FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Part 1
BADAƘALA ✍️NA A'ISHA HAMZA2025Bismillah Wannan littafi Mai suna BADAƘALA na rubuta sane domin fadakarwa da abubuwa masu tarin yawa akwai soyayya akwai tausayi akwai badakalar kuma kamar yanda sunan littafin yake kai wani abun har ma da ban haushi inshaa Allah kuma zakuji daɗin sa kudai kawai ku biyoni a cikin wannan littafi sai daku 🤟Sai daku masoyana💜☘️💜☘️💜☘️✍️ A'isha Hamza (CHEF MUAYSH)Kwance take saman gadon ƙarfen da katifar sa gaba ɗaya a shamile take saboda lalacewar da tayi tunda tadawo daga talla ta kwanta ko sallar maghrib bata samu tayi ba saboda gajiya Wata tsohuwa ce zaune saman abin sallah da fitilar kwai a gefenta wadda ita ce ta haskaka dakin da suke a ciki addu'o'i takeyi bayan ta idar da sallah tadau kusan minti ashirin kafin ta shafa su Saida ta kammala ta mike ta nufi inda yarinyar nan take kwance dan bubbuga bayanta takeyi a hankali tana kiran sunanta Ayrah ayrah ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.