malam to wallahi yau saidai ka zaba koni ko Halima
Malam yayi tsuru tsuru don indai Inno tafara masifarta bayanda ya iya da'ita saidai ya lallaba yanzu ma hakan ce ta faru har kuɗi Saida yabata dukdan ya shawo kanta
Saida taji gidan yadan lafa kafin tasamu damar zura ƙafafuwan ta cikinsa da sallama a bakinta
Malam ne ya amsa fuskarsa babu yabo ba fallasa har ƙasa ta gaishe sa Baba Barka da dare
Barka kawai yace mata ko kallo bata isheshi ba itama ɗin bata damu ba don tasan saboda yana tare da inno ne
Kuɗin ta miƙa mata saida ta tsaya ta ƙirga kafin ta dago ta dubeta tana yarfa kuɗin tace ai ni tuwon dubu biyu da dari uku na sanya maki kika kawoman dubu biyar
Zaro ido Ayrah tayi tanajin sharrin da Inno take neman lika mata tace ɗazu da rana ɓata tayo mata yanzu kuma ƙari
Ta cigaba da faɗin kagani ko malam abinda nake gaya maka akan yarinyar nan bakajiko, na gaya maka maza take bi yanzu waya bata kuɗi har haka
Mallam kuwa kamar shima jira yake ya fisgo Ayrah yana faɗin zonan ja'ira waya baki kuɗi so kike ki janyo man masifa a gari ana ganin mutunci na koh
Ƙara ta saki jin wata azaba da kunnen ta keyi da malam ya rike shi gam kamar zai fisge mata shi
Inno ta mike tana
faɗin a haka zata faɗa maka inda tasamu ne malam icce ta dauko ta mika masa aikuwa yafara zuba mata shi saman baya
KADA KU BARI ABAKU LABARIN LITTAFIN NAN DAN YANZU AKA FARA
***